← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 113

Sashe 54

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya koma gunsa ya zauna yana ƙoƙarin katse kiran Jamal yay picking call ɗin tare da sallama yana faɗin.
"Afuwan my brother na shigo gosulo ne shiyasa ban ɗaga ba"

Yah Boss anutse cikin kamewarsa ya furta.
"it's okay, Jamal! Ga ta nan."

Ya ƙarasa maganar yana kame fuska sosai ya kalleta babu wasa yana beƙa mata wayar.
Cike da tsoron yanayin da tagani akan kyakkyawar fuskarsa, jikinta yana rawa ta amshi wayan, tana kaita kunnenta.
A hankali tayi sallama tana faɗin.
"Yaya Jamal ina wuni?"

Jamal ya amsa da.
"Lafiya lau ya kike?"

A hankali ta amsa.
"Am fine"
Ta ƙarasa maganar tana kallon Yah Boss, wanda fuskarsa take akame yana danna System, ya maida hankalinsa ga baƙi ɗaya akan system ɗin.

Jamal
A hankali ya furta.
"Juhainah! Kiyi haƙuri da abinda na miki ranan, ni wajena banga wani laifi ba, amma Mamy taga laifi ne, toh kuyi haƙuri kinji?"

Junainah ranta ya ɓaci amma ganin yanda Yah Boss kame fuskarsa tayi sanyi a hankali tace.
"Alright ya wuce just bana son dizgi a rayuwata, na yafe but karka sake because idan ka sake ba zan yafe ba, kuma sai na faɗawa Mamy."

Jamal ya taɓe baki a hankali ya furta.
"Thank you bazan sake ba ma, tunda Mamy na sonki, damuwar shi ne bana sonki"

Juhainah hawaye suke ƙoƙarin cika mata idanunta, tai saurin shanye su, tayi murmushi a hankali tace.
"Nagode sosai Sweetheart Jamal Ok Bye sai zuwa daren ina jiranka sai anjima"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran tana yaƙi da zuciyarta da take wani irin zafi, sai tayi ƙoƙarin ɓoyewa.
Jamal kuwa yasha mamakin kalaman nata amma tuna tana gun yayanta zatayi fin hakan ma.

Yah Boss sai da ta gama wayar ya ɗago ya kalleta, a hankali ya furta.
"Ni kika raina wa hankali babu wanda ya miki baraza munafuka"
Kamar zata fasa ihu cike da shagwaɓa a hankali tace.
"I love you My brother Habiby please ka yafe mani ina son nay..."
Kallon da ya mata ne ya saka ta miƙe da gudu ta kwasa ta shige room ɗin ta kunna Ac tayi kwanciyarta saman Sofa tana rufa da Duvet ɗin da take ƙamshin Yah Boss....

Bai sake bi ta kanta ba, yana aikin gabansa, sai bayan da ya dawo daga masallaci yasha Madaran da Walid ya kawo masa, har lokacin da zafinta.
Fu'adh ya turawa number Zuby akan yana son aikin ya zama sirri baya son ya shafi police station ɗinsu,har ya tabbatar da ƙudirinta akan Juhainah, zata gane bata da wayo...



Su Ruwaida sunata jiran Aunty Sumy har mazajansu suka zo suka tafi dasu, amma sai kusan la'asar suka zo.
Zarah amarya kuwa hankalinta kwance.

Yau bayan la'asar Khairat ta sauko, nan suka baje da Surayya suna hirasu.
Ƙarfe shida su Suhaima suka sauko daga school, kasancewar har islamiyyar haɗe suke.
Wanka Suhaima tayi ta sauko parlour, yanayin da Al'amin yake can yana wasansa babu abinda ya masa zafi.
Suhaima tana zama kusan Khairat tana kallon Surayya tace.
"Aunty Surry! Ina Aunty J ɗina?"
Surayya tana ƴar dariya tana kallon Maah tace.
"Maah na faɗa mata ?"
Maah zatayi magana Sallamar Hajjah Mama ta karɗe parlour.
Al'amin ya miƙe yana sakin kayan wasan ya rugu da gudu yana faɗin.
"Oyoyo Hajjah Mama"

Maah ta amsa Sallamar tana faɗin.
"Barka da zuwa Hajiya Bilkisu sannunku ya gajiya?"

Hajjah Mama ta ɗauki Al'amin tana faɗin.
"A yau wannan aure ba sai an sake ɗaurawa ba, yawwa Zainab mun sameku lafiya?"
Khairat da Surayya suka mata sannu da zuwa.
Ta zauna Al'amin ajikinta tana amsawa tace.
"Khairat! Ya karatu? Surayya ko? Ina ƙawar taki Namesake?"
Tace.
"Ta ɗan fita"
Khairat ta miƙe zuwa kawo mata ruwa.
Suhaima ta haɗe gira sama da ta ƙasa ko kallon Hajjah Mama bata yi ba.

Hajjah Mama ta kalli Suhaima tana faɗin.
"Zainab! Ni kike fushi dani saboda na saka ubanki yayi aure? Haba Zainabu miye laifi na?"
Suhaima ta miƙe tana faɗin.

"Au bakida laifi ashe Hajjah Mama?
Toh shi kenan, nan gaba kaɗan ita amaryar zataga laifinki, saboda na tsaneta bana sonta, zaku ga me zanyi"

Ya ƙarasa maganar tana tafiyarta sak irin ta Nasir idan ransa ya ɓaci.

Hajjah Mama ta rabka salati tana tafa hannayenta tace.
"Na shiga uku! Ni Bilkisu, ashe haka nabar baya da ƙura? Zainab! Haka abu ya lalace? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"

Maah tace.
"Haba Aunty Bilkisu Suhaima zaki biya, ai tunda Abbah ya amince ya aureta akwai wata magana ne? Kiyi haƙuri yarinta ne jikarki ce fa gaba da baya daga ni har Harɗo waye ba naki ba? wasa take miki"

Surayya dariya take son yi ganin yadda idanun Hajjah Mama suka firfito, abu ma sha Allahu.
Ai miƙewa tai ta haye Stairs.
Hajjah Mama tace.
"Shi kenan Zainab Allah ya kyauta jikina har yayi sanyi, Wlh ni tausayi suke bani shi yasa na saka shi auren nan, kuma naga Zarah mutuniyar kirki ce"

Maah tayi dariyar zuci tana faɗin.
"Ai bakiga komai ba, gobe kya ƙara aura wa mutum irin Abbah macen da baya so"

Amma a zahiri Maah tace.
"Ai haka shi ne dai-dai tunda idan an biya ta ta shi bazai auren ba..."
Hajjah Mama tana raba idanu tace.
"Toh kin gani Zainab don Allah akwai laifi anan? Amma Zainabu ƙarama ta ɗauki zafi dani sbd Allah, ko ba san ni yayar Yakubu nake uwa ɗaya uba ɗaya ba, ke kuma da mahaifinki da namu mahaifin Abubakar Janfar da Adamu Janfar uwa ɗaya uba ɗaya bane? Take son ta nuna min ni ba kowa bace a dangin?"

Maah dai dariya zuci take tana faɗin Allah ya ƙara, zahiri tana kwantar mata da hankali tace.
"Aunty Bilkisu Suhaima yarinya ce bazata gane ƙarfin dangantakar ba, amma ko daga kamarki da ita ai tasan jini ɗaya ake"

Hajjah Mama dai tagumi tayi tana mita.


A can kuma police station ganin Maghreb ya kawo jiki ya sanar da Walid yana son tafiya gida.
Aka shirya mota.
Tunda suka shiga Mota Juhainah ta maƙale jikin kujerar da take zaune, ganin Boss ya kame fuska sosai.
Yayi hakan ne dan kar ta sako masa wani zancen shirmenta kuma a cikin motar, bare ciwon zancen ita irinsa take so, idan baiyi da gaske ba, zata sa shi a uku ne.

Kai tsaye 80 Unit suka nufa.

Can ko gidan Daga Zarah sai Azizah da Yaganah da Ramlah babbar ƙawa sai Inna Laure.
Zarah suna bedroom su duka suna fira.

Tunda motar tayi parking Juhainah taji ranta ya ɓaci Sosai.
Yah Boss ana buɗe masa ya fito a nuste, fuska kame, cikin nutsuwarsa yake tafiya, cike da izza.

Juhainah ta fito da sauri ganin har ya fara nisa.
Da ɗan gudunta ta biyosa.
Kusansa ta tsaya tana maida numfashi.

Bai ce mata uffan ba, haka suka jera ciki.
Bai tsaya ɓatawa kansa lokaci ba, dan baya son ganin kowa daga cikin dangin Zarah.
Keys ya ciro a jikinsa ya buɗe ƙofar parlour.
Ya shigo.

Juhainah ta tsaye tana rau-rau da dara-daran kyawawan idanunta.
Kallon yayi a hankali ya furta.
"Idan ba zaki shigo ba je maza Walid ya kai ki gidan su Maah, bana son damuwa"

Da sauri ta shigo ta kamo hannunsa ta riƙe tana silalo hawaye akan fuskarta.

Tsaki Yaja yana zare keys ɗinsa ya rufe ƙofar yana jan hannunta suka nufi parlour.

Ko ina ƙamshi yake tashi acikin ƙaton parlour, anutse yayi sallama.
Parlour ba kowa amma ana jiyo maganar mata.
Juhainah ta kalli hanyar ɓangaren da take juyo surutun.
A hankali tace.
"Yah Sadeeq amaryar ce da mutanen ta, sun cika mu da surutu? Yaushe suka zo ne? Harda hajjah Mama hummmm!"

A hankali ya furta.
"Ban sani ba nima, kije ki duba"

Sakin hannunsa tai ta nufi hanyar parlour na Zarah.
Da kallo ya bita yana girgiza kansa ya nufi hanyar Stairs.

Zarah tayi ɗare² saman bed tana shan dariyar labarin da Ramlah take bata.
Parlour Juhainah ta shigo tana riƙe da ƙungunta, babu kowa ta nufi bedroom ɗin.
Handle ta murɗa ta sanya kanta babu sallama, tana kame fuskarta sosai.
Ga baki ɗaya suka juyo jin ƙaran ƙofar an shigo ba sallama.
Kallon mamaki suke mata.
Ɗaya bayan ɗaya Juhainah take kallon su fuska a haɗe.
Idanunta akan Zarah ta nunata tace.

"Kece amarya ko?"
Kallon kyawun Juhainah suke har ga Allah basu yi tunanin ta iya Hausa ba, saboda haduwarta, kamar kuma ruwa biyu Fulani Buzaye ko Larabawa.
Zarah ganin yarinyar bata kama da Yah Boss bare tayi tunanin ko ƙanwarsa ce.

Tace
"Eh nice ke wacece? Ai ko wacece ba'a haka ki shigo min har tsakar ɗakin aurena babu sallama, naga dai bakya kama da masu gidan bare nayi tunanin familles ɗinsu ne"

Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin.
"Yo ya za'ayi kiga kama bayan nima matar gidan ce.

Ni kishiyarki ce, kalleni yanada ni ƙarama ƴar shila son kowa tsakanin ki da Allah me zai ɓata lokaci kanki tun safe na riƙe abuna muna tare yanzu muka shigo...."

Zarah ta zaro idanunta tana dafe ƙirjinta cikin tashin hankali tace.
"Tun yaushe ya aureki? Ƙarya kike baida aure ki ce dai kina son mijina shine kika biyo ni har gida ke fitsarariya, anya ma ba ƙananun karuwan nan bane masu bin masu kuɗi suna yawo dasu ƙasashen Turai?"

Juhainah tace.
"Shi kenan ma kin gane yadda abun yake, amma ya akayi kika bari ƴar cikinki karuwa ta amshe miki miji?"

Ai kafin Zarah tace wani abun Yaganah da Ramlah sun sauke wa Juhainah mari sun kayar da ita suna ƙoƙarin dukanta.
Ko gezo batayi ba.
Su Kansu abun ya basu mamaki.

Inna Laure ta riƙesu tana faɗin.
"Ku bakuda hankali ne? Ku kalli yadda yarinyar take kamar sandar takanɗa idan kuka karyata mu shiga ina?"

Zarah ta sauko daga bed ɗin tana kamo hannun junainah tana dariya tace.
"Sandar takanɗa a ƙara gaba ni bazan daki sauran Turawa ba, nasan ƙarya kike mijina baya binki, kiyi gaggawar barin gidan kar ma ya iskeki gidan nan Wlh"

Ta ƙarasa maganar tana hankaɗota parlour ta rufe ƙofar bedroom ɗin.
Juhainah ta miƙe tana karkaɗe jikinta, dan ita fa babu wani zafin ciwon da taji a guje ta fice ta nufi Stairs.
Chapter 54 · 0% Book details