← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 113

Sashe 2

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Khairat tana fita ba'a fi 3 minutes ba, Halima ta shigo dan gyara ɗakin yaran, dan ta maida komi muhalinsa ta share tayi mopping ta saka turaren wuta.
Khairat tana shiga bedroom ɗinta ta fara ƙoƙarin shirin tafiya makaranta.
Tana da matsakaicin tsayi, tanada yar ƙiba tanada diri sosai mai kyau fara tass tanada manyan idanu masu haske tanada hanci mai tsayi bakinta ɗan ƙarami, komai na jikinta ma sha Allah, su kam Allah ya basu baiwar kyau family's Janfar.
Ma sha ALLAH ko daga sutura jikinta da ta saka yanzu bayan gama shirin zuwa jami'ar, masu kyau da tsada ne kana kallon su zaka san suna da hali, ga ko ina jikinta rufe saboda tsananin kamun kanta.
Tana gama shirin tafiyar ta ta nufi bedroom ɗin Juhainah dan tashinta.
Dattijuwar mata farar bafulatana zaune cikin tsararren falo, gefenta dattijo ne kyakkyawan bafulatani, yana amsa waya, fuskarshi ɗauke da murmushi.
Kyawawan jikokin nasu da suka gama breakfast suka baro dining room suka dawo suka yi wa Papa kiss sukayi Mash kiss suna masu bye, Amina na riƙe da school School bowls ɗinsu suka nufi ƙofa saboda Hamza direbansu ya fara masu horn.
Maah ta kallesu cike da so da ƙaunar jikokin tace.
"Bye ayi karatu lafiya a dawo lafiya yaran albarka."
Muryar Al'amin ta fito sosai wajan amsa Amin ɗin suna tafiya Amina na biye da bayansu. Papa ma yabisu da addu'a yana ɗaga masu hannu, ba tare da ya katse wayan da yake ba.
Maah ta kalli tsaddadan agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannunta tana sake zaro ido tare da faɗin.
"Ya Allah! Wai yarinyar nan da gaske yau ma bazataje makarantar ba? Toh Harɗo ka kira Abbah yazo ya naɗa mata shegen duka kowa ya huta, banga anfanin zuwa makarantar Juhainah ba sam Wlh."
Ta faɗa tana miƙewa tsaye dan zuwa ɗakin na Juhainah.
Matashiyar budurwa ƴar shekaru 17 Kwance take akan lafiyayyan bed ɗinta, sanyin Ac ya ciki bedroom ɗin nata, ga wani ƙamshi na tashi mai sanyaya zuciya.
Ɗakin nata komai adon pink ne, hatta da lallausan quilt ɗin da take rufe pink ne.
Duka jikinta rufe yake iya kyakkyawar fuskarta ne kaɗai a buɗe.
Dole zata rufe jikinta saboda shegen ɗan ƙaramin jeans ɗin da take saye da shi, iya rabin cinyarta ne, rigan ma iya cibinta ne babu hannaye ga wani irin sanyin A'cn da cika ɗakin tamkar lokacin hunturu.
Kallo ɗaya zaka mata kasan ita ɗin bafulatana ce, sbd kyawunta, komi nata kamar ita ta zaɓa, sai dai Allah bai bata jiki ba, ƴar siririya ce, shiyasa bata jin wuyar saka kowasu irin ƙananun kaya iya cikin gidansu, saboda tsaron Abubakar Sadiq, wanda tun tashinta ta masa laƙaɓi da suna (Yah Boss).
Toh tsoransa ma bazai barta fita waje da ƙananun kaya ba, sai idan wayo zatayi ta saka acikin.
Doguwace fara amma farin nan mai ɗan duhu ne, duk sun fita hasken fata, tanada siririn dogon hanci wanda yake ɗauke da huɗa ta saka masa abun hanci mai zagaye hancin wanda zallar gold ne, wani irin kyawu yayi mata.
Idanunta dara² farare tass, laɓɓanta masu kyau sunada ɗan ƙauri jajir dasu kamar na jariri, gashin idanunta kamar zasu rufe mata idanu sbd tsayinsu, haka gashin girata lub kwance tanada dimple gefen hagu, tanada yar siririyar wushiyarta da take ƙara mata kyau idan tayi murmushi ko dariya, ma sha Allah Juhainah ta haɗu ta ko ina matsalarta ta fiye shirintaka, sai dai ramarta bata hana kyawunta fiti a fili ba, SBD tanada diri mai kyau, ga cikar ƙirji ma sha Allah.
Hadaddiyar wayanta ƙirar iphone 15 pro max, kalar pink da take saman bedside ta fara rurin neman temako.
Cikin daddaɗan baccin da Juhainah take taji Ring ɗin wayarta.
Wata irin miƙa tayi tana sake laɓewa saman bed ɗin, tare da ƙanƙame lallausa quilt ɗin da take rufe da shi.
A hankali ta fara buɗe dara-daran fararen idanunta ta sauke su akan iphone ɗinta, tana ɓata fuska.
Tattausan hannunta masu zara-zaran yatsu farare, yatsunta na Hagu ta saka masu false nails, sun mata kyau sosai.
A hankali ta beƙa hannun ta janye wayan ta ɗaukota tana dubawa.
Sunan da ta ga yana yawo saman screen ɗin wayan ne ya saka jan dogon tsaki cikin zazzaƙar muryanta take faɗin.
"Oh! My God! Surayya is useless because I will tell them the news and they will wake me up in my sleep."
Ta ƙarasa mgnar tana picking Call ɗin, ba tare da takai wayan kunnenta ba tace.
"You're a naughty girl, I'm breaking the news to you, you woke me up while I was sleeping."
Ta ƙarasa mgnar tana katse kiran tare da cilla wayan saman bed can gefe tana sake gyara kwanciyarta, tare da lumshe idanunta, tana faɗin.
"Zan kamaku sai kunci ƙaniyarku, banza kina ɓata lokacin ki gun jira Yah Boss bai ma san kina yi ba."
Tana rufe baki ana buɗe ƙofar ɗakin tare da shigowa.
Idanunta ta rufe ruf ta shiga baccin ƙarya.
Khairat ta ƙarasa wajan bed ɗin tana faɗin.
"Eh lalle ma yarinyar nan, bacci ma take abunta ta manta sunada jarabawa ko?"
Ta faɗa tana sanya hannunta ta janye lallausan quilt da take rufe da shi, ta saka hannayenta ta ɗagota tare da girgizata tana faɗin.
"Juhainah! Ki tashi ki shirya wai ba jarabawa gareku ba?
Juhainah! Ke! Bilkisu! Tashi Wlh ko yanzu na kira maki Yah Sadiq, nasan Maah ba dukanki zatayi bare Papa, ki tashi Bilkisu."
Juhainah wani irin takaicin Aunt Khairat ya cikata kamar ta shaƙo wuyanta taji, sai ta daure tana fara motsi tana shagwaɓe fuska ba tare da ta buɗe idanunta tace.
"Don Allah ki rabu dani banida lfy ni bazanje makaranta ba ehen."
Ta ƙara maganar tana fizge jikinta ta shige cikin quilt tana faɗin.
"Wayyo kaina ciwo ƙafata wuyana."
Khairat tai tsaye ta saki baki tana kallon ikon Allah, saboda tasan ƙarya Juhainah take lafiyarta ƙalau, ita kam tana mamakin tantirancin yarinyar nan, wai a hakan ma akwai wanda take mugun tsoro.
Batace uffan ba ta juya ta fara tafiya saboda tasan ɓata lokaci zatayi, tunda tace batada lafiya toh fa bazataje ba.
Tana ƙoƙarin saukowa downstairs suka haɗu da Maah tana hawa zuwa tashin Juhainah.
Khairat ta tsayar da tafiyar tana faɗin.
"Maah! Yarinyar nan fa sai kin kira Yah Sadiq shi kaɗai zai sakata ta bar gidan nan yanzu², tana can ta naɗe cikin quilt wai kanta da ƙafarta da wuyanta suke ciwo, kuma Wlh ƙarya take yi ko kunya bataji ƴaƴanta ma sun tafi school ita tana gida, a haka ne zata shiga jami'ar? Wadda secondary ma ta zame mata aiki ƙarasawa, jarabawar ƙarshe ne da zasuyi."
Maah ta riƙe haɓa tana faɗin.
"Ke Khairiyya! Kiji tsoron Allah yaushe Juhainah mai son lafiyarta fiye da komi zatayi ƙarya ciwo? tunda ta faɗa batada lafiyar bari na fito da ita muje asibiti, za'a kira makarantar tasu a faɗa ma shugaban makarantar tasu."
Khairat ta riƙe mahaifiyar Tata kamar zatayi kuka tana faɗin.
"Allah Maah Juhainah ƙarya ciwo take yi lafiyarta ƙalau, idan kina musawa ki kira Yah Sadiq yazo gidan nan yanzu Wlh tsaf zata miƙe, kunsan halinta fa bata son zuwa makaranta ne sam..."
Maah tai caraf tace.
"A'a Wlh bazan haɗawa Auta zafi biyu ba, ai ko batada lafiya idan har taga Abbah tsaye dole zata miƙe tunda baya tausaya wa wannan lange² jikin nata dakarta zai yi, ke dai kije kiyi breakfast ɗinki ki tafiyarki, Allah ya bada sa'a."
Ta faɗa tana janye hannunta taci gaba da taka Steps.
Khairat ta girgiza kanta ta juya ta ƙarasa saukowa tsararren falon da aka Barka masa uwar dukiya kamar ba'a san zafin kuɗin ba.
Papa har lokacin waya yake cikin nishɗi kana ganin dattijon kasan yana cikin jin daɗi da kwanciyar hankali ga hutu da masu gidan rana sun kwanta masa, kallo ɗaya zaka masa kasan ALLAH ya rufa masa asiri.
Khairat ta ƙaraso dab da Turkish Chair ɗin da Papa yake zaune, yana waya, ta zauna saman lallausan Carpet dab da ƙafafuwansa, tana faɗin Papa good morning fatan ka tashi lafiya?"
Kyakkyawan bafulatanin dattijo ya kalli ƴar tasa cike da ƙauna yana zare wayar a kunnansa Saboda ya yi sallama da wanda suke wayan yayarsa ce Hajjah Bilkisu.
Anutse ya amsa yana shafa kanta yace.
"Khairiyya! Har an fito? Ma sha Allah ina Auta ? Ko bata farka ba har ƴaƴanta sun tafi?"
Khairat tace"Maah ai taje ta tayar da ita, bari nayi breakfast na wuce kar na makara,"
Ta ƙarasa mgnar taƙaice tana miƙewa dan bazata ɓatawa kanta lokaci ba, tsayawa fadawa Papa yanda akayi, tunda tasan duk (Kanwar) Ja Ce, ɗaure mata gindi zasu yi ba mai son laifin Juhainah a cikin su.
Papa ya zaro rafar ƴan dubu gudu uku ya beƙawa Khairat yace.
"Allah maki albarka sai kin dawo, ke zakiyi driving ko Manu zai kaiki?"
Khairat ta amsa tana godiya ta cire hadaddiyar handbag ɗinta mai shegen kyau da tsada, ta ajiye saman Chair Turkish tana kallon mahaifin nata tace.
"Papa ni zanyi da kaina."
Murmushi yayi yana faɗin.
"Toh Allah ya tsare, Autah ma ya kamata Abbah ya bar min ita ta fara driving da kanta.."
Khairat dai murmushi tayi bata ce uffan ba, ta nufi dining room dan yin breakfast, da masu aiki suka gama jera komai tsaf sai ƙamshin daddaɗan girkin yake tashi a ƙaton dining room ɗin.
Maah tana shiga bedroom ɗin Juhainah ta hango lulluɓe cikin quilt tana rawar sanyin ƙarya.
Maah bakinta ɗauke da salati ta iso bed ɗin tana faɗin.
"Subhanallahi Juhainah! Zazzaɓi ne ko miye ya sameki?"
Ta faɗa tana janye quilt ɗin ta zauna gefen bed ɗin ta kamota ta rungumeta abunka da figagiya.
Jikinta duka ta shiga taɓa wa tana gyara mata lallausan dogon gashinta da ya zubo kan fuskarta.
Juhainah har yanzu bata buɗe idanunta ba ta narke a jikin Maah da wata kalar shagwaɓa ta fara magana da turanci.
"Maah! I'm not feeling well, my body hurts, my head hurts, even my eyes hurts."
Maah ta sake rungumeta jikinta tana shafa kanta tace.
"Subhanallahi sannu Juhainah jiki ciwo kai ciwo harda idanunki?"
Juhainah ta ƙanƙame Maah har yanzu bata buɗe idanunta ba, kai ta ɗaga mata alamar Eh.
Maah tace.
"Sannu bari na sauka a kira shi shugaban makaranta taku a faɗa masa, sai mutafi hospital, kwanta na dubo miki ko abaya ma ki ɗora akan guntayen kayan naki ke kaɗan ma bakya son abu mai nauyi."
Ta faɗa tana ƙoƙarin kwantar da Juhainah dan ciro mata abinda zata saka.
Ai kuwa Juhainah ta wani ƙanƙame Maah kamar zatayi kuka a hankali can ƙasa cikin zazzaƙar muryanta tace.
"No Maah, I don't want to go to the hospital, ni banson allura banson magani kin sani, idan na samu isasshen bacci zan tashi normal."
Maah tace.
"A'a Auta anya bacci kawai zai isa?"
Da sauri ta sake rungume Maah ta shagwaɓe fuska tace.
"Yes I will recover after waking up from sleep Maah Please."
Maah ta sumbaci goshinta tana shafa bayanta tace.
"Ok naji amma kinyi min alƙawarin idan kin tashi ba normal ba zamuje doctor ya dubaki?"
Kai ta daga a shagwaɓe a hankali tace.
"Yes Maah I promise you."
Maah ta kwantar da ita ta lulluɓeta tana faɗin.
Bazaki sha ko tea ba?"
"A'a banajin yunwa yanzun."
Maah ta sake duƙowa ta sumbaci goshinta tace.
"Ok kiyi baccin ki Juhainah Autar mata Allah ya miki albarka bari na sauka na faɗawa mahaifinki sai a kira shugaban makaranta naku a faɗa masa...."
Chapter 2 · 0% Book details