Sashe 9
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Maah tayi murmushi tace."Ko suna nan idan dai ba Twins suka zo na Mustapha ko na Sumayya ba, Al'amin ya samu sake kasan dai Suhaima ba surutu take ba, kowa sai taso take kallonsa bare wani dogon zance." Ta faɗa tana yar dariya. Ƙamshinta da takun takalminta mai ɗan tsini kaɗan sukaji, ƙwas-ƙwas, duk da tana ɗingisa ƙafar amma tafiyar tata akwai ɗaukan hankali. Dukkansu suka ɗago suka zuba mata idanuwa, amman Banda Yah Boss. Juhainah ganin Umar da Maah ya saka rauninta ya dawo idanunta na ƙoƙarin kawo ruwa, Maah da Umar a tare suka girgiza mata kai, suna ɗauke idanunsu daga kanta. Kanta ta sadda itama sbd idan tana kallonsu kuka zata fashe da shi. A hankali take takowa kusan Yah Boss ta ƙaraso ba tare da ta cire tatakalman ba, zama tayi ƙasa saman lallausan Carpet kusan ƙafafuwansa, muryanta na rawa cikin zazzaƙar muryanta tace. "Yah Boss..." Tai saurin buge bakinta jikinta na ƙoƙarin ɗaukan rawa, tana haɗa kalaman da zata faɗa tace. "My brother gani" Ta ƙarasa mgnar tana lumshe idanunta Saboda hawayen da suke ƙoƙarin fitowa daga idanunta. Umar tausayi ta basa ganin gefen bakin a kumbure fuskarta tayi Ja ga tana son yin kuka babu halin yin hakan. Fu'adh ma ta basa tausayi sosai. Maah tace. "Don Allah Abbah karka sassauta mata, har ga Allah bansan ciwon ƙarya tamin ba dan kar tafi makaranta, bayan suna jarabawa, sai kalamanta da suka fi ɗaga min hankali wai aure take so bata son karatu auren ma bata son yaro sai tsofo..." Juhainah ta buɗe manyan idanunta tana fashewa da kuka tace. "Allah Maah ba ina nuf..." Sake kaiwa bakin nata bugu yayi tare da sakar mata wani marin da ya sakata haɗiye maganan da zata yi ta haɗe kai da guiwa tana hawaye dan bata isa taci gaba da kukan da ta fara ba. Kowa shiru yayi a wajan, duk suka maida idanunsu akan Tv. Miƙewa ya yi tsaye yana maida hularsa akansa, ya kalli Maah cikin nutsuwarsa murya mai taushi ya furta. "Maah wajan aiki zan wuce, zuwa dare ko zan leƙo babu tabbas right, ke! Tashi wuce muje." Ya ƙarasa mgnar yana fara tafiya. Maah tana murmushi tace. "Ok Abbah a sauka lafiya Allah ya bada sa'a, ai yau kam nasan ma bazaka dawo ba Kanada baƙuwa a gidanka." Baice uffan ba, bai kuma juyo ba yasa kai. Jikinta na ɗaukan wani irin zafi ta miƙe tana share hawaye daƙyar take iya tafiyar yanzun, sbd zaman da tayi a takure, ga marin da ya ƙara mata da ƙarasa fashe mata bakin. Bata tsaya kallon kowa ba tabi bayansa tana sauri jiri ma take jin na ɗaukanta saboda yunwa, ga azaba haka ta jure tana bin bayansa. Fu'adh ya ɗauki mug yana ƴar dariya yace. "Maah! Wlh ina shan dariya wannan ya'ya naki, Autah idan babu Sir lamarinta sai gyaran Allah, amma har ga Allah yau ta daku kamar sakwara." Fu'adh yayi maganar cikin raha, kamar Maah ba surukarsa bace. Maah tayi murmushi tace. "Batajin magana Sam Wlh Fu'adh, dan bakaji kalamanta bane ai Wlh kaɗan ma ya mata, ba aure ba take so, ta samu nasani kudirin sa kenan akanta, banga anfanin zamanta gidan ba tunda bata son karatu, muna tausaya wa ƙananun shekarunta, da ƙaramin jikinta amma ita bata tausayn kanta." Fu'adh ya girgiza kai yana binsu dan har sun fice daga parlon, wayansa ya ciro daga aljihunsa yana danna number Jamilu Kuku. Tana fara Ringing ya ɗaga.Fu'adh yace. "Jamilu! Ya jikin naka?" Jamilu ya amsa da "Alhamdoulillah! Uban gidana, yanzu banajin komai har na fara gyaran kayan Lunch, za'a dafawa Oga Madara ne ko an dafa masa can gida?" Fu'adh da yake ficewa daga falon yace. "Ma sha Allah, Ubangiji ya ƙara sauƙi, a'a karka dafa an dafa masa, idan ka gama girkin dai ka zabu za'azo a ɗauka, za'a kai asibiti mun buge wata mata amma da sauƙi ba damuwa dayawa." Jamilu yace"Subhanallahi Allah ya kiyaye gaba, Ok in sha Allahu. "Fu'adh ya amsa da."Ameen ya Allah, Ok thank you Jamil."Ya ƙarasa mgnar yana katse kiran ya nufi compound ɗin gidan. Umar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin. "Maah ki lallashesa nasan ke ɗaya ne zaki iya hanasa, wannan mahaukaciyar ɗiyar taki waye zai aureta a yanzu da rashin jintan nan, bayan haka ma tayi ƙarama sosai saboda rashin jikinta, da tanada babban ƙashi ba za'aga ƙanƙantar shekarunta ba, don Allah keda Papa ki dakatar da shi Wlh auren zaiyi mata fa..." Maah ƙirjinta sai bugun tara yake hankalinta nason ya tashi amma kuma sam bazata iya nuna damuwarta akan hukuncin ba, tunda babban yayanta ne kuma ko bayan ransu shine ubanta. Murmushi ta saki na dattaku tana faɗin. "Kayya! Umar! Juhainah fa idan babu Abbah akwai matsala, saboda ku kamar ma tsoronta kuke ji, ku bari kawai yayi abinda ya dace shine babba, kuma Nasan ƙaunar da yake mata wallahi baya yi yawa kowa ita, kawai halinta ne yake saka masa ciwon kai, yake rufe idanunsa yana bata hukunci sbd karta lalace a dawo ana da nasani." A hankali yace."Haka ne Maah amma dan Allah ko auren za'a yi mata mijin ya tsaya mata tayi karatu koda iya jami'ar ne."Maah ta kai masa dukan wasa irin na Ɗa da mahaifi tana murmushi tace. "Ka rainani Umar! Ni ne zan zaɓa mata mijin bare kamin wannan mgna, ka tashi katafi gun yayanku ka faɗa masa, kaga idan bai sauke maka marin da yafi wanda Autah ta sha ba." Ƴar dariya yayi yana miƙewa yace."Maah zan wuce gun aiki, sai na dawo." Addu'ar sauka lafiya tai masa tana miƙewa zuwa kitchen gun masu aiki dan bada umarnin abinda za'a dafa da rana, tunda kam Yah Boss ya hanata girki, saboda takai lokacin da zata huta sosai. Suna isa gun mota bayan a buɗe masa ya zauna, yana latsa wayansa. Juhainah jikinta ya fara rawa tana raba idanunta ta rasa ina zata shiga ta zauna, front seat ko wajan Yah Boss?Muryan Fu'adh taji yana faɗin. "Juhainah! Ki shiga mana ki zauna." Ya ƙarasa faɗin yana zama front seat kusan Walid. Tana ganin hakan tasan dole kusan Yah Boss zata zauna. Addu'ar da take tayi tun ɗazu ita ta fara karantawa, ta siɗaɗa ta shiga motar ta zauna tana rufo ƙofar gudun kar taji saukan wani marin. Jikinta ta haɗe gam gu ɗaya, tanajin yadda ƙamshinsa yake neman toshe mata kofofin hanci, ga sanyin Ac da ƙamshin turaren motar. A hankali Walid yaja motar ya nufi gate. Har motar ta hau kan titi Juhainah bata yarda ta motsa daga zaman da tayi ba, tsoron kar tayi ƙwaƙwaran motsi ta taɓa jikinsa taci wani dukan. Kanta ƙasa tana wasa da Zara-zaran yatsun hannunta, da take jin takaicin cire mata false nails ɗinta da yayi. Gabanta ya faɗi tuno wayarta ta barota a gida yashe akan Carpet da ta saki saboda ruɗewa. Kamar a mafarki taji Ringing ɗin wayarta song ɗin ya fara tashi na wakar Tum Se Tum Tak. Da sauri ta dago rinannun idanunta a hankali ta waigo ta kalli gefen nasa. Ko kallon gefen da take baiyi ba kamar yadda bai ko kalli wayan da take cikin aljihun gaban rigarsa ba. Kanta ta sauke ƙasa tana lumshe idanunta, acikin zuciyarta take faɗin. "I hate you Yah Boss." Kira uku akayi ajera babu ƙaƙƙautawa, bai ko kalli wayan ba, jin satin waƙar ya saka shi yarda tabbas Juhainah soyayya take yi kuma take so a rayuwarta, wanda idan yayi wasa zata lalace masu baki ɗaya. Saboda tayi ƙarantar da zata saka love a gaba har haka, so mugune idan ya bari soyayyar wani tai mata nisa, aka samu akasi bata dace da mai kamun kai ba komi ma zai iya faruwa. Kira na biyar ne ya shigo wayanta, hakan ya saka shi ciro wayan yana zuba idanunsa duka akan screen ɗin wayan. *My bab love* Shi ne sunan da yake yawo akan screen ɗin wayan, hakan ya saka shi yin picking Call ɗin yakai wayan kunnensa ba tare da yayi magana ba, yana ɗan lumshe idanunsa masu tasiri a jikin duk wanda ya kalla.... [30/12/2025 15:17] null: _*JUHAINAH*_