← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 113

Sashe 6

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjinar ku shine ƙwarin guiwata, ina godiya sosai masu turo min sako.💃🏻🥰
+22796515805
[27/12/2025 14:46] null: _*JUHAINAH*_

Love Story💗🫂

Free Book

By
Real Rahma Ladingo

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Jinjina Dubin Gaisuwa Da Fatan Alkhairi Aunty Sumy, Ngd Ngd Da Alkhairinki Gareni, Da Gudunmuwar Da Kike Bani Acikin Rayuwata, Allah Raya Maki Zuri'a Ya Rabaki Da Iyayen ki Lafiya. Allah Yasa Sai Muta Ne Zai Fitar Dake Daga Gidan Mijinki Ameen.🙏🏼💕*

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne JUHAINAH💗 sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Page 4

"Fu'adh! Kana son ni na fito da kaina na ɗaukota saboda ceto rayuwarta na fito ne, bazaku iya ba?"

Fu'adh yana jin shigowar saƙon yasha jinin jikinsa Sir ne, dan haka ya duba wayan hannunsa ya karanta saƙon.
Cikin aljihunsa ya saka wayan cikin ƙyanƙyami duk da batada dattin a jikinta, rintse idanunsa yayi ya sanya hannayensa ya cicciɓota ya ɗaga sama ya miƙe ya nufi motar.

Walid yayi saurin nufar motar ya buɗe bayan nufinsa a kwantar da ita kusan ogan nasu.
Yah Boss ya ɗan waro lumsassun fararen idanunsa yana haɗe fuska sosai.
Ai Fu'adh kallo ɗaya ya masa ya juya ɗauke da ita ya koma gaban motar ya kwantar da kujeran ya kwantar da ita, ya zagaya ya shiga gun zaman direba.
Walid yana ganin haka ya zagaya ya shiga bayan gun Yah Boss yana rufe ƙofar, Fu'adh yaja motar suka bar gun da wani irin Speed saboda gaggauta kaita asibiti dan a bata temakon gaggawa.

Yah Boss yana latsa haɗaɗɗiyar wayansa Samsung, a hankali cikin nutsuwarsa murya mai taushi ya furta."Fu'adh! Muje can Janfar Special Clinic karka ce zamu tsaya hanya a hanya ƙananun clinic."

"Fu'adh ya amsa da.
"Ok Sir"
Yah Boss ya amshi tsaleliyar iphone ɗinsa ya kira doctor na asibitin yace a tarbesu sun samu ƙaramin accident.
Duk da yayi driving cikin gudu sai da yayi tafiyar mintina 10 kafin su ƙaraso asibitin.
Wata irin haɗaɗɗiyar asibiti mai zaman kanta, tamkar a ƙasar Larabawa, tun daga ƙofar shiga zaka san wannan asibiti ba ta yaku bayi bace.

Suna shiga kafin Fu'adh ya gama parking ma har Nurses sun iso da gadon ɗaukan marar lafiya.
Norses ɗin suka ɗauketa suka kwantar a gadon ɗaukan marasa lafiyar aka yi ciki da ita.
Fu'adh ya zagayo yana shigowa motar ya zauna kusan Yah Boss yana kallonsa yana duba saƙo a Gmail da wayansa ta business.
Jin shigowar Fu'adh motar bata sa ya daina duba saƙon ba, a nutse cikin kamalarsa ya furta.
"Fu'adh! what do you want to say?"
Fu'adh ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin.

"Sir kuje gidan kayi breakfast ɗin, Ni zan tsaya anan naga yadda jikin nata zai bada. Ai daga can gun aiki zaka wuce, har an fara kiran ka masu jiranka police station sunada yawa Sir, ga meetings na jiranka ƙarfe 2: 30pm."

Lumsassun fararen idanunsa ya ɗago ya zuba wa Fu'adh na Seconds 10 kafin ya ɗauke kansa yana mayarwa akan wayan, can ƙasa² ya furta."No let's go back to the situation before the trip.
Mutum daraja garesa ta ya mun kaɗata kuma na tafi wani uzurin na barta koda bata da hankali ai dai mutum ce kamar kowa..."
Fu'adh ya zaro manya idanunsa masu haske yana ɓoye dariyarasa, da mamaki akan fuskarshi yana kallon Sir ɗin nasa yace.
"Mahaukaciya kuma Sir?"
Yah Boss bai kallesa ba bai kuma amsa masa ba, saboda dai shi baiga alamar hankali a gun ba.
Fu'adh ya yi gyaran murya sanin ba magana zai masa ba a hankali cikin kwantar da murya yace."Wlh Sir yarinyar nan ba mahaukaciya bane, saboda kayan jikinta duk ƙoɗewan su a wanke suke tass kuma akwai ƙamshi mai sauƙi a jikinta.
Maybe tana cikin wani tashin hankali ne wanda ya fitar da ita hayyacinta ta shiga gaban motar namu, saboda akwai tsananin tsoro a idanunta kafin faruwar hakan..."

Ya kai ƙarshen maganan yana ƙara tsare Sir ɗin nasa da ido, ko zaice wani abun.

A hankali cikin nutsuwarsa ya furta."You can see her body, Allah ya bata lafiya."

Fu'adh ya amsa da"Amin bari naje."
Ya ƙarasa mgnar yana buɗe motar ya fito tare da rufe masa motar.
Walid zai bisa yace.
"A'a kasan duk da baya so ba'a barinsa shi kaɗai."Yana gama faɗin haka ya nufi ciki.

Tunda aka shiga da ita ciki likitocin suka duƙufa dan ceto ranta.
Ba'a ɗauki lokaci sosai ba akayi sa'ar farfaɗowa da ita, amma koda ta farka cikin wani irin tashin hankali tana fizge-fizge tana kuka tana faɗin don Allah karka ɓata min rayuwa kuyi hakuri zan bar maku gidanku...
Ganin haka doctor Majid ya mata alluran bacci, a aka ɗaura mata drip, kafin ayi mata dressing goshin nata dan nan kaɗai ya samu rauni, firgicine ya sumar da ita.

Fu'adh yana zaune akan bencin da yake ƙofar room ɗin da aka shiga da ita.
Ƙaran buɗe ƙofar da akayi ne ya saka Fu'adh waigawa, doctor Majid ne ya fito wata Norse na biye da shi.
Da sauri ya miƙe yana faɗin.

"Dr Majid! Ya ake ciki? Ya jikin nata? Hope babu raunuka dayawa?"Dr Majid ya kalli Fu'adh yana basa hannun suka gaisa yace.
"Alhamdoulillah! Ta farfaɗo muje officer na maka bayani ina Sir ɗin yana mota ko?"

Fu'adh ya jinjina kansa yana biye da Dr Majid ɗin.Wani lafiyayyan office suka shiga ya haɗu sosai, sai ƙamshin Ac da ya cika office ɗin.
Dr Majid ya kalli Fu'adh yana faɗin.
"Bataji ciwo sosai ba iya goshinta ne sumar da tayi ta shiga cikin tashin hankali da firgici ne, in sha Allahu idan ta farka zata tashi normal saboda alluran dana mata, sai dai akwai abinda yake damunta saboda irin kalaman da naji tana faɗa cikin rasa hankalinta, kamar akwai wanda yaso yayi Raped ɗinta saboda sambatun da take tana cikin shock mai ƙarfi."

Fu'adh sosai yaji tausayinta ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Dr Majid ya faɗa masa a halin da suka ganta kafin tsautsayi ya gifta suka kaɗetan.
Ya ɗora da cewa.

"Yanzu ba matsala zamu iya zuwa mu dawo kafin ta farka ɗin? Tunda akwai norses masu kula da ita."

Dr Majid yace."Eh mana saboda alluran zata ma iya Kaita yamma tana bacci saboda ta samu nutsuwa jininta ya dawo normal, tunda ba riƙeta za'ayi ba iya goshinta ne kawai taji ciwon."
Fu'adh ya beƙa masa hannu yana faɗin.
"Thank you so much Dr Majid, zan yiwa Sir bayani sai na dawo, ai Za'a iya kawo mata abinci ko?"

Dr Majid yace.

"Yeah"
Sallama Fu'adh ya masa ya fice.

Yah Boss zaune yana amsa waya cikin harshen turancin da ya zauna bakinsa tamkar baya jin Hausa, cikin wata irin nutsuwa da class yake magana idanunsa a ƙasa bai kalli Fu'adh da ya buɗe motar ya shigo ya zauna kusansa ba.
Fu'adh yace.
"Walid! can we go, sir he is very hungry."

Cikin nutsuwarsa da kamewa ya yi sallama da wanda suke wayan, ya ɗago idanunsa masu lumshe da tsantsar haske ya kalli Fu'adh a hankali ya furta.

"What about her body? Anxiety didn't really creep in?Allah yasa babu wata damuwar right"
Ya idar da magana a taƙaice.
Dai-dai lokacin Walid yaja motar ya nufi gate dan barin asibitin.
Fu'adh ya sauke ajiyar zuciya baiyanan na har Yah Boss na zuba masa idanunsa masu tasiri akan mutum.
Fu'adh yace."Allah ya taƙaita wahala iya goshinta ne ya samu ciwon, anyi mata alluran bacci tare da wanda zasu rage mata zafin yace idan ta farka zuwa yamma zata warware sai sallama.
Amma Sir a bayanan Dr Majid tana cikin wata matsala babba saboda har ya kawo maganan anso yi raped ɗinta Allah ya kuɓutar da ita, shiyasa ta shiga cikin tsananin shock, tayi kamar ta zare, saboda yace tayi sambatu dayawa tana faɗin a rufa mata asiri ta tsira da mutuncinta..."

Yah Boss da hankalinsa yake akan wayansa iskar bakinsa ya furzar waje baice uffan ba, har kusan 4 minutes kafin a hankali ya furta.
"Allah Ya tsare gaba"
please investigate when she returns to her senses."
Fu'adh yace.
"Amin Sir, Ok in sha Allahu.
"A ƙaton haɗaɗɗan gate ɗin gidan nasu Yah Boss Walid ya tsaya yana zuba horn.

Gata aka buɗe musu Walid ya silala hancin motar cikin ƙaton gidan.
Yah Boss ya lumshe lumsassun fararen kyawawan idanunsa ya ɗan buso da iskar bakinsa waje.
A hankali yakai idanunsa akan tsadaddiyar agogon da take ɗaure akan tsintsiyar hannunsa.9:10am. Na safe, kansa y ɗauke daga kallon agogon ya maida akan Fu'adh anutse ya furta.

"Ba sai an faɗawa Maah da Papa ba."
Fu'adh yace.

"Sir please maybe zasu iya bata wani temakon."
Yah Boss bai bi ta kansa ba, yabar wayoyin gun Fu'adh ya riƙe wacce yake anfani da ita da family's Janfar ya fara ƙoƙarin fita daga motar sbd Walid ya buɗe masa ƙofa.
A nutse ya fito da dogayen fararen ƙafafuwansa waje.
Ma'aikatan gidan suka fara gaishesa cikin girmamawa, ya amsa yana tafiya cikin nutsuwarsa, ba ƙaramin kyau tafiyar tai masa ba Uniform ɗin tana bala'in masa kyau.
Kiran Umar ya shigo cikin wayansa.
Ɗaga kiran yayi ta Glass idanunsa, yana kai wayan kunnansa, bayan ya amsa sallama da gaisuwar ya nutsu yana sauraron abinda ƙanin nasa yake faɗa masa.

Juhainah a daidai wannan lokacin ta farka daga baccinta tana miƙa cikin quilt ɗin tana buɗe dara-daran fararen idanunta da baccin bai gama sakinsu ba.
Wata irin azabar yunwa ne ta tayar da ita daga baccin, ta zuro tattausan hannunta ta janyo wayarta tana duba lokaci.
Ganin ƙarfe tara ne da ƴan mintina ta yamutsa fuska tana kallon tarin missed calls ɗin wayarta har guda 9 Surayya ta mata calls 3 Ammar ya mata calls 4 sai calls ɗin yayanta Umar guda 2.Jajayen lips ɗinta masu kauri ta motsa tana murguɗa baki ta miƙe zaune ta janye quilt ɗin ta zuro ƙafafuwanta ta zura slippers mai taushi ta nufi bathroom daga ita sai ɗin guntun Jeans ɗin da ficiciyar rigar da bata rufe mata komai na jikinta ba.
Chapter 6 · 0% Book details