Sashe 28
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙaran kiran sallar da yake tashi cikin wayarsa ya tashe sa daga daddaɗan bacci da yake.
A hankali ya buɗe manyan kyawawan idanunsa yana janye Duvet ɗin ya miƙe zaune, yana saukowa daga bed ɗin.
Ya shiga bathroom a gaggauce yayi alwala ya fito, ya saka jallabiya fara ya ɗora hula yana ƙamshi mai daɗi ya nufi masallaci jin yanzu ake kiran sallar.
Yana fitowa daga Masallaci ya koma ɓangarensa yana shigowa ya iske wayarsa anata kiransa.
Tsaki yaja yana ɗaukan wayan, ganin babu suna ya ɗauka, yana sallama.
Daga can Hajiya Ummulkhairi ta amsa tare da faɗin.
"Jamaluddin Abdallah ne?"
A nutse ya amsa da.
"Yeah"
Matar tace.
"Ma sha Allahu yaro ɗan baiwa kwangila ne akan ginin wani Companyn sarrafa Auduga zallah, Please"
Jamal ya zauna saman Sofa bed ɗinsa a hankali ya furta.
"Wani garine?"
Hajiya Ummulkhairi tace.
"Anan dai cikin Yola ne"
Kamar bazanyi magana ba, dan har sai da tace.
"Hello kanajina kuwa?"
Jamal ya furta.
"Eh Ok thank u zan kira idan na yiwa masu ginin in sunada dama, Sbd nafi yarda da aikinsu"
Ya ƙarasa maganar yana feso iskar bakinsa waje.
Hajiya Ummulkhairi tace.
"Toh Nagode Allah ya temaka"
Da Ameen kawai ya amsa bai sake magana ba, tayi masa sallama tana katse kiran.
System ya ɗauka yana fitowa parlournsa wanda yake tsaf a tsare ya zauna yana Kunna system ɗin, dan duba kalar irin ginin da zai dace da Companyn...
★
Juhainah tana gama cika cikinta lokacin ana kiran sallar la'asar, ta miƙe tana faɗin.
"Bari muyi Sallah sai na baki labarin, bari naje Stairs na dawo, muje wani bedroom ɗin, ni bazan shiga wannan bathroom ɗin ba"
Surayya tace.
"Ok muje "
Juhainah tana buɗe ƙofar taga Juhainah zaune, ta rakuɓe.
Ido ta zaro ta riƙe ƙungunta cike da fitsara tace.
"Kam lallai matar nan wato laɓe kike mana kiji me muke cewa, tsabar gulma?"
Juhainah babba ta miƙe tana marairaice fuska tace.
"A'a ba haka bane, bansan inda zanje bane shiyasa na dawo nan ɗin tunda parlour ƙanwar ki ta korani..."
Juhainah ta ɗaga murya tana faɗin.
Dai-dai Yah Boss ya shigo parlour yana riƙe hannunsu Shuraim, Khairat tana riƙe da hannun Shamsiddin.
Lokacin Suhaima ta haye Stairs dan tayi Sallah, Al'amin yana can ya gaji da wasa yayi bacci.
Muryan Juhainah ya jiyo tana masifa hanyar kitchen, hakan yasha jinin jikinsa ta iske baƙuwar nan mai sunanta.
Twins ya kalla yana faɗin.
"My Twins ku tafi Stairs Al'amin yana can"
Ai kuwa suka nufi hanyar Stairs da gudu.
Shi kuma ya nufi hanyar kitchen ɗin, Khairat na binsa jin Juhainah na zuba ruwan bala'i.
"Dalla rufe min bakinki, ke bakya jin kunyar ƴar cikinki kice ta koroki? Ta gane munafurci kike yi shiyasa, wai me ma kike jira ba kin warke ba? ko akwai nufinki ne akan Yayana shiyasa kika nace kika manne a gidan kin ƙi tafiya dan jaraba..."
Khairat da mamaki take kallon Juhainah baƙa, tana mamakin wacece wannan ɗin da Juhainah ta saka gaba da masifa.
Surayya ko jin wani irin ƙamshi na kawo ma hancinta farmaki, tai saurin waigowa.
“Kanbuuu!”
Ta faɗa acikin zuciyarta ganin wanda yake nufo gun, shi da Khairat, fuskarshi babu sauƙi, hankalinta ya tashi ta shiga rawar jiki tana son faɗawa Juhainah da take zuba masifa ido rufe tana karkaɗa ɗan ƙaramin ƙungunta, albarkatun ƙirjinta kuwa sai girgiza suke saboda yadda take girgizan, gasu Allah ya bata su dirarru.
Juhainah kuwa tana cikin masifar Allah ya bata ikon shaƙo ƙamshinsa, wanda ko acikin duba tana tantance ƙamshinsa.
Gabanta ya faɗi ta shiga tashin hankali taƙi waigowa dan kar ya gane ta gansa, kawai sai ta riƙe hannun Juhainah babba tana faɗin.
"Don Allah ki sakar min cikina Wayyo cikina, don Allah kiyi haƙuri Wlh ni ba ruwana ki kira yaya Sadeeq ki roƙesa ya aurenki, Ni ai ban isa na hanaba Suhaima ma ba ruwanta karki cucemu Nida Suhaima yaya zai aureki, don Allah ki sakar min cikina.
Ta ƙarasa maganar tana sakin hannun Juhainah ta fara ƙoƙarin Suman ƙarya ta tafi luuuu zata zube ƙasa.
Da wani irin sauri da zafin naman da Allah ya basa, ya tareta jikinsa yana girgizata, tare da shafa fuskarta yana kiranta.
“Ke! Juhainah! Me ya faru?”
Ya ƙarasa maganar yana ɗora tattausan tafin hannunsa akan shafaffan cikinta ya shafa, yana ɗago kansa ya zubawa Juhainah babba lumsassun fararen kyawawan idanunsa, wani irin mugun kallon da ba ita ba, har Surayya da Khairat ji sukayi fitsari yana neman kuɓuce masu....
[13/01 15:15] أم الأمين😘: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U
👆🏽
_*Mutanen Kirki Kuci Gaba Danna Min Followers, Zan Dinga Antayo Muku Zafafan Tsofaffin littattafai Na, Kuna Chanawa Abinku😂💃🏻🫣*_
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
Page 16
Khairat ta zaro idanunta ganin Juhainah ta buɗe dara-daran kyawawan idanunta tayiwa Juhainah babba gwalo, ta lumshe idon tana ɗauke numfashi na wuccin gadi.
Ashe Surayya ma ta gani, amma tsabar tsoron yanayin da suka ga Yah Boss aciki ya hanasu furta komai, dan zai ma iya ƙaryatasu.
Da wata irin murya ya furta.
"Ke! Mayya ce kenan kika kama min ƙanwa tana faɗin ki sakar mata ciki? Ni ne nace zan aureki? Nayi me dake? Akan hakan kike neman salwantar min da rayuwarta?"
Ya ƙarasa maganar yana mata wani irin tsawa, wacce ta sakata durƙushe wa kan guiwowinta.
Cikin yanayin da yayi matuƙar firgitata, da gasken gaske taji mahaukacin tsoron sa, tana sakin wani irin kuka na gaske ba irin na munafurcin da ta saba ba.
Cikin kukan ta kalli Juhainah da tasan sumar ƙarya tayi tace.
"Wlh tallahi banyi mata komai ba, kuma ni bansan wata magana ba akan aure wa zan aura? Yaushe mukayi da ita wannan magana"
Juhainah baƙa ta ƙarasa maganar jikinta na masifar rawa, ga baƙin cikin gwalon da Juhainah ƙarama tayi mata, a take nadamar zuwa wannan kwangila ta kamata, saboda bataga alamar akwai nasara ba, saboda ita fa ta fara gajiya da wannan cin kashin, idan zata fito da mugun halinta tuni da ta gama da Juhainah ƙarama.
Duk kwangilar da Alhaji Nuhu yake sakata su haɗu su cimma nasara kamar wannan tana son fin ƙarfinta, ko dan tazo a saliha ne.
Ai Juhainah tana jin Yah Boss ya gama wanke, Juhainah babba, dan kar asirinta ya tonu tayi saurin sakin numfashi tana ririƙe Yah Boss tana maida numfashi.
Yah Boss
Ya kalleta a hankali yana faɗin.
"Ke! Buɗe idanunki ina yake miki ciwo? Khairat zo kamata kuje parlour"
Khairat ta kamata tana mata sannu, Surayya ma ta riƙe hannunta.
Juhainah tana hawaye tace.
"Yaya cikina yake ciwo Wlh mayya ce, dan tace na mata hanya ka aureta nace ba ruwana shi kenan tace naje zan gani..."
Ya Boss ya gyara tsayuwarsa yana zuba hannayensa cikin aljihunsa, ya zubawa Juhainah ƙarama lumsassun fararen kyawawan idanunsa, tana basa labarin.
A hankali cikin zazzaƙar muryansa cikin kamewa ya furta.
"Juhainah! Ɗago ki Kalleni"
Da sauri ta ɗago kanta ta sauke idanunta acikin nasa, gashin jikinta ya yi yammm, ta gaza cigaba da masa ƙarya, ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta tana rungume Khairat ta saki sirirn kukan shagwaɓa tana ɓoye fuskarta a ƙirjin Khairat a hankali tace.
"Don Allah Yaya Sadeeq kayi haƙuri bazan ƙara maka ƙarya ba, nice banda gaskiya, amma ban saniba ko mayyar ce, kuma ni Ban yarda da ita ba, ka korata karta cutar min dakai, Wlh mutum ba abin yarda bane"
So yake yayi murmushi amma shegen zafin Kai ya hanasa, ya kalli Khairat da Juhainah ta ƙamƙameta kamar zata koma cikinta, a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Khairat kama hannunta kuje parlour.
Ke kuma Surayya kike ko? Wa? Mi ya haɗasu?"
Khairat taja Juhainah suka tafi Surayya kuwa duk ta daburci ba ɓata lokaci tace.
"Daman Juhainah tace muje bedroom ɗin ni wlh bansan akwai mutum aciki ba, amma batayi mata komai ba, kuma batace zata aureka ba..."
Cikin tsare gida ya furta.
"Me kuke aciki? Duk girman gidanan kuka rasa inda zakuje sai inda aka sauketa?"
Surayya ta haɗiye yawu tana daurewa yadda karta kwabsa ta tonawa kansu asiri, cikin dauriya ya fara shararo ƙarya tace.
"Cemin tayi na bata shawara akan kace ta fito da miji cikin kwana uku, tunda bata son, Ammar, wai na tayata zaɓa acikin samarinta uku waɗanda suke sonta bata kulasu, harda Yayana Jamal aciki ni kuma nace mata tayi haƙuri ta fito da Jamal ɗin"
Yah Boss ya furta.
"Ita da bata son Yaro sai babba Jamal engineer ai yaro ne ƙarami, Ok yanzu ya kukayi da ita?"
Surayya cikin jin daɗi Yah Boss yau ya tsaya yana magana da ita darajar Juhainah.
Surayya cikinta na ɗurar ruwa da fargar kar aje Jamal ya kwabsa su, tace.
"Sunyi magana da wayata ta faɗa masa ya fito suyi aure zaka mata auren dole yace ba matsala ai daman itane taƙi"
Yah Boss ya girgiza kansa yana beƙa mata wulleliyar Samsung ɗinsa, a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Saka min numbersa zan masa magana"
Surayya tana rawar hannu ta amshi wayan da take ɗaukan ido, sai daddaɗar ƙamshinsa take, ta shiga loda masa number Jamal, acikin zuciyarta tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
Yana amsar wayan ya saka kai ya tafi yabarsu nan tsaye ita da Juhainah babba, ba wanda ya sake kallo acikinu.