Sashe 51
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
*Page 28*
Jamal
Daga can inda yake zaune yana jin abinda yake faruwa.
Hannunsa ya ɗora saman goshinsa yana ɗan murza wa, ya buso iska daga bakinsa.
Jin ihun Juhainah yaji babu daɗi akwai tausayi Tabbas, cutar jinnu irin wannan.
A hankali ya maida hannunsa yana dafe kansa yana katse kiran.
Can a hankali ya furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ni kam wani irin aure zanyi a haka? Bana sonta ga bata da lafiya? Dole zanyi haƙuri saboda fushin mahaifiyata, ita kanta rayuwarta akwai tausayi, Allah ya bata lafiya Ameen..."
Ai ko yana rufe bakinsa kiran Mamy yana shigowa Wayarsa.
Yah Boss
Juhainah shaƙarsa tayi ba shaƙar wasa ba, tana neman cizon shi, ya hana hakan, saboda riƙon da ya mata bana wasa bane.
Saman lafiyayyar Sofa da yake huta wa ya kwantar da Juhainah, da take wani irin mahaukacin ihuuuuu mai firgitar wa, tana harbe², jikinta ya fara lauyewa tamkar Maciji.
Zama yayi gefenta yana riƙe ƙafafuwanta.
A ɗan sauti ya fara kiran Fu'adh.
"Fu'adh! Fu'adh!! Fu'adh!!!"
Wani irin zillo tayi sai gata zaune ta faɗo kansa, ta cakumesa da hannayenta duka biyu, tana wani irin ihu, idanunta sun juye.
Kokowa suka fara saboda ba dukan wasa ta fara ma Yah Boss ba.
Matseta yayi sosai jikinsa ya riƙe hannayenta yana fara tofa mata addu'a.
Fu'adh ne ya shigo room ɗin, yana kallonsu cike da mugun tausayin Juhainah, saboda yadda ta juye lokaci ƙalilan, kamar ba ita ta gama masa fira yanzu ba.
Yah Boss a hankali ya furta.
"Fu'adh ka kira min Sumayya yanzu kace ta hau Upstairs bedroom ɗina ta buɗe drawer akwai zam-zam ta ɗauko ta zo yanzu"
Fu'adh ya amsa da.
"Ok Sir"
Ya fice.
Yana fitowa ya dauki special Phone ɗin Yah Boss ya lalubo number Sumayya ya danna mata kira.
A lokacin Aunty Sumy suna tsakiyar cin abinci, ita dasu Ruwaida Rumaisa Aziza.
Wayarta da take cikin Jakarta ta fara ringing.
Rumaisa ta beƙo mata, ta buɗe Jakar tana ciro wayan.
Ganin number Yah Boss ta tsame hannunta daga abincin, ta miƙe tsam tana picking call ɗin, ta nufi hanyar Stairs, tana kai wayar kunnen ta tare da sallama.
Murya Fu'adh taji ya amsa sallamar, tare da faɗin.
"Aunty Sumy Sir yace kije ɓangarensa a bedroom ɗinsa cikin drawer akwai zam-zam ki ɗauko kizo police station yanzu²"
Aunty Sumy hankali a tashe tace.
"Fu'adh! Lafiya kuwa?"
Fu'adh ya yi gyaran murya a hankali yace.
"Kiyi saurin don Allah, Juhainah ce abunta ya tashi yanzu daga zuwa.."
Ya idar da faɗa mata haka ya katse kiran.
Aunty Sumy cikin sauri ta ƙarasa hawa upstairs ɗin.
Key ɗin yana jikin ƙofar parlour ta buɗe ta shiga a guje, kai tsaye ta nufi master bedroom ɗinsa.
Bata sha wuya gun ganin zam-zam ɗin ba, a drawer ta ɗauko ta rufe masa ƙofar ta zare key, ta rufe parlour ma ta zage key ta tafi dasu.
★
Jamal
A hankali yayi picking call ɗin kafin ma yayi magana Mamy har ta rigasa yin magana tana faɗin.
"Jamaluddin! Ka kira Juhainah ka bata haƙurin?"
Jamal kamar zai fasa ihu a hankali ya furta.
"Eh har zuwa yanzu banyi magana da ita ba, nayi miki alƙawarin kiranta na bata haƙuri Mamy tunda haka kike so"
Mamy tace.
"Ƙwarai kuwa Jamal haka nake so faɗi ka ƙara faɗi, idan kana son kwanciyar hankali na, kafin nan kafin dare ka kirata ka bata haƙuri."
Fuskarsa ya yamutsa a hankali ya furta.
"Ok alright za'ayi abinda kike so Mamy"
Mamy bata ce komai ba ta katse kiran.
Jamal ya lumshe manyan kyawawan idanunsa yanajin ɗaci acikin zuciyarsa.
A hankali ya furta.
"Duka² nawa nake saboda Allah da za'a min auren dole, karatu fa nake shekaruna duka 25, Ni anan da shekaru 5 ma wlh aure baya gabana, kuma bana son ƙanƙanuwar yarinya, babbar mace nake so, wacce tasan zafin kanta, mai kamun kai, da sanin darajar na gaba da ita.
Amma a tirsasani akan abinda bana so hummm!"
Ya furta yana kaiwa iska naushi...
Juhainah
Cizo ta fara ƙoƙarin kai wa Yah Boss akan fuskarsa.
Ya riƙe kanta sosai ya hanata aikata hakan.
Yana manna bakinsa akan kunnenta da ɗan sauti ya fara mata karatun.
Ihu take sosai tana ƙoƙarin ƙwatar kanta, amma ina Yah Boss jajirtaccen namiji ne, ta gaza ƙwatar kanta, sai ihu take.
Fu'adh yana tsugunne shima addu'ar yake tofa mata.
Aunty Sumy koda ta sauko ba wanda tace ma ga inda zata je, ta sa kai ta fice.
Waya ma take ta nufi hanyar fita daga parlourn, tunda daman handbag ɗinta a hannunta key motarta na ciki.
Wani irin gudu tai cikin mintinan da basu da yawa sosai ta iso police station ɗin.
Tunda ta hanyo Stairs take jin ihun Juhainah, da gudu ta ƙarasa bakin ƙofar ba wanda ta gaisar su ne ma suke gaisheta ganin bata hayyacinta.
Ƙofar ta buɗe ta shigo ofishin, wayam ba kowa, ta nufi room ɗin inda take jiyo ihun.
Ganin halin da Juhainah take ciki Aunty Sumy ta fashe da kuka tana faɗawa jikinta.
Yah Boss ya furta.
"Shift small, please ki bar kukan, zo riƙeta na tofa addu'o'in muga"
Aunty Sumy ta zaune inda Yah Boss ya tashi, yana riƙe da hannayen Juhainah ya beƙawa Aunty Sumy, ta riƙe shi kuma ya nufi kan table ya ɗauko Cup.
Ai ko taku biyu baiba Juhainah ta kifar da Aunty Sumy ƙasa, ta haye ruwan cikinta.
Da sauri ya juyo ya ɗauke Juhainah sama yana faɗin.
"Kinga ni Sumayya ko Wlh wannan abun nata na ɗagamin hankali, bana son dukan da take Sam-sam, Ya ALLAH ka dube mu"
Ya ƙarasa maganar yana zaunar da ita suna kokowa ya riƙe ta da ƙarfi.
Aunty Sumy ta miƙe tana riƙe ƙugunta dan ta kadu da kyau.
A hankali ya furta.
"Fu'adh zo riƙeta nayi addu'a.
Hannayenta zaka riƙe da kyau, Sumayya ki riƙe ƙafafuwanta, ki ƙoƙarta"
Fu'adh ya riƙe hannayen da kyau tana tofa masa yawu tare da faɗin.
"Allah ya tsine muku albarka tsinannu"
Yah Boss ya ɗauki zam-zam ɗin ya ɗauki Cup ya zuba ya nemi guri kusan Juhainah ya zauna.
Yawu to tofa masa a fuska tace.
"Allah ya isa tsananin mu daku mugaye masu raba ƙauna"
Yah Boss idanunsa a kanta yake addu'a cikin ruwan zam-zam ɗin.
Kokowa suka fara da Fu'adh tana son amshe hannunta.
Ƙafafunta da Aunty Sumy ta riƙe take son ƙwace wa.
Cikin mintina ashirin da biyar yayi addu'o'in Ruƙiyya masu ɗan yawa, duk da ba duka ba.
Ruwan ya watsa mata a fuskarta, ya kurɓi a bakinsa ya fesa mata a kunnuwanta.
Wani irin ihu tayi jikinta na ɗaukan rawa, ƙarfinta yana ragewa.
A hankali ya furta.
"Ku saketa"
Fu'adh da Aunty Sumy suka saketa.
Ai kuwa ta fara naɗewa guri ɗaya.
Matsowa yayi yana faɗin.
"Sumayya! Ɗago kanta buɗe min bakinta"
Sumy ta riƙeta yanzu kam ta gaza ƙwatar kanta.
Bakin ta buɗe ya kafa mata Cup ɗin mai addu'a, ya danne hancinta.
Ai kuwa dole ta fara shan ruwan.
A kanta ya zuba sauran a hankali ya furta.
"Sumayya ki murje dukan gashinta"
Ai Sumy na tsakiyar murza gashin suka ga tayi wata irin attishawa, tare da hamma.
Sai jikinta ya saki idanunta suna dan dawowa da baƙin, suka lumshe sai minshari, alamar mugun ya fece.
Jikinta ya saki lagab ta narke a jikin Aunty Sumy tana bacci.
Yah Boss yana kallonta ya miƙe tsaye a hankali ya furta.
"Sumy! Ki gyara mata kwanciya ki rufeta ga Duvet can, shegen nan baiyi nisa ba, saboda batayi amai ba, kenan akwai damuwa har yan zun, saka mata hularta Please"
Ya ƙarasa maganar yana nufar ofishinsa.
Fu'adh yabi bayansa yana faɗin.
"Ubangiji ya bata lafiya gaskiya wannan ciwon na Juhainah Sir baza'aje gun masu bada magani ba...?"
Yah Boss ya juyo yana zubawa Fu'adh lumsassun fararen kyawawan idanunsa a hankali ya furta.
"Bance ba'a samun masu badawa a warke ba, amma ai Qur'ani yafi kowane magani a duniya, shi ne mai warkar da kowacce cuta a duniya, dan haka babu inda zamu kaita, Allah yana sane damu, ya amsa mu jira lokaci, kowane irin mutum da irin tasa ƙaddaran, ita nata ne a haka, ba inda zamu je har asaka mu kauce hanya."
Fu'adh yabi bayansa yana faɗin.
"Sir nima daman gun masu ruƙiyya nake faɗin muje"
Yah Boss
Ba tare da ya juyowa ba, ya furta.
"Listen to me Fu'adh!
Wadda nake mata iya duk wani Malami da zai mata kenan, just kaga kenan mubar wa Allah ikon sa."
Fu'adh yace.
"Haka ne Sir Allah ya bata lafiya, bari naje nayi wanka naci abinci sai na dawo"
Yah Boss ya ja lafiyayyar kujerasa ya zauna yana bin Fu'adh da shegen kallo.
Fu'adh yace.
"Allah baka haƙuri Sir nasan laifina na gayyaci jama'a ɗaurin aure ba"
Yana ƙarasa maganar ya nufi ƙofar fita ya siɗaɗa ya wucewarsa.
Tsaki Yah Boss yaja.
Aunty Sumy ta gyarawa Juhainah kwanciyarta ta ɗaure mata gashin, ta saka mata hula, wani lafiyayyan Duvet ta gani fari ta ɗauka ta lulluɓeta ta nufi ofishin Yah Boss.
Yana zaune wayar Juhainah a hannunsa yana ƙoƙarin cire password yaƙi cirewa.
Tuna tace sunansa ne a sama ya saka Yah Sadeeq bai buɗe ba.
Kai ya girgiza ya saka Yah Boss.
Ai kuwa wayan ta buɗe.
Kai ya girgiza, fuskarsa na sake kamewa.
Aunty taja kujera ta zauna idanunta cike da ƙwalla tace.
"Yah Sadeeq! Me ya faru abun ya tashi kuma?"
Kallon ta yayi yana ɗaga kafaɗunsa a hankali ya furta.
"Kirana tayi tace. Wani ya kirata yana mata barazana, shi ne nace tazo, na tura aka kawota, ko zama bata yi ba suna fira da Fu'adh ta yake jiki, ina tunanin ko tsorata da kiran da aka mata ne"