← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 113

Sashe 17

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ta sauke tana gyara zamanta taci gaba da cewa.
"Mutumin da ya kirani yace min mun tsinci gawar mai wayar nan ne a cikin motarsa anan parking spaces na Super market, alamun sun nuna guba yaci cikin abu saboda bakinsa akwai kumfa.
Ni dai iya nan naji bansan ya akayi na farka na ganin a gadon asibiti wai ana maganar kwana nayi da wuni har an binne gawar Mansoor, abinda ya sakani cikin matsanancin tashin hankali kenan, naso a barsa na dawo hayyacina nayiwa mijin wanka da kaina na masa addu'a kafin shiga kabarinsa.
Har akayi sadakar sati ina asibiti saboda jin an kaisa makwancinsa, jikina ya tsananta, sai da na shafe kwana goma kafin a sallameni, sai dai na iske bala'in da ban zata ba, wai iyayensa suka shigar da ƙarana kotu Ni na bawa Mansoor guba yaci ya mutu, abinda ya zafafa ciwon nawa ya rikiɗe ya koma ciwon hawan jini.
Duk wani bincike da akayi an gano banida hannu acikin kisan mijina wanda nake so da ƙauna.
Amma ganin basu samu nasara ba, suka amshe komi da Mansoor ya mallaka min har tilon Ƴata Nadrah, sun amshe ta.
Haka na dawo Misau ina kukan rashin ta babu kalar roƙon da ban masu ba su bar min ita suka ƙi, Ni kuma banida halin jan Shari'a dasu, na barsu da Allah.
A daidai wannan lokacin ciwon mahaifiyarmu yayi tsanani na zuciya, abunuwan sunyi mana yawa, ga ina takaba, haka na rinƙa ɗaukan kayana ina siyarwa ina mata magani da abinda Aunty Hibbah ta kawo, har Gold ɗin da ya siya min na siyar na ƙara wajan magani, yau da gobe sai Allah har takai na siyar da sutura jiki duka masu tsada da kyau, sai da takai banida wani abu mai kyau a tare dani, Shekara ɗaya da rasuwar Mansoor rayuwa ta min mugun sauyi, sai gani ina siyar abinci a bakin titi wanda ban rufe wata biyar ba na daina, saboda wasu Mazan da basuda kamun kai ƙiri² suke nuna maka shashanci.
Duk wannan lokacin ban taɓa zuwa ganin Nadrah ba, saboda na dangana Nasan komin daren daɗewa ɗiya zata nemi uwarta.
Aikatau na fara anan Misau sai dai banida Sa'a gidaje uku duka bana wuce wata uku ko huɗu sai matan su koreni kamar haɗin baki, ganin haka na dawo siyar da awara a kofar gidanmu bana gusawa ko ina, Alhamdoulillah! Rayuwa ta ɗan sauya ina samun kuɗi aciki ake siyawa Mama magani mai sauƙi muci abinci.
Zawarawa a lokacin masu kuɗi da talakawa su kayi min caaaa, Allah ya sani bana sha'awar aure bare soyayya, Ni zuciyata mutum ɗaya take so da ƙauna kuma ya koma Ga ALLAH.
Mutum duk nacinsa sai ya rabu dani, dan bana amsar kyautar kowa haka bana baka fuskar da zaka dinga zuwa zance guna bare ma ka saba da ƴan gidanmu, ka fara masu alkhairi, har ka shiga raina, irin yadda ya haɗani da Mansoor.

Ganin mazan ba zasu shafamin lafiya ba, na tattara na daina awaran bayan munyi sharawa da Mama wadda yanzu Alhamdoulillah! Jikin da sauƙi maganin ne dai ba'a son yana yanke wa, Aunty Hibbah da farko taƙi shawara na daga baya dai ta amince sanin halina.
Magana muka yi da Hajja Ladi tana kai mata aikatau garuruwan Nigeria duk inda kake so tanada mutanen da ta sani can, kuma idan dai ba akasi ba bata badaka lalan hannu, ganin hakan na nemeta akan inason ta samomin aikatau wani gari, tace na zaɓa da kaina na zaɓi nan Yola, saboda inaga tafi kusa dani.
Cikin kwana biyu muka gama shirin tafiya Yola.Da farko gidan da naje aiki sosai hankalina ya kwanta da gidan, saboda yadda matar gidan take sona.
Tsawon wata biyar nayi babu wata matsala ko kallon banza, ina cika wata ake bani albashi na, ni kuma bana ɗaukan ko sisi a ciki nake aikawa gida saboda su Mama su wadata, tunda Aunty Samirah ta wadatani da komi na buƙatar mace tana siyamin.
Ranan da na cika wata shida banza manta ba, Aunty Samirah ta kirani parlo nazo na zauna, ƙasa ina jiran naji me zata ce min, abinda naji ya fito daga bakinta ya bani matuƙar mamaki, wai na amince don Allah na auri mijinta a ɓoye da na samu ciki na haihu na basu ɗan sai ya sakeni zasu cikani da dukiya mai tarin yawa na koma gidanmu babu wanda zai san abinda ya faru.

Wlh naji matuƙar tsoron kalamanta, anan take na bata haƙuri akan bazan iya wannan ɗanyan aikin ba, farko na rasa Ƴata an rabani da ita, yanzu nayi auren sirri na haihu na bayar da ɗan har abada saboda dukiyar da zan barta a duniya.
Tun Aunty Samirah da Hafiz suna lallashina ina tuɓurewa tare da neman hanyar guduwa na baro gidan, kamar sun gane Niyata.
Ban taɓa ganin sakarar mace ba marar kishin kanta da mijinta sai Aunty Samirah, kuma aƙalla zata bani shekaru 6 a haife, dan zatayi shekaru 32 zuwa da 33.Ita ta basa shawarar yayi raped ɗina ai dole zan yarda da buƙatarsu idan ciki ya shiga.
Sai dai Allah ya kareni saboda naji shawaransu a daren jiya, shiyasa naƙi yarda nayi bacci, bayan na rufe ƙofar nabar key a jikin, kusan kwana suka yi suna zuwa ana taɓa kofar sai aji a rufe.
Da safe a shirye na fito tsab na guduwa, amma ban nuna masu ba naje kitchen na ɗore girki, ina tsakiyar aiki naji mutum ajikina.
Ba ƙaramin tsoro naji ba, kokowa muka fara da Hafiz Allah ya bani Sa'a na turesa ya faɗi wanda har kansa ya fashe.
Na samu na silala ta ƙofar baya na nufi gate, Allah ya temakeni har naje gate fice daga gidan ina tafiya ina waiwaye hankali Na a mugun tashe lokacin da na waiwaya na hangi motar Hafiz tana biye dani ganin motar ne ya sakani ruɗewar da har na shiga gaban motar ku.
Yanzu Mansoor nada shekara 4 da rasuwa yayin da a yanzu Nadrah nada shekara 6, har yau Ban sake ganinta ba ina jin babu daɗi, ina sonta ina kewarta amma babu yadda zanyi tunda su suka haifi mahaifinta, wannan shine tarihina..."
Ta ƙarasa mgnar tana sakin kuka marar sauti.
Iskar bakinsa ya furzar waje, yaja numfashi yana ɗago kansa ya zuba mata lumsassun fararen idanunsa na Seconds 5 ya ma rasa da wani baki zai ce mata koda Sorry ne taji sanyi a zuciyarta, saboda taga wahala cikin rayuwarta, yaga kuma jarumtarta, da har ta iya haƙuri da ƴarta tilo batada tabbacin zata sake wata haihuwar, duk da iyayen uban yarinyar sun fita ƙarfi wajan riƙon ƴar.

A hankali ya janye idanunsa daga kallonta bayan seconds 5 ta cika, yana maida kallonsa gun Fu'adh.
Sbd tsarin sa baya wa macen da ba muharamarsa ba, kallon da ya wuce na ɗan sakanni, sai dai idan ta gidansu ce, wato ƙanninsa shima idan ta maka dole ya kalla ne zai kalle ki.
Cikin nutsuwarsa murya mai taushi ya furta.
"Kije ki kwanta ki huta, Allah ya ƙara miki ƙarfin imani, zan ba Fu'adh saƙo ya baki"
A hankali ta amsa da
"Ameen ya Allah Nagode Yallaɓai. Amma don Allah ni dai temako ka barni nayi maku aiki na nemi halak ɗina, Wlh bana son komawa gida, saboda Allah ya sani maza basa gabana, bana buƙatar aure yanzun."

Ta ƙarasa mgnar tana miƙewa ta tafi.
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zuba wa Fu'adh, ba tare da yace masa uffan ba.
Fu'adh ya miƙe ya dawo kusansa ya zauna a Chair ɗin da take facing ɗinsa.
Fu'adh yace.
"Sir a gaskiya samun jaruma mai ƙananun shekarun da ba zasu wuce 28 ba, ta cinye dukkan jarabawar wannan tayi ƙoƙari sosai, samun irinta na wahala, sbd Abin duniya baya gabanta, ga kamun kai, nan tafi burgeni ma."

Yah Boss ya lumshe lumsassun fararen idanunsa yana ɗan jingina kansa da allon Chair ɗin.
A hankali ya furta
"Kuma babu ƙarya cikin dukkan maganarta, komai tsakaninta da Allah ta faɗa.
So babu dai matsala, but zan duba idan zan iya ɗaukanta aikin.
Ko kuma taje ta huta kusan mahaifiyarta ta daina yawon aikatau, ta kuma samu ƴancin ganin ƴarta, saboda idan ƴar ta girma uwar bata nemeta ba, toh akwai matsala babba, zata iya tsanarta ko rashin shaƙuwa ya hana ƴar kyautatawa mahaifiyarta.

Ina ma Juhainar mu take da wannan kyakkyawan halin"

Fu'adh yace.
"Sir! Wlh Juhainah macace mai ɗabi'un da babu namijin ƙwarai da zai sameta ya bari ta kuɓuce masa, kuma tana sake samun nutsuwa da hutu da jin daɗi kyawunta da kyan halinta zai sake fitowa."
Yah Boss da ya maida hankalinsa akan danna laptop a nutse ya furta.

"So Fu'adh, what do you mean by that? Or do you want to make her and Khairat two women?"

Fu'adh ya zaro kyawawan idanunsa yana faɗin.
"Don Allah Sir na tuba, a'a Wlh bana so Khairat ta isheni."
Yanzu da Juhainah ƙarama taji ai na Banu, haɗi zata je ta min da my love."
Kafaɗa Yah Boss ya ɗaga, cikin kama fuska sosai da Dattaku ƙasa² kamar an masa tilas ya furta.

"Toh barta tayi aikinta tunda Allah yasa ma bata son auren ta huta,
zamu dinga temakawa mahaifiyarta, so ita tayi aikinta kamar yadda ta buƙata, ta kuma nemi alfarma, a wannan rayuwar baka tilasta mutum, naso na temaka mata da jari mai yawa amma kamar ta fi son neman guminta, a barta, duk lokacin da ta gaji taji tana son yin auren sai ta koma garin su tayi aurenta Bass."

Fu'adh ba haka ya so ba, amma sai ya sake gwada sa'arsa yace.
"Nifa Sir ba haka naso ba, bari na fito maka a mutum, ina maka sha'awar Juhainar nan, saboda su Suhaima sun samu uwa Wlh ta gari, don Allah ka aureta ka ajiye maganarta a gefe na aiki..."
[05/01 13:35] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U
👆🏼
*😂Mutanen kirki ku dinga danna Followers mana, zan dinga Antayo maku tsofaffin littattafai Na, Kuna Shoshalewa Abinku.😂💃🏻🫣*

Page 10
Chapter 17 · 0% Book details