← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 113

Sashe 91

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

My Babies Suhaima! Amiin! Ga Aunty J."
Juhainah tai saurin faɗin.

"My brother please idan na warke zanzo na sameka gida akwai maganar da zamuyi Please, ka taimaka min marainiya nake son ɗaukan nauyinta kai zaka mata komai nida Maah zamu kula da sauran tarbiyyarta, idan nazo zan maka bayani."

Yah Boss a hankali ya furta.
"Alright, Bilkisu sai kinzo naji bayanin, za'ayi mata komai duk abinda ya dace."

Amsa Babie Suhaima ga Aunty J"
Cikin farin ciki tace.

"Please Yah Boss ka bari nayi maka godiya, Allah ya albarkaci rayuwarka da zuri'arka baki ɗaya, ya kare ka ya ƙara maka buɗi, daman nasan duk abinda nake so a duniya kai ɗaya ka isheni share min hawaye ɗan uwana, Ubangiji ya kare ka da kariyar sa."

Ta ƙarasa maganar tana sakin wani irin kuka mai ban tausayi, murynta a dishe.

Iskar bakinsa ya furzar a hankali ya furta.
"Ameen Aunt Bilkisu yi Shiru mana, ya isa Kinji?"

Cikin kukan tace.
"Yah Boss! Ka barni nayi kukan nan inajin sauƙi acikin zuciyata ne, ina cikin danuwa, Wlh bana son Jamal dole zan zauna da shi, Sbd nasihar Papa da kuma kai, bana son na tsallake abin da ka zaɓa min, da kuma nasihar mahaifina, amma my brother zuciyata na min zafi, sai dai nayi alƙawarin juriya da amsar ƙaddarata..."
Ta ƙarasa maganar tana kuka sosai.

Da wani irin sauri ya janye wayan daga kunnensa, ya manna wa Suhaima a kunnenta, ya kamo hannunta ya ɗora akan wayan, a hankali ya furta.

"Oya My Babies kuje stairs kuyi fira da Aunty J, ki lallasheta ta daina kukan, kar kanta yayi ciwo ki tabbatar kin sakata farin ciki kafin ku gama wayan Ok?"

Ya ƙarasa maganar yana maida hankalinsa akan Maah.
Suhaima ta miƙe ta kamo hannun Al'amin suka nufi hanyar Stairs tana faɗin.
"Aunty J kuka kike nima kinaso nayi kukan ne? Me ya sameki muryanki ta shaƙe haka?"

Juhainah da sauri tace.
"A'a na fasa my Babies Karki yi kukan, ina My Amiin? Fatan kuna lafiya?"
Suhaima tace.
"Alhamdoulillah! Zan ce dai amma bakya kusa wani jin daɗi zanyi Aunty Juhainah, mura kike ne?"
Juhainah ta saita muryanta tace.
"Eh My Babies, ina My Amiin? Yaushe zaku zo min Please?"
Suhaima tace.
"Ɗazu da safe muna breakfast nace wa My Dadd ya kai mu yace muyi haƙuri har ki kwana biyu, kar ace dangin ki sun fiye zuwa, weekend mai zuwa zan je na kwana in sha Allahu Aunty J, ga Amiin kuyi magana"

Ta basa wayan tana riƙe da hannunsa suna taka Steps.
Amiin yace.
"Aunty J ina kwana ya jikin? I miss you Aunty J I love you..."

Juhainah tayi murmushin farin ciki tace.
"Miss you too My Al'amin Babie..."

Haka suka haye Stairs sunata fira da Juhainah, sai gata ta saki jiki harda ƴar dariya take yi, ta ƙoƙari.

Hakan ya ma Aunty Sumy daɗi ganin ƙanwar tata ta saki jikinta.
Sai kalaman da taji tana faɗa bata son Jamal, ta bata mugun tausayi, amma bazata nanu mata ba, dan karta ta tsira masa iya shege.

Maah ta sake riƙe hannun Yah Boss tace.
"Abbah! Akwai damuwa ne? Naga Bakinka kamar akwai magana a miskilancin ya hana kayi magana?"

Yah Boss a hankali ya furta.
"Inasu Hajiya Mama ne? Bana jin motsin bakin gidan? Ina Khairat?"

Maah tace.
"Ai muna gama breakfast dukkan su sun dunguma gidan Kawunku Nasiru, Khairat ai itane gaba² tace can zata kwana ma, tafi wata biyu bataje ba."

Kai ya jinjina a hankali ya furta.
"Nima wannan fitowar inada niyar zuwa can, nakai wata banje ba, da gidan Mom Lubnah na mata bangajiyar biki.
Maah! Zan saki matar nan, zata ɓata min tarbiyyar ƴaƴana, sam abinda take baya cikin tsarin irin matar da nake son zaman aure da ita, just na rabu da ita na samu nutsuwa. Because raina ɓaci yake idan ina ganinta."

Maah tace.
"Subhanallahi Zarah? Me tayi maka? Please kayi haƙuri Karka saketa yanzu auren fa bai rufe wata ba, wacce ta kawota ko komawa batayi ba, baka gudun bakin mutane?"

Yah Boss a hankali ya furta.

"But Maah a wannan zamanin baka biya ta mutum, kayi abinda zai fisheka, wanda baya Ƙaunarka ba abinda zakayi ka burgesa, because baya Ƙaunarka.
So banga anfanin zamanmu ba, tunda Bazan iya kyautata mata ba, nayi biyayya na aureta iya zaman da zan iya da ita nayi, alright"

Maah ta sauke ajiyar zuciya tana riƙe hannunsa a hankali tace.

"Abbah! Shi aure raine da shi, bazan goyi bayan ka kashe aure ba, sai dai bazan hanaka abinda kayi niya ba, amma ba hannuna a ciki."

Ɗan ƙaramin murmushi ya sakar mata kamar yadda ya saba mata, ya sumbaci hannun nata a hankali ya furta.

"Maah! Haka ma Nagode, kiyi haƙuri kinsan halina bana ƙin abu banza², sannan bana son abu banza² sai nagartacce.

Zan leƙo gidan Kawu Nasiru, daga can zan je gidan Mom Lubnah. Sai na wuce gidansu Al'amin jiya yake faɗamin Abbu baida lafiya, yaƙi aje asibiti, wai ciwon kaine kawai, zanje na lallaɓasa muje asibitin mu a dubasa.

Sumayya tace zata zo gidana, tunda taje gidan Bilkisu batada lafiya zan kirata nace daga can ta wuce gida ta huta, gobe sai taje, yaran zasu tsaya har na dawo sun ce can zasuyi weekend."

Maah tace.
"Toh Abbah sai kazo a dawo lafiya, ai gaishe da Alhaji Hisham ɗin, Allah ya basa lafiya, ba zakaci wani abun ba?"

Anutse ya furta.
"A'a Maah, sai na dawo"

Ya ƙarasa maganar yana juyawa cike da nutsuwarsa yake takunsa.

Maah ta kafe dara-daran kyawawan idanunta irin na Juhainah akan Yah Boss.
Idanunta taji sun kawo ruwa.

A hankali ta ɗaga hannayenta tana zubo hawayen, ta fara addu'a.

"Ya Ubangijin sammai 7 da ƙasai 7, Ya ALLAH kaine mai sakawa kaine mai hanawa, babu wani abu da mutum zaiyi ba tare da amincewar ka ba, Ya Hayyu Ya Qayyum, ina tawassali da tsarkakan sunayen ka 99, ina riƙon ka, ka sauƙaƙawa Abubakar wannan zuciya ta raunana, ka cire masa tunanin Khadijah ko zai ga wacce zai so yayi auren soyayya, irin na sauran ƴan uwansa, ya ƙara samun zuri'a, idan kuma Zarah alkhairi ce garesa ka sassauta wa zuciyarsa a kanta,Ya Raheem ka dubemu...."

Aunty Sumy bata bar gidan Juhainah ba sai da ta gwada mata yadda zata yi aiki da magungunan gargajiyar da ta kawo mata.

Ƙarfe sha biyu harda rabi Aunty Sumy ta tafi, da su Surayya suka zo ta lallaɓa ta tafi, anci Sa'a batayi rigama ba, Aunty Sumy tana tafiya, Surayya ta kunna Tv tana zaune kusan Juhainah ta kamo hannunta tace.

"Auntynah Wlh har na fara jin tsoron aure ganin yadda ki koma kwana ɗaya"

Juhainah ta kafe dara-daran kyawawan idanunta akan Surayya, kamar bazata yi magana ba ta harareta tace.

"Duk bake kika ja nayi auren ba, ai wlh da nasan wanda zan gamaki da shi ya rama min abinda kika saka aka min sai na haɗaku"

Surayya ta ƙyalƙyale da dariya tana rungume Juhainah tace.
"Aunty J ALLAH baki haƙuri ai Alkhairi na haɗa ko?"

Juhainah tace.
"Ni bacci nake ji so nake nayi sallah sai na kwanta...."

Suna hira har akayi kiran sallah Juhainah ta miƙe ta shiga bedroom ɗinta.

Tana idar da sallah Surayya ta shigo da manyan kulolin abinci.
Anan parlour suka baje sukaci abincin aka ɗora wa Jamal nasa akan dinning table.

Suna idarwa taje ta kwanta Surayya na zaune tana kallon TV, ita da Dijeh wacce har ta tattaro kaya, Surayya ta korata tace takai ɓangaren Mamy can zata zauna, kafin Aunty Juhainah ta kaita gun MAAH.

Nan Yah Jamal yaci mata mutunci, kuma bazai barta ta zauna ba.

Jamal na shigowa Surayya ta masa sannu ta miƙe ta gudu, dan bata son ya sake mata zancen mutum da yace zai haɗata da shi.

Bedroom ɗin Juhainah ya shiga ya iske tana bacci.
Zuwa yayi ɓangarensa yayi wanka, daman yayi sallah kafin yazo.
Wandon iya guiwa ya saka da rigar sa masu laushi, yana baza ƙamshi.

Kan dinning table ya nufa ya zauna yaci abinci ya gama ya miƙe yaje ya wanke bakinsa, ya rufe ƙofar ya nufi bedroom ɗin Juhainah.
Bed ɗin ya haye ya sanya hannayensa ya janyota jikinsa, ya rungumeta gam, ya ɗora bakinsa akan laɓɓanta masu kauri ya sumbata.

Motsi ta fara acikin jikinsa.
A hankali ya kirata cikin raɗa bakinsa dab da kunnenta yana shafa shafaffan cikinta, zuwa marata, yana lumshe idanunsa Sbd Allah ya bata jiki mai laushi, duk ramarta.

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta fara ƙoƙarin janye wa daga jikinsa, Sbd bata son wannan abubuwan sam basa mata daɗi.

Ƙamƙameta yayi a hankali yace.
"J Baby kin farka ne?"

A hankali ta zuba masa dara-daran kyawawan idanunta, sai kuma ta kame fuska sosai ta fara turesa.
Riƙeta yayi sosai yace.
"Please J Baby ya jikin naki? Wlh inacan amma ina tunanin jikin naki, babu waya gunki bare na kira ki"

Wani irin kallo ta masa sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya, sai kuma ta fashe da kuka ta sanya hannayenta ta cakumesa da wani irin ƙarfi tana zaro idanunta da suka gama juyewa daga sufar na mutum.

Da wata irin murya tace.
"Kayi kuskuren shiga gonar mu, mun rantse da mahaliccin Bil'adama da Mu Jinnu sai mun kasheka, ko lalata maka rayuwarka, idan tazo maka da sauƙi kuma ka jira kaga me zai faru..."

Ta ƙarasa maganar tana kamo wuyan Jamal da mahaukacin ƙarfi tare da wani irin uban ihuuuuun da sai da gidan ya amsa baki ɗaya, har ɓangaren su Mamy sunji ihunnnn, Sbd irin wannan ginin na masu hali ana saurin jin abu.

Sai lokacin Jamal ya fahimci Jinnun jikinta ne suka motsa.
Ɗakyar Jamal ya riƙe hannayenta da suka shaƙe masa wuya, da gaske neman kashe shi suke, dan bai iya numfashin kirki.
Chapter 91 · 0% Book details