Sashe 85
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yah Boss
Bayan sallar isha'i ya shigo gidansa Anutse ya hau Upstairs, ya daɗe yana waya kafin ya idar, ya kira Jamilu yace ya dafa masa Madara yau bai sha ba, ya masa Black tea ya ajiye masa nan down stairs, yana sauko wa.
Wanka ya sake ya canza kaya na bacci Set pyjamas brown light, yana Wani irin mayen ƙamshin ya sauko down Stairs cikin takunsa Anutse yake amsa waya.
Zama yayi saman lafiyayyar Turkish Chairs ɗin ya zuba dogayen fararen ƙafafuwansa saman Center Table, da harshen Ingilishi shi da Habibynsa Dr Amiin yake amsa wayan, kusan mintina goma, kafin ya idar.
Anutse ya ɗauki Cup ya tsiyaya Madara da take tiririn zafi.
A hankali tare da bismillah yakai Cup ɗin bakinsa ya kurɓi Madaran, ya lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa, ya haɗiye, ya sake kai Cup ɗin bakinsa ya kurɓa, ta masa daɗi sosai, shi yasa idan ba Jamilu ko Maah suka dafa masa Madara ba, tun bayan rasuwar Khadijah baya iya sha.
Zarah ce ta buɗe ƙofar parlourn ta ta fito sanye da kayan baccin, da suka dameta, kanta ko hula babu, tana baza ƙamshi, yunwa ne ta fito da ita tunda ta dawo bataci komai ba.
Yaji ƙaran buɗe ƙofar da fitowar ta, hakan ya saka shi ƙin buɗe idanunsa, hankali kwance yake kai Cup ɗin Madaran bakinsa, dan baya sha'awar cin abinci yau ita yake buƙata da Black tea ya sha shi kenan, yake ya kwanta ya huta.
Zarah ƙurawa Yah Boss ido tai ganin yadda kayan baccin jikinsa suka masa bala'in kyau, suka fito da farar fatarsa, suka sake fito da kyansa da kyan surasa ta cikakken namiji.
Wani irin yawu ta haɗiye tana kallonsa ta fara takowa gunsa tsabar Kare ya lashe mata zuciyarta.
Wayarsa iPhone ta fara ringing, dai-dai kuma ana danna doorbell ɗin ƙofar shigowa parlour'n.
A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa ya kalli wayan, bai yarda ya kalli gefen da yaji Zarah tana takowa ba, yau ta san asalin Baida kirki idan zuciyarsa bata son Abu, matuƙar tayi kuskuren taɓa jikinsa.
Ganin sunan da yake yawo akan screen ɗin wayan ya saka shi ƙin ɗaukan kiran, ya miƙe dan zuwa buɗe ƙofar.
Yana takunsa Anutse cike da izza.
Zarah ji tayi idan bata kwanta saman faffaɗan ƙirjinsa mai cike da mazantaka ba, tayi asarar igiyar sa da take kanta, dole fa yanzu sai tayi babban yaƙi mallakar mijinta ko ta wata siga ne.
Juyawa tayi ta koma parlourn ta da gudu kamar zarariya.
Bedroom ɗinta ta shiga da gudu ta buɗe drawer ta ciro wata kwalbar turare ta zuba cikin hannunta ta murza ajikinta ko ina ta rufe ta sake ɗauko wata blue kwalba itama ta zubo ta shafe fuskarta da sassan jikinta, ta lakuto a yatsarta ta ware ƙafafuwanta ta shafo ta maida kwalaban ta ajiye ta fito kamar zarariya.
Yah Boss a nutse ya iso ƙofar sai da ya leƙa ta ƙaramar ƙofar Glass mai kama da ƴar ƙarama Camera ɗaukan hoto yaga waye.
Da mamaki yake kallon su.
Ya janye idanunsa yana girgiza kansa, daman yasan yau Babie Suhaima sai tayi rigimar Aunt J sosai.
Saka tattaunsa farin hannunsa yay ya murza key ya buɗe ƙofar.
Suhaima yana buɗe ƙofar ta faɗo jikinsa tana sakin kuka ta ƙamƙame shi.
Rungumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya.
Al'amin yazo shima ya rungume Yah Boss yana faɗin.
"My Dadd nayita ba Aunty Suhaima haƙuri taƙi, tace muzo wajenka ka maido mana Aunt J ɗinmu."
Yah Boss Kallon Amiin yay ya shafa kansa yana manna ɗansa jikinsa sosai, ya maida kallon sa kan Mustapha yana kame fuska a hankali ya furta.
"Kai kuma ƙaton banza ka biye musu ka maido min su? Baka iya lallashinta ita Babie Suhaima tunda ita ne mai fitinar Aunt J ɗin?"
Mustapha yana murmushi yace.
"Allah My Big brother nayi² na lallaɓata ta siga daban² taƙi, Ruwaida ta lallasheta taƙi, harda yaranka Twins sunyi lallashi taƙi, taurin zuciya da kafiyar irin na My brother ta biyo Suhaima komai naka ne ta ɗauka ina zan iya ji da ita ni ɗaya.
Wlh sai da kanka wannan lallashin, duk munyi² taƙi tace a kawo ta wajan Dadd ya zanyi, Wlh bana son kukan nata ne shiyasa na kawota."
Yah Boss ya duƙa gabanta yadda tsawonsu zaiyi daidai ya shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi ya furta.
"My Babie Suhaima calm down, kiyi haƙuri mana, kema fa macace aure zakiyi nan da shekarun da basu kai wanda kike da yanzu ba, kina son Aunt Bilkisu ta zauna gida babu aure ne Sbd ALLAH Babie?"
Kai ta ɗaga tana kukan a hankali tace.
"Ni dai kai maido min Aunty J nah, tana sonka sosai a can bazata yi rayuwa mai daɗi ba, kewarka da tamu zata dameta, ka basu ɓangare anan gidan su dawo Please My Dadd"
Murmushi mai tsada ya saki yana ɗaukanta sama kamar Baby ya kama hannun Al'amin ya nufo parlour dasu, Mustapha yana biye dasu idanunsa yana ƙoƙarin tara ruwan hawaye, har yanzu bala'in tausayin yayansa yake na rashin matarsa abar ƙaunarsa,uwar ƴaƴansa Khadijah, da yaƙi manta al'amarin.
Zarah idanunta sun rufe sam bata lura da Suhaima da Yah Boss ya ɗauko ba, ga Al'amin hannunsa, ga Mustapha a gefe har sun shigo tsakiyar parlour, har ga ALLAH bata gansu ido rufe so take sai Yah Boss ya shaƙo ƙamshinta.
Gadan² tayi kansa.
Mustapha yayi sauri ja baya yana ɗauke idanunsa a kanta, ganin kayan baccin da take saye da su.
Shi a yadda yaganta tsorata ma yayi ya zaci jinnu ne suka taso mata.😂
Suhaima ganin Zarah a dai-dai wannan lokacin, gabanta ya faɗi tsoron Zarah ya kamata, ta ƙamƙame Dadd ɗinta tana ɓoye fuskarta ƙirjinsa tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! My Dadd karta taɓani Wlh tsoronta nakeji, me zata mana take nufo mu da gudu?"
Me Al'amin zaiyi idan ba dariya ba, ya saki hannun Yah Boss yana dariya sosai yana faɗin.
"Lah Aunty Zarah ta haukace ko uncle Mustapha?"
Mustapha yayi saurin juyawa yana faɗin.
"Zo nan Amiin yi shiru yaron kirki"
Al'amin ya nufi Mustapha da gudu da ya nufi hanyar barin parlourn.
Yah Boss ya buga bayan Suhaima ganin idan bai dakatar da Zarah ba, tana iya zubar masa da mutunci gaban yayansa da ƙanasa, ga ƴarsa ma haukan da take ya fara bata tsoro.
Cikin wata irin murya da take nuna iya gaskiyar sa zai faɗa daga bakinsa, da wani irin amon sauti ya furta.
"Idan kika kuskura kika iso nan abakin aurenki na sawwaƙe miki dukkan igiyoyin auren da suke kanki"
Ya ƙarasa maganar yana tsayawa cak.
Ai kuwa Zarah kamar yadda ake danna remote idan ana kallon Film a tsayar da ita, cak a Tv, toh haka ta tsaya, tana kallon Suhaima ta kalli Mustapha da ya juya ya nufi hanyar barin parlour, Al'amin yana bin bayansa.
Idanunta ta runtse cikin matsanancin takaici da tsanar kanta, akan son wanda baya sonta ko kaɗan.
Wasu hawaye masu zafi suka silalo mata akan fuskarta, masifar sha'awarsa da ƙaunarsa take ruruwa acikin zuciyarta.
Bataji bata gani akan ƙaunarsa da sha'awarsa.
Sam bata ga duk wannan halittun ba sai Yah Boss kaɗai take gani a gabanta.
Cike da baƙin ciki da kunyar Mustapha da Suhaima, ta juya da gudu ta nufi parlournta, tana faɗin.
"Wlh Abubakar Bazan bar gidan ka a Bazan haka ba, dole sai ka sauke min haƙƙina na aure, kowa bana baƙin cikin yasan halin da muke ciki a yanzu..."
Nasir
Daga can Hairat tace.
"My friend Nas Hairat na fushi dakai sosai Wlh"
Rage gudun da yake yayi a hankali yace.
"I'm sorry my friend Hairat, abubuwane suka min yawa, Amma zan kawo ki, sai ki yiwa Maah murna ta aurar da Autarta, sai na kaiki kiga gidan amaryar yayi ko?"
Hairat tayi murmushi tace.
"Very good my friend Nasir thank you yaushe kenan? Tunda nasan ka kusa tafiya Mission"
A hankali ya furta.
"Nan da kwana biyu in sha Allahu"
Hairat tace.
"Thank you ina jiranka please"
A hankali yace.
"Nayi miki alƙawarin hakan Ƙawata"
Dariya tayi tace.
"Ok bye sai kazo a gaishe min da matarmu da ake min Rowar ganinta"
Kiran ta katse bata bari yayi magana ba.
Kai ya girgiza yana driving ɗinsa Anutse.
Surayya jin shiru ya gama wayar da ta zargi budurwarsa ce ta ɗago kanta ta kalli titi a hankali ta ɗan juyo kaɗan ta saci kallonsa.
Ganin hankalin sa akan driving ta maida hankalinta kallon titi.
Wayarta ta sake ringing.
Kallon screen ɗin wayan tai.
Farid.
Kallon Nasir tayi cikin Sa'a ya kalleta.
Da sauri ta janye idanunta tana goge hawayen da suke dizgata gabansa na karaya da zuciyarta take akansa.
A hankali ya furta.
"Ba abinda ya dameni ki ɗaga kiran ki"
Da sauri ta ɗaga kiran takai wayan kunnenta.
Farid cikin Masifa da kishin da yake cinsa yace.
"Surayya! Kin raina min hankali ko? Wato soyayya kuke keda Sojan nan ko?"
Ɗan ƙaramin kuka ta saki na takaicin danganta ta da soyayya da yayi da Nasir.
"Eh naje nayi tunda bakada fahimtar cin zalin da ake..."
Ai tuni ta haɗiye maganarta tuna Nasir ɗin na kusa, a hankali tace.
"Kayi haƙuri gobe kazo muyi magana da safe ina..."
Kallon da Nasir ya mata ne ya sakata haɗe sauran maganar tayi ƙasa da kanta.
Tattaunsa farin hannunsa ya zura cikin hannunta ya da yake riƙe da wayan a kunnenta, ya zare wayar.
Ta ka kalleshi da sauri kallon da ya mata ne ya saka mata wani Irin abu mai wujijjiga zuciya, wani irin sanyi ya kamata, bata ma san ta lumshe idanunta ta jingina da allon kujerar da take zaune, tana haɗe jikinta guri ɗaya, Sbd sanyin da take ji.