Sashe 48
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
kema kin san ina ganin girman Hajiya Mama bazan taɓa mata musu ba. Zata zauna na wani lokaci ne kafin Suhaima ta samo masu uwa" Maah ta kallesa da dukkan manyan kyawawan idanunta tace. "Kai! Abbah! Suhaima kuma? Ita Suhaima kasan kalar wacce zata kawo maka? Don Allah karka biye wa Suhaima Please Abbah, wlh wlh da nasan haka abubuwan zasu kasance baka farin ciki da auren nan, baka sonta matsa maka akayi da na rufe idanuna na aura maka...." Da sauri ya ɗora tattausan tafin hannunsa akan bakinta yana marairaice fuska, idanunsa na ƙoƙarin fito da ɓacin ransa, a hankali ya furta. "Calm down Maah, me kike haka ne? Wa zaki aura min kuma? Da nasan ranki zai ɓaci dan nace bana sonta tirsasani akayi Wlh da nayi shiru da bakina, Maah Please mana." Maah ta kai masa duka a hannunsa tana hararensa tace. "Rufe min bakinki Wlh bazan yarda ba a nakasa min Ɗa da baƙin ciki, mace ma idan bata son namiji ya abun yake bare kai namiji" Fuska ya ɗan saki yana murmushin yaƙe a hankali ya furta. "Ba komai MAAH ki kwantar da hankalin ki, ni bana son ki nuna damuwarki akan wannan al'amari, ko dan saboda Hajiya Mama, mu barwa Allah ikonsa" Kansa da yake cikin hular ikonsa ta shafa tana faɗin. "Allah ya maka albarka Abbah, ya baka Mace ta gari wacce zaka sota kamar Khadijah, ita kuma ta ƙaunaci ƴaƴanka tsakaninta da Allah" A hankali ya furta. "Ameen Maah darajar ƴaƴana ba, ni zan wuce rana tayi sosai" Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye. Little Maah ce ta shigo parlour ta fito daga bedroom ɗin Maah tashinta a bacci kenan. Maah ta beƙa mata hannun tana faɗin. "Namesake kin tashi?" Yah Boss ya ɗauketa yana sumbatar goshinta yana faɗin. "Maah batayi miki rigima ba babu Mom ɗunta kusa?" Little Maah ta kamo hancin Yah Boss tana gwarancin ta dan bata iya magana ba, irin yaran nan ne da basa baki da wuri. Maah tace. "Ai Zainab bata da rigima Sam, bata biyo halin Autah da bata yarda da kowa sai ni da kai, ita wannan kowa nata ne fa" Yah Boss ya beƙa little Maah wajan Maah, a hankali ya furta. "Toh Maah kina son mu sake samun fitinanniya ne irin Juhainah kuma? Bari na wuce ana jirana, sai zuwa dare in sha Allahu, yaran su shirya da Khairat, da Autarki ni natafi" Maah tana murmushi tace. "Toh Allah ya tsare min kai Abbah na, a dawo lafiya" Ya amsa da Ameen. Little Maah tana ɗaga masa hannunta tana son sakin kuka. MAAH tace. "A'a wannan uba naki ina zai kaiki shi da zaije police station" Maah ta ƙarasa maganar tana goyonta. Daukan wayarta tai ta kira Aunty Sumy. Bugu ɗaya ta ɗaga da sallama. Maah ta amsa tana faɗin. "Sumayya! Wai bazaku fito bane? Ya kamata kuje can gidan yayanku tarbar amarya, karfa ku biye masa, ki shirya don Allah ki tafi, yanzu zan kira Ruwaida idan zata iya, da Rumaisa, sai na kira Haj Jamila da Karimah, sai Mom ɗinku Lubnah, ai kin isa ko?" Sumy da take kwance a parlour ta saman dirka² lafiyayyun kujerun da Yah Boss ya canza mata ko wata huɗu ba ai ba, ta yamutsa fuska a hankali tace. "Gaskiya Maah ni kaina yake ciwo, ki kira su Ruwaida, dasu Haj Jamila sun isa ai" Maah tace. "Sumayya! Don Allah kiyi haƙuri aga Ƙanwarsa agun please, saboda bazan bari Autah su koma ba sai baƙin sun koma ƴan rakiya" Sumayya ba yadda ta iya tace. "Ok ki kira Ruwaida sai na biya ta gidanta na ɗauketa, ina dangin Abun ita bazata ba?" Maah tace. "Ban saniba ki kirata taje kar ta ƙullaceni, ni bana son yawan mata magana Allah ya sani" Tana gama faɗin haka ta katse kiran. Dole Sumy ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta dan shirya wa. Juhainah tana hawa sama ta iske Surayya tayi bacci. Ai ko taƙi shan maganin tunda Khairat mai tirsasata bata nan, Yah Boss ko baya ganinta, bazai san bata sha ba. Kwanciyarta tai kusan Surayya, tana latsa wayarta har bacci ya ɗauketa. Can ɓangaren su Barrister Zarah. Misalin ƙarfe 12 da rabi na rana, suka shigo garin Yola. Kai tsaye suka nufi gidan Yah Boss da yake a anguwan 80 Unit. Lokacin Aunty Sumy dasu Ruwaida Rumaisa Haj Jamila Karimah Lubnah duk sun iso, saboda Maah ta kira su akan suje can gidan na Yah Boss tarbar amarya. Daman Fu'adh ya kira Jamilu da safe ayi girkin tarbar amarya da mutanenta. Ya ko tsantsara girki naga na faɗa. Motocin reras a jere haka suka dinga ratsa garin Yola ana guɗa kowa kallon motocin yake. Tun a hanya sauran masu zuwa ɗaurin aure, suka ɗauki hanyar gidansu, cikinsu harda Papa da Khabir Mijin Aunty Sumy. Wanda Papa yana motar Mustapha ne, Nasir da Umar sune masu raka amarya har cikin gidanta. Motar su Fu'adh tana a gaba tsaye suka a bakin ƙaton gate ɗin gidan Yah Boss, Horn ɗaya Garba ya buɗe masu gate suka saka kai. Aziza da take bin gidan da kallo tunda gate na farko ta fara tasbihi. Ƴan rakiya basu gama mamakin tsaruwar gidan ba, sai aka shiga asalin cikin gidan idan ake parking ɗin motoci. Ƙaton Parlour sai fitar ƙamshin turaren wuta yake ko ina yana ɗaukan ido tsaf. Su Aunty Sumy zaune suka dinga jiyo guɗa na tashi alamar amarya na ƙokarin isowa bakin parlour. Aunty Sumy ta miƙe tana kallon hajiya Lubnah ƙanwar MAAH, da da Haj Jamila da Karimah ƙawayen MAAH tace. "Mommy's mu tarbo baƙin ko?" Hajiya Lubnah dasu Haj Jamila suka miƙe suna amsawa da. "Toh Sumayya muje..." A dai-dai wannan lokacin Juhainah ta farka daga bacci, har lokacin Surayya bacci take yi, Sbd ta tara gajiya da baccin exam. Bottle ɗin water ɗin da yake ajiye akan drawer ɗinta ta miƙe zaune ta matso ta ɗauka tana yamutsa fuskarta. A hankali ta ɗauka ta kafa bakinta. Sosai ta sha ruwan ta rufe bottle ɗin ta ajiye ta ɗauki wayanta ta koma ta kwanta a hankali ta furta. "Oh! Ko ina duniyar Ammar love?" Ta ƙarasa maganar tana shiga wajan kira tana duba numbersa da yake ta kiranta. Wayam babu sunansa babu kiransa. Contacts ta shiga tayi neman duniya babu number sa. Laɓɓanta masu kauri ta turo gaba a hankali tace. "Yah Boss ne ya goge min dan nace bana sonsa, ai ni aurensa ne bazan ba, bansan me ya saka ba, amma yanzu ai da na roƙesa gafara kar yaga naci amanarsa, damuwar kuma Banda numbersa akaina. Allah Yah Boss Sai na tayar masa da hankali nima, yanzu², tunda gun Maah nake sai in laɓe bayanta" Ta ƙarasa maganar tana lalubo number Yah Boss wanda tayi saving da suna. *My brother Habiby* gudan kar ta saka Yah Boss ya gani. Kira ta danna masa, tana kwanciya rigingine, tana ƙyalƙyalewa da dariyar mugunta. A can police station ko. Yah Boss koda yazo police station abubuwa sun masa yawa, ga jama'a case iri², sai da ya nustu yanzu nan bai fi minti uku ba da ya samu kansa, ga shi yanada meeting, idan anyi sallar azuhur. Zaune yake a tsararren ofishinsa, wanda tsayawa faɗin kyawunsa da tsaruwarsa ma ɓata lokaci ne. Tsadaddan Glass ɗinsa manne, akan kyakkyawar fuskarsa. Binciken number Zuby yake da kansa a System bai saka kowa ba. Special Phone ɗinsa ta ɗauki ringing. A hankali ya ɗago da kansa ya kafe Phone ɗin da lumsassun fararen kyawawan idanunsa. A hankali ya furta. "Bilkisu! Me zan mata kuma?" Yatsunsa biyu ya ɗora akan Glass ɗin idanunsa ya taɓa gun ɗaukan kiran. Shiru bai yi magana yaci gaba da danna System ɗin. Juhainah jin an ɗaga kiran ta ɓare baki ta fashe da kukan ƙarya tana faɗin. " Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! My brother Habiby, don Allah ka temakeni wani ya kirani yanzu wai idan banje *Ahmed Song* yanzu² ba Wlh rayuwata tana cikin hatsari, kuma da gaske don Allah ka ceceni..." [02/02 14:22] null: _*JUHAINAH*_ Love Story💗🫂 Free Book By Real Rahma Ladingo