← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 113

Sashe 52

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙarasa maganar yana shiga gun blocking, ya duba babu number da take blocking sai ta Ammar da Zuby.
A hankali ya furta.
"Oh! My God! Yarinyar nan bataji Sam Sumayya! Wlh ƙarya take min babu wanda ya kira ta ya mata barazana, just dan ta wahalar dani ne, ta ba kanta wahalar, kalla abinda ta janyo kuma, wlh taci Sa'a yau kam da naɗa mata shegen duka, akan me zata dinga wa kanta irin wannan mugun fata Stupid.
Don Allah ke kuma ki goge hawayen ki, baza ku dai barni na huta ba, wlh zan bar maku ƙasa koda na sati ne har na samu nutsuwa, kowa yana ɗaga min hankali a yanzu"

Aunty Sumy tayi saurin goge hawayen tana kamo hannunsa ta marairaice fuska, a hankali tace.
"Please kayi haƙuri yaya Sadeeq, na daina amma Baby bataji me ya saka ta ɗaga maka hankali akan abinda ba haka ba? Kayi haƙuri da halinta babu yadda zamu yi da ita Yaya Sadeeq."

Bai ce mata uffan ba, sanin halinsa bazai ce ɗin ba, tana riƙe da hannunsa tace.
"Yaya Sadeeq naga matar taka ba laifi kamar zatayi nutsuwa da ganin darajar na gaba da ita, tana da kyau da kyan diri ba laifi, kayi haƙuri ka amsheta bamu san me ALLAH ya ɓoye ba, Please My Big brother"

Ƙin kallon Aunty Sumy yay, yana kame fuska sosai a hankali ya furta.

"Please stop it.
Ke kina goyon bayan ita ne Sumy?"
Da sauri Aunty Sumy ta sake riƙe hannunsa tace.
"No! Ita a su wa? Alright tunda baka so yaya Sadeeq, nima bana sonta ko gidan naka bazan koma ba, zan wuce gidana, daman Sadeeq yau can gidan Kakanninsa na barsa saboda yana damuna da rikici cikin mutane."
Kafe ta yay da lumsassun fararen kyawawan idanunsa, a hankali ya furta.
"Very good My sister love idan kika yi hakan shi ne kin nuna min ƙauna, ki barsu can su ƙarata"

Murmushi ta saki tana sakin hannunsa tace.
"My Big brother rigima Wlh, toh shi kenan an gama, natafi ko na jira Babyn Maah ta farka, naji Maah tana cewa zata riƙe su kwana biyu har baƙin amarya su tafi..."

Fuskarsa a kame ya furta.
"Ai Bilkisu na tare dani anan idan na tashi tare zamu je gida, ba maganar a riƙe su gida, a kanta zasu zauna ne?"

Aunty Sumy tace.
"Toh Allah ya huci zuciyar Babban Yaya, zan wuce gidansu Khabir na ɗauko Mai sunan ka mu wuce gida"
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa tsaye ta ɗauki handbag ɗinta.
Yah Boss a hankali ya furta.
"Ok ki wuce fa ki sani zan ganki idan kin koma, ki gaishe min da Ƴaƴana zan leƙasu na daɗe ban leƙo yaran ba"

Murmushi tayi tana faɗin.
"Tom zan faɗa masu Daddy ɗinsu zai leƙo kwanan nan bye"
Ta ƙarasa maganar tana nufar ƙofar fita.
A nuste ya miƙe yana zuba hannayensa cikin aljihunsa uniform ɗinsa.

Can gidan Maah ko Surayya da Hanifah suna bedroom ɗin Juhainah suna taɓa hira, Surayya da ta gaji da kwanciyar ta miƙe ta sauko Down Stairs, gun Maah, ta isko Papa sun iso, shi da Mustapha.
Har Umar and Nasir suna zaune anan parlour sunacin abinci ta sauko.
Ganin Mazan gidan sun baje saman Carpet suna lunch sai kunya, ta kamata.
A hankali ta ƙaraso ta rusuna tana gaishe da dasu, ta zauna ƙasa kusan Maah tana faɗin.
"Papa sannu da zuwa, anzo lafiya"
Papa cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin.
"Au Autatah tana gidan nan?"
MAAH tana murmushi tace.
"Anan suka kwana har yaran, amma yanzu ta tafi can gun yayanta wai ta lafta masa ƙarya yace ta sameshi police station"

Papa yana murmushi yace.
"Allah ka shirya min Aunty Bilkisu"

Mustapha yace.
"Yanzu can zai sameta ya naɗeta da kyau amma wani bai da wannan ikon, ai ina ganin ikon Allah!"
Umar ya bushe da dariya har yana ƙwarewa yace.
"Ko zamu biya don Allah muba idanun mu abinci?"
Nasir ya yagi tissus yana goge bakinsa da yake shi baisan hayaniya, a hankali ya furta.
"Hummm! Ni ai bazan taɓa manta marin da na sha ba akan kawai tana min dariya ba dalili na murɗa mata kunne, ta kafa kukan munafurci tace na naɗa mata kashi"

Mustapha yakai Cup ɗin ruwa bakinsa yana murmushi.
Maah tace.
"Yanzu saboda Allah gulmar Abbah kuke ko? Kun banu nayi recording, zan kunna masa."
Nasir yace.
"Don Allah Maah ki rufa mana asiri, su ƙarata sunfi kusa"
Papa yayi dariya yana faɗin.
"Ashe dai gulma ba daɗi kuka samu ƴaƴana kuna gulmarsu, Allah Sarki Autah ko wani hali ake ciki? Bari na kirasa naji"

Ya ƙarasa maganar yana ciro Wayarsa cikin aljihunsa ya danna number Yah Boss.
Lokacin yana tare baƙi har mutum biyu.
Amma ganin kiran Mahaifinsa ne, yay picking call kamar yadda ya saba ta Glass ɗin idanunsa.
Anutse a hankali ya furta.
"Assalamu alaikum Papa barka da zuwa ya gajiya?"

Papa yana murmushi ya amsa sallamar tare da faɗin.
"Alhamdoulillah! Abbanah, ya aiki? Yanzu nake namena Autah tah akace tayi maka ƙarya kace taje, don Allah a sassauta mata jikin ne babu ƙwari."
Yah Boss a hankali saboda mutane da suke zaune, cikin kamewarsa ya furta.
"Alright Papa in sha Allahu, Allah ya huta gajiya, zuwa dare zan shigo bangajiya"
Papa yace.
"Ok Abbanah Allah ya tsare min kai a duk inda kake, ya rufa maka asiri duniya da lahira"
A hankali Yah Boss ya amsa da.
"Allahumma Ameen Papana"

Papa ya katse kiran yana murmushi.
MAAH cikin jin daɗi take kallon Papa tace.
"Tana can ko?"
Papa yana murmushi yace.
"Eh mana Ai Autah bata ma san meye munafurci ba, idan tace ga inda zataje toh fa karkiyi shakku"

Surayya tace.
"Papa ƙarya fa da ta lafta masa wai wani ya kirata yana mata barazana da rayuwarta"

Mustapha yana murmushi yace.
"Itama wuyar da yake bata so take fa, Juhainah taurin kai."
Nasir ya miƙe yana zuba hannenysa cikin aljihun wandonsa kamar yadda Yah Boss yake anutse yana kallon iyayensa yace.
"Maah! Papa! zan isa gida Wlh nagaji Sosai"

Maah tana kallonsa idan yana komai kamar Yah Boss sak.
"Matarka na sama ka kirata sai ku tafi tare"
Da mamaki akan fuskarsa a hankali ya furta.
"Au bataje can gidan Yah Sadeeq ba?"

MAAH tace.
"Eh ta kama min aiki ne"
Daga haka ta maida hankalinta gun Mustapha da Umar tana faɗin.

"Kuma Mustapha ya kamata kuje ku ɗauki matanku."
Suka amsa da.
"TOH MAAH in sha Allahu"
Little Maah tana maƙale jikin mahaifinta tana masa gwarancinta, saboda batayi baki da wuri ba.

Nasir ya nufi upstairs.

Hanifah kwance bacci sama² ya fara ɗaukan ta.
Nasir kai tsaye bedroom ɗin Juhainah ya shigo.
A hankali ya ƙarasa bakin bed ɗin ya zauna yana duƙowa ya sumbaci idanunta da goshinta.
Tattausan hannunsa ya saka ya juyota ya tura kansa tsakiyar ƙirjinta, yana sumbatar gun tare da ƙamƙameta yana sauke ajiyar zuciya.
Allah ya sani yana masifar son Hanifah.
Kamar a mafarki taji ƙamshin Nasir yana rungume da ita.
Idanunta ta buɗe.
Da wani irin sauri ta ƙamƙameshi tana sakin kuka tare faɗin.
"I miss you I love you My husband please ka kasance dani ina sonka wallahi..."

Da sauri ya rufe bakinsa da nata, yana kissing ɗinta cikin salon da take shagala.
Kusan 2 minutes yana shan bakinta kafin tai saurin zare bakinta tana laɓewa cikin jikinsa.
Hawayen fuskarta ya goge mata, a hankali cikin zazzaƙar muryansa ya raɗa mata.
"My Hanifah wife me ya faru? Akwai damuwa ko?"
Da sauri ta girgiza kanta tana faɗin.
"A'a Wlh Babu komai, mafarki nake ashe kaine da gaske"
Kai ya girgiza yana faɗin.
"Ok me ya hanaki zuwa gidan Yah Sadeeq bayan matan yayuna suna can, harda Auntynmu Sumy ma?"
A hankali tace.
"Naga bai dace ba MAAH ita ɗaya nan, sai na tsaya"
Bakinta ya sumbata yana murmushi ya miƙe tsaye ya ɗauketa kamar Baby ya sauketa daga bed ɗin.
Yace.
"Ki shirya ina ƙasa kizo mutafi"
Ya ƙarasa maganar yana zuba hannenysa aljihunsa ya nufi ƙofar.
Da kallon Ƙauna ta bisa tanajin hawaye yana ƙoƙarin cika mata ido.
Bathroom ta nufa dan wanke fuskarta.


Yah Boss
Yana sallamar baƙinsa, ya gyara zamansa, wayar Juhainah a hannunsa.
Number da ta kira ɗazu ya kira.
Yana danna kiran ko ringing bata fara ba, yaji kukan Juhainah tana ƙwalla masa kira.
Miƙewa yayi, yanu room ɗin hutawar nasa.

Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya zuba mata, kwance take ƙasa saman Carpet tana buga kanta tana kuka tana kiransa.
Ta cire wular kanta tayi jifa da ita gashin ya barbaje, idanunta sunyi jajir alamar jinnun jikinta suna tare da ita.
Zuciyarsa zafi ta fara baisan me jinnun jikinta suke buƙata ba kuma.
Da sauri ya ɗauko sauran ruwan zam-zam mai addu'a da ya juye cikin bottle.
Da sassarfa ya ƙaraso yana duƙawa kusanta hankali ya furta.
"Juhainah! What's wrong with you?
Yanzu me kike ji ajikinki? Stop ki daina dukan kanki mana."
Ya ƙarasa maganar yana watsa mata ruwan addu'ar.
Jin muryansa a kusanta, da zafin ruwan addu'ar da suka ji, ai sai gata ta miƙe zaune kamar Baby mai koyan rararrafe haka ta fara ta iso gabansa ta faɗo masa tana kuka, ta kamo hannunsa ta ɗora tsakiyar kanta tana buga kanta da ƙirjinsa.
Ya ma rasa abinda yake masa daɗi.

Amma da yake namijin duniya ne ya sanya tattausan hannunsa ya riƙe kanta sosai yana faɗin.
"Bilkisu babu abinda zai sameki da izinin ALLAH zaki warke, waraka ta har abadan, babu wani abu da zai iya cutar dake cutarwa ta har abadan idan dai ina raye.
Nayi alƙawarin sai sun barki har abadan."
Ya ƙarasa maganar yana tofa mata addu'a a tsakiyar kanta, tare da fesa mata ruwan addu'ar acikin kunnenta...
[04/02 15:27] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 29*

Chapter 52 · 0% Book details