Sashe 42
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suhaima ta fashe da wani irin kuka ta ɗauki tray'n da kayan marmarin suke ta jefa ta ɗauki Cups Glass da suka sha juice har Uku tayi jifa dasu suka tarwatse tana faɗin.
"I hate you Dadd Wlh Abuja zan tafi"
Hanifah cikin tsoro ta janye Al'amin ta riƙe Suhaima tana fashewa da kuka tace.
"Don Allah Suhaima ki rufa min asiri karki kashe min aure Wlh Nasir baya son munafurci ni ban faɗa maki dan munafurci ba, bansan baki saniba da bazakiji a bakina.."
Suhaima ta fizge jikinta cikin ƙaraji tana kuka tace.
"Karki sake taɓani dake aka haɗu wajan cin ma'anar Ammi nah, na tsaneki kema, wlh duk wanda yake da saka hannu a auren nan bani ba shi..."
Ta ƙarasa maganar tana nufar upstairs tana kuka iya ƙarfinta.
Al'amin ya fashe da kuka ganin yayarsa tana kuka cikin tashin hankali, yabi bayan ta yana kiranta.
"Aunty Suhaima kiyi shiru kinji"
Yah Boss sun zauna da Sumy a parlour sa kenan, yaji ihun Suhaima, ya miƙe yana faɗin.
"Shi kenan ga ɗayar matsalar nan, TOH amman waye ya sanar da ita yanzun?"
Ya ƙarasa maganar yana nufo ƙofar.
Tsaye yake cikin tsantsar damuwar da baka cika gani akan fuskarsa ba.
Ƙin taka Steps yayi saboda yana tarbota tana iya juyawa taje ta faɗi taji ciwo hakan bazai iya ɗauka ba.
Tana hayowa cikin kuka tace.
"Dadd I hate you, shi kenan ka manta da Ammi nah ko? Innalillahi Wayyo Allah Ammi nah don Allah ki dawo Dadd ya manta dake"
Ta ƙarasa maganar tana nufar parlour sun da gudu.
Taku uku yayi ya damƙota yana ɗaukanta sama ya nufi parlour sa da ita a hankali ya furta.
"My Babies calm down please, zan miki bayani ina son Amminki kinji"
Kuka take kamar ranta zai fita.
Zama yayi tana jikinsa yana buga bayanta yana kallon Aunty Sumy cikin tsantsar damuwar da ba'a saba ganinta akan fuskarsa ba.
Aunty Sumy ta riƙe hannunta tana faɗin.
"Don Allah Babie ki fasa kukan Nida Dadd ɗinki zamu miki bayani duk da nima bansan me yake faruwa ba, amman na gane Dadd ɗinki baya son auren haɗawa akayi"
Al'amin ya shigo yana kuka da gudu ya nufi Dadd ɗinsu.
Yah Boss ya kamosa ya rungumesu idanunsa yana bala'in canzawa saboda a duniya ya tsani kukan ya'yansa, koda uwarsu da rai, bare yanzu da shi ɗaya gare su.
Sumbatar kumatuntu yayi a hankali ya furta.
"Don Allah karku ƙarasani keda Juhainah kuyi haƙuri nima bana sonta, hajiya Mama ta matsa min ya ku ke so nayi? Papa ma gaba take da shi Suhaima ki nutsu ko daina kukan bana so Please, kiyi shiru na maki bayani yadda zaki fahimta Babie Ok"
Cikin kuka tace.
"My Dadd bana sonta ni bana sonta ka saketa, ai kai kace na zabo maka matar da zaka aura, ina cikin nema sai kawai yanzu kayi aure Wlh bana sonta ni Abuja zan tafi gurin su Jaddat..."
Bakin ya rufe mata da tafin hannunsa yana girgiza kansa a hankali ya furta.
"Kukan ya isa haka ba inda zaki, ba inda ƴaƴana zasu tafi, akan wata, yanzu kin samo wacce kike son na aura ɗin? A yau ma za'aje neman aurenta"
Kallonsa tayi da irin idanunsa.
Kukan ta fasa tana hawaye tace.
"Ni Ban samoba ina kan neman kayi min alƙawarin zaka aura idan na samo?"
Goshinta ya sumbata yana zaro handkerchief ya fara goge mata hawayen fuskarta, ya goge wa Al'amin hawayen, a hankali ya furta.
"Nayi maki alƙawarin auren in sha Allahu, wannan kuma zata ɗan zauna ne saboda darajar Hajjah Mama, kar tace na raina ta, kin gane ai my Babies?"
Suhaima tayi kicin² da fuskarta.
Aunty Sumy na riƙe da tattausan hannunta cikin sigar lallashi tace.
"Ki haƙura Babie Suhaima Dadd na sonku, ku barta ta ɗan zauna kafin ki samo wacce zai auran ita kuma sai ya saketa"
Suhaima ta kalli Yah Boss a hankali tace.
"My Dadd promise me, idan ka auri wacce na kawo zaka saketa? Kuma ba ruwana da ita tayi rayuwarta muyi rayuwarmu nida Ƙanena da Aunty J?"
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zuba mata, hannunsa ɗaya yana shafa kan Al'amiin ya jinjina mata kansan a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Alright, I promise you my daughter"
Suhaima ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya tare da faɗin.
"Thank you My Dadd I love you"
Hawayen da suka fara bushewa a fuskarta ya riƙe fuskar yana gogewa da handkerchief, yana ɗan sakin murmushi a hankali ya furta.
"Love you too My Babies, shi kenan kin haƙura ko?"
Kai Suhaima ta ɗaga tana ɗan sakin murmushi iya lisp ɗinta.
Al'amin ya rungume Yah Boss da Suhaima yana dariya hankalinsa ya kwanta ganin Suhaima da Dadd ɗinsa suna cikin farin ciki
Aunty Sumy hawaye taji yana bin kyakkyawar fuskarta, daga Yah Boss ɗin har ya'yan sun bata tausayi sosai, saboda ba ƙaramin so yake wa ya'yansa ba, duniya zaune ma Khadijah nada rai, bare bayan ranta, yasan basuda kowa sai shi, baya ƙaunar abinda zai ɓata masu rai.
Ga Suhaima na bala'in son mahaifinta, da kishin mahaifiyarta gani take duk matar da ya aura zata iya rabasu da mahaifinsu.
Yah Boss ya kalli Aunty Sumy yana kame fuska a hankali ya furta.
"My Sumy what is this ?
Wai kunaso kuga rauni na ne ya fito fili?
Please ki barni na nustu, wai me yasa wannan auren yake saka duk abinda nafi ƙauna cikin matsala ne? Na samu Babies sunyi shiru ke kuma zaki fara naki kukan? Ita waccan na kwance babu lafiya, kuma duk ta sakawa kanta damuwar banza akan auren, But nasan me zanyi."
Ya ƙarasa maganar yana gogewa Aunty Sumy hawayen fuskarta, yana kamo kunnenta ya ɗan murɗa, ta saki ɗan ihu tana riƙe hannunsa.
A hankali ya furta.
"I don't want to see your tears again"
Al'amin dariya yake ganin Aunty Sumy na ihu kamar Baby Yah Boss yana riƙe da kunnenta.
Suhaima ɗan murmushi tayi, suna jikin mahaifinsu.
Al'amin yana dariya yace.
"Dadd karka cirewa Momy kunnenta, kayi haƙuri"
Sumy tace.
"Please yaya Sadeeq bazan ƙara ba, Wlh tausayin ku naji sosai"
Fuska ya kame sosai a hankali ya furta.
"Toh bana son kukan kin sani. My Babies waye ya faɗa maku labarin nan?"
Suhaima ta tuna roƙon da Hanifah tai mata akan karta faɗa, ta basar a hankali tace.
"Ya wuce Dadd, bari naje na duba Aunty J"
Yah Boss yana kallonta a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Kunyi sallah a school?"
Suhaima tace.
"Eh"
"Ok abinci fa?"
Suhaima ta yamutsa fuska tana faɗin.
"Eh har saura mukayi muka bayar"
Ta ƙarasa maganar tana janye jikinta ta miƙe tana faɗin.
"Amintacce muje muga Aunty J"
Al'amin ya miƙe yana kama hannunta suka fita.
Yah Boss ya bisu da lumsassun fararen kyawawan idanunsa, cike da tsantsar ƙaunarsu.
A can downstairs kuwa Hanifah zaune hankalinta yayi mugun tashi, tana jin tsoron kar Suhaima tace itane ta faɗa mata.
Kuka take sosai Surayya ta dafa kafaɗarta tana faɗin.
"Haba Aunty Hanifah kiyi haƙuri mana Suhaima tanada hankali bazata ce ke kika faɗa mata ba, abinda nake jiyewa dai zai iya gani akowane lokacin ta wayansa"
Hanifah ta zaro idanunta tana dafe ƙirjinta tace.
"Shi kenan komai zai ƙare Wlh Surayya banyi da niyar munafurci ba"
Surayya tace.
"Babu abinda zai maki ki kwantar da hankalin ki..."
Khairat ce ta shigo parlour da sallama tana kallon Hanifah tace.
"Aunty Hanifah lafiya? Surayya! Me ya faru?"
Surayya tace.
"Aunty Khairat sannu da zuwa, Suhaima ta faɗa wa yaya Sadeeq yayi aure shine take kuka kalli fashe² da ta yi"
Khairat ta zauna kusan Hanifah tace.
"Ayyah! Kibar damuwa in sha Allahu nasan yaya Sadeeq zai lallasheta da Aunty Sumy, suna Stairs ne?"
Hanifah ta share hawayen tana faɗin.
"Eh, amma banyi da niyar munafurci ba"
Khairat tana murmushi tace.
"Don Allah Aunty Hanifah ki share baya komai, bari na iskesu ba ma lallai ta faɗa ba, kinsan Suhaima bata da surutu, kuma ko yaya Sadeeq yagani bazai ce maki komai ba"
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa ta nufi Stairs.
Juhainah ta fara motsawa a hankali tana buɗe dara-daran kyawawan idanunta, tana miƙa tare da hammar yinwa.
Suhaima ta shigo bedroom ɗin ta nufi bed ɗin tana faɗin.
"Aunty J sannu ya jikin? Kinci abinci?"
Juhainah ta shagwaɓe fuskarta tana buɗe baki a hankali tana faɗin.
"Babies kuzo ku kamani na zauna jikina ciwo"
Suhaima ta hayo bed ɗin tana janye Duvet ɗin.
Al'amin ya kama hannunta ɗaya itama ta kama ɗaya suka miƙar da ita zaune.
Suhaima ta taɓa jikin Juhainah tana faɗin.
"Sannu Aunty J yanzu babu zazzaɓin, garin ya kika fasa goshi?"
Juhainah ta ɗaga kanta tace.
"Yinwa nakeji sosai, naje sauka daga bed nayi amai na faɗo"
Suhaima ta fara ƙoƙarin sauka daga bed ɗin tana faɗin.
"Toh bari na sauka na kawo maki abinci sai kici, na kawo maki lemo?"
Juhainah ta ɗaga kanta tana rungume Al'amin da ya zauna kusanta yana riƙe hannunta.
Lamo yayi a jikinta.
Suhaima ta fice.
A parlour suka haɗu da Khairat.
Khairat ta riƙe hannunta tana faɗin.
"Babie ina zuwa? Please banda rigima kinji?"
Suhaima ta janye hannunta tana faɗin.
"Aunty Khairat abinci zan kawowa Aunty J yinwa takeji"
Khairat a ranta tace.
"Alhamdoulillah! Batayi fitina ba"
A zahiri tace.
"Ki zubo dayawa zanci"
Suhaima batayi magana ba ta wuce.