← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 113

Sashe 24

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar ya katseta yana faɗin.
"Ke! Dalla dataka! Malama, Bana son iskanci da jaraba, naƙi na kashe maki wutar kije ko ina ki nema wanda zai kashe miki wutar ki, tawa wutar a kashe take, yanzu babu kowace mace a gabana wadda nakejin ƙishina zai gushe sai Babyna, ki kama kanki dan Babanki, idan kika sake kirana Allah Zuby zakici uwarki, zan koya maki hankali bani ba ke, a yanzu"

Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, yana ɗora hannunsa akan goshinsa tare da faɗin.
"Oh! My God! Kai zina batayi ba sam a rayuwa, ga shi na rasa nutsuwata daga jin za'ayi bincike akaina, shi ne wannan ballagazar zata kunno min wuta mtswwww!"
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya nufi parlour iyayensa, ya basu labarin a koda wani lokaci za'a basa izinin neman auren Juhainah...



Gidane Mai kyau yanada girma akwai yalwa abubuwan mora rayuwa dai-dai gwargwado.
Parlour ne yanada girma, yasha kayan alatu, sai ƙashi yake tashi.
Mutane Uku ne cikin parlour, dattijuwa fara sai matashin saurayi ɗan kimanin shekara 25.
Matashin cikin shiga mai kyau da kamala Yadi mai tsada baƙi sanye jikinsa, sai ƙamshi yake tashi a jikinsa, idanunsa sunada wani irin kyau da haske.
Kyakyawane, sosai fari mai fasali yanada zubin ƙarfafa, matashin ya haɗu ta ko ina kamar ƙanwarsa.
A nuste yake cin abinci a parlour plate ɗin ajiye akan Center table, saboda cin abinci akan dinning table na basa wuya wani lokacin, shegen miskiline sosai duk da ƙarancin shekarunsa amman yanayin ƙashin girmansa, da mugun son girmansa zaka ɗauka yakai shekaru 29 ko 30, a haife.
Daga ganin yadda yake cin abincin da spoon kasan wayayyene sosai.

Sai ƴar matashiyar budurwa ƴar shekaru 18, ƙanwarsa ta biyu.
Sautin Tv yake tashi a parlour.

Ƴar matashiyar budurwa ce kyakkyawa fara tanada diri ma sha Allahu akwai hanci matsagaici tana idanu, tanada madaidaicin gashi mai kyau, tasha kitson kalba ya zubo har kafaɗarta, akwai class sosai a tare da Surayya kamar ƙawarta Juhainah, duk da Juhainah ta shallaketa a kyau, ita kuma tafi Juhainah jiki saboda ita tanada ƙauri duk da ba sosai ba.
Zaune take akwai alamar gajiya tare da ita.
Mamy ta kalli Surrayya tana faɗin.
"Wai ke Surrayya! Bakya jin yunwa ne? Tunda kika zo kike famar dadaga waya.
"Jamal kanafa ganinta tunda kuka dawo daga school take danna waya batada lokacin cin abinci"
Jamal ya ɗago kansa yana zubawa Surayya idanunsa masu haske da wani irin kyau, baice uffan ba yaci gaba dacin abincinsa.
Duka Mamy ta kai masa tana faɗin.
"Jamal! baka jine?"
Surayya ta turo baki tana faɗin.
"Mamy ina neman number sister Juhainah bata shiga tun jiya Wlh, ni yanzu zanzo na tafi ma gidansu naga ko lafiya"

Jamal ya kalleta yana taɓe baki ya kauda kansa har yanzu bai tanka ba.
Mamy tace.
"Allah yaye maka wannan baƙin halin naka Jamal"
Surayya tace.
"Ameen mamy wlh yaya Jamal sai kinga yadda yake dizga ƴan mata a school ɗinsu ni har tausayi suke bani, wannan ɗan farin nasa da kyau da kuɗin da ilimin suke yiwa ko? Ko ganinsa ƙato basusan yaro bane..."
Ji tayi ya jefo mata gorar ruwa yana mata kashedi da idanunsa.
Baki ta ɓare zatayi kuka Mamy tace.
"Kiyi haƙuri da hakinsa, yayunku ma haƙuri suke da halinsa"
Miƙewa tayi tana hawaye ta buɗe baki zatayi magana ta gansa ya miƙe tsaya, yana ajiye spoon yana ɗaukan gorar ya kai bakinsa.
A guje ta nufi bedroom tana faɗin.
"Allah sai na gayawa Abba"

Jamal ko kallo bata ishe sa ba, ya nufi hanyar barin parlour zuwa ɓangarensa, a hankali cikin daddaɗar muryansa ya furta.
"Mamy nagaji sosai zan huta"

Daga haka ya sa kai ya wuce.
Mamy tace.
"Jamal! Manyan a huta lafiya, ɗazu ƙanwarka ta biyo daga gun awo tace min tana kiranka baka ɗauka me ta maka? Tayi auren ma shekara ɗaya amma baka daina fushi da ita ba? Haka ta sakani gaba tana kuka Wlh."
Kansa ya ɗan waigo ya kalli Mamy murya a tausashe yana faɗin.
"Mamy bacci nakeji nagaji sosai da sosai"
Mamy ta girgiza kanta tana murmushi tace.
"Allah ya huta gajiya Jamaluddin"


Yah Boss

Waigowa yayi yana watsa mata wani Irin kallo, sai da anci Sa'a Juhainah kanta ƙasa bata san yanayi ba.
Muryan mai daɗin sauraro ƙasa² cikin kamewarsa ya furta.
"Ok nazo na ɗauke ki kenan Na sauke ki ƙasan kici abincin Alright?"

Da sauri Juhainah ta ɗago kanta tana sauke dara-daran kyawawan idanunta akan kyakkyawar fuskarsa mai shegen kwarjini.
Idanunta suka faɗa cikin idanunsa mai matuƙar dafi acikin zuciya.
Da sauri ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta, tana ɗan shagwaɓe fuskarta, a hankali cikin kalar tausayi ta furta.
"A'a Yaya kayi haƙuri ina nufin Babies su kawo min abincin, ko Jamilu, idan naci zan ɗan samu ƙarfi naje nayi wanka na cire wannan kayan da baka so, nima bana sonsu Wlh bazan ƙara sakawa ba I'm sorry my brother."

Ta ƙarasa maganar tana kwanciya saman lallausar Sofa, taƙi yarda ta ɗago kanta ta kalleshi.
A hankali ya furta.
"Ni zaki munafunta dan ina kusanki ko? Kece zaki ƙi abinda ni bana so? Munafuka, Idan bana kusa kice i hate you Yah Boss"

Da sauri ta miƙe zaune jikinta yana ɗaukan ɗumi, bakinta yana rawa ta jure ta jefa idanunta cikin lumsassun fararen kyawawan idanunsa, tana faɗin.
"Allah kiyaye bazan taɓa tsanarka ba my brother wallahi ina sonka yaya Sadeeq, bazan iya tsanarka ba, baki bazai taɓa faɗin hakan ba, Ni Ko tunanin hakan ma ba..."
Kallon da ya watsa mata yana buɗe mata idanunsa ne, ya sakata rufe nata idanun saboda har gashin jikinta tashi suke yi, wani bala'in sanyi takeji na huɗa dukkan kofofin jikinta na ratsa asalin fatarta.

Bata zataba bata kuma tsammaci hakan ba, taji tattausan tafin hannunsa cikin tafin hannunta ya miƙar da ita tsaye Yana kama kunnenta ya murɗa can ƙasa² cikin natsuwa murya mai sautin amon daɗi ya furta.
"Ni zan maki ƙarya ne? Naji kina faɗin i hate you Yah Boss, Ni ɗan Fashine ko ɗan dabane ko ɗan kidnapping ne kike cemin Boss?"
Hawayen azaba ta fara tana kallonsa ta shagwaɓe fuskarta sosai tana riƙe hannunsa da ya murɗa kunnenta a hankali ta furta.

"Wallahi ban faɗa ba yayana ina sonka Allah i love you ni bazan iya tsanarka ba ko kasheni kake ina farfaɗowa..."

Jajayen laɓɓanta masu kyau da wani irin kauri da suka ƙara mata kyau ya sanya yatsunsa biyu ya kamo ya murza yana kame fuska sosai a hankali ya furta.
"Sakar min hannu kuma ki kama min hawayen munafurci, bana son I love youn ƙarya, Khairat da Sumy Mustapha Umar Nasir wannan su suke ƙaunata su suke gudun ɓacin raina, basa sakani ciwon kai, ke kama kici gaba da abinda kikaga dama, Bilkisu, nine maganinki idan baki fasa ba bazan fasa gana miki azaba ba"
Ya ƙarasa maganar yana jan hannunta ya nufi ƙofa da ita.
Shagwaɓe fuska tayi sosai tana hawayen tace.
"Don Allah Yaya Sadeeq kayi haƙuri ka yafe min, Ni Wlh bana son ɓacin ranka Allah kuma duka nafisu sonka suma sun sani,, nayi alƙawarin zan fasa saka ka ɓacin rai, Kuma ai aure ma zaka min kwana..."
Bakin ya buge mata yana sake murɗa kunnenta, yaja hannunta.
A hankali take shasheƙar kuka tana faɗin.
"Don Allah kayi haƙuri bana so na fasa..."
Kallon da ya mata ne ya sakata haɗiye sauran maganar tana ƙasa da kanta.
Sakin hannunta yayi yana faɗin.
"Koma ki zauna, za'a kawo maki abincin."

Ya ƙarasa maganar yana ciro wayansa ya danna number Fu'adh yakai kunnensa yana juyawa ya nufi ƙofar barin parlour, a hankali cikin nutsuwarsa yake faɗin.

"Yas inaji an fara binciken Fu'adh? yarinya kamar zata iya kai kanta gidan auren ba'a ɗaura ba, ganinan zuwa bari na canza kaya mu fita tare, Ammar zai zama mijinta idan baida aibu in sha Allah, gwara ta tafi kar ta saka min hawan jini..."
Ya ƙarasa maganar dai-dai yana buɗe ƙofar parlour zai fice.
Juhainah ta bisa da ido jikinta na ɗaukan rawa, zuciyarta na wani irin bugawa, hankalinta ya tashi sosai jin abinda yake faɗa, tsoronsa ya hanata tayi masa magana har ya fice ya rufo mata ƙofar.
Tsakiyar parlour ta zube ƙasa tana fashewa da kuka tana faɗin.
"Wayyo Allah nah! Na shiga uku! Wlh bazan auri Ammar ba ni Babban mutum nake son na aura Shuga Daddy..."
[10/01 14:20] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 14*

Surayya cikin shiga ta kece raini ta fito tana baza ƙamshi, Bluetooth manne a kunnenta magana take anutse tana sakin murmushi, sanye take da Black Abaya mai kyau da tsada, tana riƙe da handbag ɗinta ta iso parlour tana kallon Mamy tace.
"Mamy natafi gidansu Juhainah, idan naje zanci daddaɗar girkin Maah"
Mamy tace.
"Au mu nan masu girkin basu iya ba? Gwara ma nan ni ina girka wa wannan fitinannan yayan naki da baya cin girkin masu aiki, can kuwa dole dai masu aiki suke yi tunda Abubakar ya hana mahaifiyarsa shiga kitchen, idan bakici na Mamanki ba zakije kici na mamar wasu ai"

Surayya tayi murmushi tana katse kiran da yake shigowa wayanta bayan yanzu daman ta gama wayan.
"Mamy natafi bari na saka direba ya kaini sai ya dawo idan na tashi zan kira sa yaje ya ɗaukoni"

Mamy tace.
"Kin sanar da mahaifinki dai ko? Ba dan kinga baya ƙasar ba kiyi ta fita, Wlh zan maki haɗi da Jamal"
Surayya tayi murmushi tace.
"Allah Yaya Jamal sona yake cikin ƙanninsa baya zaluntata sai rana ta ɓaci"

Mamy tace.
"Ikon Allah! Ƙanni ca nake ku biyu ne ɗaya na gidan mijinta?"

Surayya dai sakai tayi ta wuce tana murmushi.

Kai tsaye ta saka direba ya kaita gidansu Juhainah.
Chapter 24 · 0% Book details