Sashe 20
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yau baisan hukuncin da zai ɗauka akan Juhainah ba, tunda ba lallai ta tashi Mutum rass ba.
Glass ɗinsa ya maida idanunsa saboda Jan da lumsassun fararen idanunsa suka koma.
Janye ƙafafuwansa yayi ta zube ƙasa saman tayis, babu alamar motsi a tattare da ita.
Kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa yana takunsa mai cike da nutsuwa.
Wata leda mai kyau da tambarin Companyn sa a jiki ya buɗe ƙaton drawer ɗinsa ya ɗaukota ya rufe drawer ya kai lumsassun fararen idanunsa akan pictures ɗinsu da Khadijah da ya'yansu, ya lumshe idanunsa ya feso iskar bakinsa waje ya buɗe idanunsa ya juya ya tafi.
Koda yazo parlour bai kalli inda Juhainah take ba, ya wuce.
Ƙofar parlon ya murzawa key, ya zare key ɗin ya saka cikin aljihunsa ya tafiyarsa.
★
Juhainah babba bata farka daga bacci ba sai Bayan sallar juma'a, koda ta farka bata yarda ta fito parlour ba, wanka tayi tai sallah, ta zauna ta kira mahaifiyarta sukayi fira amma ko kusa bata faɗa mata halin da take ciki ba, saboda gudun kar ta shiga tashin hankali...
Su Suhaima suna isa gida ta sanar da Maah Dadd ɗin su zaizo bayan sallar juma'a su tafi gidansu gun Auntie Juhainah.
Yah Boss gidansu ya wuce ɗaukan yaransa, da kaiwa Maah saƙonta.
Maah zaune a ƙaton parlour su tana jan cazbi, duk girman parlour ƙamshin turaren wuta yake tashi ta ko ina.
Khairat zaune ƙasa saman Carpet tana yiwa Maah tausan ƙafafuwanta.
Suhaima da Al'amin ne suka sauka daga Stairs, sai ƙamshi suke, Al'amin sanye da wasu tsaddadun ƙananun kaya sunyi masa masifar kyau.
Yayin da Suhaima take sanye da riga irin ta Larabawa Black tayi mata masifar kyau kana kallon rigar kasan Naira tasha kashi, haka takalmin ƙafarta rufaffe fari Tass ya mata kyau, mini Arabia mini hijab iya kafaɗarta fari an zagaye shi da ado tsaf ta fito kana kallonta kasan Tabbas jansin Larabawa ce.
Tun kafin su iso Maah tace.
"Suhaima an sha kyau, mai gida Al'amin gaskiya yau auren nan na ƙara ƙulla igiyoyi uku akan ukun sun zama 6"
Khairat tai dariya zatayi magana ƙamshin turaren Yah Boss ya bayyana shigowarsa falon.
Zazzaƙar muryansa ta ratsa kunnuwansu, shi da Fu'adh.
Maah ta amsa tana murmushi, tace.
"Fu'adh! Sannunku da zuwa"
Khairat ta kalli Fu'adh suna haɗa ido ya ɗaga mata gira yana kashe mata ido a siyasance. Tai saurin ɗauke kanta.
Al'amin da Suhaima da gudu suka nufi Dadd ɗinsu suna faɗin.
"Oyoyo Daddyn mu"
Hannayensa ya ware masu suka tafi da gudu suna faɗawa jikinsa.
Ya rungumesu ya ɗauke su dukansu kamar ba masu girma kamar bai ɗauki mutane ba, haka tafiya dasu, Al'amin yanata dariya.
Maah tana murmushi sai kallonsu take cike da soyayya.
Fu'adh ya ajiye ƙatuwar ledar mai shegen kyau a gaban Maah, ya koma ya zauna a lafiyayyar Turkish Chair yana faɗin.
"Maah ina yini, kinga yaran nan Dadd ɗinsu kawai suka tarba"
Ya ƙarasa maganar yana satar kallon Khairat cike da matsananciyar ƙaunarta.
Ita kuma kanta ta sadda tana gaishesa ƙasa².
Ya amsa yana maida hankalinsa akan Yah Boss da ƴaƴansa.
Maah tana murmushi tace.
"Fu'adh! kunfi kusa da ƴaƴanka, wannan laidar me muka samu? Naga tambarin S.A Janfar Shopping Mall."
Yah Boss yana zama kusan Maah yaran ajikinsa, a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Eh Maah jiya na kwaso maki a can na manta ban kawo ba Na wuce dasu gida"
Khairat ta gaishesa cikin girmamawa tana miƙewa tsam saboda kunyar Fu'adh bata son kallon da yake aika mata.
Yah Boss ya amsa gaisuwan cikin tsare gida ya furta.
"Ke! Har kin dawo daga school ɗin ne"
Tsayawa tai cikin girmamawa tace.
"A'a my brother yau bamuyi ba sai Monday"
Baice uffan ba, ya kalli Suhaima yana gyara mata ɗan ƙaramin hijab ɗinta wanda ya mata kyau.
A hankali ya furta
My Babies ina kayan tafiyar ko ba'a ɗaukan komai?"
Suhaima ta ɗaga kanta tana faɗin.
"My Dadd can ma ai akwai komai"
Maah tana murmushi tace.
"Abbah! Duka wannan kaya sunyi yawa daman inada saura da ko taɓawa banyi ba, fatata sai ƙara murjewa take Abbah da maiyuka da sabulu masu tsada,sannu Allah ya maka albarka ya kare ka daga sharrin dukkan abin ƙi, amma Suhaima Amina zata biku ko?"
A hankali ya amsa da.
"Allahumma Ameen My Maah, Papa bai shigo ba...?"
Sallamar Papa ne ta katse masa magana.
Papa fuska sake yake.
"Abbah! A she kazo"
Suhaima tace
"A'a ta zauna har mu dawo, akwai mai mana komai..."
Yah Boss ya katseta yana faɗin
"No! Babies zata bimu tunda kuna nan, namiji bazai shiga ɓangaren ku gyara ba, ga Juhainah ma na nan, Oya je kira Amina ko Halima."
Suhaima ta tafi cika umarnin mahaifinta.
Yah Boss ya janye Al'amin daga jikinsa ya miƙe cikin girmamawa ya tarbi mahaifinsa ya rungumeshi yana faɗin.
"Papa Barka da Warhaka Barka da sallar juma'a"
Papa ya shafa kansa yana murmushi cike da tsantsar ƙaunar ɗansa yace.
"Alhamdoulillah! Abbah ya haƙuri da Autah?"
Yah Boss baice uffan ba ya kama hannun Papa suka zauna.
Fu'adh ya gaishe da Papa cikin girmamawa.
Papa ya amsa cikin sakin fuska.
Al'amin ya koma tsakiyarsu ya zauna.
Maah tace.
"Abbah kuje dinning room an shirya komai"
Yah Boss yana lumshe kaifafan lumsassun fararen idanunsa a hankali ya furta.
"Maah bana jin cin komai yanzun, Fu'adh! Kuje kuyi Lunch sai mu wuce"
Fu'adh yana kallon uban gidansa yace.
"Ok Babies kuzo muje"
Suhaima ta maƙale kafaɗa cike da izzarta take faɗin.
"A'a sai naje gidan Dadd sai muci da Aunty Juhainah, ni indomie ma zanci"
Yah Boss ya zubawa Suhaima lumsassun fararen idanunsa, bai ce komai ba.
Maah tace.
"Kaga ƴar Juhainah, ai Fu'adh kaje ka cika cikinka karka biye masu, ai tun ɗazu nake bin kansu sunƙi yarda su ci, idan sunje sai suci a can ɗin"
Fu'adh ya miƙe ya nufi dinning room ɗin.
Papa yayi zuru yana jiran jin Yah Boss ya masu maganar Juhainah shiru, ko fuskar da za'a masa maganarta bai bada ba.
Maah tuntuni ta ankare da hakan.
Ga shi shirun nan nasa ya masu ba abinda zai kuma cewa sai zai tafi ya masu sallama.
Sun saka shi gaba sai rarraba idanuwa suke yi, ƙarshe Papa da Maah suka shiga firasu ta duniya.
Sai Al'amin ne yake surutunsa ya haye cinyar Yah Boss.
Special Phone ɗinsa Samsung ta familles Janfar ta ɗauki ringing.
Fuska ya yamutsa yana ɗaukan wayan, ganin sunan Mamah Bilkisu ya saka shi picking call ɗin, tare da sallama cikin girmamawa ya gaisheta.
Daga can Jigawa Hajjah Bilkisu dattijuwa kyakkyawa farar Bafulatana, mai tsananin kama da Yah Boss da Papa, ta amsa sallamar tare da amsa gaisuwan cikin Yaren fulatanci tace.
"Abbah! Ya aiki da yaran albarka? Fatan kuna cikin ƙoshin lafiya?"
Yah Boss ya gyara zamansa cike da nutsuwa da kamewarsa ya furta.
"Alhamdoulillah! Mamah, ya Jigawa kowa lafiya? Su Baba su Taj?"
Hajjah Bilkisu ta amsa da.
"Alhamdoulillah! Kowa ga auta yana zaune ciwon kai yake yau baije school ba.
Yawwa Abbah! Ina son gobe idan Allah ya kaimu, kazo Jigawa tunda weekend ne, umarni na baka ba neman sanin kiran da nake maka ba Bass."
Yah Boss ya ɗan lumshe kaifafan lumsassun idanunsa yana furzar da isar bakinsa waje, a hankali cikin biyayya ya furta.
"Ok Mamah in sha Allahu, zanzo ai ban isa neman sanin kirana ba"
Cikin tsare gida dan kar ya ɗauki maganarta wasa, ta furta.
"Yawwa Allah ya maka albarka Abbah sai kazo, a gaishe min da kishiya Suhaima da mijina Al'amiin"
A hankali cikin ladabi ya furta.
"Ok Mamah"
Katse kiran tayi bayan ta masa sallama.
Maah da Papa sun gane Hajjah Bilkisu ce sukayi waya, sanni su suka yi haɗin sai suka waske suka nuna ma basu san da waya yayi wayar ba.
Kallonsu yayi cikin nutsuwarsa da kamewarsa ya furta.
"Gobe in sha Allahu zanje Jigawa zanbi Flight, maybe bazan kwana ba"
Maah da Papa suka ce.
"Ma sha Allahu Ubangiji ya kaika lafiya Abbah"
Ya amsa da.
"Ameen ya Allah"
Ya faɗa yana miƙewa ya kama hannun Suhaima da Al'amin yana faɗin.
"Maah Papa mun tafi zuwa dare zan leƙo"
Fu'adh ma ya masu sallama suka tafi.
Maah ta kalli Papa bayan sun tafi tace.
"Allah ya temake mu ta shawo kansa yayi auren nan, Wlh banajin daɗin ganinsa haka nan Harɗo"
Papa yace.
"In sha Allahu za'a dace, ina Khairat?"
Maah tace
"Ta gudu ɗaki"
Papa yayi dariya yana faɗin.
"Kawo min abincina nan"
Maah ta miƙe tana murmushi.
★
Ammar kwance yake tun bayan da ya dawo daga Masallaci yake kiran Juhainah wayar switch Off, duk hankalinsa a tashe.
Zaune ya miƙe yana faɗin.
"Wai yarinyar nan miye a kanta? Ni zata rufewa waya? Ai yanzu Wlh zan tafi gidansu, ayita ta ƙare, sanin kanta ne bana jure rashin jinta a waya"
Ya miƙe yana kiran number Surayya ƙawar Juhainah, itama bai sameta ba, tana school wayan switch Off.
Shiryawa yayi tsaf cikin shigar alfarma yana baza ƙamshi, yayi kyau sosai samarta karsa ta fito, da kyansa, ya fita ta ƙofar baya saboda baya son Dady Najib ya tuhumesa.
Lokacin da ya iso ƙaton gate ɗin gidansu Juhainah, dai-dai lokacin kememiyar motar Yah Boss Walid ya danno hancinta waje.
Yah Boss ya zubawa motar Ammar ido kallon rashin sani, dan duk ƙaninsa babu mai kalar motar, kyawawan idanunsa ya zubawa Ammar da yake ƙoƙarin fitowa daga cikin motar sanin zai yi wuya a barsa ya shiga cikin gidan da motar Ba tare da izinin masu gidan ba.
Yah Boss jinin jikinsa ya sha Yaron neman Juhainah yazo, ba kowa bane sai Yaron da ɗaga kiransa wato Ammar.
Kai tsaye Ammar ya dimfari gate.
A nutsu cikin kamewarsa ya furta.
"Walid! Dakata! Yaron nan ɗazu kamar naga gilminsa agun taron da mukayi na ƴan kasuwa, but banda Tabbas, because bazan tsaya ɓata lokaci ba, ƙarewa mutane kallo
Fu'adh! yi sauri kiramin Yaron can da yayi parking yana ƙoƙarin shiga gidan.
Fu'adh ya amsa da.
"Ok Sir"
Ya buɗe motar ya fice.
Ammar ya buɗe ƙaramin gate yana ƙoƙarin shiga gidan Fu'adh yace.
"Ɗan samari bakaji ba"
Ammar ya juyo yana kallon Fu'adh.
Ya beƙa masa hannu sukayi musabaha.
Fu'adh ya jefo masa tambaya.
"Wajen wa kazo?"