← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 113

Sashe 92

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma kafin yayi wani yunƙurin sai jinsa yayi a ƙasa an jefosa daga saman Bed ɗin, har goshinsa ya bugu sosai.
Kafin ya miƙe bai san ta ina Juhainah ta diro ba, sai ganinta yayi saman ruwan cikinsa, ta kamo kansa kafin yayi wani yunƙurin har ta kafa masa bakinta gefen fuskarsa ta danna masa wani irin cizo sai ga jini. Ga hannunta ɗaya na jibgarsa kamar Allah ya aiko....
[30/03 12:23] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

_Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._

*Page 47*

Jamal dai ganin da gaske kashe shi zatayi, ya buɗe bakinsa ya fara karanto duk addu'o'in da ya san suna Ruƙiyya.
Kokowa suke da gasken-gaske, yana karatun yana tofa mata, ita kuma tana naɗarsa sosai, ga cizo, da yakushin da da take.
Saboda sunfi ƙarfinsa nesa ba kusa ba, ƙarfin jinnu ne.

Sai da ya karanta.
Ayatul'Kursi 7, Fatiha 7, Kafirun 7, Falaq 7, Ikhlaas 7 Naas 7, bakinsa har komfa yake.

Tun yana cikin karanta mata Ayatul'Kursi cikin ƙafa ta 6 su Mamy suka zo amma ƙofar parlour a rufe babu damar shigowa, duk sukayi tsaye hankulan su a tashe.

Surayya sai kuka take sai da Mamy tace ta tafi ta basu guri tunda bata iya addu'a ba.
Mamy ta kira Malam Kamilu a waya da Abbah da yake sun fita tare.

Koda suka zo ƙofa a rufe Malam Kamilu haka yake tsaye yana zabga karatu shima.
Sai da Jamal yazo Naas ta ƙarshe Juhainah ta zube jikinsa tana rungumeshi gam tana attishawa, tare da wani irin amai.
Dan addu'ar da Malam Kamilu yake Jinnun sunjita a jikinsu itama sosai, bare uwa uba ta Jamal da yayi mugun gasa masu jiki.

Jamal tsabar ya daku ko motsin kirki baya iyawa, haka ya jure wuyansa na fitar da jini ya miƙe zaune da Juhainah ajikinsa yana maida numfashi.
Sai da ta gama aman ya kwantar da ita ya cire mata kayan ya canza mata da abayar da suka tafi asibiti, daren jiya ya ɗauketa ya maida ita saman bed.

Ƙofar ya nufa dan Mamy taga aikin da aka masa.
Yana buɗe ƙofar Mamy tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Jamal! Miye wannan fuskar ka da wuyanka kamar kayi accident?"

Abba yace.
"Subhanallahi wannan Jinnun nata suna iya kashe mutum, mugaye ne gaskiya sannu Jamal"
Jamal ya matsa masu suka shigo, a hankali yana faɗin.
"Da Banida ƙarfi Abba da ilimin karatun addini wallahi har lahira Mamy wannan Jinnun nata sai sun kasheni, maso mi ne fa wannan Mamy! Abba!.

Kinga yanzu ma sai naje asibiti kalli goshina kalli kumatuna, da wuyana"

Mamy tace.
"Allah ya baka ladan kwantar dasu da kayi ya baka haƙurin jinyar da zakayi da fuskarka, Malam Kamilu muje a sake mata addu'a"

Jamal yaja su har bedroom ɗin.

Baccinta take tsakani da Allah harda rungume pillow.

Mamy ta iso tana shafa kyakkyawar fuskarta cike da tausayi tace.
"In sha Allahu zaki warke"
Abba ma addu'a ya mata, amma gaskiya ya tausayawa Jamal, zama da irin wannan mutanen sai mai ƙarfin imani da addini sosai.

Malam Kamilu ya iso kusan bed ɗin yana tofa addu'a tsawon mintina goma.
Parlour suka fito Malam Kamilu yace.
"Jinnun nan ya harzuƙa dayawa fa, kasan idan sun aure mace haka ne, ALLAH bata lafiya cikin gaggawa in sha Allahu akwai magungunan da zan haɗo mata na aiko mata zasu temaka sosai zan saka a rubuce Qur'anin duka a kawo a babbar jarka in sha Allahu zasu nakasa sai sun finta daga jikinta, sai dai ayi Haƙuri komai nada lokaci."

Abba yace.
"Allah ya bata lafiya akwai wani aminina ma shima zan saka yazo Yola mugani, baiwar Allah.
Jamal! kai kuma muje asibiti sai an wanke maka fuska an shafa magani."
Jamal bedroom ɗinsa yaje ya canza kaya, Mamy ta zauna nan parlour dan ta tsare Juhainah, Surayya ta shigo suka zauna tare...



Yah Boss

Gidan Kawu Nasiru ya fara zuwa ya gaishesa, a can yabar su Hajiya Mama, ya nufi gidan Haj Lubnah, itama sun daɗe suna fira kafin ya tafi.

Kai tsaye gidan Maah yace Walid ya maidosa, a bakin gate suna cikin mota ya kira Suhaima yace su fito su wuce gida.
Suka yi wa Maah sallama suka tafi.

Ɓangaren Zarah

Tun safe da ta farka, saƙa take da warwara, ta yadda zata rama cin mutuncin da Yah Boss yake mata.
Taci alwashin sai ya ratsa jikinta, bazata taɓa zaman banza gidansa ba, dan taji ajikinta sakinta zaiyi komin daren daɗewa.

Ƙin fitowa tayi sai Yah Boss da ƴaƴansa suka fita ta fito tayi breakfast, ta koma tayi wanka, ta fitowa parlour zauna anan babban parlour ta kunna Tv.
Ƙawarta Ramlah ta kira, wayan tana fara ringing Ramlah daga Jigawa ta ɗaga kiran tace.
"Amarsu kinsha ƙamshi, ykk ya mai gidan? Fatan yanzu babu damuwa an zama ɗaya?"

Zarah cikin takaici tace.
"Ramlah! Babu abinda ya canza ina cikin masifa, pills ɗin nan fa yasha tea ɗin amma Wlh an kwana lafiya, na rasa wani irin mutum ne mai masifar taurin kai, Ramlah don ALLAH wani irin temakon zaki min? Wlh so nake ko ta wani halin na mallaki mijina, ina sonsa ina son nasan meye a wandonsa nan da yake jiji dakai, daga ya tsallaka Ni ai girman kai da izza ta ƙare ko?"

Ramlah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Ai Wlh tunda pills ɗin nan basu masa aiki ba, sai kin jira tabbas ya wuce sanin ki, ki gwada kissa idan batayi ba ki haƙura ki nemi zaɓin ALLAH..."

Zarah tace.
"Wlh nayi kissa batayi ba, na rasa ya zan yi da wannan mutumin mai taurin zuciya..."

Fitinannan ƙamshin turaren sa mai ƙara mata sha'awarsa ta shaƙo cikin hancinta.
Da sauri ta waiga.
Yana riƙe da hannun ƴaƴansa abun gwanin burgewa ba kaɗan ba, anutse yake takunsa yana jaye da hannun ƴaƴansa, suka nufi hanyar Stairs, Sbd su Suhaima sunyi lunch gidan Maah, shi kuma bazai ma tsaya down stairs ban tunda yaga tana zaune, zai kira Jamilu ya kawo masa Stairs.

Ko shakka batayi Yah Boss yaji bayanin ta na ƙarshe.
Wani yawu ta haɗiye tana janye idanunta akansu.
Ko kallon inda take Yah Boss da Suhaima basuyi ba, Al'amin ne kaɗai ya kalleta yace.
"Aunty Zarah ina wuni?"

Zarah ta sake haɗiye yawu ta amsa da.
"Lafiya lau Al'amin ALLAH ya maka albarka yaron kirki Nagode da ƙauna, in sha Allahu sai ka zama wani abun a duniya ɗan Zarah"

Suhaima ko waiwaye dan batada lokacin ta, tunda tasan itane take yiwa habaici.

Ramlah tace.
"Hello ko kin ajiye wayar?"
Zarah cikin damuwa tace.
"Sai anjima zan kiraki sam banida Sa'a akan wannan mutumin, Wlh yaji wani abu daga wayar da muke yanzu"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran ta miƙe hankalinta a tashe, ta nufi parlournta tasan idan batayi da gaske ba tabbas a kowa ne lokaci Yah Boss zai iya sakinta.

Yah Boss
Su Suhaima suna shirin shiga parloursu, har Suhaima ta kama handle ƙofar zata buɗe, Yah Boss ya kalleta cikin kamewarsa a hankali ya furta.

"My Babies kuyi wanka kuyi alwala lokacin sallah ya kusa, idan an kira kunyi sallah sai ku kwanta ku huta.
Ko kuna buƙatar wani abun yanzu Jamilu ya muku ko Fu'adh ya muku shopping?"

Suhaima ta matso gun mahaifinta a hankali tace.
"My Dadd da yamma dai a kaimu da kanmu mu zaɓi abinda muke so a shopping mall ɗin"

Murmushi yayi sakar mata yana kwaikwayon maganarta.
Al'amin yayi dariya yana tafa hannayensa.
Suhaima ma dariya tayi ganin yadda Dadd ɗinta ya kwaikwayi maganarta sak.
Anutse ya furta.
"Ok My Babies zaku fita da Fu'adh"

Cikin farin ciki suka rungume shi suna masa godiya.
Hannayensu ya kama har cikin parlour su ya saka su cike da soyayyar su ya fito.

Kai tsaye master bedroom ɗinsa ya wuce bai tsaya parlour ba.
A nuste ya cire kayansa ya ɗaura towel ya shiga bathroom...


Jamal
Clinic ɗin da yake kusansu wadda yakai Juhainah a daren jiya, can suka tafi da Abba aka dubasa.
Fuskar aka wanke, sai da aka masa allura ko Dr Asiya tayi mamakin waye ya masa wannan cizo haka?
Sai da aka masa dressing a wuyansa, suka nufi gida.
Mmay suna zaune da Surayya a parlour, su Jamal suka shigo da sallama.
Mamy ta amsa.
Abbah yace.
"Ya jikin na Bilkisu? Ko bata farka ba?"

Mmay tana kallon Jamal tace.
"A'a bata farka ba, yanzu ma Surayya ta leƙota.
Jamaluddin! Ya jikin? Harda dressing akayi maka a wuya?"

Jamal ya zauna kusan Mamy yace.
"Alhamdoulillah! Mamy ba dole ayi ba tunda cizon ya shiga naman wuya"

Surayya haka kawai dariya take son kamata ta miƙe tsam, ta nufi hanyar fita Sbd dariya zata yi ganin fuskar Jamal kamar anyi wasan kura da shi.

Abbah yace.
"Tashi muje tunda yana nan zai kula da ita tunda ai yanzu sun tafi.
Na kira Malamin nan abokina danake gaya miki, yayi tafiya amma yace da zaran ya dawo zai zo in sha Allahu zai gwada mata aiki, ga Malam Kamilu idan aka haɗa kinga ai zamu dace in sha Allahu, ALLAH ya bata lafiya."

Mamy tace.
"Allahu Ya sha, muje"

Fita sukayi Jamal ya gyara zamansa, a hankali yake faɗin.
"Yanzu ba dan weekend bane sai na tafi school a haka, waɗanda suka san nayi aure, suyi tunanin gun kokowa da Amarya taji min ciwo"

Tsaki Yaja yana ɓata fuska.
Miƙe wa yayi ya nufi bedroom ɗin Juhainah.
Tana kwance bacci take sosai.
Bai shigo ba ya juya ya fice...

Surayya lokacin da ta fito ta nufi part ɗinsu, bata kai shiga ba, Farid ya kirata.
Kamar bazata ɗauka ba ta ɗauka ta raɓe cikin tsiwa tace masa.

"Kai Kanada bakin min magana ne? Matsoraci, wai ace a gabanka namiji ɗan uwanka ya ɗaukeni ka gaza komai, sai kira a waya kana barazanar wai idan ban faɗa ka turo gidan mu ba ka haƙura dani.
So what dan ka haƙura dani? Ance maka nayi tsawane bare na damu?"
Chapter 92 · 0% Book details