Sashe 56
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya ɗaga masa hannu yana faɗin.
A'a umarni nake baka, bakai zaka bani ba.
Gwara tazo gidanta ta tare ayi magani, ai kaima sbd ta baka tausayi kayi recording ka kawo mana, in sha Allahu zan kira ko na ɗauki Kawunka Giɗaɗo muje, haka ma za'ayi gobe zamu je, kayi fatan Alkhairi kawai.
Jamal wani irin yawu mai ɗaci ya haɗiye a han yana amsa da.
"Ameen Amin Allah yasa haka yafi alkhairi bari naje nayi wanka kafin sallar isha'i"
Surayya taja bakinta ta tsuke batayi magana ba sai da Jamal ya fice ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin.
"Mamy Abba wannan fa ya ɗauko ne dan kuce ya fasa aurenta, sai ya jajiɓowa kansa auren ma baki ɗaya.
TOH inaga bayan ta tafi police station gun Yah Sadeeq abun ya tashi, daman tun gida naga alamun kamar bata da lafiya"
Mamy tace.
"Barshi Surayya na gane ai, idan kika ga ba'ayi auren ba nan da sati biyu wlh ɗaya ne ya mutu cikinsu dani yake zance Jamal"
Abba yana kallon ta yace.
"Sadiya! Baki da haƙuri Wlh, ke Surayya kina haɗa su ko? Wlh zan saɓa maki"
Surayya ta shagwaɓe murya tana matsowa jikin Abba tace.
"Wayyo Abbana kayi haƙuri auren nasu nake so, ƙawata tun yarinta babu abinda ya taɓa haɗa mu inason zumuncin mu ya ɗore har ya'yan ƴaƴan mu...."
★
Juhainah Tv ta kunna tayi zamanta tana kallon tashar Zee Alwan series India da larabci.
Babu wanda ya fito cikinsu bare yaganta.
Juhainah
Tana zaune tana kallon Jamilu ya gama shirya abincin dare yakai dinning room ya jera, wayarta ta kalla ta ga ƙarfe 8 dai-dai.
Fuska ta kwaɓe sanin Yah Boss bai dawo ba.
Yana gama jerawa ta miƙe tana faɗin.
"Jamilu!"
Da yake da ƙarfi ta kirasa har su Zarah suka ji.
Ramlah da Azizah suka fito parlour Zarah ba kowa.
Kofar suka buɗe a hankali.
Juhainah suka gani cikin shigar gayu, tana tafiya cikin ƙwarewa tana kaɗa ɗan ƙaramin ƙungunta.
Ramlah dariyar da ta kamata ta danne mamakin da take na yarinyar.
Ai kuwa bata san ya akayi ba ta fashe da dariya.
Aziza ta kalleta tace.
"Ana wannan halin kike iya dariya Aunty Ramlah?"
Juhainah jin ana dariya ta tsayar da tafiyar ta juyo fuskarta shafe da toka.
Dara-daran kyawawan idanunta ta zuba masu, a hankali ta tako har ƙofar tana riƙe ƙugunta tace.
"Ni kuka mara ba? Yanzu kuma dariya ba? Very good kuci gaba, da kunsan halina bana yafiya da bakuyi ba Wlh"
Ta juya tana karya ƙugunta ta nufi gun Jamilu tana faɗin.
"Jamilu! Wannan baƙin amaryar marar daraja ina son ka kai masu abincinsu parlour su karka bari su je mana kan dinning"
Jamilu ya amsa da.
"Ok alright"
Juhainah ta kunna waƙar India.
RANU BOMBAI KI RANU.
Ai kuwa ta fara rawa sak yadda suke yi tana juya ɗan ƙaramin ƙungunta tana masu gwalo.
Aziza takaici da baƙin ciki ya sakata juyawa ta koma ciki.
Zarah da take tsaye tun lokacin da ta fara masu tijara ta fito daga bedroom.
A hankali tace.
"Tabbas wannan yarinya ko dai ƙanwarsa ta biyo wasu danginsu ko kuma da gaske aurenta yake. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wace irin jarabawa ce wannan? Yar cikina zata juyani a gidan nan kenan."
Ramlah ta kama hannunta suka nufi bedroom tana faɗin.
"Wannan yarinyar fa ƴar bala'i ce.
TOH nace ko dai danginta na Masar ne?
Wannan yarinya kamar dangin fir'auna."
Zarah dai batace komai ba saboda kanta yake sarawa.
Yaganah hawayen takaici suka fara zubo mata, tana kama hannun Zarah cikin baƙin cikin halin da ta jefa su tace.
"Wannan auren naki mi sunansa? Yanzu akan ki rayu a Jigawa cikin farin ciki kina aikinki baki rasa masoya ba, kika zaɓi auren haɗi, wlh Aunty Zarah mai gidan nan baya sonki, kalli can parlour su hotonsa ne dana matarsa wadda ta rasu da ya'yansa babu alamar zai cire hotonta, haka har yanzu bai ko zo inda muke ba, bare yasan wa da wa suka rako masa mata ya masu bangajiya.
Kuma inada yaƙinin bazai zo ba..."
Inna Laure tace.
"Kunsan abinda nake so daku?"
Ramlah ta girgiza kanta.
Inna Laure tace.
"Mu gaggauta barin gidan nan gobe da asubar fari, banga anfanin zamanmu ba, ita dole zatayi haƙuri ta zauna ko dan gudun bakin Mutanen Duniya, gaskiya da nasan abinda zan iske kenan bazan zo ba"
Aziza tace.
"Wlh yaban mamaki na ɗauka shi ɗin mai ilimin addini ne sosai ga na Boko ai ko baka son mutum bazaka saka a wulaƙanta shi haka ba"
Zarah ta fashe da kuka komai Yana gama fita aranta har cikin zuciyarta take son Yah Boss amma yanzu taji zata iya haƙuri da shi ko dan cin mutuncin da aka yi wa ƙannenta da ƙawarta da ƙanwar mahaifinta....
★
Suhaima tunda ta haye Stairs bata sake sauka ba, hajjah Mama kuwa abin duniya ya isheta fushin Suhaima.
Sai bayan sallar isha'i Papa ya shigo.
Cikin farin ciki ya tarbi yayarsa, suka gaisa cikin karramawa.
Yanzu ma zaune suke a parlour sunata fira.
Maah Hajjah Mama Papa Khairat Al'amin.
Anutse ya shigo parlour bakinsa ɗauke da sallama.
Hajjah Mama ita ta fara amsawa tana washe baki.
Al'amin ya miƙe da gudu ya tarbi Dadd ɗinsa.
Sama ya ɗagasa yana sakar masa tattausan murmushi, tare da sumbatar kumatunsa ya manna ɗansa ƙirjinsa yana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya raɗa masa.
"My Babies ina My Suhaima?"
Al'amin shima yayi wa Dadd ɗinsa raɗa.
"Tana Upstairs bedroom ɗin Aunty J fushi take da hajjah Mama"
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a hankali ya furta.
"Ok kaje ka kira min ita kace zamu wuce gida yanzu, Aunty J ɗinta na can gidan"
Ya ƙarasa maganar yana sauke shi.
Ai kuwa da gudu ya nufi hanyar Stairs.
Hannayensa ya zuba cikin aljihun jallabiyar jikinsa.
Anutse ya ƙaraso ya zauna kusan Hajjah Mama.
Khairat ta gaishesa tana masa sannu da zuwa.
Anutse ya furta.
"Tashi ki shirya mu wuce.
Hajiya Mama ina wuni? Ya gajiya kuma?
Papa! Maah barka da dare ya gida?"
Hajiya Mama ta amsa da.
"Alhamdulillah! Abbanah, kaga Zainab fushi take dani, tunda nazo gidan nan ta haye Beni"
Papa ya amsa yana faɗin.
"Ai sai haƙuri Aunty Bilkisu Suhaima yarinya ce"
Maah tace.
"Ai zasu saba tunda zasu zauna gida ɗaya."
Yah Boss ya riƙe hannun hajjah Mama yana faɗin.
"Haƙuri zamuyi da Suhaima yarinta ne"
Hajjah Mama tace.
"Haka ne, Abbah gobe zamu wuce in sha Allahu, ƙawarta tana da aure daƙyar mijin ya barta tazo ta baro ƙaramin yaro sabon yaye. Muje ku gaisa nasan halinka ba lallai ka shiga ba muna nan, kaga kar su ga ba'a kula dasu ba.
Idan yaso daga baya sai kuzo ta gaishe dasu Zainab."
Ba yadda ya iya amsa
.
"Ok hajjah Mama ba damuwa"
Papa yana murmushi yace.
"Allah ya maka albarka"
Anutse ya amsa da.
"Ameen ya Rabbi"
Khairat ce suka sauko tana riƙe da hannun Suhaima.
Yayin da Al'amin yana riƙe da hannun Suhaima ɗayan.
Yah Boss ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Suhaima ta ɓata fuska sosai.
A hankali ya miƙe yana faɗin.
"Sai da safen ku, hajjah Mama muje sai ki kwana da jikokin ki"
Ya ƙarasa maganar yana isa ya kamo Suhaima ya rungumeta, ya zare hannunta daga hannun Khairat yajata suka yi gaba yana mata magana a hankali.
Maah idanunta taji suna ƙoƙarin kawo ruwa ta maida.
Papa ya miƙe yana raka hajjah Mama.
Maah daga zaune ta mata sai da safe.
Ko a mota Suhaima tana gaba gun Yah Boss saboda shi ɗaya ya fito yana driving da kansa.
Da fira ya dinga janta, But taƙi tanka masa tana dai binsa da kallo.
Hannunta ɗaya ya riƙe yana faɗin.
"Ki nutsu ai mun gama magana my Babie bana son ki damu Ok?"
Kai ta gyada masa batayi magana ba....
Juhainah
Sai da ta gama tiƙar rawa ta zauna tana maida numfashi tana ƙyalƙyalewa da dariya tana faɗin.
"Ai Wlh kaɗan kuka gani, ba mari na kukayi ba, kuka kirani da ƙaruwa Turawa, Wlh sai na muku abinda bazaku manta ba acikin rayuwarku, kunci bashi akan amaryarku zan rama."
Tana idar da maganar ta miƙe ta nufi dinning room.
Cika tumbinta tai dam, ta dawo parlour ta zauna tana kiran Surayya a waya
Ko yanzu Yah Boss bai tsaya danna doorbell ba ya buɗe da key suka shiga yana riƙe da hannun Suhaima, Khairat na riƙe da hannun Al'amin.
Lokacin Surayya tana bedroom ɗinta suna waya da Farid gayen da yake haukan sonta, yake kashe mata maƙuɗɗan kuɗi kamar baya son dukiyar sa, sai da Abba da Jamal suka taka masa Burki akan basa buƙatar hakan, zuwan ma Jamal ya dakatar da shi ya basa sau ɗaya a ƙarashen wata saboda ta samu tayi karatu sosai.
Surayya tana ganin kiran Juhainah ya shigo tace masa ya katse kiran zata amsa kiran Juhainah.
Tana ɗaga kiran Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya, tana faɗin.
"My sister Surry yau fa na gasawa amare Ayah a hannunsu, ana can ɗaki ana fama da zafin zuciya, ga hukuncin da Yah Boss zai ɗauka akan marin da suka min.
Wai harda cemin karuwar Turawa."
Surayya tace.
"Kambuuuuu! Suka marar min ke? Lallai ki ce igiyar aurenta tana nan tana yawo tsakanin Yola da Jigawa.
Tabbas ƙilama ya tsinke ɗaya a ransa"
Juhainah ta sake bushewa da dariya tana faɗin.
"My sister Surry Nima haka nace acikin zuciyata, ko ya mata horon da yafi saki ba.
Baƙin ciki fa suke an ganni yarinya bugon London ake baƙin ciki, su basu san ni ƙiba bata burgeni, nafi son kaina a haka Mijina ya ɗaukeni kamar ya ɗauki Baby ƴar shekara bakwai, na zuba iskancina son raina a dinga goyona ina ɗarewa jikinsa a ko yaushe bacci ma sai samansa tunda banda...."
Ƙamshinsa ta shaƙo kafin tayi wani yunƙuri har taji salallamin Hajjah Mama tana tafa hannayenta tare da faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Oh! Ni Bilkisu me nakeji a bakin Bilkisu? Abbah kana ina Bilkisu ta lalace har haka kuna zaune acikin Yola duk kuna aikin me? Kaji kamalan da take irin macen da tayi karatun aure shekaru Ashirin baya"
Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.