Sashe 37
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye da niyar tafiya.
Ai Juhainah maganganun sun mata ciwo, tasha gabansa tana cakumo kwalar rigarsa cike da rashin kunya tace.
"Kai har ka isa kace min mace marar kamun kai, da bana sonka auren bogi naso nayi amma Wlh yanzu ni Juhainah sai na aureka na nuna maka ni ɗiyar halak nake idan kamin kan kara zan maka na itace, nafika dukkan abinda kakeji, kuma aurenka daram zama a gidanka zaka ga yadda ake wasan Jamal Abdallah Na kowa, nifa tsutsotsin kaina sunfi naka ka riƙe wannan..."
Dai-dai lokacin Yah Boss ya shigo parlour.
Idanunsa ya lumshe yana buso iskar bakinsa waje.
Jamal yana shirin bangajeta ya wuce, ganin Yah Boss ya saka shi dakata wa Dan yagani da idanunsa.
A hankali ya tako yana sanya hannunsa ya kamota ya matso da ita dab da shi yana kamo fuskarta da tattausan hannayensa a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Me kike hakan Juhainah?"
Numfashinta yake ƙoƙarin ɗaukewa baki ɗaya sai kawai taji kanta yana sarawa tana sakar masa kukan shagwaɓa tana faɗawa jikinsa tana wani irin kuka.
Kai ya girgiza yana zubawa Jamal lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya furta.
"Jamal! Akwai matsala sosai ko?"
Jamal ya girgiza kansa yana faɗin.
"Haka kawai ta shaƙeni tana maganganu marasa tushe, kamar mutanenta ne zasu motsa basa son maganar auren inaga"
Ai kuwa Juhainah cikin takaicin kalaman Jamal tayi kukan kura ta cafko wuyansa, tana shirin kai bakinta a wuyansa ta danna masa cizo Yah Boss yay saurin kamota yana girgizata ya ɗauketa da mari yana zaunar da ita akan lafiyayyar kujera, yana faɗin.
"Wlh kina motsawa agun sai na sumar dake tare da aljannu naki"
Ai shiru kakeji tana kifa kanta da cinyoyinta tana kuka ƙasa².
Fu'adh dariya yake son yi amma ganin Yah Boss zai masa ba daɗi a yanayin da ake ciki ya silala ya gudu waje.
Yah Boss ya kamo hannun Jamal yajasa suka fice.
A gun motar Jamal ya saki hannunsa, cikin nutsuwarsa a kame ya furta.
"Jamal! Kayi haƙuri, kabar biye mata, shiyasa tun kafin Baiko na faɗa maka matsalar kace kaji ka gani dan haka ka daina faɗa mata magana, idan kaga zata zame maka matsala ayi ƙoƙari a dakatar da komai..."
Jamal ya yi saurin riƙe hannun Yah Boss yana faɗin.
"I'm sorry brother in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba, bazan sake ma zuwa ba har sai ta huce"
Yah Boss ya jinjina kansa a hankali ya furta.
"Ok alright, kaima ka dinga haƙuri Please"
Jamal ya jinjina kansa yana faɗin.
"Thank you brother zan wuce inada taron da zanje."
Yah Boss ya jinjina kansa ya basa hannu sukayi sallama.
Jamal shi kaɗai yasan abinda yake ransa akan iskancin da Juhainah ta masa, sai ya rama ta hanyar da zai gama dukkan fitsarata a gidansa.
Ɗan ƙaramin murmushi ya saki yana jan motarsa zuwa gate na 2.
Yah Boss koma parlour tana nan kamar yadda ya bata umarnin zama tana kuka.
Daga ƙofar parlour ya tsaye a kame yana faɗin.
"Taso ki zo Nan"
Da sauri ta miƙe tana rarraba idanuwa.
Nesa da shi ta tsaya tana goge hawayen.
Cikin iya gaskiyar sa gareta ya furta.
"Wallahi idan na sake ganin abinda nagani yau, kina kama kwalar riga namiji, sai na datse hannayenki, irin tarbiyyar da muka baki kenan? Ke fitsarariya ko?"
Ƙaramin kukan shagwaɓa ta sakar masa tana zubewa ƙasa gaban ƙafafuwansa tace.
"Yaya cemin yayi banida tarbiyya banida kamun kai fa."
Duƙowa yayi yana kamo laɓɓanta ya buge yana faɗin.
"Ai kinyi rashin tarbiyyar ne, tunda kece kika nemosa ya aureki saboda kar namiki auren dole zan haɗaki da Annoba ko?"
Kai ta girgiza tana faɗin.
"A'a Wlh kayi haƙuri Ni yanzu Wlh zan auri duk wanda ka kawo min Ni bana sonsa..."
Tsaki Yaja ya gaji da magana daman kansa bai daina ciwon ba.
Hannunta ya kama ya miƙar da ita.
A hankali cikin kamewarsa murya a kame ya furta.
"Wallahi sai kin auresa idan ba haka ba, bani bake, na cireki cikin ƴan uwana na, har abada bazan sake ko kallon inda kike ba, nagaji nifa bazaki saka min damuwa ba, idan kina son na kasance ɗan uwanki na har abada sai kin auri Jamal, idan kuma ba haka ba, daga yau Wlh karki sake nunawa ma kin sanni..."
Da sauri ta riƙe hannunsa tana fashewa da wani irin kuka tace.
"Na amince zan auresa nayi alƙawarin bazan sake masa rashin kunya ba, kuma zan zauna da shi, akan dai ba rabu dakai kayi haƙuri don Allah Yah Sadeeq ina sonka bazan rabu da kai ba akan Jamal, zan zauna da shi.
Ido ya kafa mata tana kuka harda maji tana riƙe masa hannayensa.
A hankali ya zare hannunsa ɗaya acikin nata, ya zaro handkerchief mai fitinannan ƙamshinsa ya saka mata cikin hannunta yana zare ɗayan hannunsa a hankali ya furta.
"Naji shi kenan goge hawayen ya isa"
Da sauri ta fara goge hawayen tana barin kukan.
A hankali ya furta.
"Jeki idan na dawo zan baki wayanki"
Cikin cika umarninsa ta amsa da kanta jikinta yayi sanyi sosai tana damƙe handkerchief ɗin hannunta ta wucesa ta fito daga parlourn, yanayin ta abin tausayi kamar ba ita ne ta gama yi wa Jamal fitsara ba.
Ashe Baba ma da Babanta....😂
Bayanta yabi yana amsa waya cikin nutsuwarsa, ya nufi gun motar da zasu fita Fu'adh da Walid suna tsaye suna jiransa...
Juhainah jikinta yayi sanyi sosai, tana shiga ta haye Stairs dan tayi wanka ko zataji ƙarfin jikinta.
Jamal yau dai badan darajar Yah Boss ba, baiga abinda zai hanasa fasa auren ba, sai kuma yana son nuna mata banbancin Aya da tsakuwa. Tabbas sai ta raina rashin kunyarta...
★
Wasa² yau tsawon kwana 2 Yah Boss bai bari sun haɗu da Juhainah ba, yana son nuna mata da gaske yake son ta auri Jamal, idan ya mata wasa, zata raina masu hankali ne tace bata so, dan bai yarda da alƙawarin da ta masa ba.
Juhainah kuwa duk hankalinta ya tashi ta gane har yanzu fushi yake da ita, bata san yadda zata yi ba ya yafe mata.
Can gidansu Maah anata shirye-shirye zuwa ɗaurin auren Yah Boss gobe.
Ammar
Parlour su Mama ya shigo da Sallama jikinsa a sanyaye.
Haj Maimuna ta amsa cikin kulawa tana kallonsa.
Dady Najib da ya fito cikin shiri zai fita ya kalli, Ammar yana faɗin.
"Ammaru! Ya dai? Meke faruwa na ganka wani iri?"
Dady Najib ya ƙarasa tambayar sa yana zama kusan Ammar ɗin.
Ammar cikin damuwa yace.
"Dady har yanzu ba'a kirani daga gidansu Juhainah ace na tura iyayyena ba, kuma commissioner yace na dakata da zuwa gun Juhainah har ya kirani kuma shiru har sati ya wuce an shiga wani satin na biyu"
Dady Najib ya shafa kansa yace.
"Haba! Ammaru! Ka zama namiji mana, kar soyayyar yarinyar nan ta maida ka lusarin namiji, ka sa a kanka idan Juhainah matarka ce duk duniya babu wanda ya isa ya hanata aurenka, idan kuma ba matarka bace duk duniya babu wanda ya isa yasa ka aureta, ka dinga haƙuri da tawakali, tunda yace zai nemaka zai nemaka in sha Allahu, ka dage da addu'a Allah ya zaɓa maka abinda yafi alkhairi"
Ammar jikinsa yayi sanyi damuwa fall cikin zuciyarsa, ya dai ɓoyene saboda baya son mahaifinsa yaga baijin maganarsa.
A hankali yace.
"Shi kenan Dady Allah yasa muji alkhairi"
Haj Maimuna tace.
"Ameen ya Rabbi, yanzu kayi magana Ammar ka dinga saka haƙuri acikin al'amarin ka, gaggawa aikin shaiɗan ne, magana ake ta aure dole sai sun gama binciken su zasu neme ka"
Ammar yace.
"Toh Mama in sha Allahu Nagode..."
Jigawa
Duk wani shiri da Zarah tayi tana dab da gamawa, ta gyara kanta ta tsuma kanta cike da waje sai sheƙi take yi, saboda ita kanta gyaran amare take yi, bare abun yazo kanta.
Yanzu ma zaune take cikin parlour gidansu, ƙannenta Mata biyu duka sunada aure, Yaganah da Azizah duk da ƴaƴansu, tun Jiya suke zuwa saboda shiryen² gobe ɗaurin auren Auntynsu.
Aziza cikin Yaren Kanuri tace.
"Aunty Zarah wallahi kinyi bala'in kyau, ga ƙamshi ga ƙyalin fata, wannan Ango mai Sa'a ne, kai tsaye kika yarda da aurensa, Allah ya kawo rabo da wuri"
Murmushi Zarah tayi tana fari da matsagaitan idanunta tana faɗin.
"Sister Aziza kin kuwa san wanda zan aura? Tabdijam! Wlh Alhj Abubakar Janfar ya shallake duk wani matashin Alhaji mai ji da kyau diri kamewa cikar zati ingarman namiji, tsayi kamun kai sanin darajar ɗan Adam rashin son hayaniya, basar da abu ke yafa gama komai, ƙamshinsa kawai ya isheki samun nutsuwa, ina sonsa dayawa Wlh na shirya rayuwa a gidansa wuya ko daɗi in sha Allahu."
Yaganah tace.
"Tabdijam! Lallai commissioner Yola ya kama zuciyar Aunty Zarah dayawa, kam zamuje Yola raka Aunty muga ikon Allah, naji anace wa gidansa kamar Aljannar duniya, babu abinda da babu, karnuka ma na turawa guda Uku Cikin gidan ɓangarensu ma abin kallone raguna ake yanka masu a facebook naga masoyansa na comments"
Zarah tace.
"Wlh ni Ban ma san ya gidansa yake ba, banma san akwai karnukan Turawa a gidan ba"
Aziza tace.
"Ai kuwa zamusha kallon duniya Abban Amir daƙyar nasha kansa yabar Ni zuwa rakiyar Amarya nan fa Yola"
Zarah tayi dariya tace.
"Ku kam akwai son ƙyale² nifa Wlh shi nake so ba ruwana da dukiyarsa Allah ma ya sani"
Yaganah tace.
"Ai mun san halinki Aunty Zarah ba zai kin faɗa ba, shiyasa Allah ya kashe ya baki"
Aziza tace.
"Aunty Yaganah maganar ki gaskiya ne, Allah yasa ayi a Sa'a"
Zarah ta amsa da Ameen, sukaci gaba da gyaran kayan Zarah sababbin ɗinkuna da kayan kitchen na gani na faɗa...
★
A Can Yola
Gidansu Yah Boss Maah bakinta yaƙi rufuwa, cikin tsantsar farin ciki take Abbah zaiyi aure gobe, ƴan uwa na nesa dana kusa sai kira take tana faɗa masu.
Aunty Sumy tafi kowa farin cikin wannan aure.
Su Papa sun tsayar lokacin tafiya ƙarfe 9 na safe za'a tafi Jigawa, wanda ƙalla mutanen da Papa da Mustapha Umar Nasir suka gayyato suna yawa ko banza motoci 10 zuwa 12 zasu jera, tafiya akan ma mai gayyar bai faɗawa ko karen gidansa ba, amma Fu'adh yayi gayya, sosai daga ɓangaren su.