Sashe 102
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khairat ma sha Allahu sai gyara take sha, duk da bai kai na Juhainah ba, amman ta gyaru ciki da waje.
An zuba masu komai a gidansu an gama gyara ɗakin Khairat.
Washegari akayi kamu.
Juhainah ta saki jikinta anata shirye-shirye da ita.
Harda ita gun sakawa amarya Khairat lalle.
Ranan Lahadi aka tashi da shagalin bikin auren Khairat.
Ankon Juhainah ne aka saka Sbd Maah ta hana ayi wani Anko, amma Fu'adh ƴan gidansu sunyi tasu.
Wannan karon ba wanda Maah ta faɗawa bikin sai iya ƴan gari ƴan uwa.
Yau Yah Boss ba lokaci shi uban amarya shi uban Ango.
Bayan sallar azuhur daruruwan jama'a suka shaida ɗaurin auren tsakanin Fu'adh Tahir Yahaya Mai gold. Da Khairat Yakubu Abubakar Janfar. Anan gidan Yakubu Janfar.
Juhainah baki yaƙi rufawa tunda aka ɗaura auren take tsokanar Khairat.
Yanzu ma ɗakin cike da ƙawayen Khairat da ƴan uwa Juhainah ta shigo tasha kyau da Anko.
Hafizah ɗiyar Ruwaida mai kama da ita, ta amsa ta rungume tana mata wasa yarinyar tana dariya, tunda yanzu Babyn nada wata 4 tayi wayo, gata ɓulɓul.
Hanifah ta kalleta tace.
"Ma sha Allahu Autah wlh cikin ya maki kyau,..."
Ruwaida ta zaro idanunta tana taɓa Hanifah.
Juhainah ta juyo tace.
"Ciki? Cikin Wa kuma?"
Ruwaida ta miƙe ta kamo hannunta tana gyara mata rungumar Hafizah tace.
"Ki rabu da shirmen Hanifah je kiyi ronon ƴarki"
Aunty Sumy tace.
"Ke Hanifah me yasa Bakinki bai iya riƙe magana ba? Idan cikin ne ai ba cikin shege tayi ba ko? Kuma kiji da aikin da aka jiƙa miki ma kina zaune cikin duhu"
Hanifah tace.
"Don girman ALLAH kuyi haƙuri Aunty Sumy Wlh ban faɗa da niyyar wani abu ba, kuyi haƙuri"
Juhainah ta kalli Hanifah batayi magana ba ta fice rungume da Hafizah.
Saukowa downstairs tayi tana ta duba Maah cikin mutane bata ganta ba.
Ummah Hanifah ta washe baki zata mata magana ta zabga mata harara ta wuce tana faɗin.
"Na rantse da girman ALLAH idan Ɗiyata Hafizah tayi ko ciwon kai ajalin mutum nice..."
Jama'a dayawa sukabi Juhainah da kallo basu gane me take nufi ba.
Amma Ummah Sadiya tasha jinin jikinta ta ko haɗiye abinda taji akan Baby Hafizah.
Bedroom ɗin Maah ta nufa zata shiga zata fito.
Maah tace.
"Ma sha Allahu Autah kinga yadda Baby Hafizah take kama dake?"
Juhainah ta kamo hannun Maah suka zauna saman bed tana kwantar da Hafizah tace.
"Maah wai ciki gareni?"
MAAH tace.
"Inji wani mai shegen surutun ne?"
Juhainah tace.
"Hanifah tace wai cikin jikina ya min kyau, kuma Wlh inajin motsi Maah kalli fa yadda abun ya zama ƙato, kuma ga Auntynah Sumy can ta rufe Aunty Hanifah da faɗa"
Maah ta riƙe hannun Juhainah tace.
"Shi yasa na tsani Hanifah sam yarinyar batada kimtsi, zataji abinda ake ji indai mugun labari nada daɗi, ba mijinta yayi aure bata saniba. Uwarta ma bansan masifaffan da ya gayyato min ita ba.
Idan na faɗa maki gaskiya zakiyi haƙuri ki rungumi ƙaddara?"
Juhainah tace.
"Ai Ni yanzu Maah babu wani abu da zai sake daga hankalina bayan ayar dana gani, inada cikin ko?"
MAAH ta rungumeta tace.
"Eh Autah amma don Allah kiyi haƙuri ko dan Mamy da Surayya ma"
Fashewa tayi da kuka tana ƙamƙame Maah tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Maah cikin wannan mayaudarin fa"
MAAH ta shiga lallashinta da cusa mata son cikin har taga dai ta sauko ta haƙura ta amshi cikin, amma tace bazata ba Jamal ɗanta ko yarta ba, zata riƙe Abunta.
Maah tace ai daman bazasu bayar ba, sun isa ma a basu Baby.
A haka ta samu ta mata wayo, har ta sauko.
Ta ɗauki Hafizah ta fice, ta koma Stairs bedroom ɗinta gun Surayya da take can kwance.
Yamma lilis aka kai Amarya gidanta da yake anguwar Aliyu Mustapha.
Bayan nasihar iyaye sai da Yah Boss ya yi wa Khairat nasiha Sosai Sbd ya san halin Fu'adh Baida matsala kamar yadda itama batada Matsala.
Khairat taci kuka kamar zata haɗiye zuciya tanaji tana gani tabar Maah da Papa da Juhainah, Suhaima Al'amin da sauran ƴan uwanta da suke gidajan su.
Aunty Sumy kanta saida tayi hawaye.
Gun Kai amarya harda Juhainah tabi su Aunty Sumy.
Yah Boss abokin Ango daga shi sai Fu'adh suka tafi siyan Kaza da abubuwan da ake kaiwa amarya.
Dare ya fara ƴan kawo Amarya duka sun tafi, harda ƙawayenta, Yah Boss ya hana Fu'adh su tafi da wuri, wai ya tsani siyan bakin nan, idan sun gaji dole kowa zai bar masa matarsa ya tafi.
Ai kuwa duk an watse Shahidah ƙawar Khairat tace ai gobe sai ta dawo amsar kuɗin su na siyan baki, har Juhainah na masu dariya.
Ya rage daga Khairat sai Juhainah, daman Surayya bata zo ba, Batajin daɗi zazzaɓi yake damunta, tun Jiya gun bikin ma ɗakin Juhainah ta wuni kwance, Maah sai nan-nan take da ita.
Harda kira Dr Nafisa ta dubata.
Surayya ko harda tsoron haɗuwa da take yi da Hanifah ya sakata kwanciya.
Bata san Hanifah bata san komai ba.
Anutse Fu'adh yayi parking a bakin gate ya kalli Yah Boss yace.
"Thank you so much My Boss, Allah ya saka da alkhairi,yabar zumunci"
Yah Boss a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Ameen Amin, fito na wuce Malam"
Fu'adh yace
"Ka jira ƙanwarmu ta fito Khairat tamin message tana nan bata tafi gida ba."
Yah Boss bai ce komai ba yana jiran Fu'adh ya fita.
Gaskiya ma sha Allahu gidan Khairat ya haɗu iya haɗuwa.
Yayanta ya narka mata dukiya tun daga parlourn zaka fahimci haka.
Juhainah tana zaune ta fara hamma tace.
"Gaskiya Aunty Khairat bacci nakeji wa zai maidani gida tunda Yah Fu'adh ba zuwa zaiyi ba"
Khairat zatayi magana Fu'adh ya shigo bedroom ɗin da sallama.
Khairat da sauri ta rufe fuskarta da mayafinta.
Juhainah ta amsa sallamar tana miƙe wa tace.
"Yah Fu'adh sannu da zuwa, don ALLAH muje ka ajiyeni gida"
Fu'adh yana murmushi idanunsa akan Khairat yace.
"Ina godiya Ƙanwata nawa kuɗin siyan bakin, da fuskar my heart?"
Juhainah tace.
"Kawo dubu hamsin ma ni ta isheni, amma su Aunty Shahidah sun ce gobe sai sun dawo siyan baki fa!"
Fu'adh daman iya dubu hamsin ɗin ce a aljihunsa ya zaro yana murmushi ya beƙa mata, yace.
"Ga ta, su kuma ina jiran su gimbiyata tafi ƙarfi ko nawa zan biya, je parlour ki jirani"
Juhainah ta amshi dubu hamsin tana faɗin.
"Iye ƴan soyayya toh Nagode gobe zan sha ice cream sosai na siyo lemon tsami dayawa"
Ta faɗa tana wucewa zuciyarta cike da tausayin Khairat, dan tasan masifar azabar da take cikin daren Farko.
Fu'adh a hankali ya ƙarasa bakin katafaren Bed ɗin Khairat, ranƙwafowa ya sanya hannayensa ya buɗe fuskarta.
"Wow tsarki ya tabbata ga Ubangijin wannan hallitar matata Khairiyya"
Rungumeta yayi ya sauke ajiyar zuciya ya kamo fuskarta ya manna bakinsa akan nata, ya sakar mata sumbata ya lashi laɓɓanta ya mata raɗa a kunnenta.
"Bani minti biyar ina zuwa ɗiyar Manyan mutane ƙanwar babban mutum, wanda BANIDA kamarsa duk duniya.
Dole ne dukkan abinda ya shafesa na basa kulawa da soyayya da ƙololuwar Ƙauna."
Ya ƙarasa maganar ya Saketa yana murmushi, ya fice.
Khairat ƙirjinta wani irin bugu yayi tsoro ya kamata, ƙwalla taji ta taru cikin idanunta.
Juhainah zaune tayi parlour tana kallon manya² ledojin da suke ajiye akan Center table, ta tuna daren aurenta zuciyarta ta karaya sai hawaye.
Ɗan cikinta ya fara motsi ta sanya hannunta tana shafawa ta sauke ajiyar zuciya.
A hankali tace.
"Ya Allah ka bani ɗa ko Ƴa masu albarka, tunda nayi biyu babu ba Jamal ba Yah Boss hummm! Allah ka bani miji nagari idan na haihu, kai bana auren ma zanyi karatuna na raini abinda na haifa..."
Hawayen fuskarta ta goge zuciyarta na zafi fushinta na sake hauhauwa ba dalili.
Fu'adh ya fito yana tsokanarta yaga fuskarta shafe da toka, bakin halin yazo.
Ai bai sake magana ba, yayi gaba yana faɗin.
"My sister muje a ajiyeki"
Miƙe wa tayi tana ɗaukan Bag ɗinta kuɗin da Fu'adh ya bata a hannunta tabi bayansa.
Yah Boss zaune cikin mota waya yake hankalinsa kwance.
Fu'adh ya buɗe mata ƙofar.
Yah Boss ta gani sanye da uniform ɗinsa wanda kawai ra'ayin sakawa yayi, ta masa masifar kyau, waya yake hankalinsa kwance.
Fuska ta sake kamewa ta juya tana faɗin.
"Yah Fu'adh kaje kawai, zan samu keke napep idan nayi gaba, anguwan naku ne shiru layin ɗan rakani gaba"
Fu'adh yasha gabanta yana faɗin.
"Haba My sister Sir ne fa a motar kizo ya ajiye ki gida"
Cikin tsiwa tace.
"Toh bana son shiga motarsa ana dole ne? Kaje bana son rakiyar taka, abinda zai cinyeni ya cinye ni mana so what?"
Ta ƙarasa maganar tana wucesa fuuu fuska a turɓune.
Fu'adh ya iso gun Yah Boss yana buɗe ƙofar yace.
"Sir wannan yarinya ta ƙaro masifa fa, ta fa tafi wai bata so ka kaita"
Yah Boss yayi sallama da wanda suke wayan yana kallon Fu'adh a hankali cikin kamewarsa ya furta.
"Good night kaje ciki kawai, idan bata bini gida matsayin yayanta ba, zata bini matsayin hukuma ina sanye da uniform dolen ta."
Ya ƙarasa maganar yana kunna motar anutse yaja yabar ƙofar gidan Fu'adh.
Fu'adh ya ƙyalƙyale da dariya ya juya ya shiga gidansa ya rufe ƙofar...
[03/04 14:22] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
*Bismillahir Rahmanir Raheem*
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx
_💃🏻Masoyan JUHAINAH Kuci Gaba Da Danna Min Followers, Da Kadan-kaɗan Zaku Dinga Samun Tsofaffin Books Ɗina, A Channel Ɗin. Inada Tabbacin Zasu Ƙayatar Daku._
*🕌Juma'ah Mubarak🕌*
*Page 52*
Hanifah
Tunda ta dawo daga gun bikin tayi wanka ta kwanta a parlour, yau sama² take jinta a buƙace take.
ALLAH ya sani tayi haƙuri wata biyar babu miji a kusanta, haka babu waya mai daɗi da zata rage mata kewarsa.
Saboda ba koda yaushe yake samu network ba.
Kamar daga sama taga kiran Nasir ya shigo.
Da sauri ta daga ba wani jan aji, tace.
"Assalam Masoyinah I miss you kewa tana damuna, yau an samu network kenan?"
Daga can Nasir ya gyara zamansa a hankali yace.
"My wife yanzu² aka samu network tun ranan, hope kina lafiya?"