← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 113

Sashe 74

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juhainah fa babu wani abun kirki da ta iya dan tea ɗin ma ba iyawa tayi ba, Black tea kaɗai ta iya, taso masa irin wanda Suhaima tayi ne, bata iya ba, kananfari ta afka da citta and Mint, Lipton guda biyar ta jefa, duk abinda ta zuba yayi yawa harda su lemon tsami, ta tafasa ta tace tana washe baki ta zuba acikin Set Flask ɗan ƙarami da Cups dinsa masu kyau, ta ɗora akan ɗan ƙaramin tray mai kyau ta fito, fuskarta ɗauke da murmushi.

MAAH zaune a parlour tana amsa waya.

"No! Hajiya Najwa wannan magana ma wallahi tallahi ta mutu daga Yau, ko ku jawa kanku, duk zuri'ar ku Taurari familles kunsan Familles Janfar na gaba daku, ki kama min bakin nan naki, ko shi Kamal yayi kaɗan ya tunkaro inda nake bare ku, ai mun gama magana tun baya, dan haka karku sake kirana kuna min kukan munafurci, a yau idan Gwamna Kamal naso ya mutu da baƙin ciki ma banida case, kuma bazanji ko ɗar ba, sbd ba irinsu ake tausaya wa ba idan sun rasu..."

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran fuskarta a mugun haɗe idanunta sun fara Ja.
Ido huɗu sukayi da Juhainah tsaye da tray.
Maah ta saki murmushi tana takowa ta iso gun Juhainah tana sumbaci idanunta tana rungume ƴarta, a hankali tace.
"Autah J kallon me kike min haka? Ina zaki da kayan Tea?"
Juhainah ta narke a jikin Maah a shagwaɓe tace.
"Maah! Suwa ye familles Taurari? Waye Kamal govarner? Me haɗinki dasu suka ɓata miki rai haka? Naji na tsanesu, bana ƙaunar wanda zai sakaki acikin damuwa duk girman son da nake yiwa abun matuƙar zai ɓata miki rai wallahi sai na tsanesa tsana mafi muni..."

Maah ta rufe mata baki tana shafa bayanta cikin sigar lallashi tace.
"Ke Autah babu fa komai karki damu shi kenan naji ma ɓacin ran ya tafi, muje bedroom ɗina na baki tea ɗin ki sha, ko mu zauna a parlour?"
Juhainah ta janye jikinta tace.
"Maah na yaya Sadeeq ne fa na dafo masa yana ɓangarensa, zan kai masa"

Maah ta amshi trayn tace.
"Ok muje na raka ki, karki faɗa masa kinji ina waya kinji Autah?"
Juhainah ta ƙura wa Maah dara-daran kyawawan idanunta, tana faɗin.
"Wai kowa ya ɗaukeni maƙaryaciya ne, daga jin magana sai in faɗa?"
Maah tace.
"A'a yi haƙuri Autah muje dai, waye kika ji magana yace karki faɗa?"

Juhainah ta tuna gargaɗin Yah Boss akan idan ta faɗa ba shi ba ita.
Kai ta girgiza tace.
"Ba komai, ni na manta wacece ta faɗa ko Aunty Sumy ce tace kar na faɗa ni na manta miye ma tace"

Maah ta sauke ajiyar zuciya acikin zuciyarta tana godewa ALLAH.

Har bakin part ɗin Yah Boss Maah ta rako Juhainah.
Suna tsayawa Juhainah ta amshe tray'n tace.
"Toh ki koma Maah Nagode"
Maah ta danna doorbell tana murmushi tace.
"Juhainah! Hanani ganin Ɗana zakiyi?"
Shagwaɓe fuska Juhainah tai tana faɗin.
"Gaskiya Maah kije sirri zamuyi da Yayana"

Maah ta sake danna doorbell ɗin tace.
"Ba wani sirri bakya so dai naga Abbanah, ai na tafi ki gaishe min shi Toh"

Ta ƙarasa maganar tana juyawa ta tafi.
Juhainah zata sake dannawa taji an buɗe ƙofar.
Kallonsa take cike da soyayya ta shagwaɓe fuskarta, ganin yadda ya kame fuska sosai.
Juyawa yayi a hankali yana takunsa ya furta.
"Bakya jira da kika danna sau ɗaya?"
Biyosa tayi tana rufe ƙofar a hankali tace.
"Maah ce Habiby bani bace"

Tsayawa yayi ba tare da juyo ba ya furta.
"Ina Maah ɗin TOH?"

Ƙaraso wa tayi ta tsaya kusansa a hankali tace.
"Ni nace ta koma sirri zamuyi da Habiby nah..."

Lallausan laɓɓanta masu kauri ya kamo a hankali ya furta.
"Kika koramin Mamana sirrin me zanyi dake Toh?"

Ƙaran shagwaɓa ta saki tana matse tray'n da ƙungunta da hannun ɗaya ta kamo tattausan hannunsa na kan laɓɓanta ta riƙe tana rarraba idanuwa.
Goshinta ya zungura a hankali ya furta.
"Zaki ƙara rashin ji?"

Kasa jurewa tayi kallonsa ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta, tace.
"Allah Bazan ƙara ba Habiby I'm sorry kuma I love you"
Sakin laɓɓanta yayi nufi parlour.

Anutse ya zauna yana kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa akan Tv.
Ƙaraso wa tayi ta ajiye tray'n akan Center Table ta ɗauki Cup ta haɗa masa Tea ta miƙe ta dawo kusansa ta zauna.
Ta beƙo masa Cup ɗin.
"Habiby ga shi ka shanye duka"
Yah Boss ya amsa yana jin ƙamshin kamar abubuwan da aka saka yayi yawa.

Bakinsa ya kai Cup ɗin tare da Bismillah.
Juhainah ta washe baki tana jin daɗi ta matso kusansa sosai, har jikinsu na taɓa juna ta kamo hannunsa marar Cup tana wasa da zara-zaran fararen yatsun hannunsa masu ɗauke da zobe na gold and diamond tsaf.

Kurɓa ɗaya yayi da sauri ya janye Cup ɗin daga bakinsa, yana yamutsa fuska acikin zuciyarsa ya furta.

"Ya Salam! Waye ya dafa mata wannan shirmen?"

Cikin damuwa Juhainah ta saki hannunsa kamar zatayi kuka, ta amshi Cup ta ajiye ganin kamar ya ƙone harshe tana faɗin.

"Sannu Habiby ka ƙone ko? Duk laifina ne ban bari ya rage zafi ba na baka kayi haƙuri Bazan sake ba"
Ta ƙarasa maganar tana kamo fuskarsa mai zagaye da saje mai matuƙar kyau, da ƙaramin gyamun da yayi masa kyau, tare da gashin bakinsa mai matuƙar kyau.
Da duka tafukan hannunta ta riƙe fuskar shi, idanunta har sun fara ruwan tausayi ajinta ya ƙone harshe, bata san rashin jin daɗin tea ɗin bane, ya saka shi janyewa da sauri, yana yamutsa fuska.

Ƙoƙarin kai bakinta take akan nasa bakin wai hura masa harshensa zatayi.

Da wani irin sauri ya riƙe fuskarta ya daka mata tsawa.
Ai sai gata can gefe zaune ta rakuɓe jikin Chair tana rungume Cushion, tana hawaye ta lumshe idanunta.
Haɗiye tea ɗin da ya riƙe bakinsa yayi, yanajin azabar citta da lemon tsami da kananfari da Mint and Lipton da yayi bauri sosai.
Amma bazai nuna mata babu daɗi ba zai barta a ƙonewar yayi, Sbd bazai iya sake kurɓa ba.

Anutse ya kalli gun da taje ta rakuɓe tana shasheƙar kuka.
Tsaki yaja ya janye idanunsa, a hankali cikin daddaɗar muryansa ya furta.
"Zo nan na miki wani abun ne? Kece fa kika ƙona min harshe, ga shi ba zan ma iya shan tea ɗin ba, Zo nan nace"

Miƙewa tai cike da shagwaɓa ta fara takowa tana ƙara sautin kukan.
A kame ya furta.
"Karki iso min da kuka kwashe kayan tea ɗinki ki fice min maza"

Shiru kake ji ta fasa kukan ta tsaya ta goge hawayen fuskarta ta ƙaraso ta zauna ƙasa gun ƙafafunsa.
A hankali ya furta.
"Toh Karki kuskura ki taɓa min ƙafafuwana ki zauna ɗam"

Kai ta ɗaga alamar toh.
A hankali tace.
"Kayi haƙuri Habiby Wlh ba da gangan na ƙona maka harshe ba"

A hankali ya furta.
"Alright, Amma me yasa kika kora min Maah?"
Shagwaɓe fuska tayi ta ɗago kanta.
4 eyes sukayi ta sauke kanta tana ɓoye fuskarta kan ƙafafunsa.
Kwalin sweet ɗin ya beƙa mata yana faɗin.
"Amsa ki ajiye sai kiyi ta sha"

Kai ta ɗago taga kwalin sweet mai shegen kyau ta amsa tana washe baki a hankali tace.
"Toh Habiby ka bani ɗaya a baki Please kaji?"
Harara ya zabga mata a hankali ya furta.
"Wlh Juhainah na kuma jin wannan maganar a Bakinki, zan ɓata maki rai.

Ko ni yayanki ne bai hallata na haɗa baki da ke ba, ranan ma naga kina neman zaucemin ne da shime, bansan me zan yi ki min shiru da shirmenki ba, na saka maki sweet, amma Sbd bakida hankali da wayo kike zaton kullum zan saka miki Sweet a baki?"
Rau-rau tayi da idanunta tana kallon shi cike da soyayya tace.
"I love you Habiby kaji"

Yah Boss ya furta.
"Tashi kije ki kwanta"
A shagwaɓe tace.
"Habiby, Truth tell me you love me, please my brother Habiby"

Yah Boss idanunsa akan Tv a hankali ya furta.
"I'm your brother, same mother same father, don't mention marriage between us again, okay?"
Kallonsa take cike da shagwaɓa tace.
"Alright, I heard you, but I can't help loving you"
Kyawawan idanunsa ya zuba mata a hankali ya furta.
"So why would you stop loving me anyway?"

A hankali kamar me raɗa tace.
"I love you so much because you're my blood"
Ɗan ƙaramin murmushi ya suɓuce masa a hankali ya furta.

"Love you too Aunty J alright?"

Cikin farin ciki ta ɗaga masa kanta, ta buɗe kwalin sweet ɗin ta ciro biyu ta ɓare ta saka ɗaya bakinta ta lumshe dara-daran fararen kyawawan idanunta tana faɗin.
"Yah Habiby sweet akwai daɗi sosai"

Ta ƙarasa maganar tana buɗe idanunta ta miƙe ta zaro Sweet daga bakinta tana riƙe a yatsunta ta zauna kusansa ta nufi bakinsa da Sweet ɗin.
Fuska ya kame a hankali ya furta.
"Da wani harshen zan sha bayan kin ƙona min baki da tea?"
Kamar zatayi kuka tace.
"Ayyah! Na manta Wlh Yah Habiby"

Bakinta ta mayar ta haɗa da ɗayar tana tsotsa tana masa Surutu, ƙamshin Sweet ɗin ya cika masa hanci.

Shi kam idanunsa akan Tv ya maida hankalinsa, ita kuma kamar an jona da wutar lantarki sai zuba take.

Anutse ya kalleta yana kame fuska ya furta.
"Tashi kije ki kwanta, bakin ki baya gajiya ne?"
A shagwaɓe tace.
"Allah in kaine Yah Habiby My blood bana gajiya"
Kallon da ya mata ne ba shiri ta miƙe ta ɗora kwalin sweet ɗin akan tray'n tea ta ɗauka tana faɗin.
"Yah Habiby ka kwana anan Please karka tafi gidanka"
A hankali ya furta.
"Ok alright kije ki kwanta"

Cikin farin ciki ta juya tana faɗin.
"Good night sweet dreams bye I love you Habiby My blood"
Baice uffan ba ya maida hankalinsa akan Tv tashar CNN News.
Chapter 74 · 0% Book details