Sashe 31
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulkarim yace.
"A'a inaga dai soyayyar sukayi yanzu ta fito da shi ayi auren, Mamy wannan miskilin ɗan naki wa zai gane ma idan soyayyar yake yi."
Mamy tace.
"Ai kuwa auren za'ayi in sha Allahu..."
Jamal Da sauri ya ƙaraso yana faɗin.
"No! Mamy Ni babu wata magana tsakanina da yarinya nan, wannan munafukar itane taje suka shirya komai, auren bogi ne suke so nayi da ita..."
Mamy zatayi magana Surayya tace.
"Allah Mamy Juhainah tana sonsa ta daɗe tana sonsa, saboda shi take ƙin kula samarinta, yanzu an matsa mata ta fito da miji tunda bata son karatu tace ita Yaya Jamal take so, yayan su commissioner har ya amshi number yaya Jamal ya kirasa saboda Allah an kyauta ace bazai aureta ba, ɗiyar manyan mutane ce fa ga class yarinya..."
Ai wani irin mari Jamal ya zambaci Mamy ya shararawa Surayya sai da taji kamar zata saki fitsari, ta fashe da kuka.
Abdulkarim yace.
"Saboda an faɗi gaskiya akanka kake dukan ƙanwarka? Wai Jamal wani irin juyayyen haline dakai?"
Manyan kyawawan idanunsa da suka fara rikiɗa ya zubawa Abdulkarim, amma baiyi magana ba, ya juya ransa a mutuƙar ɓace yake wani irin taku zaibar parlourn.
Mamy tace.
"Kema shegen surutu gareki maganinki kenan, yimin shiru ko ki tashi ki shiga ɗakinki. Yaka Jamaluddin ɗan albarka zo mana, yarona."
Ai Surayya ganin ya juyo zai dawo ta miƙe daga jikin Mamy ta gudu ɗaki.
Zama yayi kujara face da ita, bai kalli kowa ba, asali ma ƙasa yayi da kansa.
Mamy ta miƙe ta koma kusansa tana kamo hannayensa cikin tausasa murya tace.
"Jamaluddin! Ai abun alfahari ne kamar Juhainah tana sonka, yarinya akwai kyau da asali, gashi tare zaku girma abinku, duk da kai ƙashin girma ne dakai amma shekaru kaɗan sai da hankalinka da ilimin da nutsuwarka sun girmi shekarunka, don Allah ka amince mu haɗa jini da Yakubu Abubakar Janfar Please yarona ina neman wannan alfarma, kuma ba nisa zakayi damu yanzu ba, kuyi zamanku Anan kafin ka kammala karatun naka, idan gidanka da ake ginawa zaku tare babu laifi...“
Jamal ya kalli mahaifiyarsa baice uffan ba, ya jinjina mata kai yana riƙe hannunta.
Ta gane nufinsa ya amince.
Rungumeshi tayi tana buga bayansa tace.
"Nagode Allah ya maka albarka Jamal, in sha Allahu zaka gama da duniya lafiya"
Abdulkarim yace.
"In sha Allahu, Mamy yanzu za'a jira Abba ya dawo daga tafiya ko muda su Kawu Giɗaɗo zamuje?"
Jamal dai ya miƙe tsam yabar parlour'n.
Mamy tace.
"A'a a jira jibi yake dawowa Sai ku tafi tare zaifi, Wlh naji daɗi sosai idan yayi auren tunda ƙuruciyarsa, ko zai rage wannan shiru da fuska kullum Babu fara'a babu hira da jama'a..."
Abdulkarim yayi murmushi yana faɗin.
"Uhumm! Mamy dai tana son shalelenta ya dawo mai hayaniya, haka halinsa yake fa, babu macen da zata canza shi..."
Surayya da ta laɓe taji abinda ya faru ta fasa ihun murna tana tiƙar rawa sister Juhainah zata dawo gidansu baki ɗaya da rayuwa.
★
Anguwan
Karewa
Misalin ƙarfe 8 na dare.
Nasir tsaye cikin shirin tafiya gidan Yah Boss, shigarsa mai ƙayatarwa ta alfarma.
Hanifah tana tsaye kusansa tana fesa masa turarensa mai daɗi.
A hankali tace.
"Wai ina zaka tsakani da Allah gabana faɗuwa yake yi, Please kar dai Taɗi zaka je?"
Nasir ya rungumeta yana sumbatar kumatunta yace.
"A'a Big brother yake nema na, ki kwantar da hankali ba gun wata zanje ba"
Kamar zata yi kuka tana shafa kyakkyawar fuskarsa irin ta Yah Boss ta sumbaci lips ɗinsa tace.
"Shi kenan sai ka dawo, Allah ya tsare"
Nasir ya amsa da.
"Ameen My Hanifah, muje ki rakani mota"
Suna riƙe da hannun juna har farfajiyar gidan.
Lafiyayyar motarsa ƙatuwa Fara ƙal, ya shiga suna ɗagawa juna hannu ya nufi gate yana yiwa mai Gadi Horn, mai Gadi ya buɗe masa gate ya wuce ita kuma ta koma ciki.
A dai-dai wannan lokacin Yah Boss ya kira Jamal akan yana jiransa.
Cikin shiga ta kece wa tsara Jamal ya fito daga bedroom ɗinsa, yana wani irin bala'in ƙamshi, ƙananun kaya ne masu masifar tsada ya saka, tun daga kan takalmin da yake sanye a fararen ƙafafunsa zuwa agogon silver da ya saka gilashin idanunsa sun isa ka sheda Jamal matashin saurayi ne mai tsada mai jini ajiki ka masu gidan Rana.
iPhone 17 pro max d take ajiye akan Center table, ya ɗauka ya jefa cikin aljihun wandonsa ya ɗauki makullin motarsa ya fito, fuskarsa babu alamar rahama ya nufi rumfar ajiye motocin gidan.
Sabuwar Ferrari ƙirar 2025 Baƙa ya shiga yaja ya nufi gate.
Juhainah tunda ta haye Stairs daga shan magani bata sake saukowa ƙasa ba, tana can cikin ƴaƴanta, Suhaima Al'amin Shuraim Shamsiddin, sunata shirmensu tana biye masu.
Sai Maghreb tayi wanka ta saka doguwar riga ta atamfa ta kame dogon gashinta ta saka hula.
Khairat ko tana can downstairs zamanta tana kallo, Sallah take kawo.
Yanzu Ma Yah Boss zaune Fu'adh gefensa, sai Khairat can ɗayan layin Set ɗin Sofa tana zaune abunta, tana kallonta, yayin da Fu'adh yake jefa mata kallon soyayya, tayi murus kamar bata gansa ba.
A she Yah Boss ya ankare da Fu'adh.
Gyaran murya Yah Boss yayi yana kallon Fu'adh ya furta.
"Fu'adh! idan kana buƙata hira ta shi kuje wancan parlour, bana son kalle² munafurci anan.
Ke! Tashi kije ya iskeki munafuka shiyasa kika ƙi zuwa gun su Juhainah kika liƙe anan, su cin abinci kaɗai ya fito dasu sukaci suka koma."
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye yabar masu gurin.
Khairat ta shiga raba idanuwa, ta shagwaɓe masa kamar zata yi kuka tace.
"Heart kaga abinda kaja min ko? Ni toh bazan yi fira ba, sai da safe ma natafi"
Ta ƙarasa maganar tana tafiya.
Da sauri ya sha gabanta yana marairaice fuska yace.
"Please Heart ina son muyi fira Please mana"
Kafaɗa ta maƙale tana tafiyarta.
Dariya yayi yana komawa ya zauna.
Yah Boss kuwa ganin kiran Nasir akan ya kusa isowa ya fito dan su shigo tare, yanada wannan karrama wa , wa familles Janfar idan yaso.
Fu'adh yana latsa wayansa yaji motsi.
Kai ya ɗago yaga Juhainah baƙa riƙe da ledar kayanta da sauran maganinta.
Da mamaki yace.
"Juhainah lafiya? Ina zaki a daren nan, ai gobe in sha Allahu za'a kaiki garinku"
Durƙushe wa tayi akan guiwowinta tana sakin kuka tace.
"Wlh ummana babu lafiya ance a matse take, hankalina bazai kwanta ba har gobe, zan samu shatar mota a daren nan na kwana a Misau"
Fu'adh yace.
"Subhanallahi ayya toh babu damuwa muje a samu shatar mota Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne, muje"
Ya ƙarasa maganar yana miƙewa ya wuce tana biye da bayansa.
Fu'adh yana buɗe ƙofar parlour Yah Boss da Nasir suna isowa.
Yah Boss kallo ɗaya ya mata ya janye idanunsa.
Nasir ya basa hannun suka gaisa yana faɗin.
"Fu'adh wannan dai ban santa a familles naku ba?"
Juhainah ta duƙa tana gaishe da Nasir.
Yayi murmushi sak kamar Yah Boss yayi ya amsa yana faɗin.
"Ya gida?"
Fu'adh yace.
"Sir gida take son tafiya mahaifiyarta na cikin matsanancin rashin lafiya, tace shayar mota zata ɗauka."
Yah Boss yana wucewa ya furta.
"Allah ya bata lafiya, Ok kayi mata duk abinda ya dace ka haɗa mata da jarin sai ka bada kuɗin zai ishi umman nata magani da zaman hospital"
Ya ƙarasa maganar yana shiga ciki.
Juhainah ta zube tana godiya.
Nasir yabi yayan nasa yana sakawa a ransa neman temako tazo.
Har tasha Fu'adh ya rakata tace batada account number, dole sai da ya dawo gidan Yah Boss ya basa 1 miliyan yasan dai zasu mata, jari da magani.
Juhainah sosai tayi wa Fu'adh godiya tana kuka, shi da Walid suna tsaye sai da direba yaja motar suka tafi, su Kuma suka koma gida.
Yah Boss ya zubawa Nasir lumsassun fararen kyawawan idanunsa, a hankali ya furta.
"Nasir! Maah tana buƙatar kuje kuyi gwajin lafiyarku tunda auren shekara biyu zaku yi uku babu labarin Baby, idan kuma mataki ne kuka ɗauka ina son sani a fasa ba mahaifiyarmu wahala?"
Nasir ya marairaice fuska yana kamo tattausan hannayen Yah Boss yace.
"Allah my Big brother bamu ɗauki matakin komai ba, Allah ne bai kawo ba, kayi haƙuri zamuje gwajin ranan Monday nan asibitin Janfar"
Yah Boss zaiyi Magana kiran Jamal ya shigo wayansa.
Ɗagawa yayi a nutse ya furta.
"Assalamu alaikum, ka iso ne?"
Jamal ya amsa sallamar yana faɗin.
"Eh Na shigo"
Yah Boss ya furta.
"Ok, Nasir kaje ka iso da shi"
Nasir bai tamabaya waye ba, ya miƙe ya tafiya aikin yayan nasan, jin yace a kawo parlour nan yasan baƙon mai daraja ne ba kaɗan ba.
Da sallama Jamal ya shigo har tsakiyar ƙaton parlour.
Yah Boss ya amsa cikin nutsuwarsa.
Jamal ya gaishesa cikin girmamawa.
Saboda duk jin kanka Yah Boss Allah ya masa wani irin kwarjini, kana tsayawa gabansa sai kayi saranda.
Yah Boss ya nuna masa kusansa yana faɗin.
"Zauna Jamal"
Zama yayi yana cire glass ɗin idanunsa.
Yah Boss ya gyara zamansa yana kallon Jamal, a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Juhainah da gaske ne kunyi magana akan zaka aureta?"
Jamal kamar ya fasa ihu, amma babu yadda zai yi tunda mahaifiyarsa ta nemi alfarma.
Cikin girmamawa ya amsa da.
"Eh in sha Allahu"
Yah Boss da yake bai cika kallon mutum ba, ba tare da ya kalleshi ba ya furta.
"Tanada jinnu masu tashi idan ta firgita ko ɓacin rai mai tsanani ko ta razana ko taga abinda bai mata ba, kuma duka suke, kana sonta zaka aure a haka?"
Jamal a cikin zuciyarsa ya furta.
"Kutumelecy, Nida nake so Naci ƙaniyarta idan anyi auren har ta gaji tace bata auren"
A zahiri kuma ya furta.
"Eh nasani ina sonta a haka, ai ita nake so ba ciwon ba, idan kana son mutum a kowane irin yanayin yake zaka zauna da shi"