Sashe 62
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fuskarta ta yamutsa tana miƙe wa zaune.
A hankali ta fara magana.
"Ko ina Yah Boss ya tafi kusan kwana 4 ban saka shi idona ba, na tambaya ba wanda yace min yayi tafiya, ni kuma nasan kawai baya garin nan"
Ta ƙarasa maganar tana sauka daga bed ɗin ta nufi bathroom.
Riga da wando ne a jikinta Pink sun mata kyau sosai kanta cikin hula.
Fitsari tayi ta fito, ta ɗauki wayanta ta fice.
Kai tsaye ɓangaren Yah Boss ta nufa.
Key kamar ko yaushe ajikin ƙofar parlour.
A hankali ta murza key ta buɗe parlour ta shige ta rufe ƙofar.
ajiyar zuciya ta sauke jin sansanyan ƙamshin parlour.
Pictures ɗinsu ta ɗaga kanta ta kalla Khadijah ajikinsa tana dariya, shi kuma fuskarsa da ƙaramin murmushi wanda yay masa bala'in kyau.
Sai Suhaima da Al'amin suna rungume da iyayensu.
Bedroom ta nufa tana faɗin.
"Allah ya jiƙanki Aunty Khadija"
Ƙofar ta buɗe da key ɗin jiki.
A hankali ta sanya kanta ta rufo ƙofar.
Sansanyan ƙamshinsa ta shaƙa.
Komai tsaf kamar yana nan.
Lafiyayyan ƙaton Bed ɗinsa ta kalla yadda yasha lafiyayyun quilt.
A hankali ta isa gun da remote ɗin Ac yake sarƙafe ta ɗauka tana kunna Ac ta haye saman lafiayyan Bed ɗin ta kwanta ta shige cikin quilt tana sauke ajiyar zuciya tana shaƙar ƙamshinsa mai sakata mantawa da damuwar da take ciki.
Wayanta da take hannunta ta cire password ta lalubo number Yah Boss ta danna masa kira.
Lokacin a can Abuja da suka gama meetings na ƙarshe ko minti biyar basu yi ba da shigowa, da yamma zasu wuce Kano jirgin ƙarfe 4.
Yah Boss
Ya gama cire kayansa yana ɗaure da towel a ƙugunsa yana ƙoƙarin shiga bathroom yayi wanka sbd lokacin sallar azuhur ya gabato.
Fu'adh kuma ya fita yayi masu order abinci.
Har ya kusa isa bakin ƙofar bathroom special Phone ɗinsa ta Familles ɗinsa yaji ta fara ringing.
Anutse ya juyo ya dawo yana kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan wayan, da ya ajiyeta akan ɗan madedecin table ɗin da yake bedroom ɗin.
Sunan Juhainah yaga yana yawo.
Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya matso ya beƙa farin tattausan hannunsa ya ɗauki wayan yana picking call ɗin, ya saka speaker a hankali ya furta.
"Yas Bilkisu"
Juhainah ta ƙamƙame jikinta tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta a hankali cikin wata irin kalar shagwaɓa tace.
"My brother Habiby I miss you, ina ka tafi ka barni? Banajin daɗin Sam kowa haushi yake bani, Yanzu ma ina cikin bedroom ɗinka, kewarka nake yayana bansan me yasa nafi sonka ba akan su Yah Mustapha Umar Nasir, su ina jure fiye da sati ko ban gansu ba, bana jin komai"
Ta ƙarasa maganar a hankali tana sakin siririn kukan shagwaɓa.
Yah Boss anutse ya zauna saman Sofar da take bedroom ɗin ƙwaya ɗaya a hankali ya furta.
"Crying won't do Bilkisu"
Ƙara sautin kukan tayi cike da shagwaɓa.
Magana ya mata yadda zata nutsu da ɗan sauti ya furta.
"Listen to me, ki bar kukan nace"
Shiru tai tana juyi saman bed ɗin, a hankali tace.
"Yah Sadeeq na bari toh kana ina Please?"
A hankali ya furta.
"Kin aike Ni ne?"
Cike da shagwaɓa tace.
"A'a ina son ganinka ni dai bana son wannan gyaran jikin da ake min aure sauran wata ɗaya har sun canza Ni da gyaran jiki, Yah Sadeeq kaga yadda jikina ya ƙara kyau? Sai walwal nake yi har ƙirjina da sun ƙara girma my brother akwai magani da Mom ta bani Allah wani irin..."
Cikin wani irin sauti ya katseta yana furta.
"Bilkisu! Ki kama min bakin ki, ban hanaki yawan surutu ba? Wlh ba Ni ba idan kika kuskura kika yiwa wani wannan maganar sai yanke bakinki idan na dawo."
A hankali tayi magana cikin sanyin jiki tace.
"Ka hanani surutu kayi haƙuri ai kaine kaɗai na faɗawa, bazan ƙara ba toh.
My brother Habiby ina ka tafi? Please in kiraka video Call?"
Tsaki Yaja a hankali ya furta.
"Me zaki bani a video call ɗin?"
Kamar zatayi kuka a hankali tana ƙamƙame pillow tace.
"In ganka inason kallon kyawawan idanunka, saurin bacci nakeyi, kuma ina samun kwanciyar hankali, please my brother kaji, in kira ka karkace min a'a don Allah babban Wana"
A hankali ya furta.
"Yeah, ki kirani karki Cinye Ni Bilkisu"
Cikin farin ciki harda ihunta ta katse kiran tana kunna Data ta kirasa video Call.
Bai ɗauka ba sai da ya miƙe ya saka rigar shadda Sbd baida kaya sai towel ɗaure a ƙugunsa.
Kira biyu tai kafin ya ɗaga.
Ido 4 sukayi ta shagwaɓe fuskarta tana sake narkewa saman bed ɗinsa ta masa ƙur tana rau-rau da idanunta.
Fuskarsa ya kama sosai a hankali ya furta.
"Bilkisu! Baki da kunya ko? Me kike saman bed ɗina? Maza sauka koma ɗakinku"
Kamar zata yi kuka a hankali tace.
"Please My brother Habiby ka barni bazan ƙara ba, yanzu zan tafi idan mun gama Video Call, kewarka nake sosai ALLAH yau kowa haushi yake bani kwana uku ne ko 4 ban ganka ba, Ni su Babies kawai nake iya magana dasu.
Hararenta yayi yana kame fuska tai ƙasa da idanunta sbd yadda gashin jikinta yake miƙewa kallon da ya mata, a hankali tace.
"I love you My brother Habiby kayi haƙuri kaji? Wlh ina sonka dayawa dayawa, kallon yayana yana sakani farin ciki"
Rage kaifin idanunsa yayi kanta a hankali ya furta.
"Did you pray?"
Kallonsa tai tana shagwaɓe fuskarta a hankali tace.
"A'a yanzu aka fara kiran sallar ma."
Babu wasa akan fuskarsa bai kalleta ba ya furta.
"Oya tashi kije ɗakinku kiyi alwala kiyi sallah maza"
Kamar zatayi kuka ta miƙe ta cire quilt ɗin ta fara ƙoƙarin sauka Pink riga da wandon jikinta masu laushi sun manne a ƙaramin jikinta da yake shan gyara ƙirjinta kamar suyi magana, komai nata special number one, ga mayen ƙamshi da take.
A hankali ta amsa da.
"Toh yayana idan nayi sallah na sake kiran ka Please?"
Idanunsa yayi ƙasa dasu a kame ya furta.
"No, I can't, if I get a chance I'll call you,
idan kika kuma kira bazan ɗauka ba, kuma bazan kira ki ba"
Idanunta ta tsira masa a hankali tace.
"Okay, sorry I won't call you, please call me brother if you get a chance.
I love you My brother Allah ya tsare ka a duk inda kake, Allah yasa duk wanda zai cuceka mutum ko Aljan ya mutu a ranan da zai aikata hakan, Allah yasa duk inda ka shiga ka zama kaine number One a gurin, Allah yasa ka zama gwamna cikin ƙaramin lokaci My brother Habiby"
Kallonta yay yana ƙoƙarin sakin ƙaramin murmushi, amma kafiya irin tasa da dakekiyar zuciya yaƙi hakan, sai ma kame fuskar da ya ƙara yi, yana ƙasa da idanunsa, a hankali ya furta.
"Bilkisu! Kije kiyi sallah maza²"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, ganin ta masa ƙuru da kyawawan idanunta tana son gane murmushi yake son yi ko fushi yake son yi dan ta masa addu'a.
Jajayen laɓɓanta masu kauri ta zumɓuro gaba tana faɗin.
Habiby my brother shi addu'ar ma bazai amsa ba da Ameen."
Yah Boss
Phone ɗin ya ajiye ya miƙe yana cire rigar shadda ya nufi bathroom cikin nutsuwarsa yake taku mai tsayawa acikin zuciya, komi yayi mai kyau ne, fuskarsa babu alamun damuwa sai dai tana kamenta tunda hakan hallitarsa ne...
Juhainah rungume pillow tayi tana ajiye wayar tana faɗin.
"Wayyo ALLAH ina son Yah Boss dayawa, Wlh banso Maah ta haife mu ba, da sai na auresa ina sonsa dayawa ALLAH tun bana ganewa na fara ganewa, ya na iya tunda ƙanwa bata auren yayanta uwa ɗaya uba ɗaya"
Ta ƙarasa maganar tana shaƙar ƙamshinsa tana ƙamƙame pillow'n da yake ɗora kansa, sbd duk yawan pillow's wanda ta rungume yafi ƙamshinsa, duk da komai na Bed ɗin wani irin fitinannan ƙamshi suke amma shi yafi ƙamshinsa.
Sako wasu siraran hawaye tai akan kyakkyawar fuskarta a hankali tace.
"Yanzu inaji ina gani Jamal zan aura shine ya halatta a gareni ba Yah Boss?"
Da sauri ta miƙe tuna yace tayi Sallah.
A hankali tace.
"Astagfirullah Wa'atubu ilaikh ubangiji ka yafe min, akan saɓon da nayi akan Yah Boss ɗinah.
Bathroom ɗinsa ta shiga tayi alwala ta fito ta fice zuwa bedroom ɗinsu, nan tabar hularta saman bed ɗin.
Surayya ta iske tana sallah itama ta saka hijabi ta shimfiɗa darduma ta tayar da Sallah.
Suna idar da sallah Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗawa jikin Surayya ta ƙamƙameta.
Surayya da mamaki tace.
"Ikon Allah! Kin nutsu kenan? Haka kawai kike cimana magani kamar munyi miki laifi"
Juhainah ta shagwaɓe fuskarta a hankali tace.
"Sister Surry kiyi haƙuri yau raina tun safe a ɓace yake, amma yanzu Alhamdoulillah! Tashi mu sauka kafin su Mom su dawo da yamma, Allah ni nagaji da wannan gyaran ma"
Surayya tayi dariya tana faɗin.
"Yayata dan baki ga yadda kika haɗu ba, sai kin susuta min brother Jamal"
Juhainah ta turo laɓɓanta gaba, anyi Sa'a bata ce komai ba, ta kama hannun Surayya ta miƙe suka fito.
Yah Boss a gurguje yaje gidansu matarsa Khadijah suka gaisa da surukansa, Sbd bai da lokaci, zasu wuce Kano, amma duk da a tsatsaye ne ba ƙaramin karramawa suka masa ba, kamar zasu goya shi.
Su tambaye sa kowa lafiya ya amsa, da yake shi ba mutum mai magana bane bai sanar dasu bikin Juhainah ba, haka yake komi ya faru idan ba tambayar sa zakayi ba, baya taɓa faɗa maka halin da ake ciki...
A Kano yau kwanansu biyu, yau suke kammala taron da yamma suna gamawa sai Yola.
★
Tsawon kwanaki uku
Ammar yanata jiran Raudah ta kira shi shiru bata kira ba, ɗaurin auren ya rage sauran kwanaki uku kenan.
Juhainah tun randa sukayi video call da Yah Boss, ta nutsu kuma taji kashedin sa bata sake kiransa ba, bata saki zance ba, gun kowa, kullum cikin jiran ya kiranta take kamar yadda yace zai kiranta shiru, hakan yasa duk ta damu sosai sai dai tana dannewa. Ga shi taji ana cewa gobe zata koma gidansu gun Maah.