← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 113

Sashe 32

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yah Boss ya sauke ajiyar zuciya yana zuba dogayen fararen ƙafafunsa saman ƙaton Center table à hankali ya furta.
"Very good thank so much, zanyi tafiya sai Monday zan dawo dan haka zuwa ranar Talata ina son ganin manyanka can gidan mu babba a tsayar da magana, amma inason taci gaba da zuwa makaranta"
Jamal ya amsa da.
"Ok in sha Allahu babu matsala"

Yah Boss idanunsa akan Tv ya furta.
"Thank you Jamal naji daɗi sosai...."

Jamal sallama ya masa ya tafi Nasir ya rakasa har mota ya dawo gun yayan nasa sukaci gaba da tattaunawa.

Raudah suna zuwa bayan gari ta tsayar da direba ta fito ta shiga wata mota da take jiranta anan kusan awa ɗaya.

Suna fara tafiya ta beƙa hannu ta ɗauki sigari ta kunna tana busa hayaƙin ta laulayo ashar ta maka.
Wani matashine yake driving, yayi dariya yace.
"Shegiya yau rana ta ɓaci a karo na farko da kika kasa cin nasarar aikin ki.. "
Duka ta kai masa tana busa sigarin tace.
"Wlh bai gagareni ba, fasawa nayi su nemi wani sai naga bayan wannan shegiyar hankalina zai kwanta, mayya jaraba Masifa naci munafuka duk ni ɗaya, wai harda sharrin nace zan auresa, ai Wlh ni soyayya bata gabana duk naji inason sa amma bana ba soyayya nasara a rayuwata, because tana hana cimma nasara, Kai dai muje na huta zuwa gobe na samu Alhaji Nuhu ayi gwada da gwa, dan Wlh bazan nutsu idan banga ƙarshen Juhainah ba..."



Washegari da wuri Yah Boss ya shirya tafiya zuwa Jigawa.
Juhainah na bacci tun bayan sallar asuba, Khairat da yaran sun sauko suna breakfast ya kira Khairat ya mata magana ko me ya gaya mata oho ya sa kai ya tafi, Suhaima da Al'amin dasu Shuraim har gun mota suka rakasa suka dawo sukaci gaba da breakfast ɗinsu.
Kasancewar a jirgi zasu tafi shi da Fu'adh da Walid kaɗai suka tafi, tunda weekend ne.



Jigawa
Anguwan
ASOKORO

Gidane ma sha Allahu Mai kyau da tsari yanada faɗi sosai.
Wani parlour madaidaici an gyarasa Center table shaƙe da kayan tarbar baƙo, wani irin turaren wuta mai sheƙan ƙamshi yake tashi a parlourn.

Sai can Asalin babban parlour shima ko ina ƙamshi yake tashi, dattijuwar mata zaune mai tsananin kama da Yah Boss, jajir da ita, su uku ne zaune sunata fira cikin raha ɗayar matar bazata wuce shekaru 32 ba, fara gogagiyar ƴar boko, kana kallonta kasan Kanuri ce, duk da batada tsaga Amma tayi sigarsu ta kece raini, tana ƙamshi, tanada kyau ma sha Allahu a ko ina za'a nunata, ga nutsuwa, duk da boko ya mata nisa amma akwai tarbiyya.

Daddaɗan turarensa ya kawo ma parlour farmaki Tun bai iso ba.
Sallamarsa ce ta saka su waigowa.
Yayin da Zarah ta tsira masa madaidaitan idanunta na seconds 8 tai saurin janyewa kafin ya kamata.
Tasbihi takewa wa Ubangijin da ya ƙera Yah Boss, tabbas hajiya Mama ta gama mata komai da kyautar wannan zankaɗeɗen mijin, duk duniya bata taɓa tunanin sake son wani ɗa namiji ba, sai ga shi kallon farko a zahiri ba hotunan sa da hajiya Mama ta nuna mata ba, ya mata ɗari bisa ɗari.
Taj ne Autan Hajjah Bilkisu ya miƙe yana farin cikin ganin Yah Boss, ya rungumesa.

Cikin farin ciki Hajjah Bilkisu ta miƙe tana faɗin.
"Lale marhaba barkanku da zuwa Abbanah, Fu'adh! sannunku da zuwa. Gaskiya Yau ina cikin farin ciki marar misaltawa..."
[16/01 14:18] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 18*

Yah Boss ya ɗan saki fuska yana gaishe da hajjah Bilkisu, yana riƙe da hannun Taj ya zauna yana tambayarsa karatu.
Fu'adh ya gaisheta yana zama Walid ma.
Duk ta amsa cikin sakin fuska.
Yah Boss yaji ana faɗin.
"Sannunku da zuwa ina yinin ku"
Ya ɗan ɗago fuska kame jin bai san muryan ba.
Kallo ɗaya ya mata ya janye idanunsa ya amsa da.
"Lafiya"

Hajjah Bilkisu tana washe baki tace.
"Abbah baka santa ba ko?"
Tsam Zarah ta miƙe ta nufi bedroom wai kunya.
Fu'adh a ransa yace.

"Tabdijam! Zaki gama sune-sunan-ki ne"

Ba tare da Yah Boss ya kalli kowa ba dan bai ma san ta tashi ya furta.
"A'a"
Hajjah Bilkisu tace.
"Zarah ɗiyar marigayi Maryamu aminiyata tun ina amarya muke tare da ita anan Jigawa, a hannuna aka haifeta Ita da yatunta da ƙanninta, tayi aure shekara biyar baya mijin ya rasu a Saudiyya yaje umara ciwon ciki, kuma kaga baiwar Allah bata haihu ba ma. Lawyer ce"
Fu'adh yace.
"Allah Sarki abun tausayi mutuwar miji Allah ya kawo babban Rabo."

Yah Boss ko uffan bai ce ba, saboda ya gano inda magana ta dosa, akanta akace ana nemansa Jigawa, tabbas a yau ko zasu koma Yola, gwara yaje guest house ya huta amma babu maganar kwana a Jigawa har biyu.

Hajjah Bilkisu ta amsa da.
"Ameen in sha Allahu ta samu, Abbah ku tashi muje kuci wani abun"

Yah Boss daman neman abinda zai rabasa da parlour yake, zuwat ya miƙe yana kallon Taj cikin kamewarsa ya furta.
"Muje ka bani labarin ya karatun akwai daɗi shiga secondary school."

Taj dariya yayi yana riƙe hannun Yah Boss.
Hajjah Bilkisu ta shiga bedroom ta iske Zarah kwance sama bed tana danna waya.
Tace.
"Au kwanciya kikayi? Sai fa kinyi haƙuri da halinsa, kema kin ɗanɗana mutuwar miji shekara huɗu baya, ba daɗi dan haka karki damu da halinsa zai saba dake da zaran an ɗaura auren, kin tare a gidansa, ke dai ki kasance mai haƙuri da juriya zakici riba kinji?"
Zarah tayi murmushi tace.
"Ba komai Hajiya Mama nasani mutuwar miji ko mata akwai zafi, shekara 4 ina cikin shock"
Hajjah Bilkisu tace.
"Yawwa bare naje na samesa ke zuwa anjima idan nayi magana da shi zan turaki ku gaisa"

Ta ƙarasa maganar tana wucewa.
Zarah ta lumshe matsagaitan idanunta tana jin farin cikin da ta rasa shekaru 4 baya, suna son dawowa Ba tare da ta shiyawa hakan ba.

Zaune suke a parlour da aka sauke su, Yah Boss waya yake cikin nutsuwarsa da kamewa, ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Hajjah Bilkisu ta shigo da sallama tana washe baki.
Su Fu'adh suka amsa suna miƙewa.
Hajiya Bilkisu tace.
"A'a ku zauna kuci abinci Fu'adh ina zakuje"
Fu'adh yace.
"Muna dawowa Hajjah Mama, ku gaisa sosai da Sir"
Ya ƙarasa maganar suna ficewa shi da Walid, wanda yake gyara bindiga jikinsa.

Hajjah Bilkisu ta zauna kusan Yah Boss tana jiran ya gama wayan.
Sallama yayi da wanda suke wayan ya ajiye wayan yana kallon Hajjah Mama.
Murmushi tayi tana tsiyaya masa ruwa marar sanyi ta beƙa masa tana faɗin.
"Abbah saki ranka sha ruwa ba auren dole zan maka ba"
Cup ɗin ya amsa yay Bismillah yasha kaɗan ya rage yana ajiye Cup ɗin.
Ta ɗauki plate ta zuba masa lafiyayyun girkin da ta masa da kanta ta ajiye masa gabansa, tace"Ci Please"

Yah Boss ya ɗauki spoon lomar farko ya jinjina kansa baice uffan ba.
Hajjah Mama tayi murmushi tana faɗin.
"Ai nasan kana son kalar girkin"

Ba laifi yaci kusan spoon 8 Sbd shi ba mutum bane mai yawan cin abinci sosai kaɗan yaci bass sai dai yanada son fruits sosai.
Yanzu ma fruits yaci ba laifi ya yagi tissus ya goge bakinsa, yana Hamdalla.
Hajjah Mama tace.
"Abbah! Kanada wacce kake so ko ku ka ajiye magana da ita a yanzu?"

Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zuba mata, yana danne yanayin sa.
A hankali ya furta.
"A'a Hajjah Mama Banida, ban ma ji ina son ba, bare na taya ɗin"

Hajjah Mama tace.
"Ayyah! Allah Sarki! Ubangiji ya jaddada rahma ga Khadijah, don Allah Abbah kayi haƙuri kayi aure shi ne mutuncin mutum, kaga wannan Zarah da ta gaisheka shekara 4 da rasuwar mijinta a Saudiyya, ita ma irinka ce, tace bazata sake aure ba, amma Wlh tunda na nuna mata hotonka ta amince da kai, ita da ban haifa ba ma.
Don Allah ka amince da ita ku daidaita kanku. Lawyer ce batada matsala, akwai kirki da jajir cewa ta ƙwatowa mutum haƙƙin sa, a yadda kake nan dole sai wayayya mai ilimi sosai"

Yah Boss ji yayi kamar ana soka masa mashi a ƙahon zuciyarsa, tabbas yau bazai iya kwana a Jigawa Ba, kar zuciyarsa ta tarwatse, zai lallaɓa Hajjah Mama ya tafi.

Lumsassun idanunsa ya ɗan juya yana ɓoye ɓacin ransa, ya kalli Hajjah Mama yana ƙoƙarin murmusawa a hankali ya furta.
"Ok Mama duk abinda kike so shi za'a yi banida ja, amma sai na lallaɓa Suhaima saboda bana son ta shiga damuwa"

Hajjah Mama ta shafa kansa tace.
"Allah yayi maka albarka ya kare ka daga sharrin mutum ko Aljan, bari na turota ku gaisa sai ka amshi numberta"

Yah Boss ya jinjina kansa a hankali ya furta.
"Hajjah Mama Juhainah batajin magana aure za'a mata, jiya munyi magana da Yaron zai Turo iyayensa zuwa ran talata"

Hajjah Mama tace.
"Oh Ni Bilkisu takwarata sai gyaran Allah, kai aganinka auren zai gyara mana ita ne?"

Yah Boss a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Haka nake saka tsammani Mama, inata addu'ar hakan, tare addu'ar Allah ya rabata da mugun aljaninta nan, ko rashin jin zai ragu"
Hajjah Mama tace.
"Toh Allah yasa hakan, ashe dai mun kusa tafiya Yola in sha Allahu, Ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi, Juhainah da babu acikin rayuwarta bamu san yadda zamuyi ba, bari in turo Zarah ku gaisa."

Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Yah Boss baice uffan ba.

Su Fu'adh tana fita Yah Boss ya kirasa ta waya akan su shigo suyi abinci.
Chapter 32 · 0% Book details