← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 113

Sashe 15

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maah tayi murmushi tana kallonsa tace.
"Ai Harɗo yau kam Autarka ta ɗauko magana yau..."
Labarin komi ta basa bata ɓoye masa komai ba, a matsayinsa na mahaifinta.
Ta ɗorawa da cewa.
"Karka masa magana ka barsa don Allah yayi mata hukuncin da ya dace."
Papa yace
"Ya Allah! Juhainah batajin magana, kalamanta yayi tsauri ai daman babu batun nayi masa magana, auren da take so nasan halin Abbah shi zai mata tabbas, mu idone namu, Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi."
Maah cikin farin cikin jin Papa bazai dakatar da Yah Boss daga koma mi ya yanke akan Juhainah, ta amsa da.
"Ameen ya Rabbi Harɗo"
Papa ya kalli Khairat yana faɗin.
"Khairiyya! Ki kama jikin ki, saboda nasan Abbah yana gamawa da matsalar Juhainah zai waiwayeki, duk da kuwa yasan halin ku ba ɗaya ba, amma Yanzu zaiji tsoron lamarin."
Maah tayi ƴar dariya tana kallon Khairat tace.
"Ai Khairat kam ita babu matsala tunda akwai nata a hannun, ita ce daman yake son ƙarasa shekaranta ɗaya University, shima yasan da maganar Harɗo, kaima kasan maganar ko dai hiran Autan ya ruɗaka ne?"
Tana faɗa tana murmushi sosai akan kyakkyawar fuskarta.
Papa ya shafa kansa yace.
"Ai kinsan mace ba mamaki akwai wani a ɓoye, da take tattaunawa da shi, tunda shi wannan yaron ba yawan zuwa yake ba, saboda ya bata damar ta kammala karatun nata."
Khairat kunya taji rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi.
Maah tace"Kaga amsar ka Harɗo? Dan haka tana son abunta, yaron kwarai mai Amana samun masoyi kamar Fu'adh a Zamanin nan yana wahala, ko zamansa da Abbah, a ƙaddara ma baice yana sonta Wlh zamu iya basa ƴarmu, bare shi ya gani yana so."
Papa yace
"Haka ne Allah ya tabbatar da alkhairi."
Maah ta amsa da"Amin ya Raheem."

Suhaima duk da bata shigar sabgogin hiran da bata shafe ta ba, jin Aunt Juhainah na gidan Dad ɗinsu, yana bata horo saboda irin laifin da tayi, abun yaso bata dariya, ta juye tana zuwaba kakannin nata kyawawan idanunta masu haske, a hankali ta matso jikin Harɗo tace.
"Papa zanje gun Aunt Juhainah, muyi kwana biyu Please"
Harɗo ya shafi fuskarta irin Yah Boss sak, yayi murmushi yana faɗin.
"Har kinyi kewan Mamanki kenan? Toh ki kira Dad ɗinki sai ki sanar da shi, amman zuwa gobe ko?"
Suhaima ta juya idanunta wanda abin ya zama kamar sabo a hankali ta amsa da.
"Ok sai goben da yake juma'a da wuri muke saukowa daga school."
Al'amin cikin farin ciki ya rungume Maah yana faɗin.
"Yeee gobe zamu kwana gidan Dad ɗinmu."
Khairat tace
"Eh lallai ma Sweetheart har murna kake ka tafi kwana biyu ka barni?"
Sakin Maah yayi yazo ya rungume Khairat ya sumbaci kumcinta yace.

"Toh kiyi hakuri my Aunt zamuje dake."
Khairat ta zaro kyawawan idanunta tace

"Wai Ni? No! Allah rabani da ɓacin rai, Ban zuwa, Juhainah na can ana gana mata azaba ni naje ta rinƙa min rashin kunya na lakaɗa mata duka, nayi laifi gun Yah Sadeeq."
Maah tace
"Ki kasheta Khairat! Ba duka ba, tana can tana fama ina ita ina rashin kunya."
Papa yayi murmushi yana girgiza kansa, yasan dai ba damar a kushe Juhainah gaban mahaifiyarta.
Khairat ta miƙe tana faɗin.
"Allah ya baku haƙuri Maah, Al'amin muje kamin tilawa naji."
Suhaima ta miƙe batayi magana ba amma tabi bayansu stairs, itama tayi tilawar.
Papa ya kalleta yana faɗin
"Zainab! Ina rabaki da fifita Autah akan sauran ya'yanmu, shi Abbah kowa yasan ƙaunarki garesa shi babba ne, baka haɗa ɗan fari da kowa, amma Wlh na Juhainah ki rage, barin ma nunawa Khairat please."
Hannayensa ta kamo ta riƙe cikin nata kamar zata yi kuka tace.
"Toh ya zanyi? Allah ne ya saka min tsananin ƙaunarsu ita da Abbah..."

Bakinta ya rufe da tafin hannunsa yana girgiza kai alamar tabar abun ranta.
Kai ta jinjina masa alamar taji...


Misalin ƙarfe 9 na dare Yah Boss suka kama hanyar gida, a matuƙar gajiye ya kira Maah ya faɗa mata bazai samu zuwa gidan ba, ya gaji sosai kansa na ciwo.
Maah ta masa addu'ar samun sauƙi, Har ta basa labarin Suhaima nason zuwa gun Juhainah.
Murmushi kawai yayi baice komai ba, ya mata sallama yana katse kiran.

Juhainah ƙarama tana parlon sai da aka kira sallar Maghreb ta haye stairs.
Wanka ta sake tayi sallar Maghreb.
Bayan tayi Sallah parlour ya dawo,bata koma ba sai bayan ta cika tumbinta da girkin dare, ta haye Stairs saboda bata ma son haɗuwarsu da Yah Boss.

Juhainah babba kuwa tunda ta shiga ɗakin da aka sauketa bata fito ba, saboda Allah ya sani bata son jin kalaman Juhainah akan ba za'a ɗauketa aiki a gidan nan ba.

Jamilu ya kawo mata abinci har ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa ta buɗe ya bata, ya tafi.
Wannan a cikin umarnin Yah Boss ne, saboda yasan ko zata mutu Juhainah bazata nemeta dan taci abinci ba.

Koda suka iso gida kai tsaye Stairs ya haye. Yayin da Fu'adh ya nufi dining room ya ciko tumbinsa ya dawo parlon ya zauna yana jiran fitowar sa kafin ya wuce nasa ɓangaren da yake tun a gate na farko.

Juhainah kuwa tuni tayi bacci saboda magungunan da tasha, sbd jikinta ya ƙarasa warware wa.

Ruwan ɗumi ya shiga sosai kafin yayi wanka, ya fito ɗaure da towel yana ƙamshin gel.
Sama² yayi shafe-shafen-sa, ya saka wasu irin fararen kayan ƴan Pakistan mararsa nauyi, ya saka sansanyan turarensa mai daɗin gaske, ya gyara sumar kansa ya nufi parlonsa, yana danna special wayarsa, iya family's Janfar.

Wayan Juhainah ya kashe ya ajiye ta saman bedside, sai kuma ya ɗauko ya buɗe ƙatuwar wardrobe ɗinsa ya jiyeta ciki.
Bai tsaya parlon ba kai tsaye ya buɗe ƙofar ya fito yana wani irin takunsa mai cike da nutsuwa.
Ƙofar ɗakinsu Suhaima ya kalla, ganin bata rufe ƙofar parlon ba, tsayawa ya yi yana ɗan saurarawa shiru babu motsinta a parlon ko ƙaran Tv, yasan tana bedroom ɗin, yanada tabbacin ta ɓoye ne dan kar su haɗu.

Ƙaraso wa bakin ƙofar ya yi ya shigo cikin parlon, da babu haske sosai.
Ƙofar bedroom ɗin ya kalla yaga nan ma bata rufe ba ta ɗan turo ƙofar dai, amma daga inda yake yana jin ƙaran gudun Ac'n
.
Bedroom ɗin ya nufa a nuste.
Babu haske sosai sai fitilar gefen gadon.
Kwance take akan bed ɗin laɓe cikin quilt sai iya kyakkyawar fuskarta ne a buɗe.
Bacci take cikin nutsuwa, Zara-zaran gashin idanunta luff kwance.

Mamakin ta yake yadda bedroom ɗin ya ɗauki wani irin sanyi sosai saboda ta kusan ƙure Ac'n, ko tsoron mura batayi, bare ita mai yawan yin mura ce.

Remote ɗin Ac'n ya ɗauka ya rage sosai, ya ajiye ya juya zai fita kamar daga sama yaji daddaɗar muryanta cikin shagwaɓa tana faɗin."I hate you Yah Boss, I hate you Yah Boss, I hate you Yah Boss"
Ja yayi ya tsaya yana juyowa da mamaki, lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zuba wa fuskarta da jajayen lips ɗinta masu ɗan ƙauri, wanda gefen yake a fashe sbd yadda ya bugi banki yau sosai.Har yanzu bakin nata faɗin i hate you Yah Boss.

Abin mamaki ya basa ganin Hawaye har sun fara gangarowa akan fuskarta.
Kuma tabbas bacci take yi.
Saboda mutum mai bacci da wanda baya bacci, da wanda yayi baccin ƙarya ya sani, don Tabbas Allah ya basa wannan baiwar tun ma baiyi karatun police ba.....
[03/01 16:27] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book

By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

Page 9

Matsowa ya sake yi dab da bed ɗin yana kallon ikon Allah!
Sbd yasan tana ce masa Yah Boss a ɓoye, ko yau ma bakinta ya suɓuce a can gida ta faɗa masa sai tai saurin kame bakinta.
Zuciyarsa ta ingiza shi kamar ya tasheta ya naɗa mata shegen dukan, da gobe zata ji daɗin cemasa i hate you ɗin, duk da yanada tabbacin bazata iya faɗa masa hakan ba ido da ido, sai bayan idonsa.
Shi yafi ma jin takaicin kiransa Yah Boss ɗin, ita fitsararriya, wato suna ta masa a ɓoye, wai Boss sai kace wani ɗan Daba, ko ɗan fashi.
Ranƙwafowa ya yi ya beƙa tattausan farin hannayensa, dan ya janye quilt ɗin yaci mata uwa, da sauri ya janye hannunsa tuna ba sutura arziƙi take sakawa ba.
Saboda yana iya buɗewa ya ganta iya pant da bra ko wasu kayan baccin da su da babu duk ɗaya, duk da tana muharamarsa uwa ɗaya uba ɗaya hakan bai dace ba, sbd shi mutum ne mai tsananin kiyaye dokokin Allah.

Tsaki yaja.
Idanunsa ya ɗan lumshe yana ɗan furzar da iskar bakinsa waje.
A hankali yaji tace.
"Yah Boss please karka ɗauki ɓakar matar nan aiki, na tsaneta bana sonta Allah, har zuciyata."
Kyawawan fararen idanunsa masu kwarjini ya buɗe cike da mamakin Juhainar, kallonta yake cike da takaicinta.

Seconds 15 yayi idanunsa akan fuskarta cikin al'ajabi, toh me baiwar Allah can ta mata ne?
Juyawa yayi ya fice yana rufo mata ƙofar bedroom ɗin, saboda idan yaci gaba da tsayuwa zai mata mugun duka, ko ta cikin quilt ɗin da take rufe ne.
Ƙofar parlon ma rufewa yayi ya nufi downstairs.

Cikin kamewarsa murya mai ɗauke da nutsuwa, Aji dattaku a hankali ya furta.
"Toh Ni nace ina buƙatar ta zauna min gidana fitinanniya? Da ina ra'ayin zamanta gidan zan ɗauketa aiki, sai dai ki mutu da takaicinta, munafuka yarinya me kunnen ƙashi kawai
Zanyi maganin ki"
Chapter 15 · 0% Book details