Sashe 50
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki Yaja yana ɗan gyara zamansa a hankali ya furta.
"Fu'adh baya nan, ki jira za'a zo a kawoki, ai maganin ki kenan tunda bakya jin magana"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, yana cigaba da danna System ɗin.
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana juyi gaban madubin tana faɗin.
"I love you My brother Habiby Yah Boss, ka dakeni nima na samu abun da zan yi na rama, ko banza na baka wahala, kuma zanje police station ɗinku nasha kallo, kuma ka tattaleni tunda baka son wani ya cutar dani. Yeee sai Ni Juhainah ta Yah Boss"
Ihun ta ya farka da Surayya daga bacci ta buɗe idanunta tana miƙewa zaune , tana murza idanunta ta kalli Juhainah da take tiƙar rawa gaban madubi.
Surayya ta ɗauki pillow ta jefe ta tana faɗin.
"Bakida hankali yarinyar nan Wlh, ina bacci na mai daɗi ina mafarkin Yah Boss kika tasheni da ihunki na banza"
Juhainah tana rawa tayi wa Surayya gwalo tana faɗin.
"Gun Yah Boss zantafi yanzu ƙarya na lafta masa yanzu, yace zai Turo a kaini"
Ta ƙarasa maganar tana yiwa Surayya gwalo.
Surayya tace.
"Please inzo muje"
Hanifah ce ta buɗe ƙofar ta shigo daga bedroom ɗin Khairat taji ihunta.
Juhainah zata yiwa Surayya magana Hanifah ta shigo, bata daina tiƙar rawa ba, ta kalli Hanifah tana turo baki tace.
"Aunty Hanifah har yanzu baki tafi gidanki ba? Ina Yah Nasir ɗin kika kwana anan?"
Hanifah ta iso gun Juhainah idanunta cike da hawaye ta riƙe hannun Juhainah a hankali tace.
"Autar Maah don Allah bakiji Maah tana faɗin abinda na mata ko cikin rashin sani bane, na bata haƙuri banajin daɗi idan tana fushi dani"
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Amma wasa kike min? Ai Maah bata da matsala yaushe ma zata yi fushi dake aunty Hanifah, ko dai wani abun kika mata?"
Hanifah tana damƙe hannun Juhainah tace.
"A'a Wlh ban saniba ko a rashin sani"
Juhainah tace.
"Toh bari idan na dawo daga gun Yah Boss zan lallaɓa maki ita naji idan wani abun kika mata zanje har gidanki na sanar dake sai ki gyara kibar kukan Please"
Juhainah ta ƙarasa maganar cike da tausayin Hanifah tana sanya tattausan tafin hannunta tana goge mata hawayen taja hannunta ya zaunar da ita gefen Bed tace.
"Kiyi haƙuri Auntynah in sha Allahu Maah zata fasa fushi dake bari dai naje na dawo, kuyi fira ku da Surayya har na dawo"
Surayya tace.
"Ni dai kam a halin MAAH da na sani tun ina ƴar shekara 7 tanada kyawun hali, bata yiwa mutum wani abun koda kuwa kayi mata kuskure, toh tana uzuri Aunty Hanifah ki dai binciki kanki"
Juhainah ta buɗe Wardrobe ɗinta tana zaro doguwar riga ta lace, kalar da ta fi so Pink colour.
Baida nauyi shar da shi sai shegen tsada.
A hankali tace.
"A'a Surry Hanifah bata da matsala, Maah ma haka kawai dai an samu akasi zan shiryasu ki mata hira kafin na dawo, kuma kimin addu'a dan Wlh ƙarya na lafta masa kar naci na jaki"
Surayya tace.
"Allah yasa ya fasa maki baki, ya fame miki goshin"
Hanifah Duk da tana cikin damuwa sai da tayi murmushi tana kallon Juhainah da babu kunya gaban su ta tuɓe tana saka kaya, Juhainah ta Turo laɓɓanta gaba tace.
"Gaskiya Aunty Hanifah ki daina kallona haka, Kinsan da banson kallon ƙurulla"
Surayya ta harareta tace.
"An kalla uban wa yace ki tuɓe a gabanmu?
Watarana Wlh sai kin tuɓe gaban Mayu sun cinyeki kin huta"
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tayi tsalle tana faɗin.
"Da sunci mutuwarsu kuwa dan Wlh kafin na mutu sai sun rigani mutu"
Ta ƙasara maganar idanunta suna canza kala jikinta na neman rikicewa Dan baki ɗaya ta fara kyarma.
Surayya tsoro ya kamata sanin wacece Juhainah, ƙirjinta ta dafe tana dirowa daga saman bed ɗin ta nufota tana riƙota tana faɗin.
"Sister J miye haka daga wasa Allah ya baki haƙuri Wlh wasa nake miki"
Ta ƙarasa maganar tana girgizata.
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin.
"Ware matsoraciya ba komai fa kawai jikin nawane ya fara rawa da kansa"
Hanifah da jikinta ya ɗauki rawa har ta fara hawayen tsoro tana neman hanyar guduwa jin Juhainah tayi magana lafiya lau, tayi ajiyar zuciya, tana kwanciya ta basu baya, bata sake kallonsu ba tace.
"Autah kin iya tsokana ai"
Juhainah tana zaro idanunta da takejin kamar wani abu yana mata yawo ciki tayi dariya tace.
"Aunty Hanifah tsoro wai da guduwa zakiyi ji kike Banda hankali ko?"
Hanifah tace.
"A'a Wlh nasan lafiyarki lau, naji tsoro ne kawai"
Juhainah tsaf ta shirya rigar ta mata kyau dai-dai ƙaramin jikinta.
Gashinta dogo har tsakar baya, irin na Fulani Fulanin ma ruwa biyu.
A biyu ta rabasa ta saka ribbons ta saka hula Pink ta ɗauko mayafi pink ta fesa turare yau komai Pink ta ɗauko har handbag takalmi komai.
Wani irin ƙamshi take.
Ta kalli Surry da Hanifah tace.
"Bye sai na dawo"
Surayya tace.
"Ina nan adawo lafiya"
Murmushi Juhainah tai tana ficewa.
A hankali take saukowa.
Maah da take zaune tana waya da Papa akan sun shingo sun biya su sauke abokansa biyu, gidajen su.
Ganin Juhainah cikin shirin fita, tabi da kallo.
A hankali ta ƙaraso tana zama kusan Maah ta rungumeta a shagwaɓe tace.
"Maah kaina ciwo yake, kuma Yah Sadeeq yace naje gunsa yanzu"
Maah daidai sun gama wayar, ta taɓa kan Juhainah tana faɗin.
"Ƙarya kike baice kije ba, so kike ki tafi can gidansa ko Juhainah?"
Baki ta Turo tana faɗin.
"Allah Maah ƙarya na lafta masa kuma Wlh idan banyi shahada ba naje yanzu, Allah idan ya kawo kansa munyi face to face jikina zai faɗa min"
Maah ta shafa kanta tana murmushi tace.
"Ai bakyaji wlh Autah, yanzu kina ciwon kan zakije? Toh bari na kawo miki magani..."
Da sauri tace.
"Na sha yanzu ai"
Wayarta ta fara ringing.
Handbag ɗin ta buɗe tana ciro wayan taga Yah Boss ne.
Kiran ta ɗaga kafin ma tayi magana ya furta.
"Ki fito bakin gate ana jiranki"
Ƙittt yana gama faɗar haka ya katse kiran.
Juhainah ta saki Maah tana marairaice fuska ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Maah ki tayani da addu'a zan tafi Allah yasa kar ya taɓa min lafiyata"
Maah tayi ƙaramar dariya tace.
"Toh naji a dawo lafiya tsuntsun da yaja ruwa...."
Juhainah tana diddira ƙafafuwanta tana turo jajayen laɓɓanta ta tafi.
Maah ta bita da kallo tana murmushi dan tasan ba makawa koda marine yau Autah sai ta sha tunda ta lafto masa ƙarya.
Tana fitowa bakin gate daga waje lafiyayyar motarsa tagani.
Tana washe baki ta nufi motar.
Walid ne da wani police ɗaya.
Baya police ɗin ya buɗe mata ta shiga, tana gaishesa ta gaishe da Walid.
Ya amsa cikin sakin fuska.
Dan Juhainah babu girman kai ko kaɗan batada jin kai, barta dai da rashin jin magana...
★
Yah Boss zaune a nuste yake amsa waya cikin harshen fulatanci, zaka rantse da Allah bai iya Hausa ba.
Ƙofar aka ƙwanƙwasa ya bada izinin shigowa.
Fu'adh ya buɗe ya shigo da Sallama.
A nutse ya ƙarasa yaja kujera ya zauna yana faɗin.
"Washhh! Gajiya"
Yah Boss ko kallonsa bai ba yaci gaba da Wayarsa.
Fu'adh ya haɗiye dariyarsa yana zaman jiransa.
Wayar Yah Boss ɗaya ta sake ɗaukan ringing kira akaro na uku.
Fu'adh ya matsa ya ɗauka yana picking call ɗin tare da sallama.
Daga can aka amsa ana faɗin.
"Tuba muke yallaɓai don Allah ka duba mana case ɗin, Wlh wlh Yaron Baida laifi"
Fu'adh ya katse mai maganar ta hanyar faɗin.
"Sir yana cikin busy yanzu bazai samu maida magana ba"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, saboda yasan har abada Yah Boss bazai amsa irin wannan mutanen ba, ta bakin wani ace mutum Bai da laifi sai yayi ido huɗu da mai laifin.
Juhainah a hankali take taka Steps hawa ofishin Yah Boss.
Sai da suka gaisa da sakataren Yah Boss, sbd ya santa duk da bata fiye zuwa ba, wani lokacin suna zuwa da su Suhaima.
A ƙofar ta tsaya tana danna door.
Fu'adh yace.
"Yes come in"
Juhainah ta buɗe ƙofar tana shigowa tana siririyar sallama.
Fu'adh ya amsa yana kallonta da mamaki.
Juhainah ta washe baki tana faɗin.
"Yah Fu'adh! Barka da rana"
Fu'adh yana murmushi yace.
"Barka Autah ya kike?"
Juhainah ta ƙaraso tana washe baki tana ƙoƙarin zama, Yah Boss yana ƙarasa maganar da yake a wayan.
Ya beƙa mata tattausan farin hannunsa ya furta.
"Bani wayanki"
Dara-daran kyawawan idanunta ta waro gabanta yana faɗuwa, idan ya shiga wajan blocking baiga number ba zaici ƙaniyarta Yau tabbas.
Jikinta yana ƴar rawa ta beƙa masa wayar, tana faɗin.
"Yah Sadeeq zan sha ruwa "
Banza ya mata yana kama fuskarsa sosai.
Fu'adh kuwa murmushi yayi, yana faɗin.
"Ga fridge can Juhainah ki ɗauko mana, ko na ɗauko maki? Dangin mata binsu ake gaki Autarmu"
Juhainah dai ganin Yah Boss ya kame fuska sosai ta matsa kusan Fu'adh a hankali ta masa raɗa.
"Yah Fu'adh ƙarya nake dan yace natafi ne ba basa gu ne fa"
Fu'adh ya ƙyalƙyale da dariya.
Yah Boss
Yah Boss yana ƙoƙarin binckar wayan kira na shigowa number babu suna.
Picking call ɗin yay, yana saka wayan a speaker.
Dai-dai lokacin kuma Juhainah jikinta ya ɗauki wani irin kyarma idanunta suka firfito kamar zasu faɗo ta fasa wani irin mahaukacin ihuuuuu, tana yanke jiki zata faɗa saman table.
Fu'adh cike da tsoron yadda kamarta ta canza cikin ƙaramin lokaci kamar ba Juhainah, da ta gama masa fira yanzu ba.
Da sauri ya riƙeta dan karta faɗi.
Wani irin tauri yaji ya gaza ɗagata sai neman ma faɗuwa suke yi sai da yayi da gaske, ya riƙeta karta faɗa kan table, ɗin da yasan zai iya ji ma ta ciwo.
Yah Boss ya miƙe cikin zafin nama ya riƙeta kafin ta ƙarasa faɗowa kan ƙaton table ɗin da yake da adon Glass.
Da ƙarfin gaske ya ɗagata sama yana nufar room ɗin da yake hutawa.
Wani irin duka take kai masa tana fizgewa tare da wani irin ihu marar daɗi kanajin ihu kasan ba asalin mutum yake yinsa ba...
[03/02 14:02] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo