← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 113

Sashe 5

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Jin an ambaci maganar aure jikinsa ya fara ƙoƙarin ɗaukan zafi, ai shi baya jin zai iya wa Khadija kishiya dan bata raye, gun haifa masa ɗa fa ta rasa ranta ita da ɗan duka ya rasasu babban rashin da yafi shekara cikin shock.
Badan yanada ƙarfin imani ba, tabbas da ya kamu da zuciya.
Shi a yanzu bai ma ga macen da zai iya so ba, babu gurbin wata mace acikin zuciyarsa bayan Khadijarsa...

Sai naga jinjinar ku masoya, yabawa shine kun amshi labarin da hannu biyu. +22796515805.😉
[26/12/2025 17:50] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne JUHAINAH💗 sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Page 3
Wani irin numfashi mai ɗumi ya furzar daga bakinsa zuwa waje.
Fu'adh ya zauna gaba kusan direba Walid ya shiga yaja motar suka nufi gate na farko, wanda tuntuni Malam Garba yazo ya buɗe ya koma Babban gate ya tsaya yana jiran zuwan su, Kamar yadda aka saba idan an iso bakin babban gate, Walid ya ɗan tsayar da motar Yah Boss ya zuge glass ya leƙo ya gaisa da malam Garba tukun suka wuce.
Dai-dai Walid ya cilla motar bakin titine Maah ta karɓi wayan a hannun Papa har Yah Boss ya fahimci Juhainah tana gida bataje makaranta...

Koda Maah ta sauko tuntuni Khairat ta gama breakfast ta fice makaranta.
Kallon Papa tayi da yake amsa waya tana zama kusansa tana faɗin.
"Khairat har ta tafi ne? Ko tana dining room yin breakfast?"
Papa a nutse yace."Ta tafi tun ɗazu ina Juhainah? Tana lfy kuwa? Amshi Abbah ne, yanata kiranki bakya ɗauka duk ya ɗaga hankalinsa."
Maah ta amshi tsaleliyar wayan Papa mai shegen kyau ga tsada ƙirar Samsung takai kunnenta, kafin ma tayi magana kamilalliyar murya mai cike da kwarjini da nutsuwa muryan mai daɗin saurara Anutse taji ance.
"Assalamu alaikum My Maah good morning fatan kun tashi lafiya? Ya Babies basu saka miki ciwon kai ba?"Maah ta amsa sallamar cikin farin cikin jin muryan ɗanta mafi soyuwa a ranta.
"Abbah! Ai kasan mutuniyar tawa Suhaima kai ta gado babu hayaniya, Al'amin kuwa mijin gado idan yana nan ma game ɗinsa yafi masa akan surutun banza.
Ya aiki? Kana gida ko ka fita? Jiya kuma kace zaka zo ka kwanan mana shiru ka wuce can gidanka, munata kewanka anan, tunda ka dawo daga tafiyan da kayi Paris kaƙi kazo mana kwana.
"Cikin wata irin nutsuwa da kamala da Allah ya basa, cike da tsananin son Mahaifiyarsa da kuma son duk abinda take so a hankali ya furta.
'' I'm sorry My Maah I'm busy, but God willing, I'll try to sleep at home today.
Yanzu ma ina hanya zuwa gidan nayi breakfast.
Maah! Ya nakejin anan magana yarinyar nan bataje makaranta ba me take nema gida a dai-dai wannan lokaci? Ina Khairat ita ta tafi?"
Maah ta fara kame² saboda tasan kashin ƴarta ya bushe tunda Abbah yana hanyar zuwa gidan nan.
Duk sai ta gigice ta rasa me ma zata faɗa masa saboda tasan halinsa saurin gane abu ne da shi. Jin shirunta ya sha jinin jikinsa, tabbas Juhainah bataje makaranta ba, ta samu ta shirya wa iyayensu gadar zare sun Hau ita Kuma ta naɗe cikin lafiyayyan bed tana rufe da quilt tana zuba iskanci.
Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyarsa, takaici da baƙin cikin ɗaurin gidan da Juhainah ta samu gurin iyayensu yake tafarfasa masa zuciya.
Yanzu da jarabawa garesu yau amma ta wuce ta saboda yanada tabbacin tuntuni a shiga class an fara exam, amma ita tana gida kwance tayi ƙaryan batada lafiya.
Zai yi maganinta yanzu nan, saboda bata isa ta kalli ƙwayar idanunsa ba ta masa ƙarya, kuma ya santa ciki da waje ido kawai idan suka haɗa yana gane ƙaryata yana gane gaskiyar ta.
Ƙoƙarin saita muryansa yayi cikin nutsuwar da yake ƙoƙarin sakawa kansa a hankali ya furta.
"My Maah! Did the workers cook you breakfast?"
Ajiyar zuciya Maah ta sauke da ƙarfi, har Yah Boss na ji ta cikin wayan hakan ya saka shi ciza jajayen lips ɗinsa masu taushi, kenan zarginsa ya tabbata yarinya sun gama ɗaure mata gindi bataje makarantan ba?
Cikin sauri Maah tace Sinasir ne da miyar ganye taji naman rago da ɗanyar gyada sai kunun alkama mai gyada da madara, Saboda Autah na sonsa sosai sai tea idan basu maka ba sai na saka su Rabi'ah su maka abinda kake so cikin sauri."
Ta sani sosai yake bala'in son kunun Alkama amma wai take maganar Auta take so haka kawai yaji baya sha'awan shansa a yanzun komi ma baya buƙata na breakfast ɗin da akayi a gidan, dan haka a hankali cikin nutsuwarsa ya danne komai cikin harshen fulatanci ya furta.
"My Maah su haɗa min Turkish tea da Meat balls ma ya isa thank you I love you. Kiba Papa phone ɗin."
Maah ta beƙawa Papa wayan tana kallonsa shi ma kallon ta yake yi yana faɗin.
"Wai me ya sami Juhainah ne? Ko dai nima naje ne naganta Wlh hankali na yaƙi kwanciya jarabawa da garesu, har 8 ya wuce na safe bata fito, batada lafiya ne...?"
Maah tai saurin matsowa jikinsa tana saka hannunta tana rufe masa baki na Seconds biyar tana masa nuni ya katse wayan kar Abbah yaji.
Ganin ya fahimci me take nufi ta janye hannunta daga bakinsa, tare da janye jikinta daga nasa.
Papa yakai wayan kunnensa yana faɗin.
"Alo Abbah! Kana jina kuwa?"
Takaici ya saka Yah Boss lumshe fararen kyawawan manyan idanunsa masu wani irin kwarjini da haske.
A hankali slowly ya furta."Hello Hello Papa banaji bari na katse har na iso."
Ya ƙarasa mgnar yana katse kiran zuciyarsa na tafasa da takaicin Juhainah...
Yana bala'in son ƙanwarsa amma da ƙarfi da yaji yanajin tsananin tsanarta da haushinta, saboda mugayen halayanta da shagwaɓa taɓara rashin mutuncinta idan bata ganinsa, ta fitini kowa, bata tsoron kowa sai shi idan shi ya mata wasa ya zasuyi da ita?
Shi damuwarsa ƙin karatun da take yi, na Qur'an ɗin ma dakyar suka samu tayi sauka shima sai da ya yi da gaske ya tsaya kanta sosai taci uban duka wajansa kafin karatun ya zauna akanta.
Wata irin iska mai tsananin ɗumi ya furzar daga bakinsa yana ɗan murza goshinsa kaɗan².
Fu'adh ya waigo ya kalleshi yana kwantar da murya yace."Sir akwai damuwa ne?"
Idanunsa masu saka mutum kasala ya ɗago yana kallon Fu'adh ya ɗan taɓe jajayen lips ɗinsa kaɗan ya ɗan lumshe masa idanun ya kauda kansa yana kallon titi baice uffan ba, ba kuma zai ce ɗin ba.
Fu'adh yasan duk duniya Juhainah take sakawa Sir ɗinsa ciwon Kai.
Shi kam baisan me ya saka ba, duk ɓoye fushinsa akan yarinyar baya iya ɓoye fushinsa, koda kuwa ya mata shegen duka ne baya saurin sauka daga fushin da ta saka shi.Sanin ba magana zaiyi ba yaja bakinsa yayi gum.
Waya ta ɗauki Ringing Fu'adh ya kalli sunan mai kiran abokin business ne, ya ɗaga da sallama yana faɗin."Sir na wani uzuri yanzu bazai samu daman amsa waya ba, zai kira daga baya."Yana gama faɗin haka ya katse kiran, saboda yasan a yanzu baya ma son wani dogon surutu kusa da shi.
Matashiyar budurwa cikin matsanancin tashin hankali, take gudu sosai.
Baza ta wuce shekaru 27 ba zuwa da 28, baƙa kyakkyawar gaske duk da baƙinta kallo ɗaya zaka mata kasan Black beauty ce.Tana da kyan diri da sura mai ɗaukan hankali duk wani namiji mai lafiya, saboda tanada ɗan jiki kaɗan.
Sai dai kallon farko kana mata kasan bata cikin wadata talauci da rashin jin daɗin rayuwa na ɗawainiya da ita, ganin yadda baki ɗaya take a firgice babu wata alamar nutsuwa a tare da ita.
Doguwan rigar da take sanye da ita ta karamar atamfa duk ta koɗe haka hijabin jikinta ma wanda kaɗan ne bai kai ƙasa ba Brown kala duk ya koɗe, sai dai kayanta tsaf a wanke babu alamun datti, haka ma tana sansanyan ƙamshin humran mai sauƙin kuɗi.
Slippers ne a ƙafarta shima Brown kala ne saboda Allah ya ɗora mata son kalar duk abinda yake Brown, ba laifi sabone alamar bai jima da siya ba.Jin zuciyarta na mugun bugawa saboda gudun da take yayi yawa, bare tanada ƴar ƙiba, dole ta gaji idan tayi gudu,tsayawa tayi tana maida numfashi,tana waigawa ganin ba'a biye da itan.
Tafiya take tana zubar da hawaye kana kallon yadda take tafiyan kasan ta gaji jure wa kawai take yi, alamu kuma sun nuna tana cikin matsanancin tashin hankali saboda sai wai waye take yi har tana haɗawa da ɗan gudu ta matsu ta fito bakin titi ko zata tsira...Dab da isa bakin titi kamar a mafarki ta hango motar gidan da ta fito dan tsira da mutuncinta, ana ƙoƙarin cimma ta.
Ƙananun idanunta masu matuƙar kyau farare ta zaro tana shiga tashin hankali ta tattara hijabin jikinta ta kwasa da mugun gudu cikin sanyin muryanta mai daɗi take faɗin.
"Innalillahi wa'inna alaihir raji'un!"Ta ƙarasa faɗa tana sakin kuka tare da wani irin gudu na neman ɗauki.
Saboda masifar tashin hankalin da take ciki bata ma san ta iso bakin titin ba bare har ta haye saman tsakiyar titin tana wani irin kuka.
Ga shi safiya ne babu jama'a sosai sai ƴan tsirarun mutane.
Tun daga nesa Walid ya hangota yana ƙoƙarin jan burki tare da zuba mata horn hankalinsa tashe ganin tana kusantar motar, ga burkin yaƙi tsayawa.
Yah Boss ne ya ɗago lumsassun fararen idanunsa don ganin abinda Walid yake zuba wa horn haka.
Idanunsa suka ga mace kamar ma mahaukaciya ce ke ƙoƙarin tarbar motar tasu.
Da ɗan sauti cikin zazzaƙar muryansa ya furta.
"Ya Allah! Fu'adh! kayi wani abun kar mu ɗauki rai, ko tayi mummunan rauni."
Fu'adh cikin zafin nama ya amshi driving in daga hannun Walid.
Ƙoƙarin taka burkin yake amma ina abun yaci tura saboda ta cimma su, yana ƙoƙarin kaucewa gangarawa bakin titi bisa tsautsayi ji kake ƙuuuttt an bigeta tayi baya ta zube ƙasa sumammiya hancinta na fitar da jini.
Ƴan tsirarun jama'ar da suke kallon abinda ya faru dukkan su suka fara salati saboda dai kowa yasan ba laifin direban ban bane, duk da motar Glass ɗin duka ɓaƙine ba'a ganin na cikin motar, amma ansan matar itace acikin shock ɗin da tai sanadin da taja aka buge ta, ga shi motar kallo ɗaya zaka yi motar kasan ba ƙaramin mutum bane a cikinta, saboda haɗuwarta da girman ta da kyawunta.
Yah Boss ya lumshe lumsassun fararen idanunsa yana ɗan jujjuya kansa, tare da ɗan jingina bayansa da allon kujera.
A hankali cikin karamin sauti ya furta.
"Innalillahi wa'inna alaihir raji'un!
Fu'adh! Ayi saurin dubata, Allah ya taƙaita wahala."
Fu'adh da Walid kusan a tare suka fito daga motar suka nufi gunta da take sheme a ƙasa babu wani lamar rai a jikinta.
Fu'adh ya duƙa gabanta yana tunanin ya zai yi da ita dole kenan shi zai ɗauketa ko ya zai yi?
Kallon Walid ya yi wanda shima shi yake kallo dan sanin abun yi.
Yah Boss da idanunsa suke lumshe, tattausan tafin hannunsa saman goshinsa.
Jin shirun ya saka shi ɗago kansa yana sauke idanunsa akan su Fu'adh da suke duƙe amma basu da niyar taɓa yarinyar ga shi baya son a yi masu wani taro a wajan, duk da yanada yaƙinin motar zata saka ma wasu daga cikin tsirarun mutanen shakkar isa gun sanin dole wannan motar ta babban mutum ne, saboda ba'a san shi da motar sosai ba duk da bata rufe wata da kawota ba, kuma bata shafi aikinsa ba idan dai yaga dama yake fita da ita police station ɗin, duk da yanada motoci kusan guda 7 kala² na kece raini amma yana son motar nan sosai.
Ganin suna duƙe gabanta basuda niyar yin abinda ya dace, ya hango waya a hannun Fu'adh, yayi saurin aika masa text cikin seconds goma....
Chapter 5 · 0% Book details