Sashe 35
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina ta fita Khairat ta kamo hannun Juhainah tana faɗin.
"Juhainah! Ki tashi kiyi breakfast ɗin"
Juhainah ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta tana kallon Khairat ta shagwaɓe fuska cikin zazzaƙar muryata tace.
"Aunty Khairat wanka zanyi jikina ciwo yake sosai"
Khairat ta kamata ta miƙe zaune tace.
"Ok bari na haɗa maki ruwan ɗumi"
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa ta nufi bathroom ɗin.
Ruwan mai ɗumi ta haɗa mata ta dawo ta kama hannunta ta rakata har ƙofar bathroom.
Can downstairs yaran zaune parlour sun gama breakfast, an shiga sana'ar ta Game, amma Suhaima tana gefe zaune tana danna wayanta.
A nuste ya shigo parlour yana amsa waya cikin harshen Ingilishi da ya kama bakinsa, sai wani irin fitinannan ƙamshi yake tashi a jikinsa.
Cikin shigar mai ƙayatarwa, fararen kyawawan kayane ajikinsa, wanda suka amsa sunansu kaya, Ni Ban ma san wannan kayan wata ƙasa bane, amma fa sun kama shi sosai ba'a maganar kyau, da kwarjini, takunsa kawai ya ishe ka kallo, sai wani irin fitinannan ƙamshi yake.
Al'amin ya miƙe da gudu ya nufi mahaifinsa cikin farin ciki yana faɗin.
"Oyoyo My Dadd I miss you tun Jiya da safe ban ganka ba, kana Jigawa"
Yah Boss ya ware masa hannayensa ya faɗa jikinsa ya ɗaga shi sama yana sumbatar shi.
Suhaima ma tazo ta rungumeshi tana zuba shagwaɓa.
Itama ɗaga sama yayi ya rungumeta yana sumbatar kumatunta a hankali ya furta.
"I love you My Babies Miss you too, ina Auntie's Ɗinku?"
Suhaima ta shagwaɓe jikin Yah Boss kamar zata yi kuka tace.
"My Dadd Auntie J batada lafiya jiya muna bacci ashe har cikin dare doctor tazo ta mata magani, da allura harda drip aka saka mata, yanzu ko breakfast batayi ba, ɗazu Amina ta kai mata breakfast bataci ba, Please My Dadd kaje ka bata taci ka bata magani Ni bana son tana ciwo duk sai inji babu daɗi kamar nice nakeyi"
Ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka duk ta damu.
Yah Boss ya sumbaci goshinta a hankali ya furta.
"Babie Suhaima kinyi breakfast kuwa?"
Kai ta ɗaga masa tace.
"Amma Auntie J bataci komai ba"
A hankali ya sauketa yana faɗin.
"Ok naji yanzu taci Ok? My Amiin sauka naje na ba Auntynku abinci"
Al'amin cikin farin ciki yace.
"Yeee i love you My Dadd"
Shamsiddin da Shuraim suka zo suka rungumeshi suna faɗin.
"Good morning my Dadd"
Ɗaukansu yayi yana faɗin.
"Morning my Twins yau an kwana gidan Dadd, toh ku sauka ku zauna zan fito yanzu"
Ajiye su yayi suka ragu da gudu gun Suhaima suna mata magana.
A nuste ya nufi Stairs ɗin.
Juhainah zaune akan Stoll tana tsane dogon gashinta da yajiƙe gun wanka, sanye take da Abaya Brown, fuskarta ta ƙara wani irin haske kamar tayi sati batada lafiya.
Khairat tana zaune gefen Bed tace.
"Don Allah Juhainah kizo kiyi breakfast kisha maganin nan lokacinsa zai wuce kalla fa goma sauran minti ashirin."
Baki ta turo gaba tana shagwaɓe fuska tace.
"Ni Wlh bana son cin komai yau komai ya fita a raina. Ni Ki kira min Yah Boss please"
Khairat tace.
"Bazan kira ba mi zai miki? Kawai ɗaukan hankali"
Shagwaɓe fuska tayi tana miƙewa tsaye tazo ta zauna ƙasa gefen gadon tana hawaye tace.
"Ni dai ki kira min yayana Sadeeq ki bani akwai abinda zan faɗa masa ya kawo min"
Ƙaran taɓa Ƙofar parlour sukaji.
Khairat tace.
"Ok kici abinci sai na kirasa kinga Amina har ta dawo kwashe kayan"
Baki ta turo tace.
"Toh banaci idan bazaki kirasa ba"
Ƙofar bedroom ɗin aka ƙwanƙwasa ba tare da anyi magana ba.
Khairat tace.
"Amina ki koma bataci abincin ba..."
Juhainah ta miƙe tana faɗin.
"Amina! Please ki tsaya"
Ta ƙarasa maganar tana nufar ƙofar.
Handle ta kama tana murɗawa a hankali kamar zata yi kuka tace.
"Amina Please ki aramin wayanki zan kira yayana commissioner..."
Ido huɗu suka yi da Yah Boss, fuskarsa a kame, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa.
Kasancewar batada wani ƙarfi a jikinta, kallonsa da tai sai ya ya ƙarasa nakasa sauran ƙarfin nata, sai tsayuwar ta gagareta, tai saurin duƙowa ta zauna ƙasa, da wata irin kalar shagwaɓa tace.
"My brother ina kwana?"
Ta faɗa idanunta lumshe.
Bai amsa ba baice mata ƙala ba, idanunsa akanta ranƙwafowa yayi ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye yajata suka nufi parlour.
Ƙaramin kukan shagwaɓa ta sakar masa tana binsa, a hankali tace.
"Yaya Sadeeq wlh ba kowa zan kira ba kayi haƙuri kaine nake so na kira, Aunty Khairat nace ta kiramin kai tace bata kira, nazaci Amina ce nace taban aron waya na kira ka Allah da gaske nake"
A hankali cikin zazzaƙar muryansa a kame ya furta.
"Idan kin kirani me zan zaki faɗa min?"
Kai tsaye a shagwaɓe tace.
"Ce maka zanyi nakasa cin komai Banida lafiya, kawai inason ko faɗa kamin kace naci abincin dole zanci..."
Da sauri ya kalleta yana kamo kunnenta yaja kaɗan, yana zaunar da ita yana faɗin.
"Saboda Ni sa'anki ne? Ko ina shaga shirmen ki?"
Kasa kallonsa tai a hankali tace.
"A'a kayi haƙuri Ni dai kace naci abincin sai naci Banida lafiya Yaya jiya kamar zan mutu"
Kansan ya kauda yana murmusawa, ya nufi bedroom ɗin.
Da Khairat suka haɗu bakin ƙofar.
Rusunawa tai tana gaishesa, gabanta na faɗuwa kar ya tasa mata hira ta Daki Juhainah.
Amsawa yayi anutse a hankali ya furta.
"Koma ki kawo kayan breakfast ɗin"
Cike da ladabi ta amsa da Toh tana komawa shi kuma ya koma parlour.
Juhainah kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta kamar wata ta kirki wai ta nutsu nan.
Kallonta yayi a hankali ya furta.
"Ke Juhainah!"
Ɗago kanta tayi dogon gashinta yana bajewa wasu tsirarun suka rufe gefen idanunta.
A hankali ta kallesa tana narkewa saman Sofa tace.
"Yaya Sadeeq don Allah kayi haƙuri Wlh banyi komai ba, yunwa nakeji"
Ta ƙarasa maganar tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta saboda bata jure kallonsa azaba ake mata a kwanyarta.
Khairat ta fito da tray'n ta dire gaban Juhainah tana haɗa mata tea mai kauri ta beƙa mata taƙi amsa Yah Boss a hankali ya furta.
"Ke!"
Ai da sauri ta amshi Cup glass mai kyau, tana kai wa bakinta a hankali...
Da sauri ya ƙaraso yana ranƙwafowa ya sanya tattausan hannunsa akan Cup ya amshe daga hannunta yana faɗin.
"Bakida hankali Sam, bakiji akwai zafi ba"
Ai kuwa baki ta saki tana kallonsa cikin yanayin da bata ma san tana yi ba, sai kawai ta tsinci kanta da murmusawa tana ɗora hannunta akan nasa mai Cup kawai takai bakinta ita so ma take ta ƙone ɗin.
Hannunta ya buge yana daka mata tsawar da ba ita ba Khairat ma ta tsorota, sai da ta zabura.
Ai kuwa take ta dawo hayyacinta tana ƙamƙame Cushion ɗin Sofa tana rufe idanunta, sai hawaye masu zafin da bata san na meye ba.
Tsaki yaja yana kai Cup ɗin bakinsa ya kurɓi tea ɗin.
Khairat ta saki baki da hanci tana kallon Yah Boss, sai da ya kurɓa sau uku ya matso kusanta ya kamo hannunta ya saka mata Cup ɗin, cikin bada umarni ya furta.
"Buɗe idanunki kisha"
A hankali ta buɗe idanun tai saurin kai Cup bakinta dai-dai gun da ya kafa bakinsa, dan bata ma san yasha ɗin ba.
Sofa da take face ɗin wadda Juhainah take ya zauna, cikin kamewarsa murya a hankali ya furta.
"Zuba mata abincin"
Khairat ta zuba dankalin turwa a soye da wainar ƙwai.
Juhainah ta shanye tea ɗin ta amshi plate ɗin ta fara Turawa cikinta dankalin turwan da wainar ƙwan sosai taji suya ta mata daɗi, harda gyara zamanta take yi tana lodawa cikinta.
Tana cin rabin wanda Khairat ta zuba mata ya furta.
"Ke! Ya isa haka bata plate"
Dole Juhainah ta dakata! Ta beƙawa Khairat plate ɗin tana lashe jajayen laɓɓanta masu kauri.
A hankali ya furta.
"Ina maganin nata?"
Khairat ta ɗauki ledar tana faɗin.
"Gasu nan"
"Ok ɓallo ki bata"
Juhainah kamar zata fashe da kuka Sai motsi² take yi bata ƙaunar magani ba yadda zatayi ne.
Khairat ta ɓallo kowanne ta bata ta beƙa mata bottle ɗin water ta zubasu can tsakar bakinta ta kora da ruwa.
Miƙewa yayi yana takunsa anutse ya nufi ƙofa, a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Khairat! Kwashe kayan breakfast ɗin ku sauka dasu, zata ƙara ne tunda bata san ciwon kanta ba"
Khairat ta amsa da toh ta miƙe.
Juhainah dai kwanciya tayi tana rungume Cushion, ko minti goma batayi ba sai bacci....
Yana fitowa ya sauka yana kiran Fu'adh wanda yaje gidansu ya dawo.
★
Raudah
Tsaye take cikin shiri taci ubansu ɗamara da jeans da wata shegiyar riga tana tauna Chigum, tsaye take ƙiƙam alamar ba mutunci.
Wani babban mutum ne baƙi zai yi shekaru 61 a zaune da gajeren wando, yana busa sigari, kallonta kawai yake yana murmushi.
Tsakanin ƙafafunsa ta dawo tana warce sigarin tana kaita bakinta ta zuƙa tana faɗin.
"Alhaji Nuhu magana nake maka fa, nace maka aikin nan a nemi wani, saboda Wlh sai na tarwatsa rayuwar Juhainah hankalina zai kwanta, dan haka tunda gaggawa kake ka samo wata"
Fizgota yayi ta faɗo jikinsa yana matseta ya shafi ɗuwawunta yana murmushi yace.
"Raudah! Ba'a saɓamin alƙawari, kinyi alƙawarin temaka min naga bayan Abubakar Yakubu Abubakar Janfar sai kawai da rana tsaka kice kin fasa? Ina No sam, dole zakici gaba ni zan taimaka ki ciki burinki akan yarinya ba shi kenan ba"
Ƙirjinsa takai wa duka tace.
"Ai aikin gama ya gama ka manta na fito daga gidan? Yanzu ta ya zan iya komawa gidan kenan? Ni kaina sai yanzu naga nayi gaggawa da cikin gidan nasu zanci uwarta sai zafin zuciyata ya fito dani da wutar ɗaukan fansa da take cin zuciyata."
Bakinta ya kaiwa cafka saida yasha mai isarsa ya saki yana shafa mazauninta yace.
"Zo in miki raɗa a kunne yadda za'a ayi Wallahi zaki ɗauki fansa cikin ruwan sanyi nima ki cika min burina na kauda tsinannan can, amma fa yanzu aiki ya dawo baya, sai munyi haƙuri"
Kunnenta ta beƙa ya mata raɗa suka bushe da dariya suna tafa hannayensu.....