← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 113

Sashe 65

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zarah tana isa ƙofar parlour ta ƙwanƙwansa ƙofar.
Har sau uku shiru kawai sai ta kama handle ɗin ƙofar ta murɗa, ƙofar ta buɗe ta sanya kanta cikin parlour....
[12/02 12:53] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

Masoyen Juhainah Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kaɗan-Kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books ɗina, A Channel ɗin.
Wanda Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku.💃🏻

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 35*

Wani irin sanyi tare da ƙamshi ya daki hancinta, ta lumshe idanunta ta buɗe ta mayar da ƙofar ta rufe, ta fara takowa tana ƙarewa haɗaɗɗan parlour kallo.
Wayoyinsa da Fu'adh ya kawo masa ajiye akan Center Table, sai system ajiye da bottle ɗin water da Cups da ƙaramin Mug ɗin dafaffiyar madaran da suka zo da ita daga gidan Maah.
Duk ansha Cups biyu anyi anfani dasu, alamar yanzu aka sha.

Ajiye tray'n tai ta maida hankalinta akan ƙaton Frame ɗin da yake ɗauke da pictures ɗinsu.
Idanunta ta tsayar akan kyakkyawar fuskar Khadijah da take jikinsa a rungume tana dariya shi yana ƙaramin murmushi.
Yaran ta kalla suna rungume da iyayensu.
Wani yawu ta haɗiye tana kallon hanyar master bedroom ɗinsa.
Tana son zuwa tana jin tsoron dizgin da zai mata.
Zama tayi saman lafiyayyar Sofa tana kallon ƙofar bedroom ɗin, tana jiran fitowarsa.

Surayya
Farid yana parking a bakin gate ɗin gidansu ta kallesa tana ɗaukan ledar takalmin da ya kawo mata tace masa.
"Baby na shiga sai da safe Banida nutsuwa my Farid good night bye"

Ta ƙarasa maganar tana ɓalle murfin motar.
Farid yace.
"Please Baby Karki saka abinda ya miki a ranki, wlh ba dan yafi ƙarfina ba Allah sai na rama miki, toh shiga sabgar Soja ne babu daɗi basuda mutunci..."

Harara ta zabga masa tana Turo bakinta gaba tana faɗin.
Ahan Ok kana nufin kai matsoraci Ne Baby?kanajin tsoron namiji ɗan uwanka? Yaci bulus shaƙar da yayi min ya murɗe min lips? Shi kenan thank you Baby, karka sake zuwa anan kusa sai na huce kaima haushinka nakeji yanzu."

Ta ƙarasa maganar tana ficewa daga motar tana banko masa ƙofar.
Fitowa yayi yana kiranta ya biyota da ɗan gudunsa yana faɗin.
"Baby ki fahimceni don Allah tsaya kiji..."

Ko juyowa batayi ba, ta buɗe ƙaramin gate ta shige tana banko ƙofar.
Kansa ya dafe yana juyawa, gun motarsa saboda yasan bazata taɓa sauraronsa ba a yanzu.

Yana shirin shiga mota motar Jamal tana isowa bakin gate ɗin yana Horn.
Farid ganin Jamal ya tsaya dan gaishesa.
Jamal shgen kaya yana kallon Farid ya basar ya danna hancin motarsa cikin gidan da mai Gadi ya buɗe masa gate.
Farid ganin haka ya shige motarsa ya mata Rivas yabar bakin gate ɗin cike da haushin Jamal.

Surayya tana shiga parlour su da sallama duk rikice take, a hankali tace.
"Abba Mamy sannunku da gida"

"I don't need it"

Ta ƙarasa maganar da gudu ta nufi bedroom ɗinta.
Tana shiga ta cire kayan jikinta ta turaren Nasir ya addabi jikinta da hancinta.
Bathroom ta wuce ta sakarwa kanta shower ta ɗauki gel tana murje jikinta.

A can parlour kuwa Mamy tabita da kallo ganin ƴarta kamar a hargitse ta shigo idanunta jajir.
Ta kalli Abba tana faɗin.
"Abban Abdul Surayya kamar ba lafiya ba, idanunta jajir da kamar ma zabura take tana tafiya"
Abba yace.
"Miƙe kije kiji ko lafiya nima naga bata cikin nutsuwarta"

Mamy tana ƙoƙarin miƙewa Jamal ya shigo parlour da sallama fuskarsa a haɗe yana raba idanuwa neman Surayya.
A hankali ya furta.
"Mamy Surayya ta dawo yanzu ko?"
Mamy tace.
"Eh amma naga duk a hargitse take lafiya?"

Dai-dai Surayya ta fito parlour sanye da hijabi har ƙasa.
Jamal ya nufi gunta, tana ƙoƙarin guduwa Sbd ganin yanayin Jamal, amma ina jikin ba ƙwari Nasir ya nakasata.

Tana cirawa ya damƙota ya wanke da mari yana zaro mata manyan idanunsa yake tambayarta.
"Daga gidan uban kike keda wancan Yaron?"
Kuka fasa tana faɗin.
"Wallahi tallahi daga gidansu yayan Juhainah ya ɗauko Ni Wlh ban tsaya a ko ina ba na rantse maka da Allah"

Bakinta ya buge yana faɗin.
"Kimin shiru munafukar banza"
Mamy ta miƙe tana amshe ƴarta tana faɗin.
"Wlh bazaka kashe min Ƴa ba, da biyu kake narkarta Jamaluddin nasani Wlh, aure kam babu fashi nasan Surayya bazata taɓa tsayawa da wani a gun da bai dace ba"

Jamal idanunsa sunyi jawur ya juya ya nufi hanyar barin parlour.
Abba yace.
"Jamalu zo mana yaron kirki kayi haƙuri kaji"

A hankali ya furta.
"Wanka zanyi Abba zan dawo naci abinci"

Yana fita Abba yace.
"Surayya! Idan na sake ganin wani ya ɗaukoki daga wani gun ba mijinki ba wanda aka saka maku ranan aure wallahi da kaina zan maki dukan da yafi na Jamal"

Surayya ta jinjina kanta tana faɗin.
"Kayi haƙuri Abba wlh ni na roƙesa amma bazan ƙara ba"
Ta ƙarasa maganar tana kuka fuskarta duk tayi jan marin da Jamal ya mata, sai zafi.

Mamy ta kamata suka nufi kan dinning tana faɗin.
"Wannan idanun naki da suka faɗa akwai yunwa muje kici abinci, matsalar me yake damunki?"
Ta girgiza kanta tana faɗin.
"Babu komai Mamy kaina yake ciwo..."


Yah Boss
Anutse ya fito daga bathroom ɗaure ɗaure da faffaɗan towel a ƙugunsa, da ƙarami yana goge lafiyayyan jikinsa wanda yake ɗigar da ruwa, Sbd yawan gargasan jikinsa.
Ƙamshin shower gel yake tashi a jikinsa.

Anutse ya shafe lafiyayyan jikinsa da body lotions masu tsada da taushi da ƙamshi.
Ƙatuwar Wardrobe ɗinsa ya buɗe ɓangaren Lafiyayyun kayan baccinsa, ya ciro wasu Pajamas Set, brown light, ya saka anutse.
Ya ALLAH!
Wani irin fitinannan kyau suka masa, ya iso gaban ƙaton madubi ya ɗauki turare mai daɗin gaske ya fesa.
Anutse ya tako gaban drawer ɗinsa ya duƙa ya buɗe ya ciro wani kwali mai masifar kyau da hoton Sweet a jikin.
Buɗewa yay ya Ciro guda ɗaya ya maida ya ajiye ya ɓare ya jefa bakinsa.
Yana ɓare wa wani irin ƙamshi gun ya ɗauka, hakan zai sanar dakai ba ta ƙananun kuɗi bace, kuma yana daɗewa da ita a bakinsa yana ɗan tsosta slowly, ƙamshinta just ya isheka idan kana kusansa.

Abinda Khadijarsa take masifar ƙauna kenan, a gare shi.
A nutse ya nufi parlour dan yana son duba wasu saƙonni a System kafin ya kira Jamilu ya dafo masa tea yasha ya kwanta.


Nasir yana fita ya kira Maah a waya yana sanar da ita Juhainah tana lafiya lau, sai rigimar banza da take.
Maah dai murmushi tayi tana faɗa masa gobe zata dawo gida kawai yau hankalinta ne yaƙi kwanciya akan ƴarta, shiyasa ma koda ta kira Khairat tace komai lafiya bata gamsu ba ta kirasa yaje ya duba, amma yanzu hankalinta ya kwanta...

Lokacin da Nasir ya isa gida ya iske Hanifah tayi wanka ta sanye da kanya bacci tana parlour zaune.
Koda ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ta miƙe da gudu ta faɗa jikinsa tana rungumeshi.
Rungumeta yayi yana shafa mazauninta yana mata raɗa a kunnenta.
"My wife kinyi kewata?"

Murmushi tayi tana sake narkewa a jikinsa tana faɗin.
"Sannu da zuwa my husband, sosai nayi kewarka Masoyi. Amma ya naji kana wani irin ƙamshi ya gauraya da turaren ka?"

Nasir ya kame fuska sosai yana janye ta daga jikinsa, a hankali ya furta.
"Daga wajan mace nake Hanifah, ko ba haka kike son cewa ba?"

Idanunta ta zaro tana ƙanƙameshi tace.
"A'a wlh ba haka nake nufi ba, kayi haƙuri masoyi"
Hararenta yayi yana Kame fuska yake faɗin.
"Haka kike nufi mana Karki canza min magana, idan baki saka wani abun a ranki ba da shiru zakiyi"

Hannunsa ta kama suka zauna tana kwanto wa ajikinsa tana shafa ƙirjinsa tare da kyakkyawar fuskarsa ta sumbaci lips ɗinsa a hankali tace.
"Kayi haƙuri bazan ƙara ba i promise you my husband."
Uffan bai ce ba ya sumbaci goshinta a hankali ya furta.
"Dafo min black tea idan kina zargina zan baki mamaki kwanan nan, dan bana ɗaukan zargi Hanifah ki kiyaye Ni bana kallon mutum da mummunan aiki ko zargi amma idan kai ka min akwai damuwa Karki sake, Kinsan halina"

Jikinsa ta kwanto tana narke fuska tana faɗin.
"Kayi haƙuri baka fahimce Ni bane bazan ƙara ba"
Ta ƙarasa maganar tana riƙe kyakkyawar fuskarsa tafukan hannunta ta haɗe goshinsu tana zaro harshenta ta fara lashe lisp ɗinsa har ta Turo harshenta cikin bakinsa ta janyo harshensa tana sha a hankali.
Ta kamo hannunsa tana ɗorawa idan yake burge shi.
A hankali a ya fara shafawa ya kafe lumsassun idanunsa a kanta, ta lumahe idanunta tana sake kame bakin nasa....


Yah Boss
Anutse ya buɗe ƙofar parlour cikin rashin Sa'a suka haɗa ido.
Wani irin mugun kame fuska yayi yana janye idanunsa ya rufo ƙofar bedroom ɗin ya zuba hannayensa cikin aljihun pajamas ɗin jikinsa ya fara takowa Sbd bazai fasa uzurin shi dan ita ba.

Kallon sa take tana sakin murmushi.
Anutse ya zauna ko kallon arziƙi bata ishesa ba, ya buɗe laptop ɗin ya kunna.
A hankali ta matso kusanta tana danne zuciyarta Sbd wani irin masifar kwarjinin da ya mata.
Ga wani bala'in ƙamshi da yake wani ƙamshi na musamman daga bakinsa iskar Ac na aiko mata.
Yawu ta haɗiye.
Cup ta ɗauka ta tsiyaya masa rabin Cup ta matso har jikinsu na haɗuwa a hankali bata yarda ta kallesa ba tace.
"Mijina sugar kaɗan ko dayawa?"

Idan ya kalleta ko ya motsa ko yayi magana dutse zaiyi Magana.

Jikinta yayi sanyi ganin yaƙi cewa ta matsa daga kusansa ma taji daɗi.
Sugar kaɗan ta saka ta motsa ta jure ta kamo hannunsa ta ɗora Cup ɗin a hankali tace.
"Please kasha my baby Hajjah Mama tace na kawo maka"
Bai kalli ko ɗan yatsanta ba ya ajiye Cup ɗin akan table ya miƙe tsam tsaye yana ƙoƙarin nufar bedroom yaji an ƙwanƙwasa ƙofa.
A hankali ya furta.
"Yas come in"
Ya ƙarasa maganar yana nufar bedroom.
Chapter 65 · 0% Book details