← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 113

Sashe 21

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar yayi murmushi yace.
"Wajan Juhainah"
Fu'adh yace.
"Ok ga yayanta can commissioner cikin mota yana son ganinka"
Ammar ya haɗiye yawun tsoro dan sai lokacin ya ankare da Fu'adh tare yake da commissioner.
Cikin dauriya yabi bayan Fu'adh.
Tun kafin su iso Yah Boss ya zuge Glass idanunsa amma ba gunsu ba.
Fu'adh ya koma mota yayin Ammar ya iso ya gaishe da Yah Boss cikin girmamawa.
Yah Boss ya amsa yana kallonsa fuska babu wasa ya furta.
"Kaine Ammar?"
Ammar yace.
"Eh my brother nine"

Yah Boss ya maida hankalinsa kan wayarsa da take ta famar ruri, a hankali ya furta.
"Ok good ka shiga motarka ka biyo mu. Walid muje"
Ya ƙarasa maganar yana rufe glass ɗin motar, ya amshi wayansa ta aiki hannun Fu'adh yana ɗaga kiran ta Glass ɗin idanunsa yana magana anutse cikin harshen Ingilishi.
Ammar wani irin yawu mai ɗaci ya haɗiye yana sauri ya shiga motar dan kan su masa nisa dan tuni Walid ya cika umarnin Yah Boss, dan ya silala motar anutse ya fara driving.

Ammar duk da yasan gidan da yake bai taɓa shiga ba, bai taɓa tunanin tsaruwa katafareren gidan Yah Boss ta kai haka ba, dan ko ƙasar waje za'aci wuya kafin a samu irin mayen gida Mai masifar kyau da tsari.
Kasancewar tare yake da mai gidan babu wanda ya hanashi wucewa har asalin gidan.
Su Suhaima ana parking suka buɗe suka fice cikin murna suna gudu.
Ma'aikatan gidan nata masu sannu da zuwa ina sun tafi neman Aunty Juhainah.
Yah Boss yana fitowa yaba Fu'adh umarnin yakai Ammar ɓangaren da parlour baƙi yake, shi kuma ya nufi ɓangarensa.

Suhaima da Al'amin ƙaton katafareren parlour suka shigo suna kiran Juhainah.
"Aunty Juhainah! Aunty Juhainah kina ina?"

Amina dai tun a farfajiyar gidan ta nufi ɓangaren da take idan sun zo gidan, tace tana zuwa yanzu zata shiga toilet ne.

Al'amin ne ya ɗaga murya yayin da Suhaima take ta raba idanuwa ta nufi kitchen tana faɗin.
"Bari nace Jamilu ya dafa min indomie, amma banda ƙwai, Al'amin! Ka hau Stairs Yanzu haka tana can tana bacci ma..."

Bakinta ne ya tsaya cak ganin wata bak'ar mata ta buɗe ƙofar bedroom ta kusan kitchen ta fito.
Suhaima ta ɓata fuska sosai tanaja baya take faɗin.
"Wacece ke har cikin asalin ɓangaren mahaifina? Me kike nema anan bangaren?"

Juhainah babba ta shiga tashin hankali kallon tsantsar tsanar da tagani idanun Suhaima, sai hawaye sharrr-sharrr na tausayin kanta, a hankali tace.
"Kiyi haƙuri mai gidan ne ya bugeni a mota, jiya aka sallameni daga asibiti, yace na zauna Anan kafin naji sauƙi a maidani garinmu"

Suhaima ta taɓe baki tace.
"Allah Sarki sannu tunda dai Dadd ne ya ja, amma ai akwai ɗakuna can bangaren yamma Me yasa za'a ajiyeki nan?"
Tayi magana cikin isa da izza irin ta Yah Boss sak tana zaro mata lumsassun fararen kyawawan idanunta.
Juhainah babba duk ta diririce saboda yarinya tayi mata kwarjini sosai kamar Yah Boss ne a gabanta tsaye.
Kanta ta sadda tana faɗin.
"Ba laifi na bane kiyi haƙuri"

Suhaima tace.
"Toh koma ɗaki Dadd ɗina yana nan karki sake fitowa idan yana nan, duk da ma bazai ko kalleki ba"

Ta ƙarasa maganar tana nufar kitchen.
Juhainah ta bita da kallon ƙaunar da ta shigeta ta yarinyar.
Suhaima tana ƙoƙarin shiga kitchen ta juyo da kanta.
Ai Da sauri Juhainah babba ta shige ta rufo ƙofar.

Yah Boss lokacin da ya shigo parlour Al'amiin ya haye Stairs neman Juhainah, yayin da Suhaima tana gun Juhainah babba bazai ganta ba daga parlour shiyasa yayi tunanin duka suna tare.

Upstairs ɗin shima ya haura.

Haɗuwa saka yi da Al'amin yana ƙoƙarin sauka.
Yah Boss ya kamo hannunsa yana faɗin.
"Babies kuje kuci abinci ina Suhaima?"
Al'amin yace.
"Daddy ta tafi ta saka Kuku Jamilu ya dafa mata indomie, Daddy banga Auntyna ba, tana ina?"
Yah Boss ya lumshe kaifafan idanunsa ya furta.
"Kaje kaci abinci maybe tana garden"
Al'amin ya zare hannunsa yana murna yace.
"Yeee bari naje na kamota ni da ita zamuyi abinci"
Ya faɗa yana tafiyarsa, ya fara taka Steps a hankali.

Yah Boss ya zaro key ya buɗe ƙofar ya zare key ɗin ya shiga ya murza key a ƙofar parlour saboda kowane lokaci yaran zasu iya zuwa kuma su shigo ɓangaren nasa kai tsaye.

Juhainah tana nan kwance inda ya barta, Sai dai yanzu ta farfaɗo, Amma yanayin da take ciki sai ya baka tsoro.
Kalllo ɗaya Yah Boss ya mata ya gane shegun kanta ne suka motsa, daga tsoron da taji ta suma, mafi lokuta haka ne.
Idanunta baki ɗaya sun juye sai farin babu baƙin, jikinta sai zanzana yake bakin na fitar da kumfa.
Wayoyin hannunsa ya ajiye akan Center table ya dawo ya sunkuya ya zaro handkerchief ya riƙe kanta yana tattare dogon gashinta da ya rufe mata rabin fuska, ya ƙulleshi ya goge mata kumfar bakinta, ya jefar da handkerchief ɗin, ya sanya tattausan hannayensa ya ɗauketa sama ya nufi bedroom ɗinsa da ita, saboda gudun karta fara ihu ya'yansa su ji su shiga tashi hankali, saboda abin nata babu kyau ga ƙarfin tsiya shi kaɗai ke iya mata ba tare da ƙarti sun riƙeta ba.
Ƙasa saman lallausan Carpet ya kwantar da ita, ya miƙe dan zuwa ɗauko cup ya zuba ruwan zam-zam yayi mata addu'a.
Sai mi wuyansa yaji an kama da ƙarfin tsiya riƙon kuma ba na wasa ba. An ɗare gadon bayansa, ana kai masa duka.
Da wani irin ƙarfi yayi watsi da ita ta zube ƙasa, idanunta na sake juyewa abin tsoro...
[08/01 13:44] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

_*Kuci Gaba Danna Min Followers, Zan Dinga Antayo Muku Zafafan Tsofaffin littattafai Na, Kuna Chanawa Abinku😂💃🏻🫣*_
👆🏽

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

Page 12

Cup Glass mai shegen kyau fari Tass ya ɗauko, ya buɗe jarkar zam-zam yayi Bismillah, ya tsiyaya ya rufe ya ajiye Cup ɗin saman madedecin table, wanda zallar Glass ne.
Saman Sofa ya zauna yana ɗaukan Cup ɗin yayi Bismillah ya saita bakinsa akan Cup ɗin Ya fara addu'a.
Juhainah juye² ta fara tana jujjuya kanta.
Idanunsa ya ɗago ya kalleta, ganin abun nason tashi baki ɗaya.
Bai fasa addu'ar da yake acikin ruwan zam-zam ba.
Tashi yayi Cup ɗin a hannunsa ya iso gabanta, ya zauna ya tanƙwashe ƙafafuwansa ya ajiye Cup ɗin Ya ɗago kanta yana ɗorawa saman cinyarsa, ya ɗauki Cup ɗin ya matse bakinta ya zuba mata ruwan zam-zam ɗin ta yadda dole sai ta haɗiye.
Tana haɗiye Wa ta fasa wani irin ihuuuuu! Yayi saurin saka tafin hannunsa ya rufe bakinta, ya ɗauki Cup ya cire headband ɗin kanta ya jefar ya juye ruwan akanta Ya sanya hannunsa yana cucuɗa dogon gashinta, mai tsayi sosai.

Cizon tafin hannunsa tai yaji zafi yaƙi janye wa, sai da gashinta ko ina ya samu ruwan zam-zam ɗin, ya riƙe sosai da hannun ɗaya ɗayan rufe da bakinta ya fara mata karatu.
Wani irin rawa jikinta ya fara tana fizge² jikinta na wani irin zanzana, ihu take son yi babu dama, ya rufe bakin sosai.
Sai da ya tabbatar sunji a jikinsu ya janye hannunsa daga rufe mata bakin da yayi, ai ta fashe da kuka tana faɗin.
"Ku ƙyalemu haka jikin mu na mana azaba, wai shin kai me ma ruwanka damu ne? A rabu dani ka shafa min lafiya nayi rayuwata da Juhainah babu ruwanka dani"

Yah Boss ya ƙara riƙeta sosai da ƙarfinsa saboda neman ƙwace wa take daga hannunsa, tunda ba ƙarfnta bane.
Cikin nutsuwarsa ya furta.
"Ni nakeda ruwa da kai, saboda jikin ƙanwata, jinina ka shiga kake zalumtarta kuma kace na rabu da kai? Tsakanin mutum da aljan babu wata alaƙa, me haɗinka da ita? Shekara kusan uku kenan Muna fama dakai kaƙi fita, amma wannan karon zakaga kalata nima.
Idan kana son cigaba da rayuwa toh Wlh ka fita salin alin, ko na zama ajalinka da izinin ALLAH, idan kana ganin wasa nake kaci gaba da zama a jikinta zan nuna maka kai ƙaramin shegene a jansin ku"

Dariya Juhainah ta ƙyalƙyala kanajin dariyar kasan ba mutum sak yayita ba.
A cikin masifa tace.
"In fita kace fa? Ka raba auren da yayi shekara da shekaru? Toh baka isa ba, bazan fita ba, ina sonta na saba da jikinta ka rabu dani kawai"

Yah Boss ya girgiza kansa baice uffan ba, ya kamo kanta ya riƙe sosai yana manna bakinsa akan kunnenta ya fara karanto Suratul Baƙarah da sauti mai wani irin daɗin sauraro.
Da farko dariya kawai yake amma ko minti goma sha ba'a rufe ba azaba ta fara cinsa.
Acikin kunnensa wani irin azabar karatun yake ji, jikinsa kamar ana zuba masa ruwan dalma a cikin kunnensa da jikinsa, fizge² ya fara, yana zuba ihu ganin Yah Boss fa ba saurara masa zai yi ba, a aguje ya gudu kamar yadda ya saba, wata irin attishawa Juhainah tayi, wani hayaƙi ya fito daga hancinta, sai wani irin amai Ja ta fara, ajikin Yah Boss.
Riƙeta yayi sosai har ta gama aman ajikinsa.
Kwantar da ita yayi ganin aman bai taɓata ba, tana maida numfashi alamar ma bacci take yi, harda minshari.
Miƙewa yayi ya nufi bathroom, dan yasan wannan baccin zata iya kai yamma lilis tanayi, amma idan ta farka ras zata farka sai dai kasala.

A cikin bathroom ya cire kayan jikinsa da ta ɓata da amai, ya zuba cikin abun tara kayan wankin, wanda ƙa'idarsa ce, ba'a barma sa datti, yana fitar da kaya ake wanke wa, a goge.
Shower ya sakarwa kansa mai sanyi yana ratsa tsakiyar kansa yana sauka a jikinsa.

Juhainah bacci take tsakani da Allah, bata ma san dukkan abinda ya faru ba.
Chapter 21 · 0% Book details