← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 113

Sashe 73

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Picking call ɗin yay ta gilashin idanunsa, kafin yayi magana yaji shasheƙar kukanta, tana faɗin.
"Yah Sadeeq banida lafiya wallahi tallahi zuciyata zafi take min na rasa wannan masifar, ka hanani na faɗawa Maah ko Aunty Sumy ko Yah Nasir Umar Mustapha Aunty Khairat cikinsu wani da ya lallasheni zan rage jin abinda nakeji ya to kare min ƙahon zuciyata, tunda ka ɗauki maganata shirme wallahi ji nake kamar bazan kai jibin ba araye..."
Ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka.
Yah Boss a hankali ya furta.

"Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil La Haula Wala Quwwata Illah Billah. Bilkisu Clam down, kin manta kinyi min alƙawari?"

Cikin kuka tace.
"Na janye tunda kaima baka ciki min ba, kace zaka bani Sweet ka hanani kace zaka kirani baka kira ba, Maah zan faɗawa gaskiya ince wallahi tallahi duk duniya ni kai nake so, dole akwai dalilin da yasa Ubangiji ya jarabeni da irin wannan Ƙaunar taka, in ma asiri ne magautanka suka yi min a nemo makarinsa, bazan bari sonka ya kasheni ba tunda baka sona Habiby"

Ta idar da maganar tana wani irin kuka.
Yah Boss miƙe wa tsayeyayi yana ɗaukan wayan tare da files ɗin ya nufi hanyar Stairs a hankali ya furta.
"Inji wa yace bana sonki? Ke fa jinina ce, ya isa bari kukan Ganinan yanzu zan kawo miki Sweet ɗin, amma karki je ki faɗawa Maah komi Please Aunty J kinaji na?"

Kukan ta fasa tana ƙamƙame quilt ɗin a hankali cike da shagwaɓa tana lumshe dara-daran kyawawan idanunta tace.
"Habiby a baki nakeso zaka bani Please?"

Yana taka Steps Anutse a hankali ya furta.
"Ok alright Amma Karki faɗawa Maah kina sona har na iso gidan yanzu Ok Aunty J?"

Sake narkewa tayi idanunta na lumshe a hankali tace.
"Yah Boss ina sonka kaji?"

A hankali ya furta.
"Naji Aunty J Nima ina sonki ai ke jinina ce ki kame bakin ki har na iso Ok?"

A hankali ta amsa da.
"Toh Habiby please kayi sauri kar na kasa jure riƙe maganar a zuciyata Sbd abin kamar ciwo Wlh ji nake idan ban faɗawa kowa ba mutuwa zanyi"

Tsawa ya daka mata yana faɗin.
"Nace ki jirani zanzo yanzu alright, miye na rikincin, waɗanda zaki faɗawa sunada maganine?"

A hankali ta girgiza kanta tana sake ƙamƙame quilt ɗin tana fitar da wani irin numfashi a hankali tace.
"My brother Habiby kayi haƙuri TOH, ina jiranka."
A hankali ya furta.
"Ok ki nutsu sosai sai nazo Bye"

Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.
Cikin mintina ƙalilan ya gama canza kaya masu mutuƙar burgewa ya fito yana baza ƙamshi. Kai kana kallon Yah Boss kasan ba ƙaramin attajiri bane, ilimi sanin mutuncin kai, nutsuwa kyau dole duk macen da ya so ta zama mai alfahari a ko ina take.

Shi kaɗai ya shiga lafiyayyar motarsa mai baƙin gilashi yaja ya tafi.
Cikin nutsuwa yake driving ɗinsa cikin ƙwarewa.
[24/03 10:43] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

💃🏻Barkanmu da Sallah, Ubangiji Yasa Ibadar Da Mukayi Karɓaɓɓiya Ce Yasa Muna Cikin Waɗanda Aka Ƴanta Aameen Ya Rahman.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Page 39*

Ammar bai sha wuya ba gun gane gidan, tunda address ne.
Yana isowa bakin gate ɗin ya fara Horn.
Raudah taba Mai Gadi umarni idan anyi Horn ya buɗe gate tasan da zuwan mutumin.
Kai tsaye ya buɗe masa gate ya shigo cikin gidan.
Yana gama parking Raudah tana fitowa taku take irin na isassun mata masu aji, ta tarbe sa.
Anutse ya tako ya nufi gunta yana mata wani Irin kallo.
Murmushi tayi tana yafito shi da hannu ta juya tana takawa tace.
"Maida yawunka ka haɗe zai fi maka alheri, Wlh ni ba tsaranka bace, na wuce da saninka ƙaramin yanyan, duk wani shege na sansa ba drugs ba, komi ka sha Wlh baka isa ka ratsa jikina ba, muje cikin ka gwada kuma, zaka san mata suna suka tara, biyo ni muje Ammaru"

Ta ƙarasa maganar tana tafiya.
Ammar yabi bayanta.
Tana shiga ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza ƙafar.
Murmushi Ammar yayi ya iso ya zauna dab da ita, har jikinsu yana haɗuwa, ya ranƙwafo fuskarsa dab da tata yana magana ƙasa², yana sanya hannayensa ya kamo ƙugunta ya riƙe sosai ya haɗeta da jikinsa.
Manna bakinsa yay akan fatar wunyata ya sumbata a hankali, sai ya kamo fatar wunyata ya tsotsa, still yana murza ƙungunta, a hankali cikin yaudara yake mata magana a fatar wuyan nata.

"Raudah! Tunda na fara jin muryan ki na kamu da soyayyar ki, Wlh baki isa kin hanani sonki ba, ban damu da ki soni ba, don girman ALLAH ki barni ni na soki mubar maganar Juhainah Please."

Ya ƙara maganan yana silalo mata hawayensa na kissa wanda ya gangara zuwa tsakiyar ƙirjinta.
Ta kallesa tana ɓata fuska da mamaki ta kamo fuskarsa ta riƙe tana faɗin.
"Ammaru ƙarya fa kake ka yaudareni, duk girman son da naji ina yiwa commissioner A.Y.A Janfar na haƙura sbd na tsani soyayya sai kuɗi kai, a jinka zaka iya yaudarata? TOH kayi kaɗan Wlh..."

Ta ƙarasa maganar tana manna bakinta saman nasa ta sumbata ta tura masa harshenta cikin tsakiyar bakinsa.
Sai da ya kamo yana niyar sha ta gantsa masa uban cizo ya saki bakin nata.
Ta tofa masa yawu a akan fuskarsa tace.
"Mayen mata ƙwalelenka har Drugs ɗin da ka sha na ganeta, idan ka isa Wlh ka haƙemin sai dai uwarka ta haifi wani a yau, ka tashi ka tafi na fasa haɗin bakin da kai zanyi abuna Ni ɗaya"

Ta ƙarasa maganar tana buge hannunsa a jikinta ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta, ta shiga ta murza key ta haye bed tana ƙyalƙyalewa da dariya, tace.
"Yana zaton ni ƙaramar ƙwarice, wasu ƙannaun Drugs ɗinsa zasuyi tasiri a kaina banza kawai ƙaramin yanyan..."

Ammar ya miƙe cikin muguwar sha'awar Raudah ga wandonsa baya kalluwa.
A hankali ya lallaɓa ƙofar bedroom ɗinta ya tsaya yana bugun ƙofar, tare da faɗin.
"Raudah! Kiyi haƙuri nayi kuskure Wlh bazan kuma ba, ni yanzu wlh son aure ma nake miki buɗe ƙofar Please? Zan taimaka miki wajan cika burin ki akan Juhainah kizo ina jiranki a parlour"

Ya ƙarasa maganar yana komawa parlour dan yayi alƙawarin yau sai ya nunawa Raudah ita ne ƙaramar yanyan sai ya haƙe mata, koda a parlour ne sai yaji ɗanɗanon ta.

Raudah kamar bazata yarda da abinda yace ba, amman jin kalamansa na ƙarshe ya sakata dariya ta miƙe zaune ta sauka ta nufi ƙofar tana faɗin.
"Aure fa? Ana zaune ƙalau ALLAH dai ya baka mace ta-gari ina maka fatan Alkhairi amman ni a'a ba daniba Gaɗa A Hurumi"
Ƙofar ta buɗe ta fito, tana yauƙi tazo ta zauna nesa da shi...


Juhainah Yah Boss yana katse kiran ta janye quilt ɗin da take lulluɓe, ta miƙe zaune ta sauka daga bed ɗin cikin farin ciki.
Sai dai jikinta yayi la'asar sosai.
Hijabi dogo ta saka akan kayan baccinta ta ɗauki iPhone ɗinta ta buɗe ƙofa ta fito.
Bedroom ɗin su Suhaima ta buɗe ta shiga har sunyi bacci, suna lulluɓe.
Karasa wa tayi bakin bed ɗin Al'amin ta zauna tana kallon kyakkyawar fuskarsa, bacci yake anutse.
Addu'a ta tofa masa tana jan Duvet ta rufe shi har wuyansa, Sbd yadda Ac'n ta kama bedroom ɗin sosai.
Kiss ta masa a goshinsa ta miƙe ta nufi gun Suhaima.
Dara-daran kyawawan idanunta ta zuba wa Suhaima da take baccinta hankali kwance, ita kam bata ma rufa ba, duk sanyin Ac'n da ya kama ɗakin.

Babu Abu ajikin Suhaima da ba na Yah Boss ba, hatta ɗan yatsunta na hannu da ƙafafu iri ɗaya ne.
Rungume Suhaima tayi ta tana murmusawa a hankali tace.
"My Babies ina sonku sosai da sosai kamar yadda nake son Yah Boss, nayi baƙin cikin babu aure tsakaninmu, ina son na rayu da Yah Boss rayuwa ta har abadan..."
Ta ƙarasa maganar tana gyarawa Suhaima hular kanta da tulun gashinta na asalin Larabawa ya fito.
Suhaima irin baccin Yah Boss take, sauti kaɗan yake tayar da ita ko magana ko ka taɓa jikinta matuƙar daman ba jikin nata kake ba kafin baccinta.

Tun lokacin da Juhainah rungumeta kafin ta fara magana ta farka daga baccin.
Amma bata buɗe idanunta ba, taji tana sambatu.
Tana ƙoƙarin buɗe idanunta tayi wa Aunty J magana taji wayanta tana ringing.
Sakin Suhaima tai tana ɗaga kiran ganin Yah Boss ne.
A hankali takai wayan kunnenta tana shagwaɓe murya a hankali tace.
"My brother Habiby"

Anutse cikin kamewarsa ya furta.
"Aunty J kizo ɓangarena na iso ina jiran ki"
A shagwaɓe tace.
"Toh Habiby in kawo maka tea zaka sha? Please Habiby kaji? Ni zan dafa maka"
A hankali ya furta.

"Ok kawo"

Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.
Cikin farin ciki ta miƙe ta janyo Duvet ta lulluɓe Suhaima ta duƙo ta sumbaci goshinta da kumatunta a hankali tace.
"I love you My Babies Allah ya raya mana ku naga nayi maki aure Suhaima Babie"

Ta ƙarasa maganar tana juyawa ta sa kai ta tafi.
Suhaima ta buɗe lumsassun fararen idanunta tabi Juhainah da kallon so da ƙauna.
Juhainah tana fita tace.
"Allah Sarki! Aunty J ashe tana son My Dadd, ga shi babu aure tsakaninsu, da nafi kowa farin cikin hakan Wlh. Maybe ma Dadd shima yana sonta.
Idan ba haka ba me yasa yazo a wannan dare yace ta sameshi a part ɗinsa? Wayyo har sun bani tausayi, irin sosai ɗin nan"

Suhaima ta ƙarasa maganar tana goge hawayen da bata ma san sun fara sauka akan kyakkyawar fuskarta ba.
Miƙewa tayi ta sauka ta nufi bathroom dan fitsari take ji sosai.
Juhainah tana saukowa ta isko parlour ba kowa duk kowa ya nemi gun kwanciyar sa.
Cikin farin ciki ta nufi kitchen.
Cikin sauri ta kunna Gas ta ɗora ruwan zafi.
Chapter 73 · 0% Book details