Sashe 90
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Sumy na zaune a saman Sofar bedroom ɗin, Juhainah ta fito ɗaure da towel a hankali take tafiyar duk da taji dama.
Aunty Sumy tace.
"Zauna akan Stoll ki shafa lotion sai kiyi simple makeup muje kici abinci, muje ki gaida Mamy"
Juhainah baki ya mutu batace komai ba, kai ta ɗaga kawai, dan yunwar takeji kamar ɗazu bataci farfesu ba.
A hankali ta shafa lotion tayi simple makeup.
Aunty Sumy ta zabo mata wani wani narkeken lace mai tsada dinkin doguwar riga an samo ɗinkin, Black ne irin lace ɗin nan marar nauyi shaƙwat dashi kamar ba lace ba sai kyau da tsada.
Ta saka ta murza mata ɗauri, ta ɗora mata gyalen a kafaɗarta suka fito parlour.
Surayya ta kora Dijeh dan kar ta masu shirme.
Surayya tun fitowar su take kallon ƙawarta cike da tausayi ganin irin laushin da Yah Jamal ya saka tayi.
Surayya tace.
"Aunty J sannu da fitowa"
Kusan Surayya Juhainah ta zauna bata ce komai ba.
Surayya sosai yau take mamakin Juhainah baki ya mutu.
Aunty Sumy ta zuba mata farfesun ta beƙa mata, ta amsa ta fara ci a hankali.
Surayya ta sake cewa.
"Aunty J sannu ashe baki da lafiya? Ubangiji ya kawo sauƙi, gajiyar bikin ne"
Juhainah ta kalli Surry ta amsa da.
"Ameen"
Dan yau magana wuya take mata.
Ganin haka Surry taja bakinta ta ƙyale salin halin ƙawar tata.
Tana gama ci, Aunty Sumy ta sake haɗa mata tea mai kauri ta bata ta sha fiye da rabi ta ajiye.
Aunty tace.
"Muje ki gaishe da Mamy idan mun dawo sai na haɗaku da Maah kuyi magana"
Jin abinda Aunty Sumy tace, batayi magana ba ta miƙe suka tafi har su Surayya.
A hankali cikin dabara da juriya take tafiyar, tunda zafin ya rage sosai, ruwan zafin maganin da Aunty Sumy ta gasata da shi, yayi aiki.
Mamy suna parlour zazzaune anata fira da baƙin da suke shirin tafiya wasu yau wasu gobe.
Aunty Sumy da Juhainah sukayi sallama suka shigo parlour.
Dukkansu suka amsa.
Mamy cikin sakin fuska take kallon su, amma idanunta akan Juhainah wadda kana gane yanayin tafiyar tata sai a hankali.
Wani irin farin ciki ne ya cika zuciyar Mamy.
"Oyoyo daughter Bilkisu sannunku da zuwa"
Aunty Sumy ta gaishe su.
Juhainah tana ƙoƙarin rusuna wa ta gaishesu, Mamy ta kamota ta zaunar da ita a hankali kusanta tana riƙe da hannunta.
Juhainah ta gaishesu cikin girmamawa.
Duk suka amsa.
Aunty Sumy ta zauna kusan Surayya.
Dijeh ta washe baki tana isowa gun Juhainah ta zauna ƙasa kusan ƙafafuwanta tace.
"Ƙwaranƙwatsi dubu Antiya Jihinah kinyi kyau hekace balarabiya, ku ƴan gidanku sunada kyau kamar mu, har kunfimu ma.."
Mamy dariya tayi.
Surayya ta zaro mata idanuwa tace.
"Tashi ki bamu guri mun kusa huta wa gobe zaku tafi..."
Juhainah cikin sanyin murya tace.
"Nagode Dijah.
Mamy! Don ALLAH ina son ganin Baba Malam na roƙesa akan yabar min Dijah, zan sakata makaranta mai kyau zan saka Yah Sadeeq ya biya mata tun daga primary har zuwa secondary, idan ya kama tayi University na kuɗin ma babu damuwa"
Ai kuwa Dijeh ta washe baki ta faɗo jikin Juhainah ta ruƙunƙumeta.
Juhainah bata san lokacin da ta saki ihun azaba ba.
Mamy tai saurin ture Dijeh tana faɗin.
"Juhainah! Anya zaki iya da wannan yarinya mahaukaciya? A'a kibarta sutafi can ƙauye su sakata school ɗin"
Dijeh tace.
"Allah zanyi agun Antiya Jihinah amarya, ba zanyi rashin ji ba, kiyi haƙuri Mamy"
Ta ƙarasa maganar harda kukan ta.
Juhainah ta kamo hannunta tana goge mata hawayen fuskarta tace.
"Ya isa in sha Allahu idan Baba Malam ya bari zakiyi.
Mamy a haɗani da Baba Malam, Wlh tausayi take bani tunda naji mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙanƙanuwa, abubuwan nan da take harda rashin gatan uwa Mamy, Ni dai ku bani ita duk da ƙarancin shekaru na, Wlh nayi alƙawarin kulawa da ita, can gidanmu na nake so ta zauna babu idanun wanda ta sani zatafi nutsuwa tayi karatun, sai na ɗauki malami ya rinƙa koya mata kullum da yamma idan sun taso Sbd ta samu ilimi sosai.
Idan school ɗin su Suhaima ne akwai islamiyya can.''
Mamy tace
"Allah miki albarka bari na kirasa naji idan yake, idan yana inda aka sauke shi sai muje"
Aunty Sumy da mamaki take kallon ƙanwar tata.
Mamy ta kira number Malam Kamilu, cikin Sa'a tana fara ringing ya ɗauki kiran tare da sallama.
Mamy ta amsa tana faɗin.
"Malam Kamilu daman ina son ganinka ne kana masauki muzo?"
Da ga can Malam Kamilu ya amsa da.
"Eh gani yanzu na gama sallar Duha, zaku iya zuwa, Ina Hadizatu? Babu rashin jin sosai ko? Rabona da ita tun wajan ƙarfe 8 tazo ta gaishe Ni tace tafi gun Aunty Amarya."
Mamy tace.
"Gata nan tare zamuzo da surukarka"
Ta ƙarasa maganar tana katse kiran tana kallon Juhainah tace.
"Tashi muje yana nan."
Kai Juhainah ta ɗaga ta miƙe cikin dauriya.
A bakin ƙofar ɗakin suka tsaya Mamy tayi knocking.
Malam Kamilu ya amsa da a shigo.
Ƙofar ta buɗe suka shiga da sallama ya amsa cikin sakin fuska.
Dijeh taje da gudu ta zauna kusansa.
Juhainah ta gaishesa cikin girmamawa, ya amsa fuska sake yana faɗin.
"Ɗiyata ya baƙunta?"
Juhainah murmushi dai tai kanta a ƙasa.
Mamy tace.
"Malam alfarma Surukarka tazo nema a wajen ka"
Malam Kamilu yace.
"Toh ma sha Allah inaji Ɗiyata faɗi kanki tsaye"
Juhainah kanta a ƙasa tace.
"Baba Malam don Allah Khadija nake so kabani na sakata makaranta ta Boko da islamiyya, in sha Allahu zakayi alfahari da hakan, a daure zan riƙe amana"
Malam Kamilu sai yaji gabansa ya faɗi jin ya bada Dijeh, hankalinsa yana ƙoƙarin tashi, amma da yake mutum ne mai kawaici da dattaku sai yayi murmushi yace.
"Hadizatu! Zaki zauna binni kiyi karatu bazaki dinga janyo magana ba?"
Dijeh cikin farin ciki ta riƙe hannunsa tace.
"Eh Baba Wlh zan zamna bana ƙara faɗa ba ina son Antiya Amarya zan zauna da ita tana sona sosai."
Kai ya jinjina yace.
"Lallai Amarya ke ɗin mai Sa'a ce Hadizatu tana sonki har haka Sbd ke ta yarda tayi karatu, Wlh na amince har cikin zuciyata Sbd na daɗe ina roƙon ALLAH akan ya kawo wa Hadizatu sauƙi akan rashin jinta da ya hanani sakata makarantar Boko ta islamiyya ma nine nake koya mata a gida"
Juhainah tace.
"Nagode Baba Malam Allah ya saka da alkhairi, in sha Allahu sai kayi alfahari da Dijah..."
Malam Kamilu yace.
"Ga sauran kayanta wancan na gida zan aiko mata idan naje"
Juhainah tace.
"A'a Baba kar a aiko zan ɗinka mata sabbi in sha Allahu, wancan a bayar sadaka Baba"
Albarka ya yayi ta saka mata suka masa sallama suka koma ɓangarensu Mamy, suna zuwa Aunty Sumy ta masu sallama suka fito, ai kuwa Dijeh har ta bisu tana washe baki.
Mamy ta riƙeta wajenta.
Suna zuwa part ɗin Juhainah suka zauna saman narka-narkan Chairs ɗin Juhainah.
Aunty Sumy tace.
"Autah mi ya kaiki wannan gangancin? Bance karki kyautatawa dangin mijinki ba, amma Wlh ki kiyaye shishige wa dangin miji, ki kyautata masu ba laifi bane sosai ma, amma harda amso riƙo bana fatan wani abu ya faru, idan wani abun ya faru gaba Wlh tsanarki zasu yi, ke kanki ba'a gama rainonki ba har zakiyi rainon wani...?"
Juhainah ta marairaice fuska tana riƙe hannun Aunty Sumy tace.
"Please Aunty Sumy Ni Wlh tausayi take bani, hannun Maah zan damƙata, dan Wlh wannan Yah Jamal ɗin mai baƙin hali, bazai barta ta zauna a gidan nan ta nutsu ba"
Aunty Sumy tace.
"Ki dinga saita harshen ki mijinki ne yanzu, zaki ƙone, can ma idan ba Suhaima ta koma gidan Yah Sadeeq ba wlh Kinsan halinta ba lallai taji daɗin zama gidan MAAH ba"
Juhainah tace.
"My Babie zanji da ita tana son abinda nake so, kuma ita nafi son ta zauna gun Aunty Khairat ko tayi auren sai taci gaba da zama a ɗakin.
Please ki kira min MAAH"
Aunty Sumy tace.
" Ai shi kenan ke kika sani, na manta ma tace na kira ta na haɗaku"
Ta ƙarasa maganar tana ciro wayanta cikin Bag ɗinta ta danna number MAAH.
Maah zaune a parlour kiran Aunty Sumy ya shigo ta ɗaga tana faɗin.
"Sumayya! Ba dai sai yanzu kika isa gidan Autah ba?"
Aunty Sumy tace.
"A'a Maah nafi 1 hour da zuwa, yanzu daga ɓangaren surukanta muka fito, gata amsa Juhainah."
Juhainah ta amsa tana shagwaɓe murya tace.
"I miss you My Maah"
Yah Boss ya shigo parlour yana rangaɗa sallama anutse.
Maah ta amsa sallamar, tana cewa Juhainah.
"I miss you too Autah ya jikin naki?"
Oyoyo Mai gida Al'amin. Ma sha Allahu Anko kuka rangaɗa? Ubangiji ya tsareko ya albarkaci rayuwar ku da mahaifinku"
Da gudu Al'amin ya iso ya zauna akan cinyar Maah.
Yah Boss Anutse ya zauna kusan Maah yana gaisheta cikin girmamawa.
Ta amsa fuska sake.
Suhaima ma jikin Maah ta zauna tana gaisheta.
Juhainah daga can tace.
"Maah don Allah kiban Yah Boss da My Babies muyi magana"
Maah ta beƙawa Yah Boss wayan tace.
"Amsa ƙanwarka tana son magana da kai"
Kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa yayi akan Maah, a hankali ya furta.
"Maah daga kaita gidanta sai kiraye² waya kuma a safiyar nan?"
Maah tayi murmushi tana riƙe hannunsa tace.
"Batajin daɗi ne Sumayya ma tana can gidan nata, da wayar Sumayya ne ma"
Ta ƙarasa maganar tana saka masa wayar cikin hannunsa.
Anutse ya kai wayan kunnensa, a hankali ya furta.
"Bilkisu! Ya jikin?"
Juhainah kamar jira take daman ta cika famm jin yaƙi mata magana tun ɗazu, faɗa ma yake me yasa ta kira.
Siririn kukan shagwaɓa ta sakar masa, cikin dashashiyar muryanta kanaji kasan batada cikakkiyar lafiya, kuma zaka gane muryan anyi ihu ne har ta dishe haka.
Zamansa ya gyara a hankali ya furta.
"Aunty Bilkisu Yi shiru ya isa bakida lafiya kar kanki yayi ciwo, ga Suhaima da Al'amin suna jinki, kina kuka gaban ƴaƴanki"
Hawayen fuskarta ta sanya bayan hannunta ta goge tana dakatar da kukan, a hankali tace.
"My brother good morning.
I miss you, where are my children?"
A hankali ya furta.
"Morning, ai na faɗa maki suna jinki kina kuka, ke bakya girma.