← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 113

Sashe 33

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa Fu'adh da Walid suna tsakiyar cin abinci Zarah ta shigo da sallama tana sunne kai.
Amsawa sukayi, har Yah Boss ba tare da ya kalleta ba.
Fu'adh ya miƙe suka ɗauki abinci yana faɗin.
"Bismillah Mrs Abubakar Bismillah ki iso ki zauna"
Ya ƙarasa maganar bai yarda ya kalli Yah Boss saboda yasan mi zai faru, yasa kai ya nufi ƙofa.
Ai kuwa wani irin kallo da Yah Boss ya yi masa, gwara da bai kalleshi ba.
Ita kuma Zarah harda jin daɗi tana sakin murmushi irin nasu na gogagun ƴan Boko wayayyu.
A nutse ta zauna tana faɗin.
"Yallaɓai barka da rana, ya gajiyar hanya?"
Tissus ya yago yana goge dogon hancinsa saboda Sam ƙamshinta shi bai masa ba, turaren babu class, shi baya son abu mai hawan kai.
Ba tare da ya kalleta ba, har yanzu tissus ɗin yake gogawa a hancinsa kamar mai mura, a hankali cikin kamewarsa ya furta.

"Barka"
Dan Zarah har ta cire ran zai amsa mata.
Murmushi tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai cike da kwarjini, a hankali tace.
"Ya yara?"

Yanzu ma sai da ya bushi isa kafin ya amsa da.
"Lafiyarsu lau.
ke yanzu har kin manta mutuwar mijin naki kin wuce babinsa aure kike so ki fara sabuwar rayuwa da wani mijin kenan?"

Da mamaki Zarah ta zuba masa idanunta.
Kallonta yayi na seconds 5 ya kauda kansa ya furta.

"Yes answer"

Zarah ta gyara zamanta tace.
"Toh ya zanyi zan yi fushi da ikon Allah ne? Da nima haka na ƙudirta araina bazan sake aure ba, saboda babu irin kalar mijin da ban samuba amma naƙi..."

Saurin katseta yayi ya furta.
"Toh me yasa yanzu kike son yin auren kai tsaye, kinada wani burine akan auren yanzu alright?"

Zarah tace.
"Eh tabbas burina na alkhairi ne akanka, tunda aka nuna min picture ɗinka naji ina tsananin ƙaunarka, zan aureka da zuciya ɗaya na zauna da ƴaƴanka da zuciya ɗaya, na kula da kai na dawo maka da farin cikin da ka rasa..."

"No! I'm possible bazaki iya ba, ko kusanta bazaki iya zuwaba, because ina sonta sosai ita ɗaya kuma ta tafi da soyayyar, don haka idan kin nace zaki aureni No problem.
Amma ki sani banida lokacin baki kulawa saboda banida lokacin soyayya, zuciyata a rufe take.
Don haka kar kiyi abinda zaki dawo kina nadama, ko kiga na shiga haƙƙin ki, ko tauye maki haƙƙi, kiyi shawara da da kyau idan kinga zaki amince banida alhakin ki, Mama mahaifiyace gareni gaba take da mahaifina ma ba Ni ba, su kansu idan ta ajiye kara basa tsallake wa bare Ni, ta tirsasani aurenki ban isa gujewa hakan ba, amma kiji sharuɗɗana saboda bana son cutar da kowani rai.

Idan kinji kin gani good idan kuma kina buƙatar auren soyayya da samun kulawa Please kije kice mata Wlh ban miki ba da kika ganni pace to face, dan Wlh Suhaima ma bazata saurara miki ba, kishin mahaifiyarta take sosai, sannan akwai ƙanwata Juhainah abu ɗaya suke so da Suhaima, bazaki ji daɗi a gunsu ba, kuma bazan damesu akanki ba. Bayan haka nima bana ra'ayinki, Banida lokacin baki lokaci ba, ki guji wannan auren na faɗa maki gaskiya.
Kiyi shawara Please."

Ya ƙarasa maganar yana ɗaukan bottle ɗin ruwa yakai lips ɗinsa masu sheƙi.

Zarah acikin zuciyarta take faɗin.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil"

Amma a zahiri tace.
"Allah Sarki! Duka rayuwar nawa take, zama guri ɗaya na canza komai, Allah ya sani ina sonka zan juri duk wata huƙuba a gidanka, har Ubangiji ya canza al'amarin sa."
Ba tare da ya kalleta ba cikin nutsuwarsa muryansa cike kamewa ya furta.
"Alright na fita haƙƙin ki, zaki iya faɗa min nawa kike buƙata sadakin naki, da kuma ranan da kike son a daura auren, tarewa kuma duk lokacin da kike so Banida Matsala tunda babu anfanin da zaki min à gidan."

Zarah tayi murmushi tana kallonsa tace.
"Naira miliyan ɗaya, ɗaurin auren rana ya ta yau har tarewan sati ya isa na gyara jikina"
Kafaɗa ya maƙale ya furta.
"Ok amma ki sani ba sai kinzo da komai ba, akwai komai, bana son tarkace a gidana, bani account number na tura kuɗin da zaki siyi sabbin sutturo, Please ki canza wannan turaren da kike anfani da shi, zai takurawa mana Nida ƴaƴana"

Zarah tayi murmushi tana faɗin.
"A'a ka barsa zan siya aiki nake fa inada rufin asiri, sadakin ya isheni kai nake so ba kuɗin ka ba"
A hankali ya furta

"Ok zaki iya tafiya, tunda kin zaɓi baƙin ciki akan farin ciki."

Miƙewa tayi tana marairaice fuska ta beƙa masa wayanta tace.
"Number please"
Tsaki yaja yana amsar wayan ya saka mata number business ɗinsa, ba asalin special number sa ba.
Godiya tayi tana faɗin.
"Ai zaka barni naci gaba da zuwa wajan aikina na lawyer ko? Zaka temaka juyen gun aikin bazai bani ciwon kai ba, tunda mijina commissioner of police ne."

Ko kallonta bai ba, baice uffan ba.
Ƴar dariya tayi tana ficewa cike da taku mai burgewa, mazauna nan ma sha Allahu sai motsawa suke Allah ya bata su kima².
Tsaki yaja yana ɗaukan Phone ɗinsa.
Fu'adh ya kira yana ɗauka cikin kamewarsa ya furta.
"Kayi mana booking tickets yanzu Please mubar garin nan"
Ya ƙarasa maganar yana katse kiran.



Yola

80 Unit
Sai ƙarfe 11 Am.
Juhainah ta farka daga bacci tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa blue tayi kyau sosai ta murza ɗaurin ture kaga tsiya tana ƙamshinta mai sanyaya zuciya, ta sauko parlour.
Suhaima tana hangota ta miƙe ta kamo hannunta tana faɗin.
"Aunty J sai yanzu kika tashi? My Dadd yayi tafiya Jigawa da safe"
Juhainah ta sumbaci hannun Suhaima tana faɗin.
"Eh wlh My Babies tun jiya da nasha maganin ciwon kai na Yah Boss nake ta bacci, yanzu ma yunwa ta tada Ni, bari nayi breakfast, Wayyo inda ma an tafi dani gun hajiya Mamana."
Ta ƙarasa maganar tana kallon Khairat da take waya alamar Aunty Sumy ce.
Al'amin yace.
"Aunty J ina kwana kinata bacci Dadd yace kar a tashe ki, yanzu kije kici abinci toh kizo muyi Game"
Shamsiddin da Shuraim suma suka gaisheta suna faɗin.
"Aunty J kije kici abinci kizo muyi Game"
Juhainah ta ware hannayenta tana faɗin.
"Muahhhhh i love you My Babies, Ok bari nazo. Aunty Khairat ki gaishe min Aunty Sumy kice nace i love you"
Ta ƙarasa maganar tana nufar hanyar kitchen.
Khairat tace.
"Aunty Sumy kina jinta ko?"
Aunty Sumy tace.
"Hummm! Najita Juhainah manya, Allah ya nuna mana tayi hankali ta nutsu..."

Bayan sun gama waya Khairat ta miƙe ta nufi Stairs.
Bedroom ɗin Yah Boss taje ta ɗauko bottle inda ya faɗa mata, wani blue kala ne, mai kyau yanada ɗan girma.

Juhainah bata wasa da cikinta sai da ta sha tea sosai wanda yaji Madara, tana shanyewa ta zuba farfesun kayan Ciki ba kaɗan ba, kamar ba mutum ɗaya zaici ba, ta zuba wainar shinkafa guda biyar ta fara lodawa cikinta, gefe ga Chips ta ajiye tana jiran ta cinye wannan.
A haka Khairat ta sameta ta ajiye bottle ɗin tana faɗin.
"Ke! Juhainah! Bakida hankali ne ke ɗaya zakici duka wannan abincin? Kayan cikine fa, bakya tsoron kiyi zawo, ko cikinki yayi ciwo?"

Dara-daran kyawawan idanunta ta zaro mata tana tura spoon ɗin da ta ciko da farfesun da romo bakinta, saida ta tauna ta haɗiye tace.
"Ina ruwanki ai cikina ne, ya kasheni ma, kawai kin tsaneni abincin ma bakya son kiga inaci, ko Yah Boss zai hanani cin abinda naga dama bare ke"

Khairat tace.
"Fitsarariya a bayan idanunsa ko, ke kika sani kici ɗin, amma Wlh kika kuskura kika tasheni ina bacci cikin dare ko kallon ki bazan ba"

Ta ƙarasa maganar tana jan kujera ta zauna tana jiran ta gama ta bata ruwan addu'an.
Juhainah ta ƙara turo ɗaurin ɗan kwalinta, taci gaba da lodawa cikinta farfesun da waina, sai da ta cinye wanda ta zuba tass, taci Chips kaɗan sbd ta ƙoshi sosai tayi gyatsa tana miƙewa tare da faɗin.
"Alhamdoulillah!"
Khairat ta bita da kallo tana faɗin.
"Sai masifar ci ba'a gani ajikinki sai bushewa ma da kike ƙarayi"

Juhainah ta ƙyalƙyale da dariya tana riƙe ƙugunta tace.
"Ku kuka damu da ƙiba Wlh na tsaneta ban sonta, a haka dai maza suke rububina ina korasu,dan haka abarni naci nayi Haniƙan."
Khairat ta miƙe tana faɗin.
"Amsa zauna kiyi Bismillah ki sha, yaya Sadeeq yace na baki idan kinyi breakfast, idan baki sha ba yace na kirasa yanzu"

Juhainah baki ta mele tana amsar bottle ɗin ta koma ta zauna tana faɗin.
"Ni duka zan sha ko kaɗan?"
Khairat tace.
"Rabi zuwa dare idan zaki kwanta bacci zan baki rabin"
Juhainah ta turo baki gaba tana Bismillah ta kafa bakinta tasha sosai har rabin saboda ruwan koma na miye ya mata daɗi sosai.
Ba Khairat bottle ɗin tayi tana miƙewa.
Khairat ta amsa ta rufe tana tafiya dan adanasa kafin daren.

Juhainah ko da ta shiga tsakiyar ƴaƴanta ta zauna tana faɗin.
"Toh my Babies nazo kuzo a fara wasan..."
Dukansu sukayi ihu banda Suhaima, ta dai rungumota tana faɗin.
"Aunty J dani za'a fara yi"
Juhainah tace.
"Tom mu fara Babies, daga ke sai My Amiin sai my Twins"
Ihu saka sake yi suna gyara zamansu....

Ana sallar la'asar Yah Boss sukayi sallama da hajjah Bilkisu wacce take cikin farin cikin auren da Yah Boss ya amince, hakan ma ya saka bata hanasa tafiya ba.

Suna shigowa Yola bayan sunbar airport kai tsaye ya bada umarnin Walid ya kaisa guest house ɗinsa ya huta kansa kamar zai tsage, ko Fu'adh ya tsorata da ganin yanayin Yah Boss yau.
Kai tsaye guesthouse ɗin Walid ya nufa, wanda yake a (Shagari Phase )

Gidane madaidaici tsararren gaske na hutawa, babu abinda babu najin daɗi.
Suna isa kai tsaye shiga ya tube ya sakarwa kansa shower mai sanyi Saboda yadda yake jin jikinsa ya ɗauki ɗumi sosai.
Chapter 33 · 0% Book details