← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 113

Sashe 46

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaye take gaban madubi tana fesa turare tana faɗin.
"Kici gaba da dariya tunda bakida hankali, ki tashi muje muyi breakfast "
Sanye take da rigar atamfa baƙa mai adon Pink, doguwa cif ɗinkin dai-dai ƙaramin jikinta tayi kyau sosai saboda yadda ɗinkin ya fito da kyawun ƙirjinta, idan ka kalleta sai ka ƙara kallonta.
Gashinta ta ɗauresa tsakiya ta kameshi jelar har tsakiyar bayanta, sai raito take, gashin ya sha gyara sai ƙamshin turaren gashi mai tsada ke tashi akan nata.

Surayya tace.
"Tun yaushe, munyi breakfast Nida Aunty Hanifah, su Babies da Aunty Khairat ai sunyi 2 hours a school, ke kina bacci"
Juhainah ta ƙara fesa turare ta ajiye tana shafa lipstick tana taɓa goshinta gun dressing ɗin tace.
"Muje ki rakani toh"
Surayya tace.
"Wlh baccin nima zanyi, har yanzu Ban rama baccin jarabawar da muka gama ba. Don Allah my sister J ki temaka min na auri Yah Boss yayi ta biyu dani Wlh kullum ƙara sonsa nake"
Juhainah ta hararenta tana mele bakinta tace.
"Bakida hankali ni ba ruwa Wlh, kiyi kamun ƙafa da My Babies Suhaima zaki fi samun hakan gunta, na tafi nayi breakfast."
Ta ƙarasa maganar tana sa kai ta tafi tana takunta mai burgewa, sai dai fa an haɗa da karya ƙugun abin ya zama sabo.😂

Tana saukowa down stairs ta hango Maah tsaye can hanyar bedroom ɗinta tana waya, alamar wayan tana da mahimmanci sosai, sai dai kamar cikin fushi² take maganar a hankali.

Gun Maah Juhainah ta nufa.
Rungumota tayi ta baya tana faɗin.
"Good morning My Maah lovely"
Maah tace.
"Morning Babyn Maah kije kiyi breakfast har na gama wayar, ga wayarki can ajiye saman Kujera yayanki jiya ya bani na baki."

Da gudu ta nufi gun Chairs ɗin.
iPhone ɗinta ta ɗauka tana ihun farin ciki ta nufi dinning room ɗin.
Kujera taja ta zauna tana kunna wayan ta ajiye ta, ta haɗa tea mai kauri ta ajiye ta zuba fankasun alkama da miyar ganda tana wani irin ƙamshi.
Agaggauce ta dinga shan tea ɗin cikin mintina kaɗan ta shanye tea ta fara cin fankasun, ta ko zubasa dayawa, gandar ma yanka biyar manya ta saka.

A hankali taji ƙamshinsa na shiga hancinta.
Ta saka lomar fankasun bakinta tana waigowa.
Tsaf ta gansa cikin uniform ɗin da ta masa kyau.
Har bata san lokacin da ta furta.
"Wow! My brother, may God bless you, my brother, you are a great man."
Anutse ya ƙaraso dinning room ɗin.

Idanu suka haɗa lokacin da take ƙarasa maganar, tana tura ganda bakinta.
Tsaf yaji duk abinda ta faɗa.

Fuska ya kame yana sanya hannunsa ya kamo jelar gashinta yaja kaɗan, baiyi magana ba.
Ɗan ƙaran shagwaɓa ta saki tana shirin riƙe hannunsa, ya saki jelar gashin nata ya zagaya ya wuce.
Kujera yaja ya zauna cikin kamewarsa, ya ɗaukan Cup ya fara ƙoƙarin haɗa tea.
A hankali cikin kamewarsa anutse ya furta.

"What did you say?"

Dara-daran kyawawan idanunta ta kafa masa, uniform ɗin ta masa bala'in kyau.
Ƙoƙarin haɗe gandan bakinta take.
A hankali tace.
"Yah Sadeeq ina kwana? Ni bance komai ba fa"
Amsawa yayi a hankali ya furta.
"Idan kin haɗiye na bakinki ya isa haka, tunda baki san ciwon kanki ba, dole zakiyi ta rashin lafiya, ci dayawa bashi da wani anfani.
Bare ke da baya nuna hakan a jikinki, kuma kije ki nemi hula ki saka a kanki, tun ban ɓata ranki ba, masu lafiya ma ya suka ƙare kansu a buɗe"

Miƙewa tayi kamar zatayi kuka a hankali ta koma Kujeran kusansa ta zauna tana siɗe hannunta, kanta ƙasa.
Cup ɗin tea yakai bakinsa ya kurɓa da Bismillah, ya kalleta a hankali ya furta.

"Mi zan miki da kika dawo nan?"

Dara-daran kyawawan idanunta ta ɗago ta kallesa sai tayi ƙasa da kanta a hankali tace.
"Yah Sadeeq amarya tazo jiya?"
Tea ɗin ya sake kurɓa idanunsa akan wayarta a hankali ya furta.

"Ban sani ba ban kwana gidan ba nima"

Cikin farin ciki ta kallesa tana riƙe hannunsa mai Cup.
Kallonta yayi da sauri yana kame fuska sosai.
Idanunta ta lumshe taƙi sakin hannunsa.
A haka takai Cup ɗin bakinsa.
Anutse ya kurɓi tea ɗin ya haɗiye, ya sake kurɓa a karo na biyu, ya kafe ta da lumsassun idanunsa, na seconds 10 ya janye idanunsa.
Ta buɗe idanunta tana kallonsa tana murmushi sai ta karkato da cup ɗin ta nufi bakinta da shi, hannunta riƙe gam da nasa hannun, mai riƙe da Cup.

Bai hana hakan ba sanin tea ɗin babu zafin da zai cutar da ita.
Ya kafa mata Cup ɗin saman lallausan laɓɓanta masu kauri, ta lumshe dara-daran kyawawan idanunta tana kurɓar tea ɗin.
A hankali ya furta.
"Ki riƙe Cup ɗin ko na saki ya zube a jikinki"
Da sauri ta riƙe tana yiwa tea ɗin shan ruwa, tanajin ɗaɗinsa fiye da wanda ta haɗa wa kanta.
Plate ya ɗauka ya zuba fankasun guda biyu ya zuba ganda yanka guda da miya kaɗan ya fara ci.
Juhainah ta matso kamar zata shige cikin jikinsa ta ajiye cup ɗin ta saka hannunta cikin palet ɗin fankasun da yake ci, ta zare na hannunsa a hankali tana shirin kaiwa bakinta, har fankasun ya taɓa laɓɓanta tana shirin sakawa a harshenta.

Hannunta ya buge fankansun ya koma plate ɗin, ya watsa mata kallon da ya sakata miƙewa tun kafin ma yace ma ta tashi ya basa guri, tuntuni ta shiga hankalinta ta gudu tabar gurin, ko ta kan wayarta bata bi ba ta gudu, ta nufi gun Maah ɗinta...
Jikin Maah ta faɗa da take zaune a parlour har yanzu waya take.
Ta ƙamƙame Maah tana ɓoye fuskarta a ƙirjin Maah ɗin.

Yah Boss
Yana tsakiya da cin abincinsa Anutse, iphone ɗin Juhainah ta ɗauki ringing.
A hankali ya kafe Phone ɗin da lumsassun idanunsa.
Number babu suna cigaba yayi da cin abincinsa.
Tana katse wa aka sake kira, ta katse aka sake wani kiran.
Dogon farin hannunsa mai gargaza ya beka ya ɗauki wayan, yayi picking call ɗin ya saka wayan speaker ya ajiye yana cin abincinsa hankali kwance.
Zuby
Daga can inda take tsaye jikin window tana sanye da mini skirt, alamar kamar tana cikin maye kaɗan, dan har yanzu ita bata tafi ba, anan Ammar ya barta.
Murmushi Zuby tayi a hankali jin an ɗauki kiran yanzun.
A hankali tana canza murya kamar yadda take da baiwar canza murya a hankali tace.
"Ke ƙaramar ƴar iska Juhainah kike ko wa? daga yau ki rubuta ki ajiye ƙaddaraki zata fara...
[26/01 13:15] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVELS. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku

*DEDICATED TO*
*Aunty Sumy, (Sumayya Umar💕)*
*Congratulations Ƙawar Amana🫂*
*Allah ya Sauke ki Lafiya Yasa A Haifo Mana Twins Jigawa Tayi Manyan Baƙin Niger Haj Rahma Mrs Sulaiman Ɗan Baiwa.💃🫂😘*

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
Chapter 46 · 0% Book details