Sashe 105
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Matsalar baisan yadda zai iya ma shawo kanta ba a yanzun, yasan halinta tunda ta nuna bata son aurensa tun farko yanzu ma hakan ne, yafi son sai ta haihu ya tunkareta tunda yanzu zaman iddah take yi.
Haj Maimuna ce ta shigo ɗakin da sallama tana kallon sa tace.
"Lafiya? Tunanin me kake yi?"
Ammar ya zabura yace.
"Ba komai Momy me kika gani?"
Baki ta taɓe tace.
"Komai ma nagani, tunda ka rasa wacce yarinyar kake neman maida kanka sakarai ko?"
Kai ya girgiza yace.
"Ba haka bane Momy"
"Dadynka na kiranka yana parlour"
Miƙewa yayi suka fito tare.
Dady Najib na zaune Ammar ya shigo da Sallama.
Ya amsa yana kallonsa.
Kusansa ya zauna, yana faɗin.
"Dady barka safiya"
Dady Najib ya amsa yana faɗin.
"Ammar! Tunda ka rasa yarinyar nan nayi² ka fito da mata kaƙi, dan haka kaje Nasarawo gidan Alhaji Ibrahim abokina munyi magana akwai ƴarsa data gama karatu kwananan ku daidaita bana son wata magana idan dai Nine mahaifinka ina so ka Auri Amirah"
Ammar ƙirjinsa ya buga daram! Ya zaro idanunsa, aure ake nufin zaiyi na haɗi?
Dady Najib yace.
"Ko bakaji ne?"
A hankali yace.
"Ok Dady naji in sha Allahu zanje..."
★
Khairat anci azaba ba kaɗan ba, dan da safe wajejen ƙarfe 6 bayan sunyi sallah asuba, sai da Fu'adh ya kaita asibiti, kai tsaye kuwa Special Clinic Janfar ya Kaita, dan Ta samu kulawa.
Anyi Sa'a Dr Nafisa ce ta kwana asibitin itane ta kula da ita sosai, ta kuma yaba mata da kai mutuncinta gidan miji.
Sai wajan ƙarfe 8 har da mintina suka dawo gida.
Zaunar da ita yayi a parlour ya zauna yana rungumeta tare da saka mata albarka, ya manna bakinsa kunnenta yana mata raɗa hannayensa na yawo a jikinta, wai massaging yake mata.
Kallonsa tayi tana mai jin nauyinsa saboda jin irin tarɓar da ya zuba a daren jiya, duk da tana cikin azaba amma ta riƙe wasu kalaman.
A hankali yace.
"My heart kallon fa?"
Idanunta ta rufe cike da kunyarsa.
Suna zama ba'a fi mintina biyar ba, Jannat ƙamwar Fu'adh ta shigo da manyan Warmers shaƙe da Lafiyayyun abinci gidan.
Doorbell ta danna.
Fu'adh ya janye Khairat daga jikinsa yana sumbatar lips ɗinta da yake shigen na Juhainah, dan dai na Juhainah yafi kauri.
A hankali yace.
"Zumata bari na buɗe ƙofar Jannat ce"
Khairat ta ɗaga masa kanta tana ƙoƙarin gyara zamanta ɗakyar.
Fuskarsa cike da murmushi.
Kyakkyawar baƙar beautiful doguwa mai matsagaicin jiki, kamar su ɗaya da Fu'adh, bazata wuce shekaru 22 ba.
Kana kallonta kasan akwai kamun kai da ilimin boko da addini, ga class irin sosai ɗin nan.
Yana buɗe ƙofar ta sakar masa murmushi tana faɗin.
"Good morning my brother, ya Auntynah?"
Fu'adh ya sakar mata murmushi yana faɗin.
"Ga ta can parlour ɗauki Warmers muje"
Murmushi Jannat tayi tana ɗaukan Warmers ɗin ya bata hanya ta wuce.
Da sallama ta shigo parlourn.
Khairat ta amsa.
Kan haɗaɗɗan dinning Table ɗinsu ta wuce ta ajiye ta dawo ta zauna kusan Khairat tana faɗin.
"Aunty Khairat good morning fatan kin tashi lafiya?"
Khairat tayi murmushi ta amsa da.
"Alhamdoulillah Jannat yasu Mama?"
Jannat zatayi magana Fu'adh yace.
"Je kitchen ki ɗauko mana plate kizo ki wuce gida"
Jannat ta miƙe tana dariya tace.
"Kai Yah Fu'adh harda kora? Shi kenan"
Ta miƙe ta nufi kitchen.
Fu'adh ya ɗauki Khairat sama tana faɗin.
"My heart please ka ajiyeni Jannat zata ganmu fa"
Bakinta ya kaiwa sumbata yana murmushi.
Kujeru yaja ya zaunar da ita ya zauna kusanta yana jiran Jannat.
Plates ta kawo musu ta ajiye tana faɗin.
"Aunty na tafi Mama tace kar na zauna"
Khairat tace.
"Ki zauna mana muyi breakfast sai ki tafi"
Jannat murmushi tayi taƙi zama ta musu sallama ta tafi.
Fu'adh da kansa ya ciyar da ita yana cikata da kalaman soyayya.
Suna gama breakfast, ya ɗauki Matarsa suka koma bedroom rungume da abarsa sai baccin gajiya.
★
Karfe 9 da ƴan mintina Yah Boss ya sauko down stairs, sanye da uniform yana baza ƙamshi.
Dinning room ya nufa yayi breakfast a gaggauce ya wuce gun aiki, Sbd yanada baƙi.
Jigawa
Zarah ta koma bakin aikinta na lawyer gadan², sai abinda yake zuciyarta game da Yah Boss bai canza ba.
Yanzu ma cikin shirin tafiya gun aiki take ta fito compound ta nufi gun motarta ta buɗe ta shiga.
Kiran Ramlah ya shigo wayar ta.
Picking call ɗin tayi tana faɗin.
"My Ramlah ykk?"
Ramlah tace.
"Ina lafiya Ƙawata ya haƙuri?"
Zarah tace.
"Hummm! Bari Ƙawata ƙaddarata kenan son Abubakar Wlh na rasa yadda za'ayi na ciresa a raina, nayi mugun haɗiya masa yawu, nifa ji nake kamar nabi malamai akansa"
Ramlah tace.
"Wlh karma ki fara, ALLAH zai baki wanda ya fisa, ai idan dai malaman zamani ne zasu cinye maki kuɗinki a banza ne. Ƙarshe ma su fake da lalata dake"
Zarah tace.
"Shi kenan amma ina sonsa zan san abun yi nan gaba, tunda ba auren zai sake ba"
Ramlah tace.
"Ki dage da addu'a ALLAH ya miki zaɓi mafi alkhairi yafi Zarah"
"Shi kenan Nagode Ƙawata gun aiki zan wuce."
Sukayi sallama taja motarta ta tafi ba wai dan ta ɗauki shawarar Ramlah na, zata duba taga me ya dace.
★
Yau fa wuni gudu Fu'adh na gida tare da Khairat sai nuna mata tsantsar tsagwaron so da ƙauna yake, sai tarairayarta yake kamar jaririya.
Abincin rana ma daga Mama aka kawo musu.
Sai bayan sallar la'asar ne ya fita zuwa gidansu ya dawo.
Juhainah ta rigayi su Suhaima dawowa daga school.
A gajiye tazo tana zuwa wanka ta fara yi ta zauna taci abinci kaɗan, ta miƙe ta hanye Stairs.
Gun da ta ɓoye wayan ta ɗaukata ta zauna gefen gadonta tana dubawa.
Dara-daran kyawawan idanunta ta zaro tana faɗin.
"Tabdijam! Kira 49 duk a yau?"
Picture ɗin da yake kan screen ɗin wayan ta ƙurawa idanunta.
Khadijah na zaune akan cinyarsa ta tallafe kyakkyawar fuskarsa tana dariya yana mata wani irin kallon Ƙauna, hannayensa a saman ƙugunta.
Ajiyar zuciya ta sauke ta tsinci kanta da kwanciya tana saita bakinta akan lips ɗinsa da ya turosu alamar Khadijah ta sumbace shi.
Kiss ta manna dai-dai saitin bakinsa ta ajiye wayan.
Idanunta ta lumshe tana miƙa saboda wani irin azababban Feeling da take ji tun lokacin da ta samu wannan cikin haka take fama.
Sai yanzu da ta san tanada ciki ta tabbatar.
Ajiyar zuciya ta ƙara saukewa, tana sanya tattausan hannunta tana shafa cikinta da yayi girma sai motsi yake.
Wayanta ta ɗauki ringing.
Ta waigo ta kalli gun da take ajiye.
Yah Boss ne mai kiran.
Ji tayi tana buƙatar jin muryansa.
Bari tayi sai da ta kusa yanke wa tayi picking call ɗin, takai wayan kunnenta.
Daga can Yah Boss da yake ofishin sa zaune, anutse cikin kamewarsa ya furta.
"Duk fitinar da zaki min, ki kiyaye in kiraki ki ɗauka babu sallama,hakan zai saka nayi fushi dake, bana so"
Kamar jiransa take yayi magana ta fashe masa da kuka, tana faɗin.
"Kaje kayi fushin dani mutuwa zan yi? Ko dole sai da kai zan yi rayuwa, nafi son kayi fushin dani har na mutu karka sake min magana, so what?"
Yah Boss ya lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa yana furzar da iskar bakinsa waje.
A hankali ya furta.
"Ok haka kike so?"
Cikin kuka da tsiwa tace.
"Eh sai me? Nifa ba irin rayuwar baya zanyi da kai ba, nafi son yanzu kowa yayi sabgar sa Ni da kai, ba ga Yah Nasir ba, Ga Yah Mustapha Umar, da sauran mazan Familles."
A hankali ya furta.
"Alright Amma har ki haihu lafiya bana son abinda zai sakaki damuwa a yanzu, na miki alƙawarin da zaran kin haihu zan fita daga cikin rayuwarki.
Ba ga Sumayya ga Khairat.
Fannin yaran familles nan Yola, waɗanda suka hallata na aura ma...
Ga Rahma Hamidah Nimrah Nuratuh Jalilah Saudat A'ishah Saddiqa, duk sun isa nayi zumunta dasu har aure ma idan ya kama, babu dole sai nayi magana dake alright.
Zan miki abinda kike so Bilkisu, duk duniya ke ɗaya zaki furta haka na saurara miki, da watace cikin familles Janfar bake ba, Wlh daga yau Abubakar ya rufe babinta cikin rayuwarsa har abadan..."
Cikin wani irin tashin hankali da kuka mai tsuma zuciya tace.
"My brother Habiby My blood ka kasheni don ALLAH ka huta kaji, ka rabu dani ɗin Yah Boss, ka rabu dani zan rayu cikin farin ciki da salama, dukkansu da ka zano ka aure su kaga harda ƙwaƙwara irin na sarki.
Yah Boss I hate you I hate you I hate you."
Idanunsa ya runtse a hankali ya furta.
"Hate you too Bilkisu"
Kittt ya katse kiran yana jifa da wayan.
Miƙewa tayi zaune tana kuka ɗan cikinta yana mata motsi sosai.
Saukowa tayi daga bed ɗin ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta fito.
Wardrobe ɗinta ta buɗe ta Ciro Abaya Maroon colour sabuwa cikin kayan lefenta, ta cire kayan jikinta ta saka, ta yane kanta da mahafin abayar.
Ta ɗauki wayansa, ta ɓoye a jikinta.
Down stairs ta sauko.
Maah zaune su Suhaima shigowarsu kenan.
Suhaima taje da gudu ta rungumeta a hankali yadda bata takura ɗan cikinta ba.
Juhainah ta rungumeta tana sauke ajiyar zuciya.
A hankali tace.
"Welcome My Babies ya gajiya?"
Al'amin ya rungumeta shima yana faɗin.
"Alhamdoulillah! Aunty J"
Suhaima tana ƙamƙame da ita tace.
"Aunty Juhainah ina zaki? Wlh kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi tace.
"Da ƙaton cikin nayi kyau My Babies? Zan je na dubo Aunty Surry batada lafiya"
Suhaima tace.
"ALLAH Sarki! Auntynmu, ki gaisheta"
Kiss ta manna wa Suhaima da Al'amin.
Ta sake su suka nufi Stairs dan su tuɓe.
Dijeh ta kalla da take tsaye ta cika tayi fam har idanunta sun kawo ruwa, kishin Suhaima da Al'amin take yadda suka rungume Juhainah suka hanata isa gunta.
Juhainah ta mata murmushi tana faɗin.
"Welcome my Dijeh, ya dai? Akwai damuwa ne?"
Dijeh ta rugo da gudu zata faɗa jikin Juhainah Maah cikin tashin hankali tace.
"Khadija! Baki ganin abinda yake jikinta? Ki isa a hankali"
Dijeh taja ta tsaya guiwa sake bata isa ba, duk haushi ya cikata.
Bata son ana hanata kusantar Auntynta.