← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 113

Sashe 110

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


Ranan asabar weekend ne, su Juhainah dasu Suhaima gidan Aunty Sumy suka tafi, sai da akayi sallar la'asar suka tafi gidan Khairat sai bayan sallar isha'i Fu'adh ya maida su gida.

Juhainah rayuwar Auntynta Khairat da Fu'adh tayi masifar burgeta.
Washegari Lahadi Juhainah
Wuni tayi tana bacci, shiyasa da dare yau idanunta tar batajin bacci, har yara suka haye Stairs sukayi kwanciyar su, tana parlour, Maah nan ta barta taje tayi kwanciyarta Sbd tasan batajin baccin.

Misalin ƙarfe 11:53 na dare

Juhainah zaune parlour ta miƙe ƙafafuwanta saman Chair, tana kallon Tv India Hausa, bata cika kallinsu ba, yanzu ma Film ɗin ya mata daɗi sosai tana cin dariya, Vijay thalapathi na bata dariya a Film sosai Sbd ya iya barkwanci.

Zamanta ta gyara tana ɗora hannunta saman cikinta da ya ƙara girma, motsi ne yake ma yanzu.

Wayarta ta ɗauki ringing ta kalli screen ɗin wayan.
Yah Boss ne.

Baki ta turo gaba kamar karda ɗauka sai ta gaza jurewa ta ɗauki wayan.
Sbd tafi sati bata gansa ba, kuma bai kirata ba.
Mafi akasari lokacin da zai zo da safe tana school, wani lokacin da dare kuma tayi bacci, tunda yanzu bata iya daɗewa farke.

Picking call ɗin tayi ta saka wayan Handsfree ta ajiye akan cinyarta, a hankali tace.
"Assalamu alaika"

Yah Boss daga can yana zaune parlour da na Stairs ya amsa sallamar, can ƙasa ya furta.

"You miss me a lot, that's why you greeted me, right?"

Cikin tsiwa tace.

"No, honestly I forget about you in my world."

Sansanyan ƙaramar murmushi ya sakar mata ta wayan, sai da ta lumshe idanunta.

A hankali ya furta.
"Seriously?"

Kai tsaye tace.
"Eh, lafiya ka kirani yanzu a tsohon daren nan?"

Yah Boss a hankali ya furta.
"My sister nafi sati bamu gaisa ba, ban ganki ba, ai dole na nemi Ƙanwata.
Hope kina lafiya?"

Shagwaɓe fuska tayi tace.
"Nima ban saniba ko ina lafiya"

A hankali ya furta.
"Kina lafiya nagane hakan daga muryanki"

Baki ta cinno gaba tace.
"Ba wani nan, ka damu dani ne? Ko ɗan Orange ɗin ma ka fasa kawo min sai Yah Mustapha da Yah Umar suke kawo min"

Hannunsa akan System a hankali ya furta.
"Ai duk ɗaya ne ni da su, kuma waye ce miki bana kaiwa?"

"Hummm! Ban saniba Ni Yah Boss idan na haihu Gombe zan koma da karatuna nabar maka garin"

Kai ya girgiza a hankali ya furta.
"No! Anan dai Yola zakici gaba, alright"

Kukan shagwaɓa ta sakar masa ba dalili tana faɗin.
"Bana so ai ba'a dole..."

A hankali ya furta.
"Aunty Maman Baby ina zaki dinga yawo da Baby ƙarami? Kici gaba anan har zuwa yaye, idan waje ma kike so zakije, kukan ya isa alright"

Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, a hankali tace.
"Kirani video Call toh"

Can ƙasa² ya furta.
"Kinaji Aunt Bilkisu banida data, sai gobe..."

Katse shi tayi tana faɗin.

"Sbd ka ɗauke ni mahaukaciya ko? Gidanka ba WiFi bane, shine zaka ce min bakada data?"

Numfashi ya furzo a hankali ya furta.
"Baya yi ki yarda"

Fushi tayi ta kashe kiran dan ta ɓata masa rai.
Ai kuwa bai sake kiranta ba, tsawon kwanaki masu yawu kuma basa haɗuwa da gangan yayi hakan Sbd ta Nutsu ta fasa kashe masa kira baya ƙaunar hakan acikin rayuwarsa.


Sannu-sannu cikin Juhainah har ya shiga watan haihuwa.
Yah Boss yana karɓar hukunci bai san me ya mata, shi dai baya son ya mata abinda zai sakata damuwa dole yake dannewa.
Ɓangaren su Mamy kakaf duk abinda ake nema idan mace zata haihu babu abinda basu siya ba.
Hakan ya faranta ran Maah da ƴaƴanta.

Surayya harda Anko ta fito da ita wanda zasu saka ran suna, wanda duk an siya Hanifa nacen sake baki bata saniba.
Ga shi har yanzu Nasir ba'a samunsa, amma Maah sun saba haka ne wani lokacin sai yayi wata uku ba'a samunsa, shiyasa ba wanda ya tayar da hankalin da anata masu addu'a dai.

Tunda Juhainah aka bata sati biyu a asibiti ta fasa zuwa school Sbd tayi nauyi sosai, cikin yayi wani irin girma kamar ba cikin farko ba.

Yau ta kama juma'a tun asuba Juhainah take karɓa gashi, naƙuda take sosai.
Amma wani ikon ALLAH tayi muguwar jarumtar da ba'a taɓa zato ba.

Ko Maah da suke ɗaki ɗaya bata sani ba.
Sai kusan ƙarfe 8 azabar ta fara fin ƙarfinta, da kanta ta shiga kiran Maah.
Maah tana shigowa taga Juhainah ta gama zufa tana dafe da ƙungunta.
Da gudu tazo ta kamata suka fito tana faɗin.
"Autah Allah ya buɗe idanu lafiya"

Suna fitowa Khairat da Fu'adh suna shigowa.
Maah tace.
"Yawwa Alhamdoulillah! Fu'adh kamata muje mota, babu kowa sai Ni ɗaya

Fu'adh sama ya ɗauki Juhainah Khairat tabisa da gudu.
Maah ta koma ta ɗauko dukkan abinda ake nema Labour.

Khairat ta zauna kusanta a gidan baya, tana riƙe da ita Maah ta shigo suka sakata tsakiya.
Fu'adh yaja motar suka tafi.

Suna isa Special Clinic Janfar, aka amshi Juhainah aka shiga Labour room.

Khairat ta riƙe hannun Maah tace.
"Maah a kira Yah Sadiq da Aunty Sumy da su Mamy."
Maah tace.
"Nafison sai ta sauka lafiya kar tayarwa da kowa hankali..."

Fu'adh ya masu sallama ya tafi Maah tace kar ya faɗawa Yah Boss har ta haihu.

Ana shiga da Juhainah ba'a fi mintina goma ba, norse ta fito ta amshi robar kayan ta koma.
Juhainah ana amsar gashi amma Sbd abinda yake ranka baka mantawa.
Daidai kan ɗa zai fito ta rantse idanunta cikin dauriya ta buɗe bakinta tace.

"Ubangiji kaine tsaye da kanka ba ɗan aike ba, ya ALLAH idan akwai ɓoyayaan Al'amari tsakanina da Abubakar Janfar ka gaggauta bayyana shi, kasa in zama Matarsa na jure dukkan abinda zai biyo baya, Ya Raheem ina roƙon ka, idan akwai aure tsakaninmu ka matso mana shi cikin gaggawa, idan babu Ya Ubangiji ka cire min wannan ƙaunar danake masa, kabani miji nagari wanda zanso shima ya soni tsakani da ALLAH.."
Tana rufe baki kan jariri ya danno a guje.
Dr Suhailat tace.
"Wow! Ma sha Allahu, an samu Baby girl"

Ai Dr Suhailat bata rufe baki ba wani kan ya fara ƙoƙarin fitowa.
Juhainah ta runtse idanunta tana karkarwa jiki, wata irin azaba take ji, ciwo ne da bata taɓa jin irinsa ba a duniya.
Dr Suhailat tace.
"Daure Juhainah, yi nishi kiyi ta kiran sunan ALLAH"

Juhainah tayi nishi da ƙarfi tana tana faɗin.
"Ya ALLAH!"
Sai kan baby ya danno.
Itama macace, ma sha Allahu kyawawan yara sunada girma sosai bazaka taɓa cewa wannan siririya mai ƙananun shekaru ta haifesu ba.

Ai kuwa a tare suka saki wani irin kuka da ƙarfi, suna shura ƙafafuwansu.
Cibiyarsu ɗaya ce, kamar su ɗaya basu da banbanci da Jamal kamar yayi kaki yaran sak shi suka fito ubansu.
Cibiya akan yake.

Juhainah ta bugu sosai ga shi ta ƙaru, Sbd yaran manyan ne.
Dr Suhailat Anan take ta fara mata ɗinki, tana jin azaba amma haka ta runtse idanunta tana kiran sunan Allah, da ƙara ganin girman Maah, bata taɓa sanin haka uwa take shan azaba ba sai yau, haƙiƙa ta jinjina wa uwa a duk inda take a faɗin duniya.
Norses biyu suka tafi dan gyara Babyn, a saka masu kaya.

Norse ɗaya da gudu ta fice zuwa bada labarin abin farin ciki gun su Maah......
[09/04 10:10] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*Alhamdoulillah! End Book One*

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

Last Page Book One free
*Page 56*

Maah ana buɗe ƙofar ita da Khairat suka nufi gun Norse, ganin tana washe baki.
Maah tace.
"Alhamdoulillah! Wannan farin cikin naki an sauka lafiya ko?"

Norse tace.
"Maah an sauka lafiya Twins mata wallahi kamar ba ita ta haifa ba, suna can ana gyara su..."

Maah ta riƙe hannun norse tace.
"Don ALLAH da gaske Bilkisu ta haifi ƴan biyu yanzu a wannan kawotan da mukayi kuma daga tsatsonta? Allahu Akbar kudirar Ubangiji nada yawa, Alhamdulillah Allah shine abin godiya, za mu iya shiga ganinta yanzu?"

Norse tace.
"A'a ɗinki ake mata sai zuwa anji ma dai Maah, bari yanzu za'a fito maku da Baby's ɗin."

Khairat baki yaƙi rufawa sai murna take, ta ciro wayanta ta kira Yah Boss.
Lokacin yana tsakiya da meeting, amma ganin number Khairat ya saka shi dole ɗaga kiran, kafin tayi magana cikin kamewarsa ya furta.
"Assalamu alaikum, My sister ina tare da baƙi har ajima."

"Da sauri Khairat ta tari numfashin sa tace.
"Yah Sadiq Juhainah ta haihu yanzu Twins duk mata muna asibiti."

Yah Boss labarin yazo masa a surprise, wani irin daɗi yaji, tamkar shine uban cikin, da wani irin sauti mai daɗi anutse ya furta.

"Baarakallahu laka fil-mawhuubi laka, wa shakarta-l-waahib, wa balagha ashuddahu, wa ruziqta birrahu.
Thank you my sister Khairat, zan baki goron albishiri bye."

Ya Ƙarasa maganar yana katse kiran.

Maah ta riƙe hannun Khairat tana faɗin.
"Zo mu zauna tunda hankali ya kwanta, ki kira min kowa da kowa, ni ko wayan ban ɗauko ba."

Khairat ta zare hannunta tace.
"Toh Maah bari na kira Fu'adh na sanar da shi kafin wasu."

Ta ƙarasa maganar tana kiran Fu'adh ta matsa daga kusan Maah.

MAAH ta tafa hannayenta tana faɗin.
"Khairat mai tsananin kunya da kawaici aure ya buɗe mata idanunta tar, oh ni Zainabu"

Fu'adh yana ɗauka ta laɓe inda Maah bata ganinta a hankali tayi masa sallama tana faɗin.
"My heart muahhhhh I love you."

Fu'adh yana driving ya rage gudu a hankali yace.
" Muahhhhh love, I love you too My heart Baby ƴar baiwa ta, ya Juhainah?"

Khairat cikin farin ciki tace.
"My heart Autah ta haihu Twins, mata"

Fu'adh sai da ya taka Burki da ƙarfi yana faɗin.
"Wai Juhainah? Baby's har biyu, ALLAH mai yadda yaso, ma sha Allahu, Allahumma Barik, zan shigo anjima Company zan leƙa"
Khairat tace.
"Ok my heart bye Allah ya tsare"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran, ta dannawa Aunty Sumy kira.
Tana ɗauka tace.
"Albishirin ki Aunty Sumy? Juhainah ya'ya biyu mata gamu asibiti"
Chapter 110 · 0% Book details