Sashe 53
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da Nasir ya sauko down stairs, ba kowa parlour, Mustapha da Umar sun tafiyarsu.
Umar ya tafi da ƴarsa little Maah ta maƙale masa, Maah tace ai daman ɗan wani ya tafi da abinsa.
Papa kuma ya shiga dan yayi wanka Maah taje haɗa masa ruwan ɗumi.
Surayya ce kaɗai zaune tana kallon tashar Aljazeera, da MAAH take yawan kallo.
Ko da ya ƙaraso bai mata magana ba, asali ma bai kalleta ba, bare ya mata magana.
Saboda baida yawan magana, zama yayi akan lafiyayyar Turkish Chair yana danna wayansa, number MAAH ya kira.
Tana ɗauka anutse ya fara magana.
"MAAH! na sauko bakya parlour zamu wuce gida"
Daga can MAAH tace.
"Ina wani uzurin kuje kawai Allah ya huta gajiya"
A hankali ya amsa da.
"Ameen ya Allah Maah, sai zuwa gobe zan shigo"
MAAH da
"Toh"
Kawai ta amsa, ya katse kiran.
Surayya ta kallesa tana faɗin.
"Yah Nasir! Aunty Hanifah tayi bacci ne?"
Bai kalleta ba a hankali ya furta.
"Do you have a problem with her sleeping?"
Baki ta turo gaba tana ɗaukan remote tana canza channel.
A hankali tace.
"No! pardon me, brother Nasir."
Banza ya mata yana duba saƙon da yake shigowa wayarsa, akan zasu je Mission 20 ga watan April. Wato nan da kwana 21 kenan.
Idanunsa ya lumshe a hankali ya furta.
"Ya Rabbi! Wlh bana son tafiyar nan dole zata saka naje, akan aiki ba yadda na iya"
Ya ƙarasa maganar can ƙasan maƙoshi, yana kafe lumsassun idanunsa akan Hanifah da take takowa kamar ƙwai ya fashe mata a cikin cikinta.
Hanifah tana kallonsa ya miƙe yana faɗin.
"Muje"
Hanifah kamar zatayi kuka tace.
"Banyi sallama da MAAH ba"
Nasir anutse a hankali ya furta.
"Papa na nan bazaki ganta ba, maybe sai yayi wanka ta basa abinci ko zata fito, muje na faɗa mata a waya"
Kai ta ɗaga tana kallon Surayya tace.
"Surry mun tafi idan Autah tazo ki faɗa mata"
Surayya ta kalleta tace.
"TOH Aunty Hanifah a gaida gida"
Ta ƙarasa maganar tana kallon Nasir da har yayi gaba, yana takunsa a nuste, kana kallon sa kasan takunsa irin manyan matasan Soja ne masu jini ajiki.
Baki ta taɓe, shi sai jin kan tsiya, take faɗa acikin zuciyarta...
Jamal
Zaune yake yayi tagumi ya saka wayar a kunnensa yana jin duk abinda yake faruwa.
Kasancewar yayi picking call ɗin kuma Yah Boss ya taho da wayan a hannunsa, ya ajiyeta ƙasa saman Carpet lokacin da zai ɗauki ruwan addu'ar.
Hakan ya saka Jamal yake jin duk abinda yake faruwa.
Recording ya danna yana ɗaukan komai ko Allah yasa Mamy ta barsa ya huta da maganar Juhainah.
A hankali ya furta.
"Allah ya bata lafiya"
Ai Juhainah tun da aka fesa masa ruwan a kunnenta abun ya rikiɗe ta fara ihun neman temako, tana ƙoƙarin ƙwace kanta amma ta gaza.
Cikin roƙo aljanin yace.
"Zan fita ka barni haka, wai kai me yasa azzalumi ne? Baka da imani? Jikina ya fara ƙonewa, kayi wa Allah ka rabu dani naje nayi jinyar kaina"
Yah Boss cikin fushi ya furta.
"Ai in sha Allahu nayi alƙawarin sai naga bayan ka na ƙona ka baki ɗaya kabar duniya idan dai har baka fita ka shafa mata lafiya ba."
Cikin kukan azabar da yakeji yace.
"Toh ai ni bana son kowa ya sota sai Ni ku fasa mata auren zan rage kawo mata ziyara, kuma ɗazu naga anason sabauta mata lafiyar sansan jikinta ne a can gid....."
Wata irin azaba da yaji ya saka shi ficewa da gudun bala'i ta bakinta.
Ai Juhainah ta fara kelaya amai.
Yah Boss ya riƙe kanta tana aman saman Carpet baƙi ƙirin harda hayaƙi cikin aman da wasu ƙananun abu masu gashi².
Yana riƙe da kanta har ta gama tana maida numfashi.
A hankali ya furta.
"Bilkisu! Sannu kin gama?"
Kallonsa tai tana maida numfashi a hankali tace.
"My brother me nake anan? Me naci kalli aman nawa baƙi da wasu abu cikinsa me naci? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
Tausayi ta basa sosai ya zaro handkerchief ya goge mata goshinta da bakinta, ya miƙar da ita tsaye.
Ya bata bottle ɗin ruwan zam-zam ya furta.
"Oya sha kije bathroom ki wanke fuskarki"
Amsa tayi tana kafawa bakinta tasha sosai, ta beƙa masa a hankali take tafiya ta shiga bathroom ta rufe ƙofar, yanzu kam ta saku kamar batayi ciwo ba.
Ofishin sa ya koma yayi kira a waya.
Cikin minti goma aka gyara room kamar batayi aman ba.
Juhainah ko sai da ta ɗauki minti goma sha biyar a bathroom dan sai da ta cire kayanta ta watsa ruwa mai ɗumi saboda ciwon da jikinta yake mata, tana wanka taji ta dawo normal.
Yah Boss yana zaune ta fito.
Kanta tsaf ta kamasa ta saka hula ta fito cikin sanyin jiki tana raɓewa jikin bango.
Fuska ya kame a hankali ya furta.
"Bilkisu! come here"
A hankali kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki, ta fara takowa hawayen shagwaɓa ta fara masa, a hankali tace.
"My brother I'm sorry bazan ƙara ba, Allah nima bansan me ya saka na maka ƙarya ba, ka yafe ban ƙara wa"
Ta ƙarasa maganar tana zubewa ƙasa gaban ƙafafuwansa.
A hankali ya furta.
"Miƙe karki kuskura ki kama min ƙafafuwana, tashi ki zauna, kuma kar naga hawayen munafurci"
Miƙe wa tayi tsaye, taja kujera ta zauna, tana kallon sa.
Cup ya nuna mata cike da lafiayyan coffee, wanda shi kansa sai da ya karanta mata Ayatulƙursiyu ƙafa 7, ya tofa a cikinsa, ya zuba garin habbatul'sauda a ciki.
Da sauri ta ɗauka tana kafa bakinta.
Da sauri ya furta.
"Juhainah! Kiyi bismillah"
A hankali tace.
"Bismillahir rahmnir Raheem"
Ta ƙarasa faɗin tana kurɓa coffeen da yaji kayan haɗi. Bata san magani bane.😂
Lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya kafa mata yadda take shan coffeen tana tanɗe bakinta tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta.
Tana gama shan coffeen sauran kaɗan ciki, ya nuna mata plate a rufe.
A hankali ya furta.
"Ɗauka ki shiga room kici, sauran kiyi mugun ci kuma"
Cikin sauri ta miƙe Cup da ta sha coffeen a hannunta ta matso kusan Yah Boss tana marairaice fuskarta, amma taƙi yarda ta kalleshi, bata jure hakan.
Kallonta yay yana kame fuska a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"I don't want problem, mi ye kuma?"
Kallonsa tai tana saurin janye idanunta, ta gaza jure kallonsa, tai ƙasa da kanta ta sake matsowa kusansa kamar zata shige jikinsa, a hankali cike da shagwaɓa tace.
"My brother Habiby please kasha coffee ɗin na rage maka kaɗan yayi daɗi, amsa Please"
Ta ƙarasa maganar bata wani tsaya ba, bata kalli ƙwayar idanunsa ba bare ta gaza aiwatar da aikinta.
Cup ɗin ta manna masa a jajayen laɓɓansa ƙananu masu taushi,tana riƙe kansa a hankali kamar zatayi kuka tace.
"Please Yah Sadeeq kasha kaji, zanji daɗi sosai idan ka sha Allah"
Idanunsa mai cike da zara-zaran gashin ido, ya rufe rufff ya buɗe laɓɓansa tana juye masa sauran coffee ɗin da ta rage ɗan guntu.
Anutse ya haɗiye.
Ta zare Cup ɗin daga bakinsa tana farin ciki, takai Cup ɗin bakinta ganin idanunsa a lumshe.
Sauran ta kurɓe dai-dai saitin bakinsa tana jin ɗanɗanon yafi daɗi yanzu.
Ajiye Cup ɗin tai ta ɗauki haɗaɗɗen plate ɗin mai abinci ta nufi room ɗin.
Wayanta da take hannunsa a nutse yana zuba ƙafafuwansa akan ƙaton Table ɗin gabansa, ya jingina bayansa da allon lafiyayyar kujerasa, ya dannawa number ɗazu kira.
Jamal lokacin yana driving yaga kiran ya shigo.
Da ɗan sauti ya furta.
"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil, wannan masifar fa ina dalilinta? Haba! An hanani sukuni, an hanani jin daɗi."
Ya ƙarasa maganar yana picking call ɗin yaƙi Magana.
Yah Boss a nutse ya furta.
"Assalamu alaikum, waye me wannan number?"
Jamal jin Yah Boss ne ya amsa sallamar anutse tare da gaishesa cikin girmamawa, yana faɗin.
"Jamal ne my brother"
Yah Boss anutse cikin kamewarsa ya furta.
"Jamal! Na kira ka ɗazu bamu samu munyi magana ba, Juhainah ciwonta ya tashi, amma yanzu Alhamdoulillah! Tana normal, kabani two minutes zan baka ita."
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran, ba tare da ya tsaya yaji me Jamal zai faɗa ba.
Jamal kuwa wayan ya ciro daga kunnensa yana ƙara gudun motar, a hankali yana faɗin.
"Darajar Mamy dakai zan aureta saboda kasan darajar ɗan Adam"
Juhainah ta baje tana kwasar girkin da ya mata daɗi sosai.
A nutse ya shigo room ɗin, yana kafa mata lumsassun fararen kyawawan idanunsa.
Ta ɗago kanta ta zuba masa dara-daran kyawawan idanunta tana tura spoon ɗin bakinta, kamar zatayi kuka a hankali tana ƙasa da kanta tace.
"Yah Sadeeq ban ƙoshi ba, zan ƙara Please"
Yana maida hankalinsa akan wayar hannunsa a hankali ya furta.
"Na maki magana ne?"
Kai ta girgiza, tana maida hankalinta gun cin abincin.
A hankali ya furta.
"Ki sameni idan kin gama"
Da sauri tace.
"Toh Yah Sadeeq zakaci abincin na rage..."
Kallon da ya mata ne ya sakata haɗiye sauran maganar tana cin abincinta.
Yana zama baifi minti biyu ba ta fito da plate ɗin ta cinye duka abincin.
Ta nufi fridge ta buɗe ta ɗauki bottle ɗin water, ya dakatar da ita.
"Ki maida ki zo ga ruwa nan"
Ba yadda ta iya ta maida tazo kusansa ta tsaya tana kama kujeran da yake zaune.
Bottle ɗin mai ɗauke da addu'a da ya mata ya beƙa mata.
Ta amsa ta koma ta zauna tayi bismillah kamar yadda yace tayi, ta sha.
Tana idarwa, ba tare da ya kalla ba, ya kira number Jamal.
A hankali ya furta.
"Jamal zai miki magana ki nutsu banson rashin kunya, da shirmenki nan"
Kallonsa tayi tana marairaice fuskarta kamar zata yi kuka a hankali tace.
"Yah Sadeeq ni bana sonsa irinka nake so, Ni mutum idan baya da yanayin ka bazan taɓa son shi ba don Allah Yah...."
Bai ma san ya aka yi ya iso gun ta yana ɗora tattausan tafin hannunsa akan laɓɓanta masu kauri.
Ya murɗa mata kunnenta sai da tayi ƙara tana riƙe hannunsa tana ƙoƙarin faɗawa jikinsa, ya matsa da sauri yana kai wayar kunnensa har lokacin ringing take.