Sashe 72
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Waya ya fara a nuste cikin harshen Ingilishi, har suka iso gidan waya yake, daga bakin gate yace Walid ya tsaya kar ya shiga ya kalli Juhainah yana faɗin.
"Bilkisu! Shiga ki ɗauko abinda kike buƙata kizo mu wuce gidan Maah, har Khairat da Suhaima su fito"
Kallon sa tayi kalar tausayi zatayi magana ya furta.
"Sauka mana"
Kai ta ɗaga tana buɗe motar ta fice cikin sanyin jiki.
Surayya
Nasir yana parking a ƙofar gidan su, baiyi magana ba, yana jiran ta fice.
A hankali ta buɗe ƙofar tana riƙe da jakarta.
Sai da ta fito ta rufe masa ƙofar ta ƙwanƙwansa Glass ya ɗan janye kaɗan yana kame fuska.
Harara ta zabga masa tana faɗin.
"Wlh kana kallona kasan nafi ƙarfin fita yawon Banzan tunda Ni ba a gantale nake ba, kuma wlh Ni ba fitsarariya bace har zaka ce wai daman ya tafi dani ALLAH yafi mutum ah Toh..."
Ta ƙarasa maganar tana murguɗa masa bakinta ta sheƙa da gudu.
Nasir hankalinsa kwance ya yiwa motar key yayi Rivas yabar gun, yana murmushin mugunta, dan Wlh sai ya mata abinda zai saka mata mugun tsoronsa, dan gaba ko Ance tayiwa Nasir fitsara sai taji mugun tashin hankali.
Surayya bata fasa gudu ba sai da ta ganta farfajiyar gidansu ta tsaya tana maida numfashi. Harda zufa take, tana faɗin.
"Shi ji yake yaci bulus ne, tabbb ai Wlh bana barin bashin bak'ar magana"
Ta ƙarasa maganar tana nufar ciki.
Khairat Suhaima Al'amin suna zaune parlour, sukaji ana danna doorbell.
Suhaima ta miƙe tana faɗin.
"Ko su Aunty J ne bari naje"
Tana buɗe wa suka haɗa ido, Suhaima ta rungumeta tana faɗin.
"Aunty J ashe gun Dadd kika tafi? Ina Dadd ɗin?"
Juhainah ta zumɓuro baki gaba tana faɗin.
"Yana can bakin gate a cikin mota, duk ya tsaneni ma, sai hantarata yake, ALLAH fushi zan masa ma"
Suhaima tayi murmushi tana faɗin.
"Kai Aunty J ai ke da Dadd kunfi kusa ba ruwana"
Baki ta turo tace.
"Muje yana jiran mu gidan Maah zamu"
Surayya
Parlour ta shigo kamar an jefota tana sallama.
Mamy zaune suna hira dasu Farida.
Wata kyakkyawar yarinya fara mai jiki akwai gashi ba laifi na asalin Fulani, tanada manyan idanu, wanda ƙwayar su take irinta turawa sak, shekarunta tara amma zaka zata takai shekara 11 zuwa 12 Sbd yadda take da buɗaɗɗan jiki.
Tana gani Surayya ta nufi gunta da gudu tana faɗin.
"Lah hikenan ma ga antiya Suraiya"
Surayya tace.
"Ni bari ɓata min suna don Allah, Dijah yau she kuka zo? Ina Kawu Malam? Har yanzu bakya rabo da shan maji ko kina janta kamar kuturwa"
Dije ta faɗa jikin Surayya tana dariya tace.
"Alqur'an na fasa he jiƙojiƙo kuma inason nazauna a sakani makaranta bazan fasawa kowa kaiba he wanda ya higemin hanci da gudunduna"
Surayya ta gaishe da su Farida tana faɗin.
"Bari nayi wanka nazo"
Mamy tace.
"Wai faɗuwa kukayi a Keke napep ɗin nake ganin ƙasa a jikin ki?"
Surayya tace.
"Eh Mamy amma banji ciwo ba, Dije muje kiban labarin Mayo Ban, irin rashin jin da kike masu acan"
Dije tana washe baki tabi Surayya ɗaki.
Mamy tana faɗin.
"Allah ya tsayar nan shiyasa hankali na ya gaza kwanciya..."
Suhaima ita ta taya Juhainah shirya kayanta cikin akwatin.
Khairat ta shirya nasu dana su Suhaima suka sauka.
Khairat ta nufi ɓangaren Zarah.
Juhainah cike da tsiwa tace.
"Wlh ke dai Aunty Khairat bakida zuciya, miye na zuba gunta, mu mun tafi wlh bazamu jiraki ba. My Babies muje Yah Boss na jiran mu bazamu tsaya shirme ba"
Taja hannunsa Amina na janye da akwatinsu tana biye dasu.
Tana zaune tasha kwalliya doguwar rigar atamfa, sai baza ƙamshi take.
Zaune a parlournta tana waya hankalinta kwance Tv a kunne, Khairat tayi knocking ɗin ƙofar.
Katse kiran da take tayi tana faɗin.
"Buɗe shigo"
Khairat ta buɗe ƙofar parlour ta shigo da sallama.
Zarah ta amsa tana sakin fuska.
Khairat ta iso tana faɗin.
"Aunty barka da dare, zamu tafi can gida Yah Sadeeq na jiran mu a bakin gate, ban saniba bayan biki ko zamu dawo ko can gidan zauna mun tafi sai kinzo ran ɗaurin aure"
Zarah tace.
"Ayyah! Khairat ki dawo mana bayan bikin don Allah, Ok sai nazo gobe ma zan leƙo in sha Allahu..."
Juhainah ta buɗe ta shige tana zama kusan Yah Boss, yayin da Suhaima ta zauna kusanta, Al'amin ya zauna kan cinyar Yah Boss, yaƙi zama ɓangaresa na Gabas.
Yah Boss ya sumbace shi yana rungumeshi a hankali ya furta.
"Ina Khairat?"
Juhainah ta Turo laɓɓanta tana kallon sa a shagwaɓe tace.
"Yo ba tana can gun wannan matar taka ba"
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya kafe Juhainah yana kame fuska, a hankali ya furta.
"Me take can?"
Rau-rau tayi da dara-daran kyawawan idanunta tana ƙasa da kanta tace.
"Gulma mana mutafi Habiby please"
Dogon hancinta mai ɗauke da tilla sanye da abin hancin zinare, ya kamo a hankali yaja, cikin kamewarsa yana furta.
"Aunty J bana son kije gun Maah kina fushi, oya murmushi"
Kallonsa tayi tana narke fuska cike da soyayya ta saki murmushin a hankali ta furta.
"I love you My brother Habiby"
Da Lumsassun idanunsa ya nuna mata su Suhaima tayi murmushi tana kallon Suhaima tace.
"I love you My Babies"
Suhaima ta rungumeta tana faɗin.
"I love you too My Aunt J"
Al'amin yayi dariya yana faɗin.
"My Dadd Wlh kunyi kyau kai da Aunty J da ta zauna kusan ka"
Yah Boss ya sumbaci kumatunsa, baice Komai ba.
Khairat tana isowa ta buɗewa Amina can baya su Yah Boss ta buɗe mata kujara guda ta zauna, da yake ba mai zama can.
Ita kuma ta shiga gaba kusan Walid tana faɗin.
"I'm sorry My brother naje munyi sallama da Aunty Zarah ne"
Bai ce mata uffan ba, Juhainah take ƙoƙarin magana ya mata wani kallo taja bakinta.
Walid yaja motar yabar bakin gate ɗin.
Walid na isa bakin gate ɗin gidansu Maah Yah Boss ya bada umarnin Walid yayi parking.
Ya kalli Juhainah a kame ya furta.
"Oya kuje ciki anjima zan dawo"
Kamar zatayi kuka ta riƙe tattausan farin hannunsa a hankali tace.
"Habiby baka bani Sweet ɗin ba Please ka temakeni..."
A hankali ya furta.
"Tana gida zan kawo miki, Karki sake min wata magana kuma kije ciki zan kiraki anjima muyi fira ai haka kike so ko?"
Jin zai kiranta cikin farin ciki ta sumbaci hannunsa, ta fice daga motar dan su Suhaima tuntuni sun fice.
Tana fita yaja murfin yaba Walid umarnin su tafi bayan ta shige cikin gidan.
Su Khairat na sallama Maah ta fara baza idon inda zataga ƴarta.
Aunty Sumy tace.
"Ban gane ba ina Autah?"
Khairat ta zauna kusan Aunty Sumy yayin da Amina ta nufi Stairs da akwatuna.
Suhaima ta zauna jikin Maah.
Khairat tace.
"Tana mota gun Yah Sadeeq"
Maah murmushi ya faɗaɗɗa akan fuskarta.
Aunty Sumy tayi dariya tace.
"An shirya kwana biyu Sbd zatayi aure ko?"
Hajjah Mama tace.
"Ai yanzu naga ƙugu ma yake ɗaure mata tayi shegantaka..."
Da sallama ta shigo parlour ta nufi Maah da sassarfa ta faɗa jikinta tana ƙamƙameta tana sumbatar ta.
Maah cikin farin ciki ta rungume ƴarta tana faɗin.
"Autah ma sha Allahu kinga yadda kika yi kyau kuwa? Sai wani mayen ƙamshi kike yi, Gsky na godewa Aminan arziƙi Haj Jamila da Karimah da Mom ɗinki Lubnah"
Juhainah kamar zata yi kuka ta laɓe jikin Maah tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta taƙi cewa kowa, ita yanzu Yah Boss ne kawai jinta da ganinta, dan dai ba yadda zatayi ne ya hanata koda yiwa wani zancen soyayyar da take masa da ta rage raɗaɗin da yake cikin zuciyarta.
Maah ta kamo fuskarta tana faɗin.
"Autah minene naga kamar kina cikin damuwa?"
Da sauri ta ƙyalƙyale da dariya ta juriya tana ƙamƙame Maah tace.
"Babu komai kawai dan naga ko kin damu dani ne"
Balaraba tace.
"Ja'ira yarinya, mu ko sannu da zuwan ba'a mana ba.."
Sai lokacin Juhainah ta lura da baƙin, dan Ruwaida duk sun tafi sai Hanifah kaɗai da take jiran Nasir.
Gaishe su tayi tana miƙewa ta nufi hanyar Stairs.
★
Misalin ƙarfe 9:30Pm
Raudah
Zaune take a haɗaɗɗan gidan da yake mallakinta.
Cikin wata irin shiga take ɗinkin atamfa ne mai tsada jikinta ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana taunar Chigum.
Number Ammar ta kira.
Ta fara ringing ya ɗauka.
Murmushi tayi tace.
"Ammaru manyan samarin Yola ya kaga address ɗin da na maka text ɗasu da yamma? Amma ya naga har yanzu baka zo ba ina jiranka na hana kowa ganina"
Ammar yace
"Ina shirin tafiya ai yanzun"
"Ok sai ka iso Wlh inada tabbacin abinda zan nuna maka da shawarar da zan baka sai kafina kwaɗayin son ɗaukan fansar cin amanar da Juhainah ta maka fiye dani"
Ta faɗa tana katse kiran tana dariya bata jira Ammar yace wani abun ba ma.
Ammar
Cikin shirinsa na alfarma ya fito ya nufi rumfar ajiye motoci, waya a hannunsa yana danna wa.
Mota ya shiga yaja ya nufi gate yana zuba Horn, ya matsu ya isa gun Raudah ta ga miye zata nuna masa akan Juhainah, kuma wace irin ƙira ce gareta har da take ikirarin bata son yin soyayya.
Ƴar dariya yayi yana ƙoƙarin silala hancin motarsa waje.
A hankali ya yace.
"Raudah yau sai kinga namiji uban mazaje sai na sakaki sambatun da baki taɓa yi wa kowane ɗa namiji ba, Asali ma salon da zan shigo miki da shi tun a lokacin zan saka miki muguwar sha'awata baki isa hanamin kanki ba..."
Ya ƙarasa maganar yana jefa wasu drugs a bakinsa yana taunawa, yana tsula gudu saman titi dan ya matsu...
★
Juhainah tunda sukayi lunch ta haye Stairs tayi kwanciyarta, wayarta akan ƙirjinta tana jiran Yah Boss shiru.
Duk tabi ta damu ga wani irin yanayi da takeji acikin jikinta marar misaltawa.
Yanzu ƙarfe goma sauran daƙiƙan mintoci tana kwance lulluɓe cikin quilt.
Tsaki taja tana kallon wayarta number Yah Boss ta danna wa kira.
Lokacin yana down Stairs zaune, yana duba files, sanye yake da narkakkun kayan bacci farare tass farin Glass manne akan kyakkyawar fuskarsa.
Wayar ya kalla sunan Juhainah ya gani yana yawo a screen ɗin wayan.