← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 113

Sashe 34

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


Juhainah tun yamma takejin cikinta na murɗawa, harda ciwo² amma ta basar sunata aikin Game da ƴaƴanta.
Ai zuwa bayan sallar Maghreb sai zawo bata minti 20 sai ta shiga bathroom.
Khairat tana lure da ita, ta basar ai tasan mugun cin da tayi dole tayi Gudawa.

Misalin ƙarfe 9 na dare.
Maah Papa Nasir Hanifah da suka zo gaishesu duk suna zazzaune.
Kira ya shigo wayan Papa.
Maah ta beƙo masa ajiye akan Center table.
Yayi picking call ɗin yana faɗin.
"Assalamu alaikum Hajjah Bilkisu! Ya gida da baƙo?"
Hajjah Mama tana murmushi tace.
"Yakubu! Al bishirinka, ɗana ya amince fa har sun daidaita da barrister Zarah, sun tsayar da magana rana ya tayau za'a ɗaura aure ta tare kuma, wlh yau ina cikin matsanancin farin ciki, ya koma Yolan tun yamma, murna ta hanani dakatar da shi."
Papa yace.
"Alhamdoulillah! Na daɗe banji daɗin danaji yau ba, Nagode sosai Hajjah Bilkisu Allah yabar zumunci"

Hajjah Mama tace.
"Karka sake gode min ɗanane fa, ba ɗan wani ba, sai ku fara shirin zuwa tunda sun tsayar da magana tsakaninsu."
Papa yace.
"Ma sha Allahu Allah ya kaimu ga Zainab nan"
Ya ƙarasa maganar yana ba Maah wayar.
Maah tayi sallama tana gaisheta.
Hajjah Mama ta amsa tana faɗin.
"Barkanmu Zainab Abbah dai Allah ya temake mu ya amince da zabin dana masa mace mai hankali"
Maah harda ƙwallar farin ciki tace.
"Alhamdoulillah! Hajiya Bilkisu naji daɗin labarin nan sosai..."

Hira sukayi sosai har tana faɗa masu ashe Juhainah aure za'a mata, Maah tace Eh duk da batan meke faruwa ba...


Anguwan
Shagari phase

Misalin ƙarfe 12:30 na dare.
Yah Boss yana cikin bacci saboda wani lokacin yana bacci da wuri sbd idan ya fara ƙarfe biyu ko uku na dare baya sake kwanciya sai bayan sallar asuba, ko lokacin Khadijah haka rayuwarsa take, idan ba larura ba bai taɓa raya dare yana bacci ba.
Yanada addini sosai da bautawa Ubangijinsa da Naiman gafara da addu'ar kariya shi da ya'yansa.

A hankali yaji special Phone ɗinsa da baya kashewa da garaje tana ringing.
A hankali ya ɗan motsa yana buɗe lumsassun idanunsa, bakinsa ɗauke da salati.
A hankali ya beƙa hannu cikin duhun saboda baya son bacci da haske ko kaɗan.
Wayan ya ɗauko da take ajiye gefensa saboda girman Royal Italian Bed ɗin.
Sunan Khairat yaga yana yawo.
A hankali ya furta.

"Babu lafiya Khairat yanzu? Fitinanniya nan taci wata masifar kenan? Ya Rabbb!"

Ya ƙarasa maganar yana picking call ɗin.
Kukan Khairat yaji cikin tashin hankali tana faɗin.
"My brother Juhainah babu lafiya zata mutu bansan ya zanyi ba, amai take da ciwon ciki..."

Katseta yayi yana faɗin.

"Me taci?"

Khairat da take riƙe da Juhainah ta galaɓaita, cikin amai ko idanunta bata iya buɗe wa tace.
"Da safe taci farfesun kayan Ciki dayawa da waina, da rana taci farfesun Kifi dayawa tasha dafaffiyar madara sosai na hanata taƙi tanata min rashin kunya, har na ɗan doke ta..."

Katseta yayi ta hanyar cewa.

"What?

Kice kin mata mugun bugo dukan ya koma mata cikin ciki ko Khairat?"

Idanunta cike da hawaye tace.
"Wallahi tallahi ka duba yaya a wayanka a parlour ne na ɗan kai mata dukan saboda tanata min fitsara wai na tattara kayana na tafi gida bata son saka ido na takurata sai maganganu take min na rashin kunya..."

A hankali ya furta.

"Sai kika jibgeta kamar kin samu jaka ko?
Oh! My God! Ai daman nasa sai tayi wani rashin jin da zai damu mutane kuma, shiyasa na kawoki, ashe keku ma naɗarta kikayi.

Yanzu tana ina? Bani ita"

Khairat tace.
"Gata a cinyata bata gane komai fa, gamu cikin amai wlh tsoro nakeji idanunta sun juye Yaya bansan mi zanyi ba, Wlh ba dukanta nayi ba"

Ta ƙarasa maganan cikin kuka dan tana tsoron haɗuwar su yayan nata, ga Juhainah na neman macewa.....
[17/01 13:32] أم الأمين😘: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U
👆🏽
_*Mutanen Kirki Kuci Gaba Danna Min Followers, Zan Dinga Antayo Muku Zafafan Tsofaffin littattafai Na, Kuna Chanawa Abinku😂💃🏻🫣*_

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 19*

Yah Boss ya miƙe zauna yana jingina bayansa da allon Bed ɗin, ya ɗauko ɗayan wayansa ya kunna ya danna number Dr Majid.
Cikin rashin Sa'a bata shiga, ya danna number Dr Nafisa matarsa.
Cikin Sa'a ta shiga, tana fara ringing aka ɗauka tare da sallama.
A nutse ya amsa yana faɗin.
"Dr Majid wayansa switch Off Kuna tare ne? "
Dr Nafisa tace.
"Ƙarfe 8pm ya sauka ni na hau ina hospital yanzu Yallaɓai lafiya?"
Yah Boss a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Ki samu ko norses biyu kuje can 80 unit Juhainah batada lafiya, ciwon ciki da amai take, ku gaggauta saboda tana matse."

Dr Nafisa tace.
"Subhanallahi Ok yallaɓai in sha zamuje yanzu"
A hankali ya furta.
"Ok thank you"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.
Ya maida ɗayan wayan a kunnensa a nutse ya furta.
"Yanzu Dr Nafisa zasu zo na faɗa mata matsalar, kibar kukan ya isa, Juhainah bata da nustuwa, ga cin asara bata wani cigaba, kullum a bushe, sai masifa ta saka a gaba, gobe da safe zan shigo Allah ya bata lafiya."

Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.
Khairat ta gyarawa Juhainah kwanciyarta akan cinyarta tana faɗin.
"Juhainah! Ki buɗe idanunki ya kike jin jikin naki?"
Ina Juhainah azabar ciwo nacinta bata gane yaren Khairat dan ko idanunta bata iya buɗe wa.

Ba'afi minti talatin ba Dr Nafisa suka iso gidan Yah Boss, ba shamaki aka buɗe masu gate suka wuce saboda Yah Boss ya kira security's ya faɗa masu, Dr Nafisa zata zo.
Khairat tanajin ƙaran doorbell a ƙasa ta sauko tazo ta buɗe masu, Dr Nafisa ita da norses biyu suka taho.
Ko Dr Nafisa da taga halin da Juhainah take ciki ta tsorata.
Gwaje² ta fara mata kafin ta fara bata temakon gaggawa, allurai ta mata aka ɗaura mata drip.
Khairat ko ta gyara parlour da Juhainah tai masa amai sosai.
Dr Nafisa ta rubuta magunguna ta ba Khairat tana faɗin.
"Amsa zuwa safe sai kije can asibitin ki amso a pharmacy, koma zamuyi akwai marasa lafiya sosai yau, da suke matse Yanzun ma nazo saboda dole abu na gida ne, zan dawo gobe da safe idan na sauka a aiki sai na duba, ai zaki iya cire mata drip ko?"
Khairat ta amsa tana faɗin.
"Eh Na iya, sannu Aunty Nafisa mun gode Allah ya saka da alkhairi"
Dr Nafisa ta amsa da.
"Ameen ya Rabbi"

Tare suka sauka Khairat ta rufe ƙofar, ta dawo ta kwanta saman kujera tana kallon Juhainah da take baccin wahala.

Ammar
Cikin kwana biyu nan Ammar cikin tashin hankali yake baya samun wayar Juhainah, ga shi har yanzu shiru babu wanda ya nemasa akan maganar auren Juhainah.
Yanzu ma tsakiyar daren nan zaune yake sanye da kayan bacci, wayarsa a hannunsa yanata kiran Juhainah baya samunta.
Cikin Wata irin murya mai ɗauke da tashin hankali yace.
"Wai mi yake faruwa ne?. Baby kewarki zata kasheni Wlh"
Ya ƙarasa maganar yana danna number Surayya, cikin Sa'a tana ringing, sai dai tana bacci, har kiran ya katse ba'a ɗaga ba, kira uku yayi ba'a ɗaga ba tana bacci wayan na Silent.
Ammar kasa bacci yayi har kusan asuba yana saƙe², ga yana shakkar Yah Boss bare ya sake komawa can gidan da safe ko zaiga Juhainah hankalinsa ya kwanta.

Washegari
Da safe ƙarfe shida da ƴan mintina, Surayya ta ɗauki wayanta ta ga kiran Ammar.
Ƙirji ta dafe tace.
"Cafff! Kira tsakiyar dare lafiya Ammar?"
Ta ƙarasa tana kiran number nasa.
Cikin bacci yaji ringing ɗin wayansa ya buɗe yana matsowa ya ɗauki wayan, ganin Surayya ce ya ɗaga kiran yana kai wayan kunnensa yana faɗin.
"I'm sorry sister Surayya na takura ki jiya ko?"
Surayya ta taɓe baki tace.
"Lah! Babu komai Ammar nayi bacci ai da na ɗauka, ina kwana"
Ammar ya amsa da.
"Ba lafiya Surayya, dan Allah ya za'ayi na samu nayi magana da Babayna ta hanyar ki?"
Surayya a ranta tace.
"Ai kaida magana da ita har abadan in sha Allahu"
Amma a zahiri tace.
"Ayyah! Toh inaga fa ko ka samu damar ganinta sai bayan an saka maku ranan aure tana can gidan brother ɗinta, ya hanta fita ko ina"
Ammar cikin jin daɗi yace.
"Kenan kinji maganar auren namu?"
Surayya ta shirya ƙarya tace.

"Eh mana ai anata bincike akanka an kusa cewa ka fito, dan haka ka kwantar da hankalin ka, Juhainah ma kai take so, kwanan nan, dai zakuyi aurenku"

Ammar tsabar farin ciki harda ihu yana faɗin.
"Gaskiya naji daɗin labarin nan sosai sister Surayya, tukuicin ki na musamman ne in sha Allahu, Nagode sosai..."
Surayya tace.
"Nagode Ammar sai anjima."

Surayya na katse kiran Zuby na kiran Ammar.
Tsaki yaja yana ɗaukan kiran cikin tsawa yace.
"Allah wadaran mutumin da baida zuciya wlh, Uwar me zan maki da sassafen nan? Ke wai kare ya cinye maki zuciya ne?"

Zuby tana zubar da hawaye tana riƙe marata tace.
"Don girman Allah Baby kamin rai, ka temakeni, nayi maka alƙawarin idan ka kashe min wannan wutar bazan ƙara kiranka ba, matuƙar ba kai ne ka kirani ba, don Allah kayi haƙuri"
Ammar yace.
"Ƙarya kike munafukar banza, kece fa da jaraba, ko na miki abinda kike son bazaki shafa min lafiya ba, dan haka bazan yi ba ki rabu dani mayyar banza..."
Ya faɗa yana katse kiran ya yi kwanciyarsa.
Zuby kuwa tayi jifa da wayar tana kwanciya rigingine tana sakin kuka, Ammar na wahalar da ita a rayuwa...



Misalin ƙarfe 9 Juhainah kwance saman bed ɗin Suhaima, yayin da yaran suna can ƙasa parlour.
Khairat tana zaune gefenta ta gama waya kenan da Fu'adh.
Ƙofar parlour aka ƙwanƙwasa Khairat tana kallon ƙofar tace.
"Yes Amina shigo"
Amina ta shigo parlour ta zarce bedroom.
Ƙofar bedroom ɗin ta buɗe ta shigo da Sallama ɗauke da tray'n kayan breakfast.
Ajiye wa tayi akan ɗan ƙaramin table mai kyau tana faɗin.
"Ya mai jikin? Allah ya ƙara sauƙi"
Khairat ta amsa da.
"Ameen ya Allah taji ma sauƙi sosai"
Chapter 34 · 0% Book details