← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 113

Sashe 77

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soyayen dankalin yakai bakinsa yana taunawa anutse, ya furta.
"Are you going to eat?"
A hankali tana narkewa saman bed tace.
"Eh naci My Blood Habiby"

Ɗan ƙaramin murmushi ya saki, ya maida fuskarsa ya kame, a hankali ya furta.
"Very good ki sake bacci ki huta sosai yanzu"
Shagwaɓe fuska tayi a hankali tace.
"Yah Boss Habiby Nah, ina Phone ɗina?"
A hankali ya furta.

"Na haɗiye ta alright?"

Ƙyalƙyalewa tayi da dariya tana faɗin.
"I love you My blood Habiby ka riƙe min ita Ni yanzu bana son jin murya kowa sai taka bayan aurena zanje na amso, nace ya harshen naka Please?"
A hankali ya furta.

"Ya warke."

Cikin jin daɗi tace.
"Alhamdoulillah! Allah ya ƙara maka lafiya, I love you bye Yah Boss ɗina"
Ta ƙarasa maganar tana katse kiran ta rungume wayar ƙirjinta tana dariya ƙasa².

Yah Boss ya girgiza kansa yana yagar tissus ya goge bakinsa, ya miƙe tsaye cikin kamewarsa.
Naman Kazar ko rabin ƙirjin bai ciba, haka cin abincinsa yake, bai fiye cin abinci ya wuce kai bakinsa sau 7 ba, sai idan yana jin muguwar yunwa, yafi shan tea sosai da dafaffiyar Madara.

Bottle ɗin water ya ɗauka ya buɗe yasha kaɗan ya ajiye.
Anutse ya fito parlour fuska kame.
Fu'adh a zaune yana amsa waya.
Yah Boss ya zuba hannayensa cikin aljihun uniform ɗinsa ya kalli Fu'ada, baice masa uffan ba ya nufi hanyar fita daga parlourn.
Fu'adh yayi sallama da wanda suke wayan ya miƙe ya biyosa harda ɗan gudunsa yana faɗin.
"Sir har an gama wayan? Yanzu police station zamu ko gun taron?"
Tsayawa yayi yana Kame fuska ya waigo ya kafe lumsassun idanunsa akan Fu'adh.
Fu'adh yayi saurin wucesa Sbd yasan magana zai yaɓa masa cikin ruwan sanyi yanzu.
Yah Boss hankali kwance cikin nutsuwarsa ya furta.
"Kanaji Fu'adh!"

Fu'adh ya tsaya yana danne dariyarsa ya fuskanci Yah Boss, yana fadin.
"Eh Sir inaji"
A hankali ya furta.
"Ina son ka faɗa min hadisin da ya haramta Yaya yayi waya da ƙanwarsa, sai a kiyaye alright"
Ya ƙarasa maganar yana takunsa a nuste.
Fu'adh yace.
"Afuwan Sir babu gaskiya muje yanzu ina muka nufa babban yayanmu?"

Yah Boss yay saurin damƙosa yana murɗa masa hannunsa baya.
Fu'adh ya fasa ihu yana dariya yace.
"Don girman ALLAH kayi haƙuri Sir, wai me na maka tsaka da Allah?"

Fuska kame ya furta.
"Bana son munafurci kaci gaba kuma"

Ya ƙarasa maganar yana sakin hannunsa yayi gaba.
Fu'adh sosai yaji azabar murɗe masa hannu da Yah Boss yayi, a ransa yake cewa.
"Wannan mutum akwai mugunta me na masa toh?"

Sai yayi ƴar dariya yabi bayansa, shiyasa baya yarda ya tsaya kusansa idan ya takalesa...

Sai da Yah Boss ya shiga mota har Walid yaja ya nufi gate ya furta.
"Fu'adh! Ya maganar Zuby take ko wa?"

Fu'adh yace.
"Sir ai ina waya da ita Wlh yanzu ta fita daga sabgar Juhainah, amma ban gama gamsuwa ba, so nake a gama bikin gobe zuwa jibi zan haɗu da ita, tunda bata san ni waye ba, zan gama samu duk abinda nake so, Ammar dai ba ƙaramin ƙwalon ɗan iska bane, watsewar da suke da yarinyar sai a hankali"
Yah Boss a hankali ya furta.
"Tun farko zuciyata bata yarda da ishi ba, can su suka sani matuƙar ba su shiga rayuwar ƙanwata ba"

Fu'adh ya cigaba da basa labarin guraren da yake ganinsu, a ɓoyayyen waje.
Yah Boss bai sake magana ba yana dai sauraren shi.


Surayya
Baki ɗaya daren jiya baccinta banda mafarkin Nasir babu abinda take, ko da ta tashi sallah da asuba jikinta yayi sanyi, amma ta danganta hakan da ta tsorata ne jiya rashin kunyar da ta masa da ya kamata zata raina kanta.

Gidansu ma sha Allahu cike da jama'a anata aiki, ƙarfe sha biyu na rana tana tsaye gaban madubi tana fesa turare sanye take da riga da wando ƴan Pakistan Maroon colour tayi kyau sosai.

Dije ce ta shigo bedroom da gudu tana kallon Surayya ta washe baki tana faɗin.
"Alquran Antiya Suraiya kinyi kyau, he ƙanhi kike ina zaki inazuwa"

Surayya ta kamo kunnenta tace.
"Bana hanaki cemin Antiya Suraiya ba? Keda bakyajin magana zan kaiki gidan mutane kiyi ɓarna ba ruwana ki zauna a gida, Dijah"
Dije ta riƙe hannun Surayya tace.
"Na rantse da ƙwaranƙwatsi dubu Aradu zanji magana Bazan taɓa kowa ba ina zaki zan biki"

Surayya tace.
"Gidansu amaryar yaya Jamal zanje kije ki saka hijjab ke wannan ɓukekiyar ai ba haka zaki bini ba aje Mayun zamani su kamaki na shiga uku."

Dije ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin.
"Aradu ba hegiyar mayyar da ta isa kama wannan tsokar naman Baba Malam kullum sai ya min Addu'a a ruwa naha, kuma nima na iya azkhar"
Surayya tace.
"Toh kije ki sako hijibin kizo mutafi"
Cikin murna Dije ta fice da gudu mazauna irin cikkakun ƴan mata masu class, Allah ne ya bata Abunta.

Surayya ta fito parlour Mamy bata nan sai baƙi da ƙawayenta da maƙota da matan yayun Surayya zazzaune.
Ta gaishe su tana kallon Wasila yayarta tace.
"Aunty Wasila! Ina Mamy?"
Wasila kyakkyawar matashiya shekarunta 22 ita ke bin Jamal, cikinta ya fara tsufa.
Tana tsananin kama da Jamal.
A hankali tace.
"Tana part ɗin yaya Jamal"
Surayya tace.
"Ok bari na sameta gidansu Juhainah zanje ko kinje?"

Wasila tace.
"A'a banjin daɗin jikina"
A ƙofa suka haɗu da Dije taci ubansu kwalliyar ƙauye harda janbaki kanta waye.

Surayya ta fashe da dariya tana faɗin.
"Ke Dijah wannan kwalliyar fa? Gaskiya Gogeta bazaki bini ba."

Dije ta saka bayan jibinta da yake baƙi ne ta goge tana riƙe da hannun Surayya suka fito.
Jamal zaune fuska haɗe Mamy tana riƙe da hannunsa tana masa nasiha.

"Don ALLAH Jamal ka saki ranka, shin me Juhainah ta rasa a jikin ɗiya mace? Ko ramarta ce baka so?"

Kallon Mamy yayi yana faɗin.
"Haba Mamy duk miye kike tayar da hankalin ki? Na amince da auren amma duk baki gamsu ba?"

Mamy tana sake riƙe hannunsa tace.
"Wallahi ban gamsu ba Jamaluddin! Sbd ni na haifeka ba riƙo akan ba"

A hankali cikin ƙosawa da maganar yace.
"Mamy! Yanzu me kike so nayi ki daina zargina?"

Cikin farin ciki tace.
Yawwa ɗan albarka, Ni mahaifiyarka ce bazan ɓoye maka komai ba, tunda haraka ta aure ce.
Ina son don girman ALLAH don darajar Annabi S.A.W, ka sauke haƙƙin wannan yarinyar a gobe nake so idan an kawo ta gidanka ku zama ɗaya kai da ita, a lokacin ne hankalina zai kwanta zan kuma yarda kai ɗana ne wanda duk duniya banda irinka, kamin biyayya ka aureta ka cika sunnar Annabi, Wlh idan ka aikata haka na yafe maka tun daga ɗaukan cikinka zuwa haihuwar ka da rainon da na maka da komai da duk wani laifin da kamin har girmanka zuwa wanda zakayi gaba amma ba na gangan ba."

Cikin wani irin farin ciki Jamal ya rungume Mamy a hankali ya furta.
"Na gode Ya Mahaifiyata nayi maki alƙawarin abinda kike naman nan in sha Allahu idan shi zai saka na samu albarka da yafiyarki har barin numfashina na ƙarshe na amince a gobe ba zan baki kunya ba"

Bayansa ta buga tace.
"In sha Allahu ɗana, idan ba kun zama ɗaya da Juhainah ba, hankali na bazai taɓa kwanciya ba"
Surayya da take laɓe taji komai ta shigo da Sallama tana kallon Jamal da ya saki Mamy yana kallonta fuska kame yace.
"Ke! Akwai wanda ya ganki yana sonki babban mutum ne, zan turo sa bayan bikin nan idan na Nutsu sai kuyi magana"
Surayya ta zaro idanunta tana dafe ƙirjinta tace.
"A'a gaskiya ni Wlh yanzu Inason Farid tunda na rasa Yah Boss"

Miƙewa yayi yana zaro mata idanunsa yace.
"Ni sa'anki ne?"
Mamy ta kamo hannunsa tana miƙewa tace.
"A'a karka fara Jamal bazaka fa nakasa min Jaririya ba, haka kawai bataga mutum ba sai ka aura mata shi? Kaine ubanta"

Jamal ya ɓata ransa yace.
"Ni aka min auren dolen? Mamy dattijo ne fa zai yi kirki alamunsa"

Mamy tace.
"Naji ka bari bayan aurenka zan zaunar da ita naji ta bakinta"
Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Aradu Wannan Katon Jamala ɗin dariya yake bani hi he tsama da kyan banza ba dariya, yo ina dalili da garinmu ne da an jeheka da duwatsu, nagudu kaci Sa'a kai dan uwan Baba Malam ne ehe"

Jamal ya kame fuska ya nufota yana faɗin.
"Ke ƴar tuliya kema shegiyar ƙauye ko? Zan karya ki Wlh"

Mamy ta sake riƙe hannunsa tace.
"Ka rufa min asiri Malam Kamilu zaka saka ya koma ba'a ɗaura auren ba, ba'a zagar masa ƴa, bare duka, wannan ba irin Surayya bace da ka samu ƴata kamar jaka kake naɗa"

Surayya tace.
"Mamy na tafi gidansu Juhainah sai dare zan dawo"
Jamal ya taɓe baki ya nufi bedroom ɗinsa Dije na masa dariya tana kwaikwayon tafiyarsa.
Mamy tace.
"Dijah Wlh dukanki zaiyi ki rabu da shi kin ji? Surayya karki wuce Maghreb ki dawo."
Surayya tace.
"Tom Mamy daga an shafa lalle zan dawo"
Ta faɗa tana kama hannun Dije Mamy tace.
"Ki kula fa kar taje ta masu ɓarna"
Surayya tayi dariya taja hannun Dije suka tafi.


Yah Boss tun guraren 12 na rana ya fara jin wani irin yanayi a cikin jikinsa, ya basar yana lamurran gabansa.
Amma zuwa sallar azuhur abun ya hauhawa.
Yana dawowa daga masallaci ya shiga bathroom ɗin da take cikin room ɗin da yake hutawa ya cire duk kayansa ya sakarwa kansa shower mai sanyi sosai.
A hankali yake sauke numfashi tare da ajiyar zuciya.

Ya ɓata lokaci kafin ya fito ɗaure da towel ya goge jikinsa ya maida kayansa, ya zauna anutse ya buɗe Flask ɗin da Fu'adh ya kawo masa dafaffiyar madara ya tsiyaya da zafinta.
Anutse ya fara kurɓa.
Idanunsa ya lumshe yana jin yadda jikinsa yake buƙatar dukkan abinda ya shafi mace.
Chapter 77 · 0% Book details