← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 113

Sashe 82

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonta yayi yana ajiye tissus ɗin da ya goge bakinsa a hankali can ƙasa² cikin wani irin sauti ya furta.

"Ina sonki Aunt B alright"

Tsalle ta dinga yi saman bed ɗin tana tafa hannayenta tace.
"Sai Da Kai Yah Boss Habiby Nah, I love you more Wallahi"
Kansa ya girgiza yana janye idanunsa a kanta.

Ɗayar Phone ɗinsa ya ɗauka ya kira Hamza direba, bugu ɗaya ya ɗaga kiran tare da sallama.
Juhainah ta gyara zamanta ta masa ƙuri da dara-daran kyawawan idanunta, sai murmushi take, zuciyarta fara ƙal.
Anutse ya amsa sallamar Hamza yana faɗin.
"Hamza! Kazo yanzu gidana, akwai saƙon da zaka kawai Bilkisu, can gida, ka kira Babie Suhaima ka bata sai ta kai mata"

Hamza cikin girmamawa ya amsa da.
"Ok in sha Allahu Yallaɓai Allah ƙara girma da kwarjini"

Yah Boss ya katse kiran yana amsawa da Ameen.
Ya kira Jamilu yana ɗaukan kiran a nutse cikin kamewarsa ya furta.

"Jamilu! Ɗauko abinda zaka zuba croissants, ka fita compound ka jira Hamza yanzu zai zo ya amsa."

Jamilu cikin girmamawa ya amsa da.
"Ok Yallaɓai in sha Allahu yanzu nan"

Yah Boss ya katse kiran yana kallon screen ɗin wayan, Juhainah ta masa ƙur da ido tana tafa hannayenta fuskarta ɗauke da murmushi tana faɗin.
"Bravo my blood Habiby ina sonka"

Fuska ya kame a hankali ya furta.
"You've gone very crazy Aunt Bilkisu, Bye za'a kawo miki yanzu croissant ɗin"

Shagwaɓe fuska tayi tace.
"Please da zoben ƙaramar yatsarka, zai min a babbar yatsata Habiby please"

Lumsassun kyawawan idanunsa ya kafe akan kyakkyawar fuskarta, yana kame fuska. Tayi dariya tana rufe fuskarta da fararen hannayenta da suka sha Jan lallen amare irin na Chad.
A hankali ya zare zoben daga ƙaramar yatsarsa, a hankali ƙasa² ya furta.
"Buɗe idanunki kalla zai kawo miki harda zoben yanzu Mayya kawai"

Cikin farin ciki ta cire hannunta daga fuskarta tana murna, zatayi magana,
Kittt ya katse kiran.
Ta kwanta tana murna sosai.
Suhaima suka shigo da Al'amin, ya zauna kusan Juhainah, Suhaima ta sake kiran Yah Boss video Call ya ɗauki kiran suka fara hira da Amiin.
Jamilu yazo ya zuba croissants ɗin guda 5 Sbd yasan mugun cine da ita, tana iya cinyesu koda zatayi amansu ne.

Yah Boss a hankali ya furta.
"Jamilu! Ƙara masu saka 10, akwai mutane ai. Amsa wannan zoben kaba Hamza Babie Suhaima zai ba taba Bilkisu"

Jamilu hannunsa har rawa yake ganin gold ɗin yana walwal, ya amsa ya saka cikin aljihun wandonsa yace.
"Ok in sha Allahu Yallaɓai...."

Yah Boss sai 12 dai-dai na rana ya fito daga dinning room ɗin, sosai sukayi fara da Amiin da Suhaima, Juhainah tana takurasa da shagwaɓarta ba dalili ta amshe wayan tana masa fitina dole ya kashe kiran, Al'amin da Suhaima suna mata dariya suna kiranta Aunty J Babe ɗin Daddy...

Zarah yau bata ma son ganin Yah Boss, Sbd idan ta gansa jarabarta ƙaruwa take akansa kamar ta sha wani abun, haka take fama tun jiya.
Tana jin fitarsa itama ta shirya cikin kayan kece raini ta saka Ankon bikin a jaka mai kyau ta kira Fu'adh a waya tana son zuwa gun yinin biki ya turo Walid yazo ya kaita.

Hamza yazo ya amshi saƙon yakai yana isowa ya kira Suhaima da yake yanada numberta.
Suhaima ta fito ta amso croissant da zoben, ai kuwa murna gun Juhainah ta saka zoben a babban ɗan yatsanta nan kaɗai zai zauna, yayi mata kyau sai sheƙi yake, taci croissant guda biyu yau kaɗai.

Sha biyu da rabi Surayya taci ubansu kwalliya ta tafi gidan su Juhainah, Dijeh ta nace mata sai sun tafi tare.
Ganin jiya sun tafi bata masu ɓarna ba tajata suka tafi da sharaɗin da yamma zata dawo da ita.

Yah Boss yana fita gun baƙinsa ya tafi domin su gaggaisa.


Bayan an dawo daga sallar juma'a jama'a daban² suke tururuwar zuwa ɗaurin aure ƙofar gidan Yakubu Abubakar Janfar.
Misalin ƙarfe 2:30 ƙofar gidan Yakubu Abubakar Janfar cike take da nau'in motocin hawa kala² waɗanda suka zo ɗaurin aure.
Ƙaton farfajiyar gidan ta cika maƙil da jama'a, Sbd isowar angwaye.
Jamal wata irin shiga yayi kana kallonsa kasan shine angon cikin jama'arsa.
Mustapha Umar Nasir kaya iri ɗaya suka saka wata ɗanyar shadda bugagga fara ƙal.
Yah Boss yana kusan Papa Zaune sai su Nasir kusansa sai, sauran familles nasu da abokan Papa da maƙota ma sha Allahu abun ba'a cewa komai.
Babban malamin da yake maƙocin Papa hannun dama shi ke jan sallah a masallacin da yake haɗe da gidan na Papa wanda Yah Boss ya ginasa katafare.

Gyaran murya yayi yace.
"Ina Waliyin Ango? Ina Waliyin Amarya sai ku matso..."
[26/03 20:27] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 43*

Alhaji Abdallah, da Giɗaɗo da Malam Kamilu, suka matso kusan Liman, yayin da Papa da ƙaninsa mai binsa mai sunan Nasir suka matso, wato (Kawu Nasiru)
Malam Kamilu ya gyara zamansa ya kalli Papa yace.
"Ni Kamilu ina nema wa Jamaluddin ɗana auren Ƴarka Bilkisu, bisa tsari na addinin Islama"

Kawu Nasiru ya gyara zamansa yace.
"Ni Abdulnasir na bawa ɗanka Jamaluddin auren ƴarmu Bilkisu kowa ya sheda"
Sadakin Giɗaɗo ya beƙa Naira dubu ɗari biyar.
Kawu Nasiru ya amsa ya beƙawa Papa, Papa ya beƙawa Yah Boss ya amsa ya ƙirga ya faɗa wa Liman iya yawan kuɗin.
Liman yace.
"Yaku taro Al'umma Nan da kuka zo don shaida ɗaurin aure, tsakanin Jamaluddin Abdallah da Bilkisu Yakubu Abubakar Janfar, Alhamdoulillah! Aure ya ɗauru tsakanin Su akan Sadaki Naira dubu ɗari biyar lakadan ba Ajalan ba, ku sheda ALLAH Ubangiji ya bada zaman lafiya ya basu zuri'a ɗayyiba Ameen, sai ayiwa Annabi S.A.W Salati."
Ai kuwa mai shela ya ɗauka yana yekuwa yana sanar da jama'a na cikin gidan da waɗanda suke ƙofa abokan anguna.
Jamal baka gane halin da yake ciki Sbd nasihar da Mamy tai masa yau.
Goro da kuɗin da ake ba malamai aka shiga raba wa malamai da, da sauran jama'ar ma sha Allahu.
Yayin da Mustapha Umar Nasir suka amsa gaisuwar jama'a abokansu da suka gayyato.
Yah Boss cike da nutsuwarsa ya miƙe yanata gaisawa da baƙinsa manya², zakayi mamakin yadda ya basu girma ya saki fuska dai-dai yadda zai iya, idan yana ganin darajar mutum, bare baƙin da sukayi tattaki daga garuruwa daban-daban.
Dole zai burge ka a dai-dai wannan lokacin yadda yake nan-nan da baƙin nasa...

A can gidan kuwa shelar ta iso ta ɗaurin auren.
Aunty Sumy dasu Rumaisa Khairat sai rangaɗa guɗa suke yi, Zarah an kanainaye cikin dangi miji sai washe baki take itama, dan kissa ta nufi gun Maah taya murna auren Autarta.
Zarah ta iso gun Maah ta rusuna wa tana faɗin.
"Maah congratulations Autah an girma Allah ya basu zaman lafiya"
Maah ta amsa da.
"Ameen ya Rabbi Nagode daughter Zarah"
Umman Hanifah da take zaune sun keɓe da Hanifah sunata gulma, anci abunsu gayu cikin ankon ansha gilashi, har taso fin Hanifah gayu sai gulmarta ake baƙi amma waɗanda basu san halinta ba, dan an fara ganeta son yarinta da gayu gareta.
Ta zunguri Hanifah tace.
"Halan wannan ce amaryar ogan familles ɗinku? Tashi dan tsohon ki kije kema kiyi murna, kar waccan Rumaisa ta rigaki naga tana zaƙewa, ke baki iya kissa ba ne tashi kije, ke Wlh kamar ba Nono na kika sha ba, sai shegen tsoro, ki duba kiga yadda wacce matar yayan nasu take neman kanainaye wa kamar Familles ubanta wasu matan dai ba kamun kai, tashi Hanifah kije"

Hanifah ƙasa² tayi dariya tace.
"Ita ce Umma kin samo, amma wlh batada wata daraja gun miji, kalli zaƙewar da take yi.
Ita kuma Rumaisa Umma wannan tsohuwar munafuka ce Wlh, bari zan miki gulmarta ta waya idan mun nutsu, ko da zuwa gobe ne.
Bari naje kinsan Rumaisa nan humm, ɗagin kai take min wai suruka tana sonta, ta haifo masu Ƴa mai kama da Maah da Juhainah, shine abinda yake sake bata damar raina mutane, shigeya mai ruwan turawan farko."
Ta ƙarasa faɗa tana miƙa wa.
Umman Hanifah harda dariyar mugunta, ƙasa².
Kafin Rumaisa ta ƙarasa gun Maah har Hanifah ta rigaita isa.
A hankali ta rusuna kusan inda Maah take zaune tace.
"Maah Barkanmu Autah an girma Ubangiji yasa gidanta ne, ya basu zuri'a ɗayyiba Ameen"
Maah ganin akwai jama'a sosai bata son a ɗauketa ta amsa kadaran-kada-han da.
"Ameen Amin Hanifah angode"

Rumaisa ma ta iso tana faɗin.
"Maah Barka Autah Juhainah an girma Allah yasa gidanta ne, mutuwa ce zata raba"
Maah ta amsa da.
"Ameen Amin daughter Rumaisa"
Ruwaida ma tana fama da tsohon cikinta ta matso tayi Barka Maah cikin sakin fuska ta amsa tana faɗin.
"Ya ƙarfin jikin naki daughter Ruwaida?"
Kanta ƙasa cikin girmamawa ta amsa da.
"Alhamdoulillah! Maah"
Hanifah ta koma kusan Umma ta zauna.
Umma Hanifah ta rangaɗa guɗa tace.
"Ma sha Allahu Juhainah an girma Hajiya Zainab Barka Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya"
Maah dai abu ya girmame mata, gatsal haka ta kirata Zainab bayan ta girme mata nesa ba kusa ba, amma tuna bariki ta saka gaba wannan ba komai bane.

Allah ya sani bata ƙaunar Umma da ƴarta har cikin zuciyarta, ba yadda ta iya ne, ita Barka ɗaya ma basu samu suka kame wani ba, Duk da dai taron bai gama ba, yanzu ne ma aka ɗaura auren.
A haka ta daure tace.
"Ameen Nagode Sadiya"

Aunty Sumy ma dai bata son wannan Umma ta Hanifah Sbd rashin kamun kai, ga maita, suna addu'ar Allah yasa kar su kame, ɗan kowa ko uwar wani.
Juhainah tana bedroom ɗin Maah a zaune Suhaima ta shigo da gudu tana guɗa ta faɗo kanta tace.

"Congratulations Aunty J ALLAH ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, ga shi can anata shelar ɗaurin auren ki da Yah Jamal"
Chapter 82 · 0% Book details