← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 113

Sashe 12

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Fu'adh ganin tanada niyar basa labarinta yayi saurin katse ta ta hanyar faɗin.
"I'm sorry ki daina kukan ya isa, ki sha maganin sai mutafi gida daga baya zamuyi magana zuwa gobe sai mu maida ke Misau ɗin."
Tissus ɗin da yake ajiye akan ƙaramin table ɗin ta beƙa hannunta ta ciro ta goge hawayen.
Maganin ta ɓallo ta zuba cikin bakinta ta bude goran ruwan tasha sosai ta ajiye. Ta miƙe tana tattara kayan da taci abincin, tana sakawa cikin Basket, ta shiga gyara gadon.Tsaf ta gyara komai.
Fu'adh kallonta yake yana jinjina ƙoƙarinta, kana ganinta kasan bata son jiki, haka ma bata da girman kai, duk yadda yayita kyakkyawa mai kyan diri ta riƙe kanta ta iya talaucinta tana neman halak ɗin ta hanyar aikatau.
Basket ɗin yake ƙoƙarin ɗauka yana faɗin"Juhainah! Zamu iya tafiya."
Da sauri ta ɗauki Basket ɗin tana faɗin."Bari na riƙe muje"
Kai ya jinjina yana nufar ƙofar fita.
Da ƙananun kyawawan idanunta masu haske take bin asibitin da kallo, wani irin tsari da kyau asibitin gareta, idanunta ta tsayar daga kallon saboda karta shagala taje tayi tuntuɓe.
Ganin jibgegiyar motar da aka buɗe mata baya Fu'adh yace ta shiga, sai da wani irin yawu ya sarƙe mata a maƙoshinta.
Ko amarfaki bata taɓa tunanin zata shiga irin wannan motar Ba, da sai finafinan na India ko labarawa take ganinsu.
Shiga tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya jin wani irin sanyi da ƙamshi na ratsa hancinta, ƙamshin da take shaƙa wani irin daɗi yake mata tanajin wata irin kasala kamar bacci ma yake son kamata.
Gyara zamanta tayi tanajin kamar ƙamshin daga side ɗin ba kowa zaune yake tashi.
Gaza haƙuri tayi ta ɗan karkato da fuskarta tana buɗe hancinta, ai kuwa taji ƙamshin ya sake cika mata hancinta, idanunta ta sake rufewa tanajin ƙamshin na mata mugun daɗi.
Sai da motar ta hau bakin titi ta buɗe idanunta tana kallon titi tana sake godiya ga Allah da ya haɗa ta da mutane nagari.
Acikin zuciyarta tace.
"Ina ma su ɗauke Ni aiki na temakawa ummata, yanzu Misau zan koma babu wani mai temaka mana? Ga shi ina tsoron shiga gari neman aikatau na sake faɗawa mugun hannu.
"Duk acikin zuciyarta take wannan magana hawaye na gangaro mata akan kyakkyawar bak'ar fuskarta.

Juhainah wani irin bacci tayi mai tsayi tunda ta kwanta bata farka ba sai yanzun da take ƙoƙarin tashin, shima wata irin muguwar yinwa take nuƙurƙusarta, har jiwa takeji daga kwancen.
A hankali ta fara buɗe dara-daran fararen idanunta tana wata Irin miƙa da ta zame mata sabo.
Janye quilt ɗin tayi ta miƙe zaune tana hamma.
Saukowa tai daga bed ɗin tana tangaɗi saboda azabar yinwa.
Biscuits da chocolate ta samu cikin drawer ɗin Suhaima, ta ciro guda biyu ta zauna dirshin akan Carpet tana faɗin.
"Wannan magungunan ne suke saka yinwa haka, ai bazan iya sauka ƙasa cin abinci ba idan ba na danna wannan shegiyar yinwar ba da biscuit da chocolate."
Ta faɗa tana ɓare ledar biscuits ɗin ta ciro takai bakinta tana taunawa, a hankali tace"Thank you so much my Babie Suhaima."
Tass ta cinye ledar biscuit ɗin da chocolate ta miƙe.
Daƙyar tayi wanka ta rama salloli ta maida Abayarta ta gyara fuskarta tsaf saboda Hempvana cream ɗin data shafa ya fitar da mata jan marukan da Yah Boss ya mata, laɓɓanta ma sun sace sai kaɗan kumburin sai ɗan fashewar da gefen lips ɗin yayi amma da sauƙi sosai.
Haka ma ƙafarta inda ta faɗi taji zafi yanzu da sauƙi bata ɗingisawan gun ya saki, saboda lafta Hempvana cream tayi sosai a gun.
Anutse ta fito dan sauka taci abinci.
Sai ƙamshi yake lo
[01/01 14:57] null: _*JUHAINAH*_
Love Story💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo

💃🏻Happy New Year💃🏻😂😗

Ya Allah Yadda Muka Ga Sabuwar Shekara Lafiya, Kasa Muga Ƙarshenta Lafiya. Allah Kabamu Lafiya Da Zaman Lafiya A Ƙasashen Mu, Allah Azirtamu Dukiya Mai Albarka.🤲🏼

Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

Suivre la chaîne REAL LADINGO HAUSA NOVEL. sur WhatsApp  : https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

ZEEY BABY.
KAMAL NE.
AUNTY RUMAISA.
DATTIJON ARZIƘI.
TUN RAN GINI.
JIKAR BULAMA.
HALACCIN MAZA 2.
ƘADDARMU AUREN. MIJI ƊAYA.

Akwai Su Complete Ga Mai Buƙata N400.

7067712955 Aisha hafizu Umar opay.

Sai A Turo Min Shaidar Biya Ta Nan. +22796515805

*Page 7*

Fu'adh bai yi mamakin Juhainah ba, saboda yasan zatayi fin hakan, tunda fitsarariya ce, batada mutunci.
Shi abin dariya ma ya basa, yadda ta tsare su tana wani magana cikin iko sai kace ita Sir.

Sai kuma Juhainah Babba da tayi tsuru² kamar tsoron Juhainah ƙarama ya kamata.
Gyaran murya yayi yana kama fuskarshi dan ta fahimci gaskiyar magana, duk da ta san idan ba sanin Sir babu wanda ya isa ya shigo masa gida bare direct ɓangarensa.

"Juhainah! ki kula, Sir ya sakani na kawota baƙuwarsa ce, yace ki kula da ita sauran bayanin bani zaki faɗawa ba, idan yazo sai ki faɗa masa kunfi kusa ai."

Ya ƙarasa mgnar yana maida hankalinsa kan Juhainah babba, a hankali yace.

"Juhainah! Babba ni zan koma sai zuwa dare, Sir idan yazo zai neme ki ko zuwa gobe da safe, duk yadda ya kasance."
Ya ƙarasa maganan yana juyawa ya fara tafiya.
Juhainah tabi bayansa da harara tana murguɗa jajayen lips ɗinta, da har yanzu akwai ɗan kumburin kaɗan, sbd fashewan da gefen bakin yayi.

Juhainah Babba tsaye tana kallon Juhainah ƙarama da take famar harare².
Kallonta tai ta basar ta wuce zuwa kan dining room tana murguɗe² tace.
"Fu'adh! This black woman will not stay in this house.
Yah Boss baya ɗaukan ƴan aiki mata, kuma bazai fara akanta ba ehen."
Fu'adh ba tare da ya juyo ba yana cigaba da tafiya yace.
"Who told you she's a maid? This one is more of a maid in the house, one day you will remember my words."
Juhainah da gudu ta biyosa tana shan gabansa sai huci take.
Dara-daran fararen idanunta ta zuba masa tana wani irin haɗe rai.
Baya ya matsa saboda tayi kusa da shi sosai, tana cikin masifa bata ma san tana kusansa sosai ba.
Cike da fitsara tace.
"The maid's dignity will not be found in this house, one day you will remember my words."
Tana gama faɗa masa haka ta juya tana tafiyar tata ta fitsara karye-karye.
Fu'adh kai ya girgiza baice uffan ba yasa Kai, saboda yasan Sir zaiga duk fitsaran da tayi ta wayansa.
Hakan ya saka shi ƙin biye mata, saboda yasan yana ƙaunar ƙanwarsa, idan ya mata wani abun ɓacin rai zai iya jin zafinsa, koda bai nuna masa ba.
Juhainah ta kalli, Juhainah babba tana mele baki tace.
"Ki saka a ranki wannan gidan babu gurbin zaman aikin ki, Allah har cikin zuciyata baki kwanta min ba, kuma banza taɓa barinki zama gidan yayana ba"
"Tana gama faɗa ta juya ta nufi dining room dan cika cikinta.
Juhainah babba ƙirjinta taji yayi wani irin bugu, sai dai bata ma kalli Juhainah ƙarama ba, saboda ta shiga shock.
Nan ƙasa ta zauna tsinin Carpet ta rakuɓe tana shiga tunani, dan ita gidan ma tsoro yake bata kyawun yayi yawa.
Idanunta suka sauka akan ƙaton picture ɗin iyalin Yah Boss, wanda a take taji ta fita daga cikin shock ɗin da Juhainah ta sakata.Ƙato frame ne aka saka picture ɗin matar da mijin da ya'yan biyu.
Tsira masu ƙananun kyawawan idanunta tayi, tana kallon zallar kyau madarar kyau, soyayya da babu sirki a cikin picture ɗin.
Ɗaya bayan ɗaya Juhainah Babba ta dinga kallon pictures ɗin da suke zagaye da bangon parlon, frame kansu da aka saka hotunan abin kallo ne.
Ji tayi yaran sun shiga ranta matuƙa.
A hankali idanunta akan picture ɗin da yafi shiga ranta tace.
"Ma sha Allah, Ubangiji yayi baiwar kyau anan, daga uban uwar ya'yan Ni daman tun daga Namesake nasan akwai jinin larabawa a gidan, ashe kuwa larabawan ne, Hausa kawai nasan suka koya.
Ko ina suka tafi wuni naji Fu'adh yace sai zuwa dare zasu dawo.
Ya Allah kasa inada rabon aiki a gidan nan, Ya Ubangiji ka duba maraicina kasa su ɗauke Ni aiki, Ya Allah ka ɗora akan Namesake karta saka aƙi ɗaukana.
In sha Allahu Ubangijina ya dubi halin da nake ciki a ɗauke Ni aiki gidan nan, saboda kana kallon su baza su taɓa cutar da kowa ba."
Ta ƙarasa mgnar tana murmushi idanunta akan fuskar Yah Boss yadda ya rungume Khadija lips ɗinsa akan gefen kumcinta, ita kuma tana dariya ta masa kyakkyawar runguma.
Ƴaƴansu ma sun rungume dasu namiji yana dariya macen na wani irin murmushi, ita sak mahaifinta ne, shi kuma namijin mahaifiyarsa ya fito sak...


Khairat agajiye ta dawo daga makaranta yau, wanka tayi taci abinci tana fashin Sallah, hakan ya a saka ta sauko downstairs.
Maah zaune Aunty Sumy tazo ita da ƙaramin ɗanta Sadeeq.
Khairat ta zauna kusan Maah tana faɗin.
"Aunty Sumy ina yini? Yah Sadeeq inasu Twins? Wai Maah ina Juhainah! Na leƙa ɗakinta bata nan?"
Maah tayi murmushi tace.
"Tana gidan Abbah,yau kam tayi rashin Kunyar da horonsa daga nesa ya yi mata kaɗan, sai suna guri ɗaya..."
Labarin duk abinda ya faru ta faɗa masu.
Chapter 12 · 0% Book details