Sashe 107
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hanifah tace.
"A'a fa Umma muje kawai idan mun biya wlh zata zarge mu, yo ko mun haukata yarinyar saninta sukayi, wuce mu tafi.
Surayya fa taci kai, shekaran jiya ma gun auren Khairat, naga tana wani zaro idanunta tana laɓe² kamar yanzu tsoron mutane take wuce mu tafiyar mu."
Ummah tayi dariya tace.
"Yo ke Hanifah a ƙawayen Juhainah kika ga za'a samu mai hankali, duk irinta ne, bakiga kwana ɗaya da aurenta ba miji ya banka mata ciki ya sakota, ALLAH yasa ma cikinsa ne."
Hanifah tayi dariya tana tsayar masu da keke napep tace.
"Ummah mu biya ta gidana, na zuba miki farfesun Kifi ki kawai Babana yana sonsa sosai..."
Keke napep ɗin suka hau suka faɗa masa inda zai kai su.
★
A dai-dai wannan lokacin kuma Juhainah tana zaune a parlour, zuwanta kenan daga school tagaji, su Suhaima sun rigayeta isowa.
MAAH zaune gefe suna waya Haj Lubnah.
Su Suhaima ita da Al'amin suna zaune Tv suke kallo Mbc 3.
Dijeh tana ninniƙe da Juhainah tana bata labarin abinda aka koya masu yau a makaranta.
Sauran Orange ɗinta da Yah Boss ya siya mata, sauran guda 3 ta yanka tana sha.
Fuskarta ta yamutsa ta kalli Dijeh tace.
"Dijeh ALLAH yau bana son yawon magana kije gun Suhaima kuyi kallo, amsa orange ki sha. Babies kuzo kuma ku amsa"
Suhaima tace.
"A'a My Aunt bana sha. In ƙaro miki ne?"
Juhainah tace.
"A'a ya ishe Ni Babie ai babu ma, sai dai ki kira Yayana ya kawo min"
Dijeh ta saka hannu ta ɗauka tana sha, ta sake ninniƙe Juhainah tace.
"My Aunti kiyi haƙuri bazan ƙara surutun ba, zan zauna kusan ki ɗam"
Suhaima ta sabga mata harara tace.
"Ke! Tashi ki dawo nan, ki barta ta huta"
Dijeh kamar zatayi kuka ta miƙe tana kallon Juhainah ko ta hanata tafiyan.
Juhainah tayi kamar bata ji su ba, Sbd bata son ninniƙe wan ne ajikinta.
Al'amin yayi dariya yana ɗaukan yankan Orange ɗaya, yakai bakinsa ya koma ya zauna gurinsa.
Ai Juhainah kamar a tsikareta ta zabura tana sakin plate ɗin, ta dafe kanta da sauri tana fasa wani irin mahaukacin ihu, sai da su Suhaima suka ji tsoro.
MAAH ta katse kiran tana ajiye wayan ta miƙe tana faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Ziyara a wannan halin da take ciki Sbd Allah Dan rashin imani?"
Wani irin kyarma jikinta ya ɗauka, zata faɗo daga saman Chair ɗin Maah ta iso ta tare ta, ina bazata iya ba suka zubar da Maah a ƙasa.
Suhaima ta fashe da kuka ta iso ta rungume Juhainah tana faɗin.
"Don ALLAH kuyi haƙuri ku tafi ka shafa mata lafiya, kar acutar mana da Baby"
Ai sama ta ɗauki Suhaima kamar ta ɗauki takalmi, zata bugata da ƙasa, kamar daga sama ALLAH ya kawo Mustapha da Umar, sun fito daga Company.
Da sauri Umar ya cafke Suhaima, yayin da Mustapha ya damƙe Juhainah ta ƙarfi suka fara kokowa bada wasa ba.
Umar ya ajiye Suhaima ya kamawa Mustapha riƙe Juhainah.
Da ƙarfin ƙarti biyu suka kaita ƙasa, suka riƙeta da kyau.
Duk tare suka fara mata karatun kowa abinda yake karantawa daban dana ɗan uwansa.
Suhaima ta kamo Maah ta miƙe tana riƙe ƙungunta.
Suhaima tace.
"Maah bakiji ciwo ba?"
Maah ta zauna tana faɗin.
"Zainab ina ma nasani tsohon ƙashi ko da naji ba yanzu ba zan gane, amma wlh na bugu, wannan masifar Allah ka yayewa Bilkisu tare da sauran masu irin wannan larura. Kema Zainab Barka da ba'a buga ki da ƙasa ba"
Dijeh tsoro kamar farar kura ta maƙure gefe tana sharɓar kuka tana faɗin.
"My Aunti Allah ya baki lafiya, zance wa Aunti Suraiya ta kira Baba malam ya kawo maki magani"
Maah tace.
"Toh zo ki zauna Khadija, bazata miki komai ba, tunda an fara addu'a."
Suhaima taja tsaki tana ɓata fuska, tace.
"Maah bari naje Stairs na Ciro Phone ɗina acaji na kira Dadd yazo a kama mata karatun..."
MAAH tace.
"Don ALLAH ki barsa ga shi nan su Mustapha sunayi, zai fita in sha Allahu"
Al'amin jarumin yaro shima kusan Mustapha ya zauna yana tofawa Aunty J ɗinsa iya addu'a da iya, dan ma sha Allahu yayi nisa a islamiyya, duk ƙanƙantar shekarun sa, jiya ya shiga cikin
Al Fath.
Umar da mugunta yake masu karatun yana ɗaga murya, yana riƙe da Juhainah game a jikinsa.
Yayin da Mustapha ya riƙe ƙafafuwanta Sbd karta dinga harbe² ɗan cikinta ya samu Matsala.
Ai jin azabar da ake musu suka buɗe baki.
"Wayyo ku tsaya mu tafi daman fita ne zamu yi zamuje ɗaukan fansa, ana shegenta mana cikinmu."
Mustapha yace.
"Ƙarya kake baƙin munafuki, waye ya shegenta mata cikin? Baƙin azzalumi"
"Da gaske Hanifah da Ummata sun fito daga gun Malam Kabiru mai gyaran aure, yace musu Nasir yana shirin ƙara aure acikin hasashen sa, shine sukace a haukata masu yarinyar ko amata kurciya, tabar ƙasar baki ɗaya, har Surayya ƙawarmu tajisu,Mamy ta aiketa siyan cabbage, a zatonta da ita suke, su kuma basu san wacece ba, tunda malam Kabiru baiga fuskar wacece ba.
TOH fa shine suka fara zagar mana mata, wai haukanta da fitsara ya saka aka mata ciki a kwana ɗaya aka sake ta, wai suna kokonton ma ba cikinsa bane, shine abinda ya harzuƙa Ni, kuyi haƙuri ku barni naje na koya masu hankali, yanzu haka Ummah na gidan Hanifah tana cin ɗanyan nama mai ƙanƙara, an zuba mata farfesun Kifi zata kaiwa Baban Hanifah..."
Umar yace.
"Jakar uban nan, brother Mustapha don ALLAH mu barsa yaje yaci min uwayensu wai da gaske dai Mayya ce uwar Hanifah?"
Jinnun yace.
"Wlh Mayya ce ai shekaran jiya badan muna kusa ba da ta cinye Hafizah ɗiyar Mustapha jaririya mai kama da matarmu."
Mustapha yace.
"What? Ɗiyar tawa? Wallahi tallahi da sunyi cin ƙarshe..."
Ai Jinnun na samu wannan sararin an dakatar da karatun wufff ya fece ta bakinta, anan ta fara amai a jikin Umar.
Riƙeta Umar yayi a jikinsa yadda zata amayar da masifar.
Dijeh ta dafe ƙirjinta tana faɗin.
"Innalillahi aunti Hanifah mayya ce?"
Maah da tayi mutuwar zaune a saman Chair, tunda Jinnun Juhainah suka fara ɓarin zance ta dasƙare zaunen, ta girgiza da jin abinda Hanifah da uwarta suke aikatawa.
Kenan so suke su sabauta mata ɗa ko mi?
Kallon Dijeh tayi tana faɗin.
"Kinga idan baki kama Bakinki ba Khadijah zasu cinye ki suna ganinki lutiya dake."
Dijeh ta riƙe Maah tana sakin kuka tace.
"Wallahi na fasa Maah ba wanda zan faɗawa, kowa bazan gayawa ba."
Suhaima tace.
"Ƙarya kike wannan maganar har school sai anjita,kina faɗa sai na tona maki asiri ince daga ƙauye aka kawo ki, kuma ba haɗin mu dake, tunda bakya son ace ke ƴar ƙauya ce"
MAAH tace.
"Ya isa Suhaima kiyi mata haƙura bazata faɗa ba, ta ɓata mana suna ace mun haɗa iri da Mayu"
Dijeh tace.
"Allah Suhaima Bazan faɗa ba kiyi haƙuri Karki ce daga ƙauye nazo"
Mustapha yayi dariya yace.
"Ai ko maganar ki ana ganewa Dijeh daga gida aka fito, idan kin ɓoye banda yarinta ba Mahaifinki na can ruga ba?"
Hawaye ta fara tace.
"Ai na fara gogewa kuma Baba Malam nada kuɗi a ƙauyen mu"
Umar ya miƙe tsaye ɗauke da Juhainah da take bacci ya nufi hanyar bedroom ɗin Maah da ita...
Umar dariya yake yiwa Dijeh yana faɗin.
"Yaro Man Kaza"
Maah tace.
"Idan ka biya Shemanta zaka saka ka ciwon ciki ai"
★
Gidan Nasir.
Ummah Hanifah ta baje saman Carpet tana cin ɗanyen nama, da Hanifah ta Ciro mata a fridge, harda ƙanƙara a jikinsa, sai daddaga yaji take.
Tana ci tana daddaga yaji, suna fira.
Yayin da Hanifah take zaune tana danna wayar ta, tace.
"Ummah wlh yau komai cikin juriya nake yi ashe namiji munafukine? Mugun banza nuna min yake bayada budurwa ashe shirin aure ma yake yi, nayi baƙin cikin da ba'a ga fuskarta ba, amma zan so ya mata kurciya shegiya tsinanniya. Shi kuma zai sani sai kame kurwarsa tunda ya zama munafaki, yayi aure dan masifar namiji ga yayunka nan zaune kowa da matarsa ɗaya sai kai uban jaraba, miye banida shi a jikin mace"
Ummah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Ai na daɗe da faɗa miki ki kame kurwarsa kamar yadda na yiwa tsohonki, kika ƙi ke ƴar daɗi miji"
Ummah ta ƙarasa maganar ta ɗauki tsokar naman zata kai bakinta aka riƙe naman kusan bakinta yana yawo shi ɗaya.
Idanunta ta zaro tace.
"Na shiga uku! Me nake gani Hanifah kalla, tsokar nama na yawo kusan bakina ba wanda ya riƙeta"
Ai cikin bakinta aka tura naman bai tsaya a ko ina ba, sai maƙoƙwaronta.
Aka zabga mata mari tare da shaƙeta aka cirata sama idanunta suka firfito.
Hanifah ta saki wayar ta, ta fasa ihu tana faɗin.
"Innalillahi Ummah! Me nake gani?"
Bakin Hanifah aka buge da mugun ƙarfi atake haƙorin gaba guda ya faɗo ƙasa jini yana zuba, ta zube ƙasa tana fasa ihu cikin tashin hankali, mahaukacin tsoro ya kama Hanifah ganin abinda ake musu ba'a ganin me yin.
Ummah wata irin shaƙa aka mata sai ga naman da taci duk tana amansu, tana sama tana yawo babu wanda ya riƙe ta.
Sai da ta gama aman aka jefota ƙasa ta bugu da Center Table, kanta ya fashe ƙafarta ta samu targaɗe, aka shiga lafta masu bulala ita da Hanifah suna ihu, har muryansu ta dishe.
Tsabar azaba Ummah sai da ta suma, duk sunyi fitsari a inda suke kwance.
Cikin ikon ALLAH kamar daga sama Jawahir ƙanwar Hanifah ta fito daga gun bikin Sunah tace bari ta biyo, taci karo wannan tashin hankalin.
Ai ihu ta fasa tana kuka tana faɗin.
"Waye ya maku wannan abun Ummah Aunty Hanifah...?"
Hanifah cikin azaba bakinta ya kumbura sumtum tace.
"Jawahir ki fita ki samo keke napep muje asibitin su Nasir..."
Ai kuwa a sume aka ɗauki Ummah cikin fitsari, sai asibiti.