← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 113

Sashe 71

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nutsuwarta da harshen Ingilishi tace.
"My friend sai kazo dai hira tafi ƙarfin waya, kuma idan kazo fa sai munje naga amaryar Mu"

Nasir a hankali ya furta.
"Bakinki ne amaryar ai, shekara biyu da Allah ya kawo rabo da ɗanki ko ƴarki tana koyan tafiya zakici amarya"

Murmushi tayi mai class tana faɗin.
"Allah amarce tunda bata haihu ba, Allah ya kawo masu albarka, bye sai goben ko?"

A hankali ya furta.
"Yeah bye ki ajiye min tsarabata ta da matata"

Hairat tace.
"Ok alright bakada Case"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran.

Nasir ya ɗan lumshe lumsassun idanunsa na seconds 2 ya buɗe yana cigaba da driving, bai son Surutu dayawa amma Hairat sai ta saka shi, ba yadda ya iya, yana ganin darajarta baya iya share ta Sbd kirkinta, da yadda take darajanta duk wani wanda yake tare da shi, haka Mahaifinta shine silar samun duk muƙaminsa a Soja.

Nahe ganin mota na nufosa duk da mai motar wucewa zaiyi shima ya wuce, amma hankalinsa yaƙi kwanciya ya dinga waiwayan Surayya ganin kanta ya zuro yana kallon waje kuma saitin inda motar zata wuce.

Nasir anutse yake driving ɗinsa, kamar Ance ya kalli me keke napep ɗin.
Ya ɗago lumsassun idanunsa ya kalli gun.
Akan fuskarsa Surayya ya sauke idanunsa, mayafin abayar kanta ya kwance ya sauka saman wuyanta kitson bikin da aka mata jelar ya sauka kafaɗarta.
Kallon mai keke napep ɗin yayi ya gansa a rikice ganin soja ne mai motar har yana sakin hanya.

Nasir ya taka Burki da ƙarfi ya fara ƙoƙarin shan gabansa, Sbd haka kawai bai yarda da mutumin ba, ga Surayya alamar ma bata hayyacinta idanunta a rufe, bayan haka ma me zai kawo ta hanyar jejin wannan mai haɗari.

Nahe ganin Nasir zai tona masa asiri ya ƙara gudu, cikin mugun tsoro ya karkatar da keke napep Surayya ta faɗi ƙasa, wanda sauran kaɗan Nasir ya take ta ya kauce, yana taka Burki da ƙarfi, Allah yasa cikin rairaine da sai taji ciwo.
Da wani irin sauri Nasir ya furta.
"Nine zan kamaka da hannuna da izinin ALLAH, ba dai wannan hanyar kake bi da mata ba"

Fitowa yayi ya nufi gunta tana yashe acikin ƙasa, jakarta ta makaranta tana rataye a wuyanta alamar shine yayi mata hakan.

Duƙowa yayi gabanta yana kiranta.
"Ke! Surayya! Surayya!!"
Shiru
Hannunta ya kamo ya matsa yaji shiru.
Guiwowinsa ya ajiye kasa ya ranƙwafo ya duƙo da kansa yaji shiru alamar ta suma.
Kafaɗunta ya kamo da hannayensa ya ɗagota ya girgizata a hankali ya kirata.
"Surayya!"

Miƙewa yayi ya cicciɓeta sama, ya ɗauketa tunda larura ne, babu muharaminta a gun.
Motarsa ya nufa da ita.
Gaban ya kwantar da kujara ya kwantar da ita, ya shiga ya zauna, ya rufe motar ya mata key yaja yabar gurin.
Inda Allah ya rufa asiri ma jefota da yayi bataji ciwo ba, bai sani ma kuma ko cikin jikinta.
Gudu yayi sai da ya hau kan titi ya samu guri can gefen titi yayi parking, yana parking Wayarta na ɗaukan ringing, a jakarta.

Bai ɗauka ya ɗauki gorar ruwa ya buɗe ya ya zuba mata a fuskarta zuwa ƙirjinta, cikin ikon Allah daidai duk inda ruwan da Nahe ya watsa mata ne ruwan ya sameta, daman makarinsa ruwan maganin daga an zuba maka ruwa idan dai yanada sanyi ko yayane a take zaka farfaɗo daga suman.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana fasa ihu, tana kiran Mamy tare da ƙoƙarin buɗe idanunta da suka mata mugun nauyi.
"Wayyo Yaya Jamal ka temaki Mamy Yaya Abdul! Yaya Nazifi Wayyo Aunty Wasila zasu yanke min..."

Nasir da sauri ya riƙeta yana faɗin.
"Ke! Dalla kiyiwa mutane shiru uban waye ya aike ki fitowa yawon da Maghreb?"

Jin muryan Nasir ta ɗan dawo hayyacinta tana bude kyawawan idanunta tana tabbatar shi ne ta faɗa ƙirjinsa ta ƙamƙameshi sosai tana sakin kuka tare da faɗin.
"Don Allah Yah Nasir ka ɓoye Ni ka ceceni kar ka bari su cutar dani, Wlh wani ruwa ya watsa min ban ƙara sanin inda nake ba, ba daga yawo nake ba daka school na biya gidan Aunty Wasila"

Ta ƙarasa maganar tana kuka sosai jikinta rawa yake tsakaninta da ALLAH a mugun tsorace take.

Nasir ganin gaba ɗaya bata hayyacinta, ta shaƙesa sosai ta gagara tsayawa gu ɗaya a jikin nasa.
A hankali ya furta.
"Ok naji ai daman na temakeki sakeni ki zauna babu wanda zai taɓaki yanzu, buɗe idanun ki kiga kina cikin mota na ne"

A hankali ta fara buɗe kyawawan idanunta ta kalli motar ta kallesa tai saurin ƙasa da kanta, ta janye jikinta daga nasa ta zauna akan kujara tana goge hawayen.
Ɗan kwalinta ya beƙa mata ya furta.
"Amsa ki yafa, babu inda kikaji ciwo a jikinki?"

Kai ta ɗaga masa tana yafa mayafin.
Motar ya tayar yana faɗin.
"Gobe sai ki sake zuwa yawon daga school ɗin, tunda bakuda hankali Ance maku kowa ake hawa keke napep ɗinsa, ai daman ya tafi dake ɗin ya koya maki hankali fitsarariya, ashe ma muguwar matsoraciya ce"

Kallonsa tai tana musmus da baiknta, tana son maida masa martani, amma tuna azabar da ya mata Shekaran jiya dole ta maida rashin kunyar, barinsa zatayi sai ta sauka daga motar ta rama maganganun da ya yaɓa mata.

Anutse yake driving ɗinsa.

Wayarta ta sake ringing.

Ta buɗe jakarta ta ciro wayan.
Ganin Mamy ce ta ɗaga kiran tana kai wayan kunnenta tana faɗin.
"Mamy keke napep ɗin dana hau ya lalace ganinan na kusa isa gida, babu abinda ya sameni"

Mamy ta sauke ajiyar zuciya tace.
"TOH shi kenan Allah ya kawo ki lafiya"

Surayya ta amsa da.
"Ameen Mamy..."

Yah Boss
Ana idar da sallar Maghreb bayan yayi azkhar ya dawo kasancewar yabar Juhainah.
Lokacin da ya shigo tana room ɗin da yake hutawa zaune akan darduma.

Yana zama Fu'adh yana shigowa.
Yah Boss ya kallesa yana amsa Sallamar.
Zama yayi yana faɗin.
"Washhh! Allah! Yau na bugu, wa ya kawo abincin Sir?"
Yah Boss baice masa uffan ba, yana duba saƙon da ya shigo cikin wayansa.
Fu'adh yace.
"Sir gobe Alhamis Kanada ganawa da Alhaji Nuhu, akan maganar zuba hannun jari a Company ka na buga Boots. Ban san me yasa ya nace Wlh."

Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya ɗauki plate ya fara zuba abincin.

Yah Boss ya gyara zamansa yana kallon Fu'adh fuska kame cikin nutsuwarsa ya furta.
"Kace masa bazan samu ganawa da shi ba gobe, kuma bana haɗa hannun jari da kowa ma ba shi ba, akan wannan Company na buga Boots, su basa buƙatar duk wani abu da zai zama kayi shi Quality ka siyar da sauƙi kowa ya samu, a'a so suke na dinga narka kuɗi kamar dai yadda ake kawosu daga waje, No bana ra'ayin hakan."

Fu'ada yana cin abincin yace.
"Ga shi baida zuciya komai zaka faɗa masa zai shanye, mutum kamar maye..."

Juhainah ce ta fito tana washe baki tana faɗin.
"Yah Fu'adh! Ina wuni? Kaima yunwar kakeji ko?"
Ta ƙarasa maganar tana zama.

Fu'adh cike da mamaki ya kalleta ya kalli Yah Boss da hankalinsa yake akan laptop ɗin da yake dannawa fuska kame.
Fu'adh yace.
"Toh fa sabuwar shaƙuwa amarya ce anan?"

Kai ta ɗaga tana kallon Yah Boss da ya ɗago kansa fuska kame ya kafe lumsassun fararen kyawawan idanunsa a kanta, yana mata gargaɗin idan ta furta wani abun zata sani.
Kwaɓe fuska tayi tana ƙasa da kanta tace.
"Eh abincinku na kawo maku"

Fu'adh ya ƙyalƙyale da dariya yana faɗin.
"Gsky mun gode sosai Mrs Jamal, ya shirye² bikin? Wani mawaƙin kika gayyato mana? Nasan ƙanwata da son casu."
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Nifa ba auren so..."
Tsawa Yah Boss ya daka mata yana faɗin.
"Kema haukan zakiyi irin na Fu'ada kuna ihu dariya mai yawa na rage imani."

Haɗiye maganar tayi tana faɗin.
"Allah baka haƙuri my brother Habiby"

Fu'adh ya ƙara kwashe wa da dariya yana ɗaukan plate ɗinsa ya nufi ƙofar fita daga ofishin, dan yana tsoron Yah Boss ya jefe shi da wani abun, dan Wlh dole sai yayi dariya, tunda yaga abinda dariya.
Yah Boss yabi Fu'ada da ido yana furta.
"Kaje ka ɗauki magani Fu'ada ƙwaƙwalwanka baya saiti"

Fu'adh yana dariya yace.
"Nagode Sir ya za'ayi tayi saiti Sbd ALLAH, yarinyar nan fa idan kun haɗu sai kun sakani dariya"

Juhainah ta miƙe da sauri zata bi Fu'ada da wata irin murya ya furta.
"Ɗauki handbag ɗinki mu tafi, sai na fasa maki baki Wlh idan baki nutsu ba"

Handbag ɗinta ta ɗauka ta isowa gabansa kamar zatayi kuka tace.
"Kayi haƙuri bazan ƙaraba, ai ban faɗa masa komai ba, kuma bazan faɗa ba kaji Habiby"
Bai kalleta ba yayi gaba.
Da gudu tasha gabansa tana riƙe hannunsa kamar zatayi kuka tace.
"Kayi haƙuri Yah Sadeeq bazan sake ba kaji?"

Bai ce komai ba yaja hannunta suka nufi ƙofa.
Fu'ada yana ganinsu ya haɗiye dariyarsa yana faɗin.
"Amarsu sai gida ko?"
Ƙin magana tayi ta ɗaga kanta dan ma kar ta ɓata masa rai.
Walid ne ya tuƙasu suna baya zaune yayin da Fu'ada ya tsaya gyara takardun da suke kan table ya kashe laptop ya maida komai gunsa ya ɗauki basket ɗin ya rufe masa ofishin ya fito sukayi sallama da sakataren sa ya tafi.

Yah Boss ko kallonta bai ba cikin motar.
Kallonsa take tayi shiru ta matso kusansa batace komai ba, tasan haushin sakin zancen da taso tayiwa Fu'ada yake ji.

Hannunsa ta kamo a hankali cikin yanayin shagwaɓa tace.
"My brother Habiby nayi alƙawarin ba wanda zan sake yi..."
Bakin ya buge yana watsa mata kallon ki shiga hankalin ki.

Hawaye ta fara tana kallon Walid da yake driving sam ta manta.
Ƙoƙarin kwanciya jikinsa take ya riƙe ta a hankali kusan kunnenta ya furta.
"Juhainah Please ki nutsu zan bar miki garin a yau, tunda duka baya maki, ina alƙawarin da kika min?"

Ƙaramin kukan da yake cinta ta saki yayi saurin rufe mata bakin yana mata wani Irin kallo, na kashedi ya saki bakinta.
Haɗiye kukan tai.
Idanunta ta rufe tana matsawa ta manne da kujara ta ɗan nustu, ganin bada wasa yake mata ba, kar yakai mata mari.
Chapter 71 · 0% Book details