Sashe 27
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juhainah ta zaro idanunta tana cire wayan daga kunnenta, cikin fitsara tace.
"Surry wannan yaya Jamal fa ɗan rainin hankali ne, Ok fa kawai yace min ya katse kiran, babu wani lallashi yaji ina kuka ko tambayata halin da na shigan har nake neman temakonsa"
Surayya ta sheƙe da dariya tana kaiwa Juhainah duka a cinyarta tace.
"Au kin zaci gidanku kawai ake da Mai izza da shan ƙamshi da miskilanci? Ai Wlh ki godewa Allah ma da har ya amsa da Ok"
Juhainah ta zumɓuro baki tana faɗin.
"Allah dan yana yayanki ne zan raga masa, hummm!"
Surrayya tace.
"Ragawa kuwa dole koda ba yayana bane, tunda kina neman taimako emergency"
Juhainah ta zubawa Surayya dara-daran kyawawan idanunta, zata yi magana aka ƙwanƙwasa ƙofar.
Juhainah tace.
"Shigo Jamilu"
Buɗe ƙofar yayi da sallama ya shigo ɗauke da kayan abincin.
Sallamar suka amsa ya ƙaraso cike da mamakin mi Juhainah take anan dakin da aka sauke baƙuwa? duk yawan ɗakunan ta rasa inda zasu zauna sai nan, kuma ya sani neman fitina ne. Ai ko sirri zasu yi inda Yah Boss bazai gansu ta wayoyinsa ba, Akwai sauran bedroom's ɗin da babu na'urar a ciki ba dole sai anan ba.
Ajiye masu tray'n yayi gaban su ya juya ya tafi, yana rufe masu ƙofar.
Juhainah tana ɗaukan plate shaƙe da lafiyayyan jalof rice taji niƙaƙen naman Kaza, da kayan lambu sai wani irin ƙamshi yake tashi, gefe an zuba 🥗.
Spoon ta ciko takai bakinta da Bismillah tana taunawa tace.
"Toh my Surry na amince ki tutunɓesa kiji idan ya amince Sai ki basa number na, muyi magana, zan lallaɓa Yah Boss ya bani wayata"
Ta ƙasara maganar tana sake ciko spoon takai bakinta tana ɗaukon juice ta buɗe ta tsiyaya takai bakinta tana sha.
Surayya ta ɗauki nata plate ta ɗauki spoon, lomar farko tace.
"Kan Uba Jamilu da maca ne da mijinta ya huta Wlh"
Juhainah ta kwashe da dariya tana tura wata lomar da spoon bakinta tana faɗin.
"Shegiya kin kwaso yinwa ne.
Ke kam jiya kiran mi kika dameni da shi ina bacci?"
Surayya tace.
"Uhumm bari ke dai Wlh kawai so nake naji mi yasa yaya Sadeeq ɗinku baya son aure tunda Aunty Khadijah ta rasu? Allah masifar sonsa nakeyi ki temaka min mana"
Juhainah ta ɗauki Cup ta kai juice bakinta tasha sosai ta ajiye tana sake kai loma bakinta ta kalli Surayya tace.
"Bakida hankali Wlh ki nemi wanda zakiji daɗin auren,kullum ina faɗa miki bakyaji, ko kin auresa kin Banu, tunda baya sonki, wai ke kam wannan baƙin ran nasa ta yaya zakiji daɗin soyayya da shi? Muda muke da Burin auren shuga Daddy su tattalemu. Toh shi shuga wuya zaka sha sunan auresa, idan dai ba shi yake sonki ba"
Surayya tace.
"Bakida hankali yo yaya Sadeeq akwai wanda zai fisa iya tattalin mace, da nuna mata soyayya? Ni dai ki bani tarihinsa don Allah wlh labarin daɗi yake min"
Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tace.
"Ƴar wahala tarihin dai ɗaya ne kinsan kowa gidanmu, tun muna primary school ko?"
Ta ƙarasa maganar tana sake lodawa cikin daddaɗan abincin.
Surayya tace.
"Ni dai ki sake bani tarihinsa daɗi yake min"
Juhainah tace.
"Ke kam kin Banu my Surry, toh ki bari na gama cika tumbina..."
Suhaima zaune tana kallon Tv tashar Mbc 3 duk hankalinta agun Juhainah yadda taja Surayya suke keɓe bata san wani ɗaki suka shiga ba, amma taga sunyi hanyar kitchen, dan tunaninta ma bazai bata bedroom ɗin da bak'ar matar nan take suka shiga ba.
Al'amin ko yana can Stairs yayi baje² da kayan wasansa dan bai kwanta ba kamar yadda Yah Boss yace masa, wasansa yake cikin kwanciyar hankali.
Juhainah babba ce ta shigo parlour ganin Suhaima a gun tai saurin juyawa zata koma, ckin rashin Sa'a Suhaima ta ganta, tace.
"Wani abun kike nema? Mi ya shigo dake parlour Dadd ɗina?"
Juhainah babba ta juyo kamar zata yi kuka tace.
"Kiyi haƙuri babu abinda nake nema, daman Juhainah ne suka shiga ɗakin da nake zasu yi maganar sirri, tace na fito na basu guri"
Suhaima ta taɓe baki tana faɗin.
"Toh kije ki nemi wani gurin ki zauna a can hanyar bedroom ɗin mana, miye na zuwa nan?"
Juhainah ta ɗaga kanta batace komai ba, ta juya ta koma.
Suhaima ta bita da harara, tana ɗaukan remote ta canza channel...
★
Maah suna zaune itada Mustapha da Twins ɗinsa, Shuraim da Shamsiddin
Yah Boss ya shigo parlour da sallama, saboda Fu'adh ya wuce wani gun aikin Yah Boss.
Maah suka amsa sallamar.
Yayin da Shuraim da Shamsiddin suka miƙe cikin farin ciki suka tarbi Yah Boss suna rungumeshi, suna faɗin.
"My Dadd ina kwana"
Daukansu yayi cike da ƙaunarsu a hankali cikin zazzaƙar muryansa ya furta.
"My Twins yanzu ina wuni ake cewa, kuna lfy?"
Shuraim yace.
"Eh my Dadd ina Al'amin?"
Mustapha ya miƙe fuskarsa mai kama da ta Yah Boss duk da bai kaisa tsayi da girma ba, amma farinsu zai kusa zuwa ɗaya, tunda kowa najin kansa da kuma jin daɗi duk da Yah Boss ya shallake komai.
Mustapha shi yake bin Aunty Sumy.
Rungume Yah Boss yayi tare da yaran, yana sakin murmushi muryansa na shigen ta Yah Boss yace.
"Barka da yamma my Big brother, ina yarana? Yanzu Maah tace min ɗazu kun tafi dasu"
Yah Boss ya kalli ƙanin nasa cikin kamewarsa a hankali yana faɗin.
"Eh sun takura ne, Mustapha fitinanniya yarinya nan Bilkisu na can kasan kuma basa nisa da ita"
Mustapha yayi murmushi yana dafa kafaɗar Yah Boss yace.
"Umar ya faɗa min komai, naci dariya sosai ai kaine maganinta, don Allah ka aurar da ita, da tsohon shegiyar yarinya fitsarariya batada kunya, ga saka shegun kaya a cikin gida sai kace ɗiyar Yahudawa..."
Yah Boss ya sauke Twins yana faɗin.
"My Twins kuje kuyi wasa."
Suka ruga da gudu suna faɗawa jikin Khairat, suna mata surutu.
Yah Boss ya zubawa Mustapha lumsassun fararen kyawawan idanunsa, yana kame fuska sosai, yadda Mustapha yake ta zagin Juhainah.
Farin tattausan hannunsa ya beƙa ya buge bakin Mustapha yana sake kame fuskarsa sosai, a hankali cikin zazzaƙar muryansa ya furta.
"Idan bazaka iya ƙoƙarin ɗaukan mataki a rashin jinta ba tafi ƙarfin ku, toh kaja bakinka kayi shiru, ba ruwanka da duk abinda da take, meye na zagin nata, kana ce mata shegiya daman ubanta daban ba Yakubu Abubakar Janfar ya haifeta ba?"
Mustapha ganin cikin ƙaramin lokaci yayansa ransa ya ɓaci da gaske yayi saurin riƙe hannunsa yana faɗin.
"A'a Wlh yaya Sadeeq ban faɗa dan na ɓata maka rai ba, kayi haƙuri nima fa inason ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya, I'm sorry My Big brother bazan sake ba..."
Baki Yah Boss ya taɓe yana faɗin.
"Last time da zaka sake zagin Juhainah a gabana."
Mustapha mamaki kamar zai kashesa ya rungume Yah Boss yana sake basa haƙuri ganin da gaske yake yaji zafin zagin da yayiwa Juhainah, bayan shi dukanta ma yake kamar sakwara idan tayi ba dai-dai ba, kuma yace su ko zaginta baza suyi ba, gwara ma Aunty Sumy ce kawai baya tsawatarwa idan ta rufe ta da faɗa ko dukan ma.
Yah Boss ya janye jikinsa yana kallon Mustapha cikin kamewarsa ya furta.
"Na bata kwana 3 ta fito da miji ko na aura mata duk wanda naga dama"
Ya ƙarasa maganar yana nufa gun Maah
Khairat cike da girmamawa tace.
"Sannu my brother"
Bai kalleta ba ya amsa da.
"Barka Khairat, yawwa ki shirya tunda baka school sai Monday kije can ku zauna gobe idan naje Jigawa Ba zan dawo ba sai Monday da safe ina son na huta kwana biyu, yarinyar nan ta saka min ciwon kai kwana biyu"
Ya ƙarasa maganar yana zama kusan Maah yana zuba dogayen fararen ƙafafunsa saman babban Center table ɗin yana lumshe kaifafan lumsassun idanunsa.
Khairat ta amsa da.
"Tom my brother bari na shirya"
Maah ta kalli Mustapha da yake mata gulma da idanunsa.
Da ido tai masa nuna ya iya bakinsa ba ruwanta, ya fita sabgarsa a yanzun alamu sun nuna baya cikin nutsuwarsa.
Gum Mustapha yayi ya nemi guri kusan Yah Boss ya zauna, yana masa magana akan tafiyarsa Jigawa.
Maah ta kalli Yah Boss tana taɓa kansa tace.
"Abbah! Ya dai? Naga ka dawo kayi shiga kamar angon ma sha Allahu, ko suruka zan samu?"
Da sauri ya buɗe kaifafan lumsassun idanunsa ya zubawa Maah, yana faɗin.
"No! Maah please mana, haba ina Sam, akwai meetings da zanje ne ƙarfe 5.
Maah! Yarinyar nan na bata kwana uku ta fito min da wanda take so, saboda wacan yaron tace bata sonsa, idan kuma bata fito ba, bazan rasa na bata ba.“
Ya ƙarasa maganar hankalinsa kwance idanunsa akan Tv ba wanda ya kalla cikin parlour.
Maah tace.
"Yawwa kayi dai-dai haka ake son babba, Allah ya maka albarka Abbah"
A hankali ya amsa da.
"Ameen, ina papa?"
Maah tace.
"Ya fita kai da kasan halinsa bai son zama gida, wai tsohon jini yake masa yawa"
Mustapha yace.
"Yaya Sadeeq! Kamar na biki Jigawa"
Yah Boss ya kallesa baiyi magana ba, ya kamo hannun Shamsiddin yana masa magana cike da so da kulawa.
Maah
a ranta tace.
"Allah mai iko Abbah bansan me yasa baya ƙaunar a zagi Autah ba, amma shi ya iya naɗa mata na jaki"
Murmushi tayi tana Hamdalla gun Allah.
Yah Boss ya kira Papa a waya sukayi magana akan hukuncin da ya yanke, papa ya goyi bayansa ya saka masa albarka.
Khairat ta fito cikin shirin tafiya ya duba lokaci yace mata su tafi, dan yanada sauran lokacin meetings ɗin.
Ta yiwa Maah sallama.
Twins suka fara rigima sai sun tafi.
Yah Boss ya kwashe su suka tafi akan Mustapha zuwa dare ko gobe yaje ya kawosu tunda tafiya Jigawa zai yi.
Dole gidansa ya nufa a sauke Khairat da yaran, ya canza kaya saboda hannun Shamsiddin da yaci chocolate ya goga masa ga shi meetings zai shiga ƙarfe biyar.
★
Jamal