Sashe 98
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da suka zo Juhainah tana bedroom ɗin MAAH kwance, tana hutawa Sbd rashin ƙarfin jiki, ga magungunan da take sha akwai saka kasala.
Bayan sun gaggaisa ne, Abbah ya kalli Papa yace.
"Don ALLAH kuyi haƙuri Wlh jiya jiya hankalin mu ya tashi da mukaji wannan labarin a bakinsa. Tabbas aure ya ƙare tsakaninsu abun babu daɗin ji sam"
Papa yace.
"Ai duk muminin kirki dole ya amshi ƙaddara, haka ALLAH yaso, bamuda ja da hakan, kuma munji daɗin da kuka fahimci aure ya ƙare tsakanin su. Fatan mu Allah ya basa abokiyar rabonsa, itama ta gama idda ALLAH ya bata miji nagari Amin."
Mamy harda hawaye tana basu Haƙuri.
Maah tace.
"Komai ya wuce ALLAH yasa haka yafi zama Alkhairi Amin..."
Jiki a sanyaye sukayi sallama suka tafi, dan yaunin ganin Junainah suke ji, shiyasa ma basu nema ta ba.
Da dare bayan sallar isha'i Yah Boss ya kama hanyar gidan su.
Zazzaune suke a parlour, Khairat na duba Books ɗin makaranta.
Juhainah tana zaune parlour ta manne jikin Maah kamar zata koma cikinta.
Shiru bata magana sai jan carbi take.
Sanye take da Abaya Pink ta yane kanta da ɗan kwalin abayar, itama Yah Boss ya siya mata.
Anutse ya shigo parlour da sallama.
Suka amsa.
Anutse ya fara takowa.
Kusan Papa ya zauna, yana gaishesu.
Amsawa sukayi Maah tana murmushi tace.
"Ka amshe min yaran nan ko?"
Yah Boss a hankali cikin nutsuwarsa ya furta.
"Maah gobe daga school nan zasu dawo ai. Ya me jikin? Tana shan maganin?"
Maah ta kalleta tana faɗin.
"Eh, jikin alhamdoulillah! Farin cikina batamin koke² ta jure, kana ganin carbi hannunta. Karatun Qur'ani ake ana yawan azkhar.
Matsalar bata magana idan bata zama dole ba"
Yah Boss ya furta.
"Ma sha Allahu hakan yayi, idan bacci take ta tashi ta koma ɗaki."
Khairat ta gaishesa ya amsa.
Juhainah idanunta lumshe tanajin sa taƙi buɗe idanunta, amma ta buɗe kofofin hancinta tana shaƙar ƙamshinsa da yake mata masifar daɗi.
Jin abinda ya faɗa ta ɗago kanta ta sauke dara-daran kyawawan idanunta akan kyakkyawar fuskarsa.
Hankalinsa akan Papa zai masa magana yaji ana kallonsa.
A hankali ya ɗago ya kalleta.
Ido suka haɗa.
Idanunta sun fara cikowa da ruwan hawaye. A hankali tace.
"My brother ina wuni"
Fuska ya kama a hankali ya furta.
"Kinajin yunwa? Ko bacci?"
A hankali ta amsa da.
"Duka nakeji"
Miƙewa yayi anutse ya nufi dinning room a hankali ya furta.
"Taso kizo"
Sakin Maah tayi ta miƙe tabi bayansa jiki a sanyaye.....
[01/04 18:41] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
_💃🏻Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._
*Page 50*
Raudah Sa'idu
Zaune take cikin parlourn ta, sigari take busawa tana amsa waya hankalinta kwance, kana kallon ta da yanayin shigarta kasan tantiriya ce ta gidan gaba.
"Ai ka barta Musbah, Wlh ina sane na bari akayi auren, fansar da zan ɗauka tana ɗakin mijinta sai tafi zafi in sha Allahu, kajira kaka gani, yarinya tana son fin ƙarfina, na gagara yi mata komai har yanzu.
Shi kuma Ammar kabari kaga yadda zanyi da shi, ba dai shi iskanci yake taƙama ba, Dai-dai nake da shi, ko yanzu Wlh yasan Allah ɗaya ne, ba kowacce mace zaka haƙewa ba, babu son ranta ka kwana lafiya, ka zuba ido kaga yadda zan masa Musbah.
"
Alhaji Nuhu da yake zaune a gefenta yana kai komo da hannayensa cikin jikinta, ya cire hannunsa daga jikin nata.
Warce wayan yayi ya kashe kiran.
Wani irin kallo ta masa tana faɗin.
"Alhaji Nuhu! meye haka? Nifa bana son irin wannan halin naka na kishi, bayan kasan ni ba soyayya gabana, Musbah babu abinda yake tsakaninmu da shi bayan kwangila, da mutunci, yana temakona a duk abinda na saka a gaba.
Nace maka kaje ka samu wata tayi maka aikin nan ka nace sai Ni.
Toh ka jira mana tunda ni kake so nayi maka aikin, sanin kanka ne shiga rayuwar Abubakar Janfar hatsari ne idan ba'a shirya ba.
Ga shi Juhainah kawai na gagara cimma burina kai tsaya sai nabi ta bayan gida, kai idan shigarsa ribane kaje kai tsaye ka cika burinka mana, Wlh ina sonsa so na haƙiƙa amma nafi son kuɗi da aikina na kwangila akansa, na watsar da soyayyar amma baka gani ba.
Aiki idan na haɗari ne, a sannu ake bi, ko ayi biyu babu."
Alhaji Nuhu cikin ƙufula ya jefa mata Wayarta ya miƙe yana faɗin.
"Ai ke daman tun farko an faɗa min ƴar kunama ce, duk wanda ya goye ki sai kin harbesa, na rufe idanuna nace naji nagani aikinki nake so, Sbd son da nake miki na aure, ashe ke tsinanniya ce.
Ga shi nan kin bani kunya wajan wata 6 ace kin gaza komai, har damar shiga gidansa kika samu, kwananki nawa a can? Baki tsinana komai ba. Har abada idan baki cika min burina ba kema naki bazai cika ba in sha Allahu. Kije bana son ma aikin zan canza sheƙa."
Yana idar da maganar ya juya fuuu ya tafiyarsa yana baza babbar riga.
Raudah ta bisa da kallo bata ce masa komai ba, ta ɗaga kafaɗunta tana dariya, dan tasan aikin da ya gagareta cikin gaggawa, TOH samun mai yinsa a gaggawa ba'a jinkirta ba, toh tabbas yakai kansan ga halaka...
★
Yana tsaye akan dinning hannayensa cikin aljihu, ta iso ta tsaya kusansa, tana ƙara buɗe hancinta tana shaƙar ƙamshinsa, ta masa ƙuri da dara-daran kyawawan idanunta, amma bata masa magana ba.
Ɗan ranƙwafowa yayi, dab da fuskarta ya hura mata iskar bakinsa mai matuƙar ƙamshi.
A hankali ta sanya hannayenta ta kamo rigarsa ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya.
Janye hannayenta yayi daga rigarsa.
Kujera yaja ya zauna a hankali yana faɗin.
"Ki zauna"
Kusansa ta zauna tana kallon zobensa da yake Babbar yatsarta yana walƙiya, ya ƙarawa hannunta kyau.
Zoben ta sumbata tana sake gyara masa zama a yatsar.
Da kansa ya zuba mata lafiyayyan farar shinkafa da miyar ƙwai, ya zuba mata salad gefe, ya tura mata yana kame fuska ya furta.
"Oya ci kije ki kwanta"
Batace komai ba, ta ɗauki spoon ta fara ci.
Iya salad kaɗai ya zuba, ya fara ci.
Juhainah motsi kaɗan sai ta kalleshi, hankalinsa gun wayar sa da yake duba saƙo.
A hankali ya furta.
"Mai da hankali kici abinci Bilkisu, hope ba inda yake miki ciwo yanzu?"
Salad ɗin da zai kai bakinsa tai saurin kamo hannunsa takai bakinta ta juye salad ɗin.
Kallonta yayi.
Ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta tana sakar masa spoon ɗin.
Janye hannunsa yayi yana sake ɗauko salad a spoon ɗin yakai bakinsa a hankali ya furta.
"Idan kika kuma zan mareki"
Batayi magana ba, ta saka hannunta plate ɗin da yake cin salad ɗin ta tsakura takai bakinta tana lumshe idanunta, ta fara taunawa.
Anutse yake kallonta a hankali ya furta.
"Bilkisu! Maida hankali kici abinci, salad bazai miki ba, ba komai cikinsa"
Kai ta girgrza bata son cin abincin, a hankali tace.
"Yah Boss zan sha tea da bread Please"
Kallonta yayi da mamaki ya furta.
"Da daren?"
Kai ta ɗaga masa tana shagwaɓe fuska tayi rau-rau da idanunta.
A hankali ya furta.
"Alright"
Number Khairat ya kira tana ɗauka yace mata.
"Halima ta dafo tea yanzu"
Khairat ta amsa da.
"Yah Sadiq akwai a ɗakin Maah cikin Flask an dafawa Juhainah ɗazu"
A hankali ya furta.
"Ɗauko Flask ɗin"
Khairat ta kawo tea ɗin ya zuba mata ya haɗa mata da kansa, ya tura mata.
Ta ɗauka batayi magana ba ta fara sha.
Da mamakin sa tsaf ta shanye taci bread sosai.
Tana gamawa ba wasa fuskarsa ya furta.
Muje ki kwanta"
Miƙewa tayi tana biye da shi suka fito.
Bedroom ɗin Maah ya nufa da ita.
Yana tsaye ta kwanta ya sakata tayi addu'a ya sake mata da kansa, ya kunna mata A'c ya zauna akan Sofa ya shiga amsa waya.
Ƙura masa idanunta tayi.
Shi kuma hankalinsa gun wayan da yake yi.
Lumshe dara-daran kyawawan idanunta tayi, magana ne bata son yi,a hankali tace.
"My brother please akawo min My Babies"
Bai tankata ba, Sbd waya yake.
Kafin ya gama wayar har tayi bacci, abinda ya basa dariya harda minshari take yi ta rungume pillow.
Miƙewa yayi ya fice ganin tayi bacci.
Lokacin da ya fito Khairat ta haye Stairs.
Papa da Maah sukace.
"Tayi bacci ko?"
Zama yayi yana faɗin.
"Alhamdoulillah! Bilkisu ta fara hankali, ko kuma wannan abun ne yake cin zuciyarta?"
Maah tace.
"Abbah! Me yasa ka saki Zarah?"
Papa yace.
"Idan da hali ka maida ta don ALLAH"
Yah Boss Kai tsaye ya furta.
"Kuyi haƙuri bana musu daku Wlh Bazan iya maida ta ba, idan ta gaji zata tafi ai, batada kamun kai sam, Ni rayuwata a yanzu haka tafi min daɗi, bana ƙaunar duk abinda zai takura Ni, kuyi haƙuri"
Maah ta girgiza kanta tace.
"Tabbas sai ka sake aure Abbah"
Shiru ya musu ya miƙe yana zuba hannayensa aljihu a hankali ya furta.
"Good night, wai kusan yanzu da zan shigo Jamal yana ƙofar gidan nan, Sbd Bilkisu na zaune ne ban faɗa ba kar ta tayar mana da daru."
Maah tace.
"Ai har abada bazai shigo gidan nan ba in sha Allahu, marar mutumcin yaro"
Yah Boss ya masu sallama ya tafi.
★
Bayan kwana uku da sakin Juhainah Yah Boss ya samu tafiya zuwa, ƙasar China karatun wata 3 kawai zaiyi ya dawo, matemakinsa na kula da komai kamar yana ƙasar.
Ɓangaren Companynsa da sauran abubuwansa akwai Mustapha da Umar, da Fu'adh. Ya hana a faɗawa Juhainah Sbd kar tayi rigima duk da yaga ta nutsu.
Nasir ma bayan tafiyar Yah Boss da kwana biyu ya tafi Mission, da zai ɗaukesa tsawon wata 6. Shi baya nan za'a yi auren Khairat, amma Yah Boss ya roƙi Fu'adh an ƙarasa sai ya dawo, Sbd yana son ya masa komai, kamar ba Ƙanwarsa zai aura ba.