Sashe 64
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yah Boss bai amsa ba, ya dai tsaya ba tare da ya juyo ba.
Nasir ya ƙaraso gun yayan nasa yana faɗin.
"My brother sannu da zuwa, yanzu kuka shigo?"
Yah Boss cikin kamewarsa ya kamo kunnen Nasir ya murɗa ya furta.
"Ai bazaka ganni ba, ka samu ɗiyar mutane kana zalunci, ko dan Bilkisu da sai kayi haƙuri ka barta"
Nasir shagwaɓe fuska yana riƙe hannun Yah Boss yana faɗin.
"My brother banida Imani tace min fa"
Yah Boss bai tsaya jin duk me ya kawo faɗan ba, anutse ya furta.
"Karka sake taɓata babba da hƙr aka sansa, ku Soja ba hƙr Sam"
Ya ƙarasa maganar yana riƙe da hannun Nasir suka shigo parlour.
Juhainah ta fara tsefewa Suhaima kai dogon gashinta wanda aka yi mata kalba da shi.
Yayin da hajjah Mama suna fira da Zarah Al'amin yana sana'ar Game a TV, Khairat ko na upstairs tunda Fu'adh ya kirata ta gudu.
Zazzaƙar muryansa ta karɗe parlour da sallama, tare da ƙamshin sa da ya gauraya da na Nasir.
Juhainah ta saki kan Suhaima ta miƙe da wani irin farin ciki aguje ta nufi gun Yah Boss.
Suhaima ta bi bayanta tana ihun farin cikin ganin Dadd ɗinta.
Hajjah Mama da Zarah suka amsa sallamar.
Yah Boss ya saki hannun Nasir ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa a kanta, a hankali ya furta.
"Bilkisu! Karki iso min nan kina gudun nan, ki tsaya nan Karki iso ma."
Ai kuwa taja burki ta tsaya cak, tana rau-rau da dara-daran kyawawan idanunta, tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta tayi ƙasa da kanta duk kunyar dizga ta da yay ta cikata.
Suhaima ta faɗa jikinsa ya ɗagata sama kamar Baby yana sumbatar goshinta.
Al'amin ya miƙe shima da gudu ya faɗa jikin mahaifinsa.
Shima sama ya ɗaga yana sumbatar sa.
Nasir ya saki ƙaramin murmushi yana isowa gun Juhainah ya kamo hannunta yana janta suka nufi narka² Turkish Chairs ɗin parlour, a hankali yake mata magana.
"My sister kin fiye sangarta ne yanzu da zuwa zakiyi ki cakumesa idan bai dakatar dake ba, baki san kin girma ba?"
Ƙaramin kukan shagwaɓa ta sakar wa Nasir tana faɗawa jikinsa ta ƙamƙame shi, cikin kuka take faɗin.
"Yah Nasir! Kaga Yah Sadeeq baya ƙaunata, tunda ya tafi nake tunanin sa banajin daɗin rayuwa, amma yanzu daga zuwansa ya dizga Ni a gaban maƙiyana, haka ranan na kirasa yace zai kirani shiru, dan yasan ina sonsa dayawa"
Yah Boss ya kafe lumsassun idanunsa akansu yana kame fuska sosai, a nutse yana riƙe hannun Suhaima and Al'amin ya fara tako wa gun hajjah Mama da take famar masa sannu da zuwa, dan ita ta fita daga sabgogin Juhainah kar ta saka mata hawan jini, dan taji habaicin da take bai wuce da ita da Zarah take wa.
Nasir kuwa ya ɗan waro lumsassun idanunsa yana danne dariyar da take son kamasa, ya shiga buga bayanta a hankali yake faɗin.
"Ya isa bari kukan yana sonki fiye damu, matsalar ke kin fiye sangarta bakya barinsa ya zauna lafiya Autah, yanzu dai muje mu zauna Maah ta aikoni naga lafiyarki, amsa harda chocolates na kawo maki keda Babies, ina Khairat?"
Ya ƙarasa maganar yana janyeta daga jikinsa ya kama hannunta yana manna mata bluen ledar chocolates ɗin yajata suka zauna, tana ninniƙe da Nasir har yanzu hawaye take yana goge mata.
Suhaima ta sakin Dadd ɗinta ta iso ta zauna kusan Juhainah tana kamo hannunta tace.
"Kiyi haƙuri Aunty J in ɓare miki chocolate ɗin?"
A hankali ta ɗaga kanta, taƙi yarda ta kalli ɓangaren da Yah Boss yake.
Anutse Yah Boss ya zauna kusan Hajjah Mama yana gaisheta.
Zarah a hankali tace.
"Sannu da zuwa fatan anzo lafiya ya gajiya?"
Ba tare da ya kalli gefen da take ba, a hankali ya furta.
"Alhamdoulillah!"
Yana kallon Juhainah da Suhaima da Al'amin suna lallaɓata.
Nasir ya miƙe ya dawo kusan Hajjah Mama yana zama cikin nutsuwarsa ya gaske da hajjah Mama da Zarah.
Zarah baki a washe ta amsa tana faɗin.
"Yasu Maah da Papa?"
Juhainah ta waigo tana zabga mata harara ta Turo laɓɓanta gaba.
Yah Boss ya girgiza kansa yana miƙewa tsaye a hankali ya furta.
"Hajjah Mama zanje na watsa ruwa"
Hajjah Mama tayi caraf tana faɗin.
"Matarka ta kawo maka abinci saman ne?"
Da wani irin sauri amma cikin kamewarsa bazaka gane ba yayi saurin furta.
"A'a munci abinci a hanya, tea kawai zan sha shima ba yanzu ba idan ina buƙata zan kira sai a kawo."
Ya ƙarasa maganar yana tafiya Nasir ya miƙe yabi yayayansa akwai maganar da zasuyi.
Zarah tabi Yah Boss da kallo tana sauke ajiyar zuciya.
Fu'adh koda ya shigo da kayan Yah Boss bayan sun gaisa da hajjah Mama da Zarah ya wuce Stairs ɗin.
Hajjah Mama ta miƙe tana faɗin.
"Barci nakeji Zarah natafi sai da safe, don Allah ki dafa masa tea mai daɗi ki kai masa ba wai sai ya kira ba, amma yafi sun Black tea da dare"
Zarah ta amsa da.
"Toh Mama, sai da safe Allah ya tashe mu lafiya"
Suhaima ta harareta tana kallon Juhainah ta mata raɗa.
"Aunty J don Allah ki tashi kije ki dafa tea ki kawai My Dadd kar waccan matar ta dafa masa"
Juhainah ta zumɓuro kakkauran laɓɓanta gaba tana faɗin.
"Nayi fushi ba kina gani ba ya dizga Ni gaban kowa, kuma ina kuka bai lallaɓa Ni ba."
Zarah ta miƙe tsam tana takunta ta nufi hanyar kitchen, dan har cikin zuciyarta taji daɗin dizgin da Yah Boss ya yayiwa fitsarariyar Ƙanwarsa.
Suhaima ta marairaice fuska tana sakawa Juhainah chocolate a bakinta tana faɗin.
"Kinga ta tafi kitchen ɗin fa, don Allah muje ki dafa masa"
Juhainah ta maƙale kafaɗa tana silalo hawaye akan kyakkyawar fuskarta, tayi kwanciyarta saman Chairs tana rungume Cushion, tana hawaye.
Ita dai a kullum idan kaga kukanta toh Yah Boss ne.
Shi kaɗai ne batada taurin zuciya akansa.
Suhaima ta sanya tattausan tafin hannunta tana share wa Juhainah hawayen ta miƙe tsaye, ta nufi hanyar kitchen cikin ɓacin rai.
Surayya ko tana zuwa ta shiga motar Farid tana faɗin.
"Muje ka ajiyeni gida yau bazan kwana ba"
Kallonta yay yana.
"Baby keda waye kuke rikici?"
Hawayen takaici ta sako tana faɗin.
"Yayan sister Juhainah ne Nasir..."
Ta basa labarin abinda ya faru."
Farid dariya abin ya basa amma ganin tana sama ya waske yana faɗin.
"Kar fa aje ku fara soyayya daga haka, a kasheni da raina?"
Ya ƙarasa maganar idanunsa yana canza launi.
Surayya ta zaro kyawawan idanunta tana dafe ƙirjinta tace.
"Wlh Allah ya kiyaye bakaji yanda na tsanesa ba a yau, haka kawai yake neman kasheni Allah sai ya saka min"
Farid yayi murmushin ƙarfin hali yaja motar yayi Rivas yabar gun yana faɗin.
"Ga handbag ɗin duba kiga tayi"
Surayya ta cirota a leda tana kallon tace.
"Wow Baby tayi kyau sosai Wlh sai kuɗi kalar takalmin ce wlh"
Murmushi yayi yana driving....
Suhaima lokacin da ta isa kitchen Zarah har ta ɗora ruwan zafi.
Kallonta tayi sama da ƙasa ta watsar ta fara ƙoƙarin ɗaura nata tea ɗin, SBD ta iya haɗa tea dan har girki Suhaima ta iya sama², dan ta iya aiki sosai lokacin Khadijah da ranta, komai tare suke tana koyawa yarta.
Kananfari citta duk ta zuba dai-dai misali ta kunna Gas ta ɗora.
Ta yanka Ananas ta matse ruwan rabin ƙaramin cup, ta ajiye gefe tana tsaye.
Zarah dai bata tanka ta ba, tana gefe tana nata uzurin.
Ta rigayi Suhaima tunda ita Black tea ne.
Ta juye a Flask ta ɗauki Cups 2 ta ɗora a tray ta fice tabar Suhaima.
Nasir ya ɗan jima gun Yah Boss suna magana ta sirri Sbd ya kusa tafiya Mission ganin goma na dare tayi ya masa sallama ya sauko ganin Juhainah kamar tana bacci ya tafiyarsa.
Sai bayan tea ya tafasa Suhaima ta ɗauko Ananas ta juye cikin tukunyar ta kashe Gas ɗin ta ɗauki ƙaramin Flask mai kyau ta juye ta ɗaura saman tray'n tangaran ta ɗauki Cups Glass kalar Brown har guda uku ta jera ta ɗauko ta fito parlour.
Ajiye tray'n tai saman ƙaton Center Table ɗin ta iso gun Juhainah da take kwance idanunta rufe tana rungume da Cushion.
Zama tayi tana kamo hannunta a hankali tace.
"Aunty J ki tashi muje waccan matar fa ta tafi gun Dadd please ki tashi muje"
Juhainah ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta da suka rikiɗe sukayi Ja.
A hankali ta miƙe zaune tana kallon Suhaima a hankali tace.
"So kike ya sake dizgani yasha nata tea mu yaƙi shan namu?"
Suhaima tana ɓata fuska sosai tace.
"Allah bazai dizga mu ba ki tashi muje idan bama mata abun takaici bazata bar gidan ba fa"
Juhainah ta goge hawayen fuskarta tana miƙewa tsaye tana gyara hular kanta yanzu ma riga da wando ne a jikinta kalar da Yah Boss yake anfani Brown colours (Walnut)
Kasancewar yanada duhu sosai sun mata kyau a ɗan ƙaramin jikinta, saboda a buɗe suke kayan akwai taushi.
Suhaima tace.
"Ɗauki tray'n muje, kuma don Allah Aunty J karkiyi kuka a gabanta, ɗazu na lura tana cikin farin ciki da ta ga kina kuka.."
Juhainah dai bata iya magana ba ta ɗuka ta ɗauki tray'n suka nufi hanyar Stairs.
Ɓangaren Zarah sai da ta biya ɓangarenta ta gyara fuskarta ta can kaya zuwa riga da skirt na Material ta canza turare, ta saka na tayar da sha'awa ga dukkan namiji mai lafiya idan ya shaƙa sai yaji wani abu a jikinsa. Haka a tea ɗin ma ta zuba ƙwayoyin tayar da fitina ta siɗaɗa ta tafi.
Tana tafiya ne Suhaima ta fito daga kitchen...
Zarah tana hawa Stairs Khairat ta fito daga bedroom ɗin da suke yanzu da Juhainah, tana waya zata sauko suka haɗu da Zarah.
Khairat zatayi mata magana Zarah ta tare ta tana faɗin.
"My Khairat! Ina ne ɓangaren Yayanku?"
Khairat ta nuna mata da hannu tana faɗin.
"Kina ga ma ƙofar shiga parlour nasa ta fita daban da kyau"
Ta ƙarasa maganar tana tafiya ta nufi hanyar sauka tana yi wa Fu'adh magana.
"Sorry heart ina magana da Aunty Zarah ne..."