← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 113

Sashe 112

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dai-dai wannan lokacin A
Anguwan Misirata.
Government house.

Cikin ɗakin taron da yake cikin Government house ɗin, wani magidanci ne zaune, Ƴan jaridu ne tsaye zagaye da shi, ana jiran saitai kayan aikin na gidan radion da zasuyi fira da shi, da TV.

Kyakkyawan buzu ne amma farinsa mai duhu ne, bazai wuce shekaru 50 ba, sanye yake cikin shigar alfarma ta kece raini, wani irin kyau da kwarjini gareshi.
Security's ɗinsa tsaye kansa ɗauke da bindigogi.
Kamal Mubarak Sanda Taurari kenan cikakken Buzun asali. Mai sauran jini a jiki.
PA ɗinsa ya beƙo masa Phone ƙirar Samsung tana ɗaukan ido.

Da harshen French yake magana cikin daddaɗar muryansa da yaren French ya kama bakinsa sosai.

Kusan mintinan biyar yana wayan kafin ya beƙawa PA ɗinsa wayan ya bada umarnin a fara ɗaukan shirin wanda za'a haska a gidan Tv da Radio kai tsaye, jin sanarwar dubban mutane suna gaban Tv masu Tv waɗanda basuda suna sauraron rediyo, wasu YouTube.

Babban ɗan Jarida Falalu Na kowa,ya fara da masa sallama tare faɗin.

"Allah ya ƙara lafiya da girma zamu fara da tambaya ta farko, muna jiran umarnin ka."

Murmushi Gwamna Kamal Sanda yayi, a hankalin cikin taushin murya yace.
"Bismillah ina sauraren ku, kowacce tambaya akwai amsarta da izinin ALLAH"

Falalu Na Kowa yace.
"Godiya muke Mai girma Gwamna.

Jama'ar gari suna raɗe-raɗin saboda baka haihuwa ne mata basa zama dakai, wasu kuma saboda arziƙin ka suke aurenka idan suka ci sai su rabu dakai su tafi, wannan maganar haka ne?"
Kamal Mubarak Sanda Taurari

Wani irin murmushi yay yayi cike da izza yace.
"Fatan dai har YouTube da duk wata kafar sadarwa a yanzu a buɗe take kai tsaye masu Tv da Youtube zasu iya ganin wannan saƙon a kowace ƙasa? Sbd inason Familles Janfar suji su gani su kuma shirya Taurari Familles na tafe garesu dan ƙwato Tauraruwar Taurari Familles"

Falalu Na kowa yace.
"Yes Ranka shi daɗe zamu watsa wannan abun duk duniya tare da izinin ka"

Murmushi mai ƙayatarwa yayi yana ɗaga babbar yatsarsa.

A hankali ya fara magana.
"Sunana Kamal Mubarak Sanda Taurari, maganar bana haihuwa bata taso ba, na haifi ɗana na farko namiji AbdulSamad, da matata ta farko ya rasu, muka rabu da ita lokacin da zan auri mahaifiyar Bilkisu, tace bazata zauna da kishiya ba.
Kuma sai Ƴata ta biyu Tauraruwar Taurari Familles, Bilkisu Kamal Mubarak Sanda Taurari, amma aka min fin ƙarfi Sbd ƙaddara ta sakani kuskure cikin ƙuruciyata.

Dan lokacin cikin Bilkisu Wlh ina ganiyar jin kaina da kuɗi, da zugar abokai da wasu cikin dangi ya sakani nayi nadama ta gaskiy, na kira wanda nake ganin shi za'a samu sassauci a gunsa amma shi nema fitinannan, an aurar min da ɗiyata ba yawuna, nayi haƙuri amma Kashhh ƙaddarata ALLAH ya nuna min abinda nayiwa mahaifiyarta shi ne aka maimaita wa ƴata.

Wlh naji zafi nayi kuka nayi nadama, abinda ya hana ni ɗaukanta cikin da ta samu, bana son taji ciwon da mahaifiyarta taji a kaina, wanda har yau taƙi yafemin, yanzu kuma Alhamdulillah ta haihu gobe suna na saka mutane na ana suna da kwana ɗaya su ɗauko min ƴata da jikokina.
Maganar mata suna guduna babu shi, Ni nake sakin su idan na gano nufin su akaina suna son hallakar dani.
Ko yanzu akwai mata masu bibiyata naƙi ne, sbd duk son ƙarya ne suke min.
Abinda yasa na bayyana gaskiya kowa ya gani idan na ɓoye ALLAH ya sani, yanzu burina ƴata ta dawo da jikokina."

Falalu Na kowa yace.
"Allahu Akbar Ubangiji ya kawo komai cikin sauƙi, yallaɓai baza ka faɗa mana abinda kayiwa uwar Bilkisu ba? Kuma kana ganin Bilkisu zata amsheka a matsayin uba?"

Kamal Sanda yace.
"In sha Allahu zan kiraku indan tazo. Maganar kuma na faɗa maku abinda ya faru har na Saketa nace na yafe cikin bana so, Bazan faɗa maku ba."
Falalu Na kowa yace.
"Mun gode mai girma gwamna, Allah ya ƙara lafiya. Jama'a duka² ana muka gama tattaunawa da mai girma governor Kamal Sanda Taurari, amma nasan in sha Allahu gaba zamu samu wani ƙarin labari, shi dai kowa yasan mutumin kirki ne kowa najin daɗin mulkinsa, a garin Agadez, wannan rayuwar da yayi a yarinta yake bamu labarin ta...."



Nigeria
Yola

Jamal yazo ganin ya'yansa amma Juhainah taƙi ya ganta ko kusa.
Ƴaƴan ma sai da taga ɓacin ran Maah tabar Surayya da Maah suka kai masa.
Harda kukansa da yaga yaran, sak shi ne.

Misalin 11 na dare Juhainah da Surayya sunyi bacci.
Su Suhaima sunyi bacci.

Maah tana ɗakin Papa kiran Aunty Sumy ya shigo.
Ta ɗauka da sallama.
Aunty Sumy cikin tashin hankali tace.
"Maah! Mun shiga uku Taurari Familles Sanda ya fallasa mu, ya kira sunan Janfar Familles, duniya zataga komai fa...."

Labarin dukkan abinda ta gani a YouTube ta shiga ba Maah.
Maah tace.
"Tsinanne ƙarya yake Wlh bai isa ba, Ni zan gwada masa Bilkisu ta haramta a garesa har abada, ALLAH tsinewa Kamal Sanda albarka bazai gama da duniya lafiya ba, shi wannan abun kunyar yake iya fallasa wa Sbd haihuwa ta gagaresa? Ni ban san wasu jahilai bane suka zaɓesa har ya samu wannan kujerar da yake kai a zaune."

Papa ya riƙe Maah yana faɗin.

"Zainab! Me yake faruwa?"
Tace.
"Harɗo babu lokaci maza² ka kira Nasiru da Ahmad su Mustapha Umar, da Malam liman Musa ina so a ɗaurawa Bilkisu da Abba aure cikin daren nan, ban amince sai da safe ba, kuma bana son shima ya sani sai gobe zan faɗa masa, ita kuma a barta ta gama jego jikinta ya warware ta koma karatunta, kar Abunta ya motsa ga jinin jego.
Zan Haɗa Bilkisu aure da ubansa wanda ya fisa zafin kai, ya fisa Izza da jin kai, da tashin hankalin ma baki ɗaya, idan Kamal Sanda yana ƙarya kuɗi ko mulki ga Babansa nan Abubakar Yakubu Janfar, zanga ta inda ya isa ya taɓa masa matarsa."

Papa ya riƙe Maah a jikinsa sosai yace.
"Zainabu mubari har asuba, ki nutsu abi komai a sannu"

Cikin fushin da yake cinta ta ƙwance jikinta tace.
"Mu ke da ƴaƴan Bilkisu ne? Mu zamu musu fatihar sunah? Can gidan ubansu za'ayi, namu nan taron bikine, ƴan uwa da abokan arziki, da nasa ƴan uwa, Toh faɗa min wai za'a jira da sai gobe a ɗaura auren? Idan baka son ciwon zuciya ya kashe Ni kafin goben, aje a ɗaura auren nan yanzu, babu wanda ya sani, daga Abbah har Bilkisu wa ya isa ya tsallake maganata? Ko kana kokwanto ne akan auren bai halatta ba? Ni da kai duk ba jahili cikin mu.
Allah ya ce.
Wa ulaatul-ahmaali ajaluhunna an yada‘na hamlahun.
Iddar mata masu ciki ita ce su sauke abin da ke cikinsu, me muke jira tunda ta sauke? Bazan sake yarda Bilkisu tayi wani auren daga waje ba.

Shi kuma Kamal Sanda zanyi masa abinda zai saka ciwon zuciya ya kashe tsinannan. Yayi wannan abun ne dan ya tozarta mu, bai isa ba."

Papa ganin masifar Maah ta motsa, idan abun yazo bataji bata gani, matsalar mai haƙuri kenan bai iya rikici ba, ya santa kamar yunwar cikisa.
Kuma hukuncin nata shi ne daidai, a hankali yace.

"Shi kenan kiyi haƙuri yanzu za'a yi ɗaurin auren, bari na ɗauko sadakin ALLAH ya taimake Ni akwai Cash, ɗazu da yamma Abba ya bani dubu ɗari Cash yace ko zanyi wani abun gobe sunan matana biyu"

Maah banza ta masa Sbd a sama take.
Papa ya buɗe drawer ya cirosu sabbin kuɗin da Yah Boss ya basa, ko zaiyi wani abun.

Wayarsa ya ɗauka ya kira Kawu Nasiru yana ɗauka ya sanar da shi halin da ake ciki.
Cikin farin ciki yace yana zuwa yanzu.
Yana katse kiran ya kira Alhaji Ahmad ya sanar da shi, shima yayo murna yace zai fito yanzu, ya kira Musa.
Mustapha da Umar ya sanar dasu wani irin farin ciki suke.
Liman Papa yana sanar da shi yace su isko shi daman yana cikin masallacin yana lazimi bai shiga gida ba, sai dare ya raba yake tafiya gida, bari ya kira Jama'a a waya wanda yasan irinsa ne basa baccin wuri.

Cikin mintina talatin duk sun hallara.
Liman ma ya kira jama'a cikin ikon ALLAH ƙarfe sha biyun dare harda mintina, amma mutanen da aka samu kusan mutum 52 suka hallara cikin masallacin.

Liman yace.
"Ma sha Allahu ina Waliyin Ango ina na amarya?"

Kawu Nasiru yace.
"Gani Waliyin Ango Abubakar Yakubu Abubakar Janfar"

Papa ya matso yace.
"Gani Waliyin Amarya Bilkisu Kamal Mubarak Sanda Taurari"

Liman yace.
"Alhamdoulillah! Bismillah"

Kawu Nasiru yace.

"Ni Abdulnasir ina nemawa Ɗana Abubakar Auren Ƴarka Bilkisu"

Papa yace.
"Ni Yakubu Abubakar Janfar Nabaka auren Ƴata Bilkisu"

Sadakin Alhaji Ahmad ya ciro daga aljihunsa ya beƙawa Mustapha.
Ya amsa ya ƙirga dubu ɗari.
Beƙawa Liman yana faɗin.
"Gasu dubu ɗari"
Liman yace.
"Ma sha Allahu Alhamdoulillah! Jama'a ku sheda Aure tsakanin Abubakar Yakubu Janfar da Bilkisu Kamal Sanda ya ɗauri akan sadaki dubu ɗari lakadan ba Ajalan ba, Allah Ubangiji ya basu zaman lafiya ya kawo ƙazantar ɗaki."

Kowa da yake masallacin ya amsa da AMEEN.
Umar ya buɗe huhun goron da ya shi ne ya siya. Sbd dare yayi akwai maƙwabcinsa mai siyarwa, nan ya buga masa gida ya siyo.

Aka raba wa jama'a.
Liman nata kawararo addu'a, ana amsawa da AMEEN.

Kowa da farin ciki yabar masallacin.
Mustapha da Umar Papa ya hanasu shigowa gidan yace su tafi gidansu wai dare yayi.

Papa yana shigo parlour ta miƙe tsaye tarbesa tana faɗin.
"Ya dai Harɗo? An ɗaura auren?"

Papa ya kama hannunta yana faɗin.
"Muje ki kwanta ki nutsu an ɗaura ga goron nan ki ajiye gobe sai a raba wa wanda ya dace, tunda dangi zasu hallara gobe Sunah"

Ai Maah ta faɗa jikin Papa tana sakin kukan farin ciki tace.
"Alhamdoulillah! Yanzu hankali na ya kwanta, Kamal Sanda ƙaryar rashin kunya yake, yazo ya tunkari Abubakar Janfar akan matarsa yaga tashin hankali.

Yawwa nace Mustapha yayi min videon ɗaurin auren ya min?"
Papa ya kama hannunta suka nufi bedroom ɗinsa yana faɗin.
"Sosai kuwa Yayi video gobe zai kawo maki..."
Ɗakyar Papa ya samu Maah tayi bacci...
Chapter 112 · 0% Book details