← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 113

Sashe 38

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari ranan ɗaurin aure misalin ƙarfe 8 na safe. Su Khairat sun tafi school, mintina 20 da suka wuce.

Yah Boss anutse yake taka Steps yana wani irin sansanyan ƙamshi, sanye yake kayan gyam jikinsa, kalar Brown, tsananin taushin kayan da kyawunsu suka kama masa lafiyayyan jikinsa mai cike da mazantaka, hasken fatarsa ya ƙara fitowa, fuskarsa kame sosai yake taka Steps ɗin.
Yana gama saukowa wayansa na ɗaukan ringing.
Bai ɗaga ba a nutse ya nufi dinning room saboda jiya bai zauna ba, sau ɗaya yaci abinci, yanzun kansa na ciwo sosai yana son shan tea kafin yaci wani abun....
[20/01 14:38] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 21*

Juhainah
Zaune take akan dinning, sanye take da riga da skirt ƴan Pakistan, pink colour, duk ta kuma figewa sai idanu da hanci, fuskarta ta ƙara haske, bakinta ya bushe, ta rasa abinda yake mata daɗi acikin rayuwarta.
Matsalar ɗaya duk yanayin da zata shiga bata iya hana kanta cin abinci koda tanaci tana kuka ne zata cika cikinta dam, saboda bata iya jurewa yinwa a rayuwarta.
Yanzu ma plate ne a gabanta tana cin Brunch, tana haɗawa da tea mai kauri yaji Madara.
Ƙamshinsa ta shaƙo takai Brunch bakinta har zata waiwayo sai ta fasa, ta ajiye Brunch ta ɗauki Cup ɗin tea takai bakinta.
A nuste yaja kujara ya zauna, yana ɗaukan Cup ya ajiye gaban ƙaton Flask mai kyau ya danna madannin tea ɗin mai azabar ƙamshin, ya dinga tarara cikin Cup ɗin Glass mai kyau kalar Brown.

Juhainah tunda ya zauna ta ɗago ta kafa masa dara-daran idanunta, rauninta yana sake bayyana, ta ma manta yau kwana nawa bata gansa ba.
Abun takaicin kamar ma baisan tana gun ba, ko kallon ɓangarenta bai ba.
Haɗiye Brunch ɗin tayi tana kallonsa kamar zata fashe da kuka cikin sanyin da jikinta yayi tace.
"My brother good morning I miss you, I'm sorry, idan nayi maka wani abun ka yafe min, Wlh bazan kuma ɓata ranka ba promise.
Nace maka na amince zan auri Jamal akan ka raba zumunci dani, idan kowa zai ƙyaleni cikin familles Janfar zan ɗauka banda kai da Maah da Papa, kayi haƙuri Please Yaya Kaji."

Bai kalleta ba, baice uffan ba, ya fara haɗa tea ɗin a nuste ya fara sha fuskarsa kame, wayansa tana ringing.
Juhainah ko ta ƙura masa dara-daran kyawawan idanunta ganin yadda kayan motsa jikin sukayi masa bala'in kyau.
Yah Boss
Ganin number taƙi fasa kiransa kira na 5 kenan.
Picking call ɗin yay yana saka wayan a speaker ya ajiye yana shan tea ɗinsa cikin nutsuwarsa.

Hawaye suka fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta, ta ajiye Brunch ɗin hannunta tana ware idanunta tana more kallonsa, cikin shagwaɓa a hankali tace.
"My brother don Allah nace kaji?"

Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ɗago ya zuba mata, tai saurin kifa kanta akan table ɗin ta fashe da siririn kuka, marar sauti.
Goshinsa ya ɗan shafa ya tura hannunsa cikin sumar kansa, ya sake kai Cup ɗin bakinsa.

Daga can Zarah tayi masa sallama bata jira ya amsa ba a hankali cike da kissa tace.
"Baby mi kayi wa my daughter take kuka?"
Yah Boss yana kallon Juhainah a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"No! Ki nemi Babynki tun dare bai maki ba, ke kunya bakya ji tsofai-tsofai dake wai Baby, wai ke wace irin matane? Miye na kiran nawa? Akwai abinda zan miki ne?"
Zarah tayi murmushi tace.
"Eh inaso idan zakuzo ɗaurin auren kayi shigar da babu angon da ya taɓa irinta duk Nigeria..."

Katseta yayi a cikin nutsuwarsa a hankali muyansa mai daɗi ya furta.

"Waye zaizo ɗaurin auren naki? Toh ki cire ran hakan, kuma duk abinda kike ganin ni inda shi akwai waɗanda suka linka ni kuɗi kyau nasaba nutsuwa ilimin komai ma akwai na gaba da kai, kina magana kamar bakida ilimin addini dana Bokon ma"

Ya ƙarasa maganar hankalinsa kwance.

Juhainah tana ɗago kanta tana hawaye ta ƙurawa iPhone ɗin Yah Boss dara-daran kyawawan idanunta.
Zarah daga can tayi murmushi tana faɗin.
"I love you My Baby, ina na tsufa? Shekaru 32 kacal fa, nidai a wannan zamanin da muke ciki banga wani matashi a Nigeria zai shallake ka ba, tabbas Babyna.

Toh kai idan baka auri irina ba Ƴar cikinka kake son aura mai ƙananun shekaru ko wace irin mata kake so Babyna...?"

Takaicin kalaman Zarah ya saka Yah Boss Jan tsaki a cikin kamewarsa yana shirin gasa mata magana ta ruwan sanyi sai kawai.
Juhainah bata san yadda akayi ba, ta dai ganta zaune kujerar dab da Yah Boss tana faɗin.
"Eh ƙaramar yarinya zai aura mi zaiyi da tsohuwar guzuma, irinki kamar yadda naji ya faɗa, dan Allah ki rabu da yayana tunda baya sonki, Allah Nima na tsaneki bana sonki, don Allah karki aure min shi Please ki temaka.."
Yah Boss ya kalli Juhainah da mamaki yadda ta naniƙewa kujerasa tana masifa ƙamshin bakinta na shiga hancinsa, sai masifa take daman kana kallonta a sama take tana neman wanda zata saukewa masifar, da take cin ta.
Zarah tayi murmushi tace.
"Ni ina sonki kece Juhainah ƙanwar Babyna ko?
Juhainah ta turo jajayen laɓɓanta da suke yanayin pink saboda kaurunsu, ta buɗe baki zatayi magana Yah Boss ya ɗora tattausan tafin hannunsa akan laɓɓanta yana watsa mata kallon kul ta sake magana.

Ita Kuma kallon sai ya sakata narkewa cike da shagwaɓa tana rufe idanunta, taja bakinta tayi gum tana sauke ajiyar zuciya yayin da ɗumin hucinta yake sauka akan tafin hannunsa.
Janye hannunsa yayi yana Kame fuska sosai.
A hankali cikin zazzaƙar muryansa kusan kunnenta ya furta.
"Bana son rashin kunya, ki nutsu Ni nace miki bana sonta ne? Kinada wacce zaki aura min ne idan ban aureta ba?"

Ya ƙarasa maganar fuskarsa kame sosai, babu wasa akan fuskarsa bare ta kawo masa raini.
Kuma yadda yayi maganar iya ita ne kawai zata iya jinta, Sbd yadda iya laɓɓansa ne suke motsawa cikin ɗan sautin muryansa mai daɗi.
Juhainah cikin sanyi jiki ta ɗago kanta tana zuba masa dara-daran kyawawan idanunta, hawaye shaɓe² akan kyakkyawar fuskarta, ta kasa jure maganganunsa, ta fashe da kuka tana kifa kanta akan ƙaton Table ɗin.

Yah Boss kallon iPhone ɗin nasa yayi jin Zarah har yanzu akan layi tana magana.

"Hello Babyna inata magana naji shiru sai kukan Juhainah nakeji, don Allah me ka mata? Karka ɓata mata rai saboda Ni, yarinta ne zata fasa watarana.
Ni yanzu ba wannan ba, don Allah yaushe ne masu ɗaurin auren zasu iso, Kawuna yace na kira na tambaya ba, kuma kazo don Allah"

Yah Boss a hankali cikin kamewarsa murya ƙasa ya furta.
Har abada bazan sakata kuka saboda ke ba, baki isa baki kai gunba, kuma bazaki kai ba, ke duk duniya ma babu macen da zan auro duk son da nake mata na saka ƙanwata kuka akan macen ki riƙe wannan Malama.
Kuma maganar yaushe zasu zo ban saniba, sai ki jira tunda kin nace, Ni kam bana zuwa ko ina ina gidana sai kin zo, kuma kiji da kyau anan ɗakunan ƙasa zaki zauna Stairs babu gun zamanki, nawa na matata Khadijah na ƴaƴana sai gudan bakida darajar da zan sakaki ciki, tunda ke kika nace Ok..."

Ya ƙarasa maganar yana katse kiran tare da kallon Juhainah da take kukan zallar shagwaɓa jin kalamansa, haka ya ƙara mata sautin kukan da shagwaɓar, har goga kanta take ajikin Table ɗin.
A hankali can ƙasa ya furta.

"Ke! Tashi ki ban waje kije parlour zakifi jin daɗin kukan, ina buƙatar hutawa Please ta shi ki ban waje ko na makeki yanzun tunda bakya tausayi na kina buƙatar sake saka min damuwa kuma, saboda bana son ƙaran kuka kin sani..."

Juhainah jin yadda yayi magana ba wasa ta miƙe jikinta na ɗaukan ɗumi zuciyarta zafi take mata haka kawai.
A hankali ta kallesa suka haɗa ido ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta tana rage kukan cikin wata irin shagwaɓa tana Turo laɓɓanta gaba tace.
"Yaya Sadeeq don Allah karka yi aure Please don Allah tunda baka sonta karka aureta Allah zan samo maka yarinya mai nutsuwa ƙarama irina ka aura Please Yaya, karkayi auren nan bana so Allah..."

Bai kalleta ba ya ɗauki Cup yakai bakinsa fuskarsa a haɗe sosai.
Ganin yanayinsa tayi saurin ɗaukan plate da Cup ta silale ta gudu parlour kar ya sharara mata mari a banza...



Ƙarfe tara da minti goma jerin gwanon motocin zuwa ɗaurin auren Yah Boss a ƙofar gidan Yakubu Abubakar Janfar motoci guda 15 cif kowace mota kagani ta kece raini ce.
Papa Sanye yake da wata dakekiyar shadda Fara ƙal Yayin da Mustapha Umar Nasir Khabir Mijin Aunty Sumy, abin ba'a magana kowa kagani Cikin shigar kece raina.
Bakinsu baya rufuwa.
Fu'adh yadda yayi shigarsa Zaka rantse shine angon dan yafi kowa farin cikin wannan auren.
Haka suka jera aka ɗauki hanyar Jigawa kowa kagani yana taya murna zuwa wannan ɗaurin auren.
Duk sai sunyi kwanan hanya wajan dawowa saboda yadda ƙasa yanzu ta lalace mugayen mutane, duk da akwai Iko dayawa a cikinsu suna kuma tare da makamansu, amma kiyaye lafiya yafi komai.

Suna fita daga cikin gari Fu'adh ya kira Yah Boss.
Lokacin yana saukowa daga Stairs yayi wanka ya saka ƙananun kaya saboda baya zuwa ko ina, amma anjima zai yi baƙi.
Parlour ya doso yana ɗaga kiran a nutse ya amsa da.
"Yes Fu'adh!"
Fu'adh yana murmushi yace.
"Sir ayi mana addu'ar sauka lafiya mun ɗauki hanyar Jigawa..."
Ƙittt ya katse kiran yana jan tsaki, ya ƙarasa gun Royal Turkish Chairs ɗin ya zauna yana ajiye wayoyinsa, ya ɗauki remote ya canza channel ɗin da Juhainah ta tafi tabari.
Chapter 38 · 0% Book details