← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 113

Sashe 22

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anutse ya fito yana ƙamshin gel ɗin da yayi wankan, da ƙaton towel ɗure a ƙugunsa faffaɗan ƙirjinsa mai yalwar gashi yana ɗigar da ruwa.
Ƙaramin towel ɗin hannunsa ya fara goge jikinsa, ya idar ya murza body lotion mai sanyin ƙamshi, ya buɗe ƙatuwar Wardrobe ɗinsa ya ciro Jallabiya irin ƴan Sudan ɗin nan Brown ya saka har ƙasa ta masa kyau, kana ganinta kasa akwai tsada saboda yadda take walƙiyar kyau.
Turarensa mai rikita mata har Mazan saboda ɗaɗinsa ya fesa ya gyara sumarsa da ta hargitsa.

Slippers Brown kala mai kyau da tsada ya jefa a dogayen fararen ƙafafunsa alamar babu idan zai fita yanzun.

Anutse ya juyo yana takowa a hankali ya zubawa Juhainah lumsassun fararen kyawawan idanunsa.
Gashinta duk ya barbaje ya rufe mata kyakkyawar fuskarta.
Pillow ya ɗauko mai taushi sai ƙamshinsa yake tashi a jikin pillow'n ya ƙaraso ya ajiye pillow ya ɗago kanta ya ɗora akan pillow ya kamo gashin ya naɗesa ya ƙullesa ya gyara mata kwanciya, duk tayi zufa sosai kasancewar bata son zafi ko kaɗan, tunda bai kunna Ac ba.
Remote ɗin Ac'n ya ciro daga gun sarƙafesa ya kunna mata A'c ya maida remote ɗin ya ajiye.
Ya juya ya nufi parlour.
Kallon picture ɗin Khadijah yayi tana dariya rungume ajikinsa.
Idanunsa ya lumshe, gun picture ɗin ya nufa.
Cirosa yayi ya saita bakinsa saitin bakin Khadijah ya sumbata a hankali ya furta.
"Allah ya jiƙanki da rahma Dijah"

Maida frame ɗin yayi ya juya ya buɗe ƙofar parlour.
Rufewa yayi amma yabar key ɗin ajiki.
Yana tsakiyar taka Steps Kiran Fu'adh ya shigo Phone ɗinsa.
Bai ɗaga ba yaci gaba da sauka.

Suhaima zaune kusan Fu'adh tana cin indomie, yayin da Al'amin yanata yawo cikin motarsa a ƙaton parlour.
Yah Boss yana takunsa mai wani irin burgewa hannenysa zube cikin aljihun riga, ya zubawa Al'amin lumsassun idanunsa.
A hankali cikin nutsuwarsa ya furta.

"Babies baka gajiya ko?"

Dariya Al'amin yayi yana ɗagawa mahaifin nasa hannu yace.
"Bye My Dadd Saudi Arabia zanje yau"

Fu'adh ya kwashe da dariya yana kallon Suhaima, yake faɗin.
"Babies kina zuwa Saudi Arabia a mota?"

Miskilar ƙarshe takai indomie bakinta tana yamutsa fuska a hankali ta furta.
"Uncle Al'amin baya yi ai, shine ba'aje da shi ba, Ni dai anje dani sau biyu"

Yah Boss yana ƙoƙarin zama ya furta.
"Oh! Guri kike yiwa my Amiin? Fu'adh ka zama sheda Umrah December zanje da yarona"
Ya ƙarasa maganar yana kallon Suhaima.
Baki ta mele alamar shagwaɓa, shegen zafin kanta ya hanata cewa uffan.

Shi ma bai sake magana ba, ya kalli Fu'adh a hankali ya furta.
"Fatan ka sanar da Jamilu akwai baƙo?"
Fu'adh yace.
"Yas tuntuni ma, ai najika shiru na kira ka"

Yah Boss baice uffan ba, ya miƙe yana zuba hannenysa cikin aljihun jallabiya ya fara takunsa a nuste yana kallon Al'amin yana gudu cikin motarsa tsakiyar filin parlour.

Suhaima ta ajiye tangaran ɗin da take cin indomie ɗin ta miƙe tana sauri ta kamo tsintsiyar hannun Yah Boss dake cikin aljihunsa tana faɗin.
"My Dadd waccan bak'ar matar me take yi a ɓangaren ka?"
Yah Boss ya gyara tsayuwar sa yana zuba mata lumsassun fararen idanunsa, a hankali ya furta.

"Babies kinada matsala da ita ne?"

Lumsassun fararen idanunta irin nasa ta buɗe sosai kamar zata fashe da kuka ta ɗaga kanta alamar Eh.

A hankali cikin zazzaƙar muryansa ya furta.
"Ok matsalan me kike da shi a kanta?"

Ƙasa tayi da idanunta saboda yadda ya tsare ta da idanunsa, babu wasa bazata iya faɗin abinda yake ranta ba matuƙar tana kallon mahaifinta mai cike da kwarjinin da Allah ya basa tsoronsa zai hanata yin magana, amman da ta ɗauke idanunta akansa.

Kai tsaye ta furta.
"Na tsaneta bana son ganinta My Dadd"
Idanunsa akanta a hankali ya furta.

"Why Babies?"
Suhaima kanta ƙasa ta furta.

"I don't want her to stay and fall in love until you marry her"

Ta ƙarasa maganar tana sakin kuka ta rungumeshi.
Yah Boss baya ƙaunar kukan Suhaima ko kaɗan, har cikin zuciyarsa yake jin kuka.

Rungumeta yayi sosai cikin jikinsa yana shafa bayanta, a hankali ya furta.
"Bab Suhaima! Saboda ita kika kuka?"
Da sauri ta ɗaga kanta.

Janyeta yayi daga jikinsa ya kama hannunta, suka nufi gun Turkish Chairs ya zauna yana zaunar da ita kusansa ya kama hannayenta, da hannu ɗaya hannun ɗaya ya zaro handkerchief ya goge mata fuska, a hankali ya furta.
"Bab Suhaima! Ke ganin ki wannan matar tayi kalana da har kike tunanin zan sota na aureta?"
Kallonsa tayi tana girgiza kanta, a hankali tace.
"A'a My Dadd naji tsoron ganinta a wannan ɓangaren Duk da tana nan ƙasa amma nasan wanda zaka sauke a wannan ɓangaren ba ƙaramin daraja garesa ba,
my Dadd ni dai ka sallameta bana sonta, bana son ka auri wacce zata rabani dakai Dadd tunda babu Ammy ta tafi."
Ta ƙarasa maganar tana sake sakin kuka.
Yah Boss ya buso iskar bakinsa yana furta.
"Ya Salam! Ya Allah Kasan halin da nake ciki tunda na rasa Khadijah"

Ya ƙarasa maganar yana rungumeta yana buga bayanta ya mata raɗa a hankali.

"Babies Nima Wlh bana sonta har cikin zuciyata, ni mata masu kyau da class ma basa gabana bare wannan kiyi shiru, wlh bazan taɓa son abinda bakya so ba, aikin ma da zan ɗauketa na fasa tunda bakya so, because ni kune farin cikina babu anfanin na ajiye abinda zai ɗaga min hankalin ɗiyata, daman Juhainah ma bata sonta, so amma duk ranan da kika samo wacce ta miki a ranki kike son na zauna da ita, ki faɗa Kai tsaye zan auro maki ita, amma ki sani ba dan so ba, sai dan ki zauna da Mama ni kuma na kare mutuncina a waje..."

Rungumesa tayi tana murna tana sumbatar kumatunsa tana faɗin.
"I love you My Dadd thank you so much shiyasa nake sonka sosai Wlh Dadd Janfar"
Dogon hancinta irin nasa yaja yana sakin wani irin tsadaddan murmushin da ba kasafai yake yinsa ba, ana ɗaukan lokaci Sosai, mafi akasari su yake yiwa shi.

Fu'adh idanunsa akansu Sam baiso irin hukuncin da Yah Boss ya ɗauka ba, akan me zai biya ƙaramar yarinya, yace ba zai aure ba, sai ranan da ta samo masa matar da take so dan raɗin kanta kuma badan soyayya ba zai aura sai dan ya faranta mata ranta, da kuma mutuncin kansa a waje.
Kamar zai yi magana ya fasa saboda yasan kafiya da taurin zuciya irin nasa tunda ya furta hakan an gama, abinda yake cikin zuciyarsa ne ya faɗawa ƴarsa da yake tsantsar ƙaunarta.
A hankali Yah Boss ya furta.
"Fu'adh! Muje na gana da Yaron can, yanada kyau yau na sallami Juhainah babba, sai direba ya kaita har garinsu."

Fu'adh da takaicin Yah Boss ya cika masa ciki, baice Komai ba ya miƙe har sai da suka fara tafiya kusan fita ƙofar parlon Fu'adh yayi gyaran murya yana faɗin.
"Sir yanzu Suhaima zata iya zaɓar maka matar ƙwarai kuwa? Kuma wadda zata jure rashin soyayyar ka a yadda kake nan, Allah ya haɗaka ta ko ina, ta zauna dan ya'yan ka?"

Yah Boss ya ɗan kallesa yana watsa masa lumsassun fararen kyawawan idanunsa, yanayin fuskarsa bazaka gane yaji daɗin maganar ko bai ji ba, ya juya baice uffan ba yana takunsa a nuste.
Dan shi Fu'adh mamaki yake basa, yadda yake son takurasa yayi aure, dan shi sam matan ma basa gabansa.

Ɓangaren Juhainah babba tun lokacin da Suhaima ta korata ɗaki, ta shiga ta zauna tana hawaye, na tausayin rayuwata da irin jarabawar da take gani.
Hannenta ta ɗaga sama tana faɗin.
"Ya ALLAH kasan halin da nake ciki ka fitar dani, idan komawa Misau itane alkhairi ka fitar min da soyayyar Ahalin wannan gida.."

Jamilu ya kaiwa Ammar abubuwan motsa baki tare da ruwan gora me sanyi da juice, har mamakin irin wannan karrama wa yayi.
Yana zaune yana danna wayarsa Yah Boss da Fu'adh suka shigo da sallama.

Amsawa yayi yana gyara zamansa akan kima-kima kujerun parlour.
Zama sukayi Ammar ya sake gaishe su.
Yah Boss yayi gyaran murya cikin kamewarsa da tsare gida ya furta.

Ammar! Duk maganar da kayi a waya akan Juhainah nine na ɗauki wayan naji, dan haka na gamsu da ƙaunar da kake mata, so abinda nake so dakai yanzu ka shirya aure?"
Ammar wani irin bala'in sanyin daɗi ya ratsa zuciyarsa, cikin rawar murya da daɗin da ya gama kashesa yace.
"Eh brother Allah ya ƙara maka girma na shirya"

Yah Boss ya kafesa da lumsassun fararen kyawawan idanunsa.
A hankali cikin basarwasa ya furta.
"Ok amma tanada matsala jinnu sai kamin alƙawarin zama da ita duk runtsi duk wuya, babu maganar sakar min ƙanwata saboda larura, idan kuma kasan bazaka iya ba tun wuri ka haƙura, bamu gaji da ita ba, za'a samu wani wanda zaiji da komai nata"

Ammar kamar zai yi kuka yace.
"Wallahi tallahi brother inasonta koda duka take zan shanye, kuma koda idan sun tashi tana wata batasan inda kanta yake ba, zan aureta zan kula da ita, nayi wannan alƙawarin"

Yah Boss ya kalleshi na kusan minti ɗaya, yana nazarinsa.
Iska mai ɗumi ya furzo daga bakinsa, a hankali ya furta.
"Ok Thank you, gobe zanyi tafiya jibi zan kira in sha Allahu, ina son ka bani adresse ɗin gidanku, Saboda aure ake magana dole zan ɗanyi bincike akan gidanku da kai kanka"

Ammar sanin iskancin sa na ɓoye ne bai damu ba, Saboda shi ɗin kamilin filine kowa ya shaida haka.
Kai tsaye ya ciro katinsa wanda yake ɗauke da address ɗin gidansu ya beƙa masa ya amsa yana faɗin.
"Thank you zaka iya tafiya bazaka ganta ba, tana fama da jikinta yanzu, ka tsaya da nemanta zan nemeka da kaina"

Ammar yayi godiya ya tafi.
Fu'adh yayi murmushi yana faɗin.
"Yaron nan fa ya zauce akan son Juhainah dayawa kaga yadda ya ruɗe sosai, amma gaskiya yanada nutsuwa sosai."

Yah Boss ya kalli Fu'adh yana miƙewa ya beƙa masa katin, a nutse ya furta.
"Ba zamu iya ganewa a haka ba, sai na bincika, mutane masu kirki a fuska nawane, kai nifa idanunsa na hango wani abun, kai bazaka gane ba saboda ba karatun kayi ba, kaje a fara bincike kawai."
Chapter 22 · 0% Book details