Sashe 79
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasir da yake zaune yana waya da Hairat ta bayan hankali kwance, kamar Ance ya ɗago kansa ya hango Surayya tana tafe sai sauri take yi waya a kunnenta.
Nasir cikin farin ciki ya miƙe yana katse kiran ya ɗanawa Surayya tarko, ya godewa ALLAH da yazo da motar gate na ɓangaren gabas.
Ba zato taji an damƙo hannunta an rufe mata baki cikin kakkausar murya yake faɗin.
"Wlh kika kuskura kika min ihu, sai kin raina wayon ki."
Surayya tana ido huɗu da Nasir jikinta ya ɗauki rawa sai hawaye tace.
"Don ALLAH kayi haƙuri Karka cutar dani Wlh bazan sake maka rashin kunya ba, ko kallon ka bazan ƙara ba Yah Nasir"
Bakin ya buge yaja hannunta har gun da ya ajiye motarsa.
Gaba yace ta shiga dole ta shiga ya rufe ya zagaya ya shiga ya kunna motar yaja ya nufi gate na ɓangaren Yamma yana zuba Horn.
Kuka ta saki zatayi magana ya daka mata tsawa yana faɗin.
"Zaki ji tsoron mai sunan Nasir ma nan gaba, ba Ni ba kika yi wa rashin kunya daga temakon ki da nayi?"
Cikin tashin hankali tana kuka tace.
"Kayi haƙuri Yah Nasir wlh bazan ƙara ba, ka ceceni na tuba, sharrin Sheɗan ne"
Fuska shafe da toka ya furta.
"Ƙaramar mara kunya sai fa na koya maki hankali"
Surayya haɗa kai da guiwa tayi tana fashewa da kuka tace.
"Kayi haƙuri don Allah akwai ɗiyar mutane da aka bani amana yanzu fita zanyi amso saƙo kayi haƙuri, Farid na jirana"
Nasir yace.
"Wlh idan kika sake magana keda ki dawo sai sha biyu na dare, idan kina musu ki sake roƙona"
Ai Surayya taja bakinta ta tsuke sai hawaye.
Farid ya kirata ta gaza ɗagawa bata san me zata ce masa ba.
Barikin sojoji ya nufa da ita.
Yana shiga ciki da motar yayi parking ya fito ya daka mata tsawa ta fito jikinta na rawa, hawaye yaƙi tsayawa.
Gaba yayi ta bisa.
Wani ɗan fili ne da yake zagaye tsakiyar rana dutse ɗaya ne ƙato yasha zafin rana, ya nuna mata cikin bada umarni yace.
"Ki shiga can ki zauna saman dutsen can, ki ɗaga kanki ki kalli rana, tsawon minti biyar Wlh idan kika ɗago kanki ya koma minti 15 idan kika motsa Sbd zafin dutsen nan, ni nasan me zan miki, ba rashin kunya kika iya ba, ai daman kince banda imani ba?"
Kai ta girgiza tana kuka tace.
"Don ALLAH kayi haƙuri Wlh Bazan ƙara ba"
Hararenta yayi yana faɗin.
"Zakiyi abinda na sakaki ko na kira waɗanda zasu miki fin abinda zan miki?"
Da sauri ta shiga zagayayyen gun ta zauna akan dutsen da kamar an zuba masa ruwan zafi.
Ta ɗaga kanta tana kallon rana tare da shasheƙar kuka.
Ƙasa azaba sama azaba haka Surayya ta gani.
Abinka da fara fata cikin mintina biyar fuskarta tayi jajir idanunta sunyi Ja sosai mazaunanta kansu sun gashe a Dutsen.
Nasir yana gefe cikin inuwa tsaye yana waya da Hanifah da ta kirasa.
Sai Surayya tai mintina 6 Nasir yace ta miƙe tazo.
Daƙyar ta miƙe mazaunanta na mata mugun raɗaɗi, idanunta na zafi kamar an zuba mata yaji, dishi² ma take gani harda majinar wahala, haka ta tako a hankali tazo har gunsa.
Gaba yayi tabi bayansa tana tafiya daƙyar cikin azaba.
Ko shiga motar daƙyar ta shiga.
Key yawa motar ja ya nufi gate.
Surayya dukkan jikinta raɗaɗi yake mata babu inda baya mata raɗaɗi acikin jikinta.
Ko kallon ta bai kuma ba, a kame ya furta.
"Gobe idan kika kuma min rashin kunya Wlh abinda zan miki sai ya linka haka, sai anje a ɗauko ki, Ni dake aga mai fasawa."
Surayya ko ƙwaƙwaran motsi bata yi ba, Sbd wani irin tsoron Nasir takeji fiye da komai a yau, ALLAH kaɗai yasan me taji acikin rana da Dutsen da ta hau.
Wayanta ta fara ringing daƙyar ta iya ɗagawa.
Marayan kuka ta saki murya a dishe tace.
"Farid! Kayi haƙuri ka kawo min gida zuwa dare Banida lafiya yanzu bazamu iya haɗu wa ba"
Farid da yake driving yace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Baby mi ya sameki haka? Please inzo yanzu na kaiki asibiti?"
Cikin kuka tace.
"A'a kar ka zo Bab zan sha magani yanzu, kazo gida da dare ina jiranka akwai maganar da zamuyi"
Ta ƙarasa maganar tana katse kiran.
Nasir bai ko kalleta ba, yanajin duk hirasu.
A inda ya ɗauketa anan yayi parking ya kalli gefen da take zaune a hankali ya furta.
"Idan kin cika Surayya don Allah idan ki fita ki zageni Kinji?"
Surayya bata ce uffan ba, daƙyar take ƙoƙarin buɗe motar ta gaza baki ɗaya batada ƙarfi.
A hankali ya ranƙwafo ya beƙo hannunsa ganin ta gaza ya buɗe mata dai-dai ta juyo zata masa magana fuskokinsu suka haɗe numfashinsu ya gauraya, gu ɗaya haka ƙirjinsu ya haɗe zuciyoyinsu suka amsa a tare.
Ido cikin ido suka kalli juna, ya mata wani malalacin kallo, yana janyewa tare da buɗe mata ƙofar yana gyara zamansa ya furta.
"Fita ki ban waje."
Surayya tsananin tsoron Nasir ya kamata ganin ta zubu jikinsa bada niya ba, amma yana mata mugun kallon ƙyama.
Wani irin kuka ta saki tana ƙoƙarin fita ta gaza Sbd ƙafafuwanta sun mata nauyi.
Tsaki Yaja yana fizgota ta dawo kusansa har tana faɗowa jikinsa, yayi saurin matsawa.
Cikin tsawa yace.
"Me na miki? Kiyi min shiru Ko Wlh naja motar na sake barin gidan dake, idan mun koma ALLAH azabar ruwan sanyi zan miki"
Haɗiye kukan tai ta saka mayafin kayan Pakistan ɗin jikinta ta goge hawayen shiru kakeji kanta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya abun gwanin ban tausayi tayi mugun laushi.
Ganin dai da gaske tsoronsa takeji yanzu, yace.
"Fita bani waje"
Ai Surayya duk azabar da take ji sai gata ta fice daga motar har tana ƙoƙarin faɗuwa.
Dariyar mugunta yayi yaja motar yana faɗin.
"Kika ce ke marar kunya ce? ƙwaila kawai"
Surayya daƙyar take tafiyar Sbd azaba, ga shi gun da ya ajiyeta zuwa bakin ƙofar parlour akwai tazara sosai.
Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar parlour ta shiga taji muryan Maah tana kiranta.
"Surayya! Lafiya? Me ya sameki?"
Maah ta ƙarasa tambayar tana isowa gunta daga gun masu aikin kayan miya take.
Surayya ganin Maah sai tayi rauni, tana son ɓoye damuwarta, dan idan Maah tasan gaskiya zata yi wa Yah Nasir faɗa, shi kuma ya sake mata azaba.
Dole tayi ƙoƙarin sakin murmushi tace.
"A'a babu komai Maah ina lafiya"
Maah ta kamo hannunta tana kallon idanunta jajir haka fuskarta ma tayi Ja tace.
"Ƙarya kike Surayya kalli idanunki da fuskarki kamar an miki Mari arba'in Kice lafiya lau.
Ni fa uwa ce gareki keda Bilkisu duk ɗaya ne, daga ina kike wa ya miki wannan aikin? Ai ɗazu ba haka kika fita ba, Ina saƙon da kika ce zaki amso?"
Surayya tayi dariya ƙarfin halin tana riƙe handle ɗin ƙofar sbd jirin da take ji, tace.
"Ɗinki ne bai gamaba Maah, Wlh Babu komai ki yarda da Ni, kawai wata ce ta ɓata min rai gun telan tana farfaɗin magana wai ita ya kamata yayi wa ɗinki akan lokaci bani ba"
Maah taja hannunta tana murmushi tace.
"Kukuma yaran zamani ba haƙuri, kika biye mata kuka daki juna ba?"
Surayya tayi dariya tace.
"Ina naga ƙarfi Maah itane dai tai saurin kaimin hannun, ba Aunty Juhainah kusa da ta rama min"
Maah tace.
"Ku dinga haƙuri karki koyi rikincin Autah Juhainah Surayya...."
★
80 Unit
Zarah tun tana saka ranta Yah Boss zai
Dawo har ta haƙuri ta shirya ta tafi gidan Maah bayan la'asar.
Yah Boss ko cikin jarumtarsa ya wuni tsaf babu wata damuwa da ya sakawa kansa, dan ALLAH ya masa haƙuri sosai da juriya akan Komai na rayuwa, mutuwar Khadijah ne kaɗai taso kassara rauninsa.
Yau dab da Maghreb ya dawo gida yayi wanka ya tafi masallaci.
Fu'adh kuwa hidima tai masa yawa ta Yah Boss, a yau kusan shi ke aiwatar da komai da ya shafi business, da wasu baƙi da meetings duk shi yayi.
Acan police station kuwa sauran abubuwan matemakin commissioner of police, shi yaji da komai yau, tun daga ƙarfe 1 na rana zuwa ƙarfe 6 na yamma.
Can gidan Maah bayan sallar Maghreb aka shafawa amaryar lalle amma miyar kuka aka saka mata itama ta sha addu'o'i tare da garin habbatul'sauda.
(Sbd sakawa mai jinnu asalin lalle hatsari ne babba, tamkar an ƙara gayyatarsu ne, amma idan anci Sa'a wasu basa komai.)
Juhainah taci kuka sosai ganin dai da gaske gobe zata bar Maah da Papa da Yah Boss da Khairat su Babies da sauran yayunta ta koma gidan wasu ƙarƙashin inuwar wasu tayi rayuwa, auren ma bana soyayya ba, a yanzu ji tayi daman Ammar ta aura, ko banza yana sonta ya damu da damuwarta, amma Jamal bai taɓa kiranta dan raɗin kansa ba, yace mata ya take.
Daƙyar Aunty Sumy dasu Khairat harda Suhaima da Hajjah Mama akayi lallaɓarta ta daina kukan, can ɗakin Maah aka maidata ta ta kwana da mahaifiyarta na ƙarshe, Dije daƙyar ta rabu da Juhainah harda su kuka ita agun Antiya Jihinah zata kwana.
Yah Boss bayan sallar isha'i ya fito daga masallaci ya zauna down stairs.
Ya kira Jamilu ya haɗo masa abincinsa ya kawo masa nan.
Wayoyin jama'a suka sha masa kai yau, ko yanzun ma zaune yake yana dinner a parlour da ya gauraye da ƙamshin turarensa haɗi da turaren wutar da Zarah ta saka masu bala'in daɗi, tun bayan la'asar.
Sanye yake da jallabiya fara tass tamkar balarabe, yana amsa waya Anutse yana cin abincin sama².
Ƙaran danna doorbell yaji, yaƙi miƙewa Sbd yaga Zarah ta fita da yamma ta wayarsa yasan itace ta dawo daga can gidansu.
Sau uku aka danna.
Murus yaƙi miƙewa.
Jamilu da yake kitchen yana jiran Yah Boss ya gama cin abincin ya ɗauko kayan, shi ya miƙe yaje ya buɗe mata.
A hankali take takunta anci ubansu kwalliya, sai ƙamshi take.
Da mamakin take kallon sa tunda ta tunkaro shi.
Normal yake zaune cikin shigar larabawa, yana cin abinci yana amsa waya a hankali cikin harshen fulatanci.
Yawun kwaɗayin sa da sonsa ta haɗiye tana takowa.
Tuna tsawar da ya mata da safe ya sakata fasa nufar inda yake, aranta tana faɗin.