← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 113

Sashe 68

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanifah cikin farin ciki tace.
"Yawwa Ngd ummata sai anjima ki gaishe min da Babah naji muryansa ɗazu"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran.
Umma tace.
"Ke uwar son miji ba za'a zage shi ba, ina zaune zaki kirani kina ɗura masa zagi idan dai baki ajiye taurin kai muka kamasa a hannunmu ba Wlh..."


Yah Boss yau da wuri ya fita gun aiki Sbd wasu manyan Case har uku da dole sai shi da kansa, zaiji da lamarin kafin ya tura su Court.
Amma kafin ya fita ya laƙo Juhainah, Suhaima ta tabbatar masa tayi sallah ta koma ta kwanta.
Hakan yaji nustuwa kaɗan, da bata tayar da rigima ba.

Gidan Daga Zarah sai Hajjah Mama sai Juhainah da take Stairs tana bacci, Khairat da yaran sun tafi school.
Ƙarfe goma Haj Jamila and Karimah suka iso gidan Yah Boss, sun iske Juhainah ta farka ta sauko kenan suka iso, tana breakfast suka fara mata gyaran jikin.
Tsumin yau da ta sha kamar zatayi amai take ƙoƙarin yi suka hata suka bata tsamiya ta dinga tsotsa har aman ya tafi.
Yau tsareta suka yi kowane haɗin tsumi sai da ta shanye, harda su kuka yau na shagwaɓa ga tana kiran Yah Boss bata samunsa, duk ta damu kanta son jin inda yake da wayoyinsa basa shiga.

Zarah yau tunda ta fito suka gaisa da masu gyaran jiki ta koma ɓangarenta bata sake fitowa ba har bayan sallar la'asar da suka tafi shima hajjah Mama da zata tafi gidansu Maah ne ta kirata ta fito sukayi sallama akan can zata zauna har ranan ɗaurin aure, Sbd baƙin da aka fara Familles Janfar sun fara zuwa za'ayi auren Autar Maah.

Misalin ƙarfe biyar na yamma gidan Yah Boss daga Juhainah sai Zarah.
Ba sabgar juna suke ba.

Juhainah tana zaune da wayanta a hannunta.
Text ta turawa Yah Boss.

*"Please, Habiby, where are you going today?*

Lokacin yana ganawa da baƙi a cikin ofishin sa.
Kasancewar special Phone ɗinsa ta Familles ne yakai lumsassun idanunsa kan screen ɗin wayan.
Juhainah ya gani.
Saƙon ya duba ya bata amsa.

*"I'm with people"*

Baki ta zumɓuro gaba ta tura masa.

*"I love you Habiby"*

Anutse ya duba ya ajiye phone ɗin, yana maida hankalinsa gun baƙin nasa.

Ganin bai bata amsa ba ta sake tura masa.

*"Missing you is stressing me out, I feel like I'm going crazy"*

Anutse ya sake duba saƙon yana gyara zamansa cikin shigar alfarma da take jikinsa.

Ya tura mata.

"Bilkisu! I'll come back at night, get ready, okay?"

Kamar yana gabanta ta maƙale kafaɗa ta tura masa.

*"A'a ba zan jure ba yanzu nake son na ganka Habiby Ɗan uwana, yanzu zan kawo maka abinci kuma ni zan baka a baki da hannuna, amma yau sai ka bani Sweet Habiby, kuma bakinka za ka manna a nawa sai ka saka min a harshena"*

Wannan karon bai duba saƙon ba yaci gaba da uzurin shi, dan haka bai san me ta rubuta ba.

Ganin bai maido ba.
Kamar an tsikareta ta miƙe ta nufi hanyar kitchen tasan yanzu Jamilu ya shigo ɗaura girkin dare.
Ai kuwa yana zubawa nama ruwa da ya ciro daga freezer, ta shigo a hankali ta masa sallama.
Jamilu ya juyo yana amsawa.
Juhainah tace.
"Jamilu yau Yah Fu'adh yazo kuwa ya amshi abincin Yah Sadeeq?"

Jamilu yace.
"A'a baizo ba, ya kirani dai yace suna busy har Madara da yake sha, sha biyu na rana, yau Fu'adh baizo ya kai masa ba, yau jama'a gare su Fu'adh yake masa sauran abubuwan meetings ɗin ma shi yaje."

Juhainah kamar zata yi kuka tace.
"ALLAH Sarki yayana bawan ALLAH ina abincin da Madaran? Zan kai masa"

Jamilu yace.
"A'a amarya da tsuntsayi jibi ɗaurin aure zaki fita? Gaskiya idan kin kai faɗa zai min baya son kina fita ko bakin gate"

Baki ta Turo cike da tsiwa tace.
"Ka manta ba jibi ɗaurin aure ba, yau za'a ɗaura shi, kuji min mutum da wani zance, TOH Wlh idan baka ban ba Allah sharri zan maka gun yayana ince ka zagi kakaf dangin Maah da na Papa, dan kace in fasa auren Jamal na aureka nace A'a..."

Jamilu ya zaro ido yana faɗin.
"Juhainah! Wace irin magana kike yi haka Sbd Allah? Ki Rufamin asiri, kije komai na kan dinning room acikin Basket, har Mug ɗin dafaffiyar madaran"
Gwalo ta masa tana dariya tace.
"Kaga yarinya da wayo ko"

Ta faɗa tana juyawa ta tafi.
Jamilu ya wanke hannunsa ya ɗauki Phone ɗinsa ya kira Yah Boss.
Ofishin sa mutum biyar zaune suna tattaunawa bazai samu damawar amsa waya ba, bai ɗauki kiran ba.
Fu'adh ya kira shima yana cikin meeting bazai ɗauka ba.

Juhainah dinning room taje ta ɗauko basket ɗin mai shegen kyau, ta kawo parlour ta ajiye akan Center Table ta haye Stairs sharp-sharp ta canza kaya yanzu ma riga da wando Pink colour ta saka masu taushi ta saka hijabi Black mai kyau har ƙasa sai wani Mayen ƙamshi take batayi anfani da turare ba wanda ake tsumata ne ya gama kama jikinta.

Hills baƙi ta saka da ƙaramar handbag ɗinta ta saka wayar ta ta sauko down stairs.

Basket ɗin ta ɗauka ta fice.

Tana fitowa ma'aikatan gidan sunata gaisheta kamar ita ne matar mai gidan.
Bata shiga mota ba, Sbd Yah Boss ya hanata driving ko da wasa bata ɗaukan mota, ganin lokacin zuwa ɗauko su Suhaima ya kusa bata ce Hamza ya kaita ba, ta siɗaɗa ta fice daga gidan a ƙafa.
Security's suna kallon amma basuyi zaton nesa zata ba.

Bakin titi ta nufa.
Tana tsaye keke napep kusan biyar kowace ta wuce a cike, ga bata son ganin mutane na yawan kallonta.
Mota uku ta tsaya dan rage mata hanya taƙi ko kallon arziƙi bata masu.
Gaba tayi tabar gun.
Tana cikin tafiya tana duba keke napep ta hango Jamal a tsallaken titi tsaye gun mai siyar da Fruits, har zata wucewarta taƙi masa magana sai ganin wani tayi ya sha gabanta a mota tai saurin tsallakawa kafin ya fito daga motar.
Tana isa gun ana basa ledar fruits ɗin da ya siya.
Ido huɗu sukayi, ya wani tsuke fuska yana ƙoƙarin wucewa.
Fuskarta a sake tace.
"Yah Jamal! Please ka kaini police station ɗin su Yah Boss zan kai masa abincinsa ban samu keke napep wadda ba kowa ba"

Wannan mutumin da ya sha gabanta ne ya iso gun nasu da sallama yana beƙawa Jamal hannu.
Jamal ya sallamar yana beƙa masa hannu.

Juhainah ta ɓata fuska sosai batayi magana ba.
Mutumin babban mutum ne zai yi shekaru 45, a hankali cikin nutsuwarsa yace.
"Don Allah ƙanina wannan yarinyar ƙanwarka ce? Wlh kallo ɗaya na mata Allah ya jarabeni da ƙaunarta"

Jamal ya kalleshi ya kalli Juhainah da take turo baki gaba, a hankali ya furta.
"Alhamdoulillah! Ai daman babban mutum kike so ko?"
Juhainah ta matso kusan Jamal kamar zata fasa kuka ta kamo hannunsa tana jansa gefe ta shagwaɓe fuskarta tana faɗin.
"A'a ba irinsa nake so ba irin Yah Boss, wannan ƙaton ciki garesa kalli ƙafafunsa kafta² ai gwara na aureka muyi zaman haƙuri da na auresa, kaje kace masa kaine mijina Please"

Jamal ya kame fuska Yana kamo hannunta yajata har gun motarsa ya danna remote ta buɗe yace.
"Shiga ki zauna"

Cikin farin ciki ta shiga motar ta zauna tana rungume basket ɗin a cinyarta, ya rufe kofar ya koma gun mutumin, da ya matsu Jamal yazo yaji wani halin yake zai samu a basa auren ƙanwarsa ko an mata miji, dan yanajin abinda bai taɓa jiba akan kowace mace sai Juhainah....

🤣Sauran kuyi comments da Sharhi kaɗan, Sbd dare ya kawo jiki, Wlh ni kula nayi kwanciyata sai bayan sallah idan munada rai da lafiya.Kasancewar bed nada girma ta raɓa tayi kwanciyarta gefen ƙafafuwansu....

[14/02 13:17] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 37*

Jamal yana dawowa ya kalli mutumin yana faɗa masa.
"Kayi haƙuri aurenta ya kasu Wlh da ace ta amince da kai zan hƙr Na baka ita, Sbd nine wanda zan auretan. Amma idan bazaka damuwa inada ƙanwa ƙawarta ce tafi ma wannan gwaɓi har shekarun, idan kana sonta zanyi maka tsaye har ka sameta."

Jamal ya ƙarasa maganar cike da mugunta yana son tayarwa da Surayya hankali kamar yadda ta tasa masa nasa hankalin.

Alhaji Ali yayi mamakin Jamal ba kaɗan ba, irin wannan karamci da sauran rana bata gama faɗawa ba an basa kyautar budurwa sukutum.
Cikin farin ciki yace.
"Gaskiya na gode sosai Allah ya saka da alkhairi, inaso tunda tana yanayi da wannan yarinya"

Jamal ya jinjina kansa yana faɗin.
"Kaban number ka zan kira ka in sha Allahu"

Ai kuwa Alhaji Ali jiki na rawa ya amshi wayan Jamal ya loda masa numbersa, ya beƙa masa wayan sukayi musabaha ya tafi ya tsallaka dan shiga motarsa.
Jamal ya nufi motarsa.

Juhainah tana zaune ya shigo yana rufe ƙofar, ba tare da ya kalleta ba ya kunna motar ya mata Rivas yabar gun.
Juhainah ta kallesa cikin son masa wayo taji yadda suka yi, a hankali cikin kwantar da murya tana basa girma kamar yadda yake so tace.
"Yah Jamal! Kuma ya kukayi da wancan ƙatun mai manyan ƙafafuwa?"

Shiru ya mata yana driving ɗinsa bai da niyyar mata magana.
Matsowa kusansa tayi kamar jikinsu zai haɗu sai ta dakata, ta leƙo fuskarsa tana shagwaɓe fuskarta a hankali tace.
"Mijina Jamal! Please mana magana nake maka ka kula matarka mana"
Ta ƙarasa maganar tana ɗora hannayenta saman nasa tana faɗin.
"Yawwa bari na tayaka driving"
Motar ta shiga tagal-tagal saman titi.
Cikin wani irin sauri ya taka Burki saboda tana neman ɓarar dasu, ya hankaɗota ta koma kujarata tana zama ta shagwaɓe fuskarta tana faɗin.
"Wayyo Allah Yah Boss za'a kashe maka Ni, washhh hannuna zafi"

Mugun kallo ya watsa mata cikin faɗa yake magana.
"Wai ke wata irin yarinya ce? Kinada hankali kuwa? Jinnu hauka ne?"
Chapter 68 · 0% Book details